Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 47

Darussan da Za Mu Iya Koya Daga Littafin Firistoci

Darussan da Za Mu Iya Koya Daga Littafin Firistoci

“Duk Rubutacciyar Maganar Allah hurarre ce daga wurinsa, tana kuma da amfani.”​—2 TIM. 3:16.

WAƘA TA 98 Nassosi Hurarre Ne Daga Allah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Me ya sa ya kamata Kiristoci su so yin nazarin littafin Firistoci?

MANZO Bulus ya tunasar da abokinsa Timoti cewa “duk Rubutacciyar Maganar Allah hurarre ce daga wurinsa, tana kuma da amfani.” (2 Tim. 3:16) Wannan ya ƙunshi littafin Firistoci. Mene ne ra’ayinka game da wannan littafin? Wasu suna ganin cewa littafin yana ɗauke ne da dokokin da ba za su amfane mu a yau ba, amma Kiristoci na gaske ba su da irin ra’ayin nan.

2 An rubuta littafin Firistoci wajen shekaru 3,500 da suka shige, duk da haka Jehobah ya adana ta “domin a koyar da mu.” (Rom. 15:4) Littafin Firistoci yana taimaka mana mu fahimci ra’ayin Jehobah. Don haka, ya kamata mu yi marmarin koya darussa daga littafin. Da akwai darussa da yawa da za mu iya koya daga littafin Firistoci. Bari mu tattauna huɗu daga cikinsu.

YADDA ZA MU FARANTA RAN JEHOBAH

3. Me ya sa ake miƙa hadaya kowace shekara a Ranar Kafara?

3 Darasi na farko: Muna bukatar mu faranta ran Jehobah don ya amince da hadayarmu. A kowace shekara a Ranar Kafara, Isra’ilawa suna yin taro kuma suna kawo dabbobi domin su yi hadaya. Yin hakan yana tuna musu cewa suna bukatar a tsabtace su daga zunubi! Amma kafin babban firist ya shiga Wuri Mafi Tsarki da jinin hadaya a ranar, yana bukatar ya yi wani abu da yake da muhimmanci fiye da a gafarta zunuban Isra’ilawa.

(Ka duba sakin layi na 4) *

4. Kamar yadda Littafin Firistoci 16:​12, 13 suka nuna, mene ne babban firist yake yi a lokaci na farko da ya shiga Wuri Mafi Tsarki a Ranar Kafara? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

4 Karanta Littafin Firistoci 16:​12, 13. Ka yi tunanin abin da ke faruwa a Ranar Kafara: Babban firist ya shiga Wuri Mafi Tsarki kuma wannan ne karo na farko a ranar. Zai bukaci ya shiga wurin sau uku. A hannu ɗaya, yana riƙe da turare mai ƙamshi, a ɗayan hannun kuma yana riƙe da kaskon zinariya cike da garwashi. Ya ɗan dakata a gaban labulen Wuri Mafi Tsarki. Cike da girmamawa, ya shiga Wuri Mafi Tsarki kuma ya tsaya a gaban akwatin alkawari. A alamance, yana tsaye a gaban Jehobah! Sai a hankali firist ɗin ya zuba turare a garwashin kuma ɗakin ya cika da ƙamshin turare. * Bayan haka, zai sake shiga Wuri Mafi Tsarki da jinin dabbobin da aka miƙa don neman gafara. Ka lura cewa ya ƙona turare kafin ya miƙa jinin dabbobin.

5. Mene ne za mu iya koya daga turaren da ake ƙonawa a Ranar Kafara?

5 Mene ne za mu iya koya daga yadda ake ƙona turare a Ranar Kafara? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa addu’o’in bayin Jehobah masu aminci suna kamar turare mai ƙamshi. (Zab. 141:2; R. Yar. 5:8) Ka tuna cewa babban firist ɗin ya girmama Jehobah sosai kafin ya kawo turaren gabansa. Hakazalika, muna bukatar mu daraja Jehobah sosai sa’ad muke addu’a. Muna godiya sosai domin Mahaliccin sama da duniya ya ba mu damar yin addu’a. Ƙari ga haka, za mu iya kusantar sa kamar yadda yaro ke kusantar mahaifinsa. (Yaƙ. 4:8) Jehobah ya amince mu zama abokansa! (Zab. 25:14) Muna daraja gatar nan sosai kuma ba za mu so yin abin da zai ɓata masa rai ba.

