Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Su waye ne Masu Taimakon Mutane da Yesu ya ambata a daren da ya mutu, kuma me ya sa aka ba su wannan laƙabin?

A daren ƙarshe kafin Yesu ya mutu, ya umurci manzanninsa cewa kada su zama masu neman matsayi. Ya ce: “Sarakunan mutanen da ba su san Allah ba sukan nuna wa mutanensu iko, kuma shugabanninsu sukan ce da kansu ‘masu taimakon mutane.’ Amma kada ya zama haka a tsakaninku.”​—Luk. 22:​25, 26.

Su waye ne Masu Taimakon Mutane da Yesu ya ambata? Abubuwa kamar su rubuce-rubuce da tsabar kuɗi sun nuna cewa Girkawa da Romawa suna so a riƙa ɗaukaka maza da kuma sarakuna da laƙabin nan Euergetes, wato Masu Taimakon Mutane. Ana ba su wannan laƙabin ne domin sun yi wasu ayyuka don su taimaka wa jama’a.

Ana kiran sarakuna da yawa da wannan laƙabin. Har da sarakunan Masar da aka san su da sunayen nan Ptolemy Euergetes na 3 (a misalin shekara ta 247-222 kafin haihuwar Yesu) da Ptolemy na 8 Euergetes na 2 (a misalin shekara ta 147-117 kafin haihuwar Yesu). Ƙari ga haka, ana kiran sarakunan Roma masu suna Julius Caesar (48-44 kafin haihuwar Yesu) da Augustus (31 kafin haihuwar Yesu–14 bayan haihuwar Yesu) har ma da Hiridus Mai Girma sarkin Yahudiya da wannan laƙabin. Wataƙila an soma kiran Hiridus da wannan laƙabin ne domin ya shigo da alkama ƙasarsu a lokacin da ake ƙarancin abinci kuma ya raba wa mabukata sutura.

Wani masanin Littafi Mai Tsarki ɗan Jamus mai suna Adolf Deissmann ya bayyana cewa a dā, ana yin amfani da laƙabin nan Masu Taimakon Mutane sosai. Ya ce: ‘Wuraren da aka rubuta laƙabin nan a dā na da yawa sosai. Idan mutum yana neman wurin da aka rubuta laƙabin, yana da sauƙin samu.’

To me Yesu yake nufi sa’ad da ya gaya wa mabiyansa cewa: “Amma kada ya zama haka a tsakaninku”? Yesu yana nufin cewa kada mabiyansa su riƙa taimaka wa mutane ne? A’a. Abin da Yesu yake mai da wa hankali shi ne dalilin da ya sa mutanen suka taimaka wa wasu.

A zamanin Yesu, masu arziki suna so a san da su. Saboda haka, suna ɗaukan nauyin wasannin da ake yi, suna gina wuraren shaƙatawa da haikalai da kuma makamantansu. Amma suna yin hakan ne don mutane su riƙa yaba musu ko don su shahara ko kuma don mutane su jefa musu ƙuri’a. A wani littafin tarihi, an rubuta cewa: “Ko da yake waɗannan mutanen sun kafa misalai masu kyau na nuna alheri, sukan yi hakan ne don son kai.” Irin wannan halin ne Yesu ya umurci mabiyansa su guje wa.

Bayan wasu shekaru, manzo Bulus ya nanata dalilin da ya sa muke bukatar mu kasance da manufa mai kyau yayin da muke ba da kyauta. Ya rubuta wa Kiristocin da ke Korinti cewa: “Kowa ya bayar kamar yadda ya yi niyya, ba tare da ɓacin rai ko tilas ba, domin Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.”​—2 Kor. 9:7.