6. Mene ne za mu iya koya daga yadda babban firist yake ƙona turare kafin ya miƙa hadayu?

6 Ka tuna cewa babban firist yana ƙona turare kafin ya miƙa hadaya. Ta yin hakan, yana tabbatar da cewa Jehobah zai amince da hadayar da zai yi. Mene ne za mu iya koya daga hakan? A lokacin da Yesu yake duniya, ya yi wani abin da ke da muhimmanci fiye da ceton ’yan Adam. Wane abu ke nan? Ya riƙe aminci kuma ya yi biyayya ga Jehobah domin Jehobah ya amince da hadayar da zai yi. Ta yin hakan, Yesu ya nuna sarai cewa ra’ayin Jehobah ne ya fi dacewa. Ƙari ga haka, Yesu ya nuna cewa sarautar Jehobah ce ta fi kyau.

7. Me ya sa yadda Yesu ya yi rayuwa a duniya ya faranta ran Jehobah?

7 Sa’ad da Yesu yake duniya, ya yi biyayya ga Jehobah sosai. Yesu ya fuskanci jarrabawa da wahala kuma ya san cewa za a azabtar da shi kafin ya mutu. Duk da haka, ya ƙuduri niyyar nuna cewa sarautar Jehobah ce ta fi dacewa. (Filib. 2:8) Sa’ad da Yesu ya fuskanci mawuyanci yanayi, ya yi addu’a da “roƙe-roƙe tare da kuka mai tsanani da hawaye.” (Ibran. 5:7) Addu’o’in da Yesu ya yi da dukan zuciyarsa sun nuna cewa yana da aminci ga Jehobah kuma ya ƙuduri niyyar yin biyayya. Ga Jehobah, addu’o’in suna kamar ƙamshin turare mai daɗi. Yadda Yesu ya yi rayuwa sa’ad da yake duniya ya faranta ran Jehobah kuma ya ɗaukaka sarautarsa.

8. Ta yaya za mu yi koyi da yadda Yesu ya yi rayuwa a duniya?

8 Muna iya yin koyi da Yesu ta wajen ƙoƙarin yin biyayya ga Jehobah da kuma riƙe aminci. Sa’ad da muka fuskanci jarrabawa, muna addu’a sosai ga Jehobah domin muna so mu faranta masa rai. Ta yin hakan, muna nuna cewa muna goyon bayan sarautar Jehobah. Mun san cewa Jehobah ba zai amsa addu’o’inmu ba idan muna saka hannu a abubuwan da ya tsana. Amma idan muna yin rayuwar da ta jitu da ƙa’idodinsa, za mu kasance da tabbaci cewa addu’o’in da muke yi da dukan zuciyarmu suna kamar ƙamshin turare mai daɗi ga Jehobah. Ƙari ga haka, mu kasance da tabbaci cewa amincinmu da kuma biyayya da muke yi yana faranta ran Ubanmu na sama.​—K. Mag. 27:11.

MUNA BAUTA MASA DON MUNA GODIYA KUMA MUNA ƘAUNAR SA

(Ka duba sakin layi na 9) *

9. Me ya sa ake yin hadaya ta salama?

9 Darasi na biyu: Muna bauta wa Jehobah domin muna yi masa godiya. Za mu koyi wannan darasin yayin da muke tattauna hadaya ta salama da Isra’ilawa suke yi. * A Littafin Firistoci, mun koyi cewa Ba’isra’ile zai iya miƙa hadaya “saboda godiya.” (L. Fir. 7:​11-13, 16-18) Zai yi hadayar ne da son ransa ba don an tilasta masa ba. Mutumin da ya yi wannan hadaya ya yi ta ne don yana ƙaunar Jehobah ba don an tilasta masa ba. Mutumin da iyalinsa da kuma firistocin za su ci namar dabbar da aka yi hadayar da ita. Amma akwai wasu sashen jikin dabbar da ba a yarda su ci ba domin na Jehobah ne. Wane sashe ke nan?

(Ka duba sakin layi na 10) *

10. Mene ne hadaya ta salama da aka bayyana a Littafin Firistoci 3:​6, 12 da 14-16 suka koya mana game da yadda Yesu ya yi nufin Ubansa?

10 Darasi na uku: Muna ba Jehobah abin da muka fi so domin muna ƙaunar sa. A wurin Jehobah, kitsen dabba shi ne sashen da ya fi kyau. Ƙari ga haka, ya ce wasu sashen dabbar har da ƙodarta suna da daraja sosai. (Karanta Littafin Firistoci 3:​6, 12, 14-16.) Saboda haka, Jehobah yana farin ciki sosai sa’ad da Ba’isra’ile ya yi hadaya da waɗannan sassan har da kitsen dabbar. Ba’isra’ilen da ya yi irin wannan hadayar yana nuna cewa yana son ya ba Allah abu mafi kyau. Hakazalika, Yesu ya yi iya ƙoƙarinsa don ya bauta wa Jehobah da dukan zuciyarsa. (Yoh. 14:31) Yin nufin Allah ya faranta wa Yesu rai kuma yana son dokokin Allah sosai. (Zab. 40:8) Babu shakka, Jehobah ya yi farin ciki sa’ad da ya ga Yesu yana bauta masa da son rai!

Muna yi wa Jehobah hidima da dukan zuciyarmu domin muna ƙaunar sa (Ka duba sakin layi na 9-12) *

11. Ta yaya hidimarmu take kama da hadaya ta salama, kuma ta yaya hakan zai ƙarfafa mu?

11 Kamar wannan hadaya ta salama, muna hidima ga Jehobah da son rai don mu nuna godiyarmu. Muna yin hakan da dukan zuciyarmu domin muna ƙaunar sa. Jehobah yana farin ciki sosai sa’ad da ya ga miliyoyin mutane suna bauta masa domin suna ƙauna sa kuma suna son dokokinsa! Jehobah yana daraja hidimar da muke yi masa da kuma dalilin da ya muke yin hakan. Hakan yana ƙarfafa mu sosai. Alal misali, idan ka tsufa kuma ba za ka iya yin abubuwan da ke yi a dā ba, ka kasance da tabbaci cewa Jehobah ya fahimci yanayinka. Ko kuma ƙila kana ganin ba za ka iya yin abubuwa da yawa a hidimar Jehobah ba, ka tabbata cewa ya san kana ƙaunar sa kuma kana son ka yi iya ƙoƙarinka. Yana farin cikin amincewa da hidimar da ka yi gwargwadon ƙarfinka.

12. Wane tabbaci ne za mu iya kasancewa da shi don yadda Jehobah yake ɗaukan hadaya ta salama?

12 Mene ne za mu iya koya daga hadaya ta salama? Yayin da wuta take ƙona naman, hayaki yana tashi sama kuma hakan yana sa Jehobah farin ciki. Don haka, ka kasance da tabbaci cewa Jehobah yana farin ciki sosai don hidimar da kake yi. (Kol. 3:23) Ka yi tunanin yadda Jehobah yake alfahari da kai. Ko da kana cim ma abubuwa da yawa a hidimar Jehobah ko a’a, ka kasance da tabbaci cewa yana daraja hidimarka kuma zai riƙa tunawa da abin da ka yi har abada.​—Mat. 6:20; Ibran. 6:10.

JEHOBAH YANA YI WA ƘUNGIYARSA ALBARKA

13. Kamar yadda Littafin Firistoci 9:​23, 24 suka nuna, ta yaya Jehobah ya nuna cewa ya amince da firistocin da aka naɗa?

13 Darasi na huɗu: Jehobah yana yi wa sashen ƙungiyarsa da ke duniya albarka. Ka yi la’akari da abin da ya faru a shekara ta 1512 kafin haihuwar Yesu, sa’ad da aka kafa mazauni a ƙarƙashin Dutsen Sinai. (Fit. 40:17) Musa ya ja-goranci taron da aka yi don a naɗa Haruna da yaransa a matsayin firistoci. Isra’ilawa sun taru don su shaida lokacin da firist ɗin yake miƙa hadayarsu ta farko. (L. Fir. 9:​1-5) Ta yaya Jehobah ya nuna cewa ya amince da firistocin da aka naɗa? Yayin da Haruna da Musa suke yi wa mutanen albarka, Jehobah ya turo wuta daga sama ya ƙona hadayar da ke kan bagadin.​—Karanta Littafin Firistoci 9:​23, 24.

14. Me ya sa yadda Jehobah ya nuna ya amince da firistocin yake da muhimmanci a yau?

14 Mene ne wuta da ta sauko daga sama ta nuna? Jehobah ya tura wutar ne don ya nuna cewa ya amince da Haruna da yaransa kuma zai goyi bayansu. Sa’ad da Isra’ilawa suka ga cewa Jehobah ya amince da firistocin, sun fahimci cewa su ma suna bukatar su goyi bayansu. Me ya sa yadda Jehobah ya nuna ya amince da firistocin yake da muhimmanci a yau? Domin firistocin suna wakiltar Yesu babban firist da kuma shafaffu 144,000 da za su yi hidima a matsayin firistoci da kuma sarakuna tare da Yesu a sama.​—Ibran. 4:14; 8:​3-5; 10:1.

Jehobah yana yi wa ƙungiyarsa ja-goranci da kuma albarka. Muna goyon bayan ƙungiyar Jehobah (Ka duba sakin layi na 15-17) *

15-16. Ta yaya Jehobah ya nuna ya amince da “bawan nan mai aminci mai hikima”?

15 A shekara ta 1919, Yesu ya naɗa ƙaramin rukunin shafaffu a matsayin “bawan nan mai aminci, mai hikima.” Wannan bawan yana yin ja-goranci a wa’azi kuma yana ba mabiyan Yesu “abincinsu a kan lokaci.” (Mat. 24:45) Hakika, wannan ya nuna mana cewa Jehobah ya amince da bawan nan mai aminci mai hikima!

16 Shaiɗan da mutanensa suna ƙoƙari sosai don su hana bawan nan yin aikinsa. Da a ce Jehobah ba ya taimaka wa bawan, da ba zai iya yin aikinsa ba. Duk da yaƙin duniya da aka yi sau biyu da rugurgujewar tattalin arziki da kuma tsanantawa, bawan nan mai aminci mai hikima yana ci gaba da yi wa mabiyan Kristi a duniya tanadin abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarsu da Allah. Ka yi tunanin yawan littattafai da bidiyoyi da muke samu kyauta a yau a yaruka fiye da 900! Wannan ya tabbatar mana da cewa Jehobah yana goyon bayan mutanensa sosai. Wa’azin da muke yi ma ya tabbatar mana da hakan. Muna yin wa’azi ga ‘dukan al’umma’ a duniya. (Mat. 24:14) Babu shakka, Jehobah yana yi wa ƙungiyarsa ja-goranci a yau kuma yana yi mata albarka.

17. Ta yaya za mu nuna cewa muna goyon bayan ƙungiyar Jehobah?

17 Muna bukatar mu tambayi kanmu, ‘Ina nuna godiya kuwa domin ina tarayya da sashen ƙungiyar Jehobah da ke duniya?’ A zamanin Musa, Jehobah ya aiko wuta daga sama don ya nuna cewa ya amince da waɗanda aka naɗa. Hakazalika a yau, Jehobah yana ba mu abubuwan da za su tabbatar mana da cewa yana goyon bayan ƙungiyarsa. Muna da abubuwa da yawa da za mu nuna godiya dominsu. (1 Tas. 5:​18, 19) Ta yaya za mu nuna cewa muna goyon bayan ƙungiyar Jehobah? Ta wajen yin amfani da abubuwan da muke koya a Kalmarsa da littattafanmu da taron ikilisiya da na da’ira da kuma na yanki. Ƙari ga haka, muna iya nuna goyon baya ta wajen yin iya ƙoƙarinmu a wa’azi da kuma koyarwa.​—1 Kor. 15:58.

18. Mene ne ka ƙuduri niyyar yi?

18 Bari mu ƙuduri niyyar yin amfani da darussan da muka koya daga littafin Firistoci. Muna so Jehobah ya amince da hadaya da muke yi. Muna so mu ci gaba da bauta wa Jehobah domin muna yi masa godiya. Mu ci gaba da yi wa Jehobah hidima da dukan zuciyarmu domin muna ƙaunar sa. Kuma mu yi iya ƙoƙarinmu don mu goyi bayan ƙungiyarsa. Ta yin hakan, za mu nuna wa Jehobah cewa muna daraja gatan da ya ba mu na zama Shaidunsa!

WAƘA TA 96 Kalmar Allah Tana da Daraja

^ sakin layi na 5 Littafin Firistoci yana ɗauke da dokokin da Jehobah ya ba Isra’ilawa a zamanin dā. A matsayinmu na Kiristoci, ba ma bin waɗannan dokokin a yau, amma ta yaya za mu iya amfana daga dokokin. A wannan talifin, za mu tattauna darussan da za mu iya koya daga littafin Firistoci.

^ sakin layi na 4 Turaren da ake ƙonawa a mazaunin yana da tsarki sosai, kuma a zamanin, Isra’ilawa suna yin amfani da turaren a bautarsu ga Jehobah kaɗai. (Fit. 30:​34-38) Babu wata alama cewa Kiristoci a ƙarni na farko sun ƙona turare a ibadarsu.

^ sakin layi na 9 Don samun ƙarin bayani game da hadaya ta salama, ka duba littafin nan Insight on the Scriptures, Littafi na 2, shafi na 526 da kuma Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Janairu, 2012, shafi na 19, sakin layi na 11.

^ sakin layi na 54 BAYANI A KAN HOTO: A Ranar Kafara, babban firist na Isra’ila ya shiga Wuri Mafi Tsarki da turare da kuma garwashi don ya cika ɗakin da ƙamshi. Daga baya, ya sake shiga wurin da jinin dabbar hadaya.

^ sakin layi na 56 BAYANI A KAN HOTO: Wani Ba’isra’ile ya kawo ragon hadaya ta salama domin shi da iyalinsa suna godiya ga Jehobah.

^ sakin layi na 58 BAYANI A KAN HOTO: A lokacin da Yesu yake duniya, ya nuna cewa yana ƙaunar Jehobah ta wajen bin dokokinsa da kuma taimaka wa mabiyansa ma su yi hakan.

^ sakin layi na 60 BAYANI A KAN HOTO: Duk da cewa wata ’yar’uwa tsohuwa ba za ta iya yin abubuwa da yawa ba, tana yin wa’azi ta rubuta wasiƙa.

^ sakin layi na 62 BAYANI A KAN HOTO: A watan Fabrairu 2019, Ɗan’uwa Gerrit Lösch memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ya fitar da sabon juyin New World Translation a Jamusanci. A yau, masu shela a Jamus suna farin cikin yin amfani da wannan Littafi Mai Tsarki a wa’azi kamar yadda waɗannan ’yan’uwa mata biyu suke yi.