TALIFIN NAZARI NA 48
“Ku Gama Abin da Kuka Fara”
“Ku gama aikin da irin zuciyar da kuka fara.”—2 KOR. 8:11.
WAƘA TA 35 Mu Riƙa Yin “Abin da Ya Fi Kyau”
ABIN DA ZA A TATTAUNA *
1. Mene ne Jehobah yake bari mu yi?
JEHOBAH yana barin mu zaɓi abin da za mu yi a rayuwa. Yana koya mana yadda za mu yanke shawara mai kyau kuma idan shawarar za ta faranta masa rai, yana taimaka mana mu yi nasara. (Zab. 119:173) Saboda haka, idan muka bi shawarwarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki, za mu yanke shawara mai kyau.—Ibran. 5:14.
2. Wane ƙalubale ne za mu iya fuskanta bayan mun yanke shawara?
2 Ko da mun yanke shawara mai kyau, muna iya yin fama don mu gama abin da muka fara. Ka yi la’akari da wasu misalai: Na ɗaya, wani ɗan’uwa matashi ya yanke shawarar karance Littafi Mai Tsarki. Ya yi ʼyan watanni yana karatun, amma sai ya daina. Na biyu, wata ʼyar’uwa ta yanke shawarar yin hidimar majagaba, amma tana yin shiririta a kan kwanan watan da za ta soma. Na uku, dattawa a wata ikilisiya sun yanke shawara cewa za su ƙara ƙwazo a yin ziyarar ƙarfafawa. Amma watanni da yawa sun wuce, kuma ba su aiwatar da shawararsu ba. Waɗannan misalan sun bambanta, amma akwai abu guda da ya sa suke da alaƙa da juna. Ba su gama ɗaukan mataki a kan shawarar da suka yanke ba. A ƙarni na farko, Kiristoci a Korinti ma sun fuskanci irin ƙalubalen nan. Ku lura da darussan da za mu iya koya daga misalinsu.
3. Wace shawara ce Korintiyawa suka yanke, kuma me ya faru?
3 A kusan shekara ta 55 bayan haihuwar Yesu, Kiristoci a Korinti sun yanke shawara mai muhimmanci. Sun sami labari cewa ʼyan’uwansu a Urushalima da Yahudiya suna fama da talauci da kuma mawuyacin yanayi, kuma wasu ikilisiyoyi suna tara kuɗin da za su tura musu. Saboda kirkin ʼyan’uwan nan da kuma alherinsu, sun yanke shawarar yin gudummawa don su taimaka musu kuma sun tambayi manzo Bulus 1 Kor. 16:1; 2 Kor. 8:6) Amma bayan ʼyan watanni, Bulus ya sami labari cewa Korintiyawa ba su yi gudummawar da suka ce za su yi ba. A sakamakon haka, zai yi wuya su iya tara gudummawarsu da wuri don a haɗa da na sauran ikilisiyoyi kuma a kai Urushalima.—2 Kor. 9:4, 5.
yadda za su yi hakan. Sai Bulus ya tura wa ikilisiyar wasiƙa kuma ya zaɓi Titus ya taimaka wajen karɓan gudummawar. (4. Kamar yadda 2 Korintiyawa 8:7, 10, 11 suka nuna, wace shawara ce Bulus ya ba Korintiyawa?
4 Babu shakka, ʼyan’uwa a Korinti sun yanke shawara mai kyau, kuma Bulus ya yaba musu don bangaskiyarsu da kuma karimcinsu. Amma ya ƙarfafa su cewa su gama abin da suka fara. (Karanta 2 Korintiyawa 8:7, 10, 11.) Labarinsu ya koya mana cewa zai iya yi wa amintattun Kiristoci ma wuya su aiwatar da shawarar da suka yanke.
5. Waɗanne tambayoyi ne za mu amsa?
5 Kamar ʼyan’uwan nan a Korinti, zai iya yi mana wuya mu aiwatar da shawarar da muka yanke. Me ya sa? Domin ajizancinmu zai iya sa mu yi shiririta. Ko kuma tsautsayi yana iya hana mu aiwatar da shawarar da muka yanke. (M. Wa. 9:11; Rom. 7:18) Me ya wajaba mu yi idan mun lura cewa muna bukatar mu canja shawarar da muka yanke? Kuma ta yaya za mu iya yin nasara wajen gama abin da muka soma?
KAFIN KU YANKE SHAWARA
6. A wane lokaci ne za mu bukaci canja shawarar da muka yanke?
6 Akwai wasu shawarwarin da ba za mu taɓa canjawa ba. Alal misali, ba za mu canja shawarar da muka yanke cewa za mu bauta wa Jehobah ba, kuma ba za mu ci amanar mijinmu ko matarmu ba. (Mat. 16:24; 19:6) Amma akwai wasu shawarwarin da za mu bukaci mu canja. Me ya sa? Domin yanayinmu yana canjawa. Mene ne zai iya taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau?
7. Me ya kamata mu roƙi Jehobah, kuma me ya sa?
7 Ka roƙi Jehobah ya ba ka hikima. Jehobah ya hure Yaƙub ya rubuta cewa: “In waninku yana bukatar hikima, sai ya roƙi Allah wanda yake ba kowa hannu sake.” (Yaƙ. 1:5) Hakika, dukanmu muna “bukatar hikima.” Saboda haka, ka dogara ga Jehobah sa’ad da kake yanke shawara da sa’ad da kake so ka canja shawarar. Zai taimaka maka ka yi zaɓi mai kyau.
8. Wane bincike ne ya kamata mu yi kafin mu yanke shawara?
8 Ka yi bincike sosai. Ka bincika Kalmar Allah, ka karanta littattafan ƙungiyar Jehobah kuma ka tattauna da mutanen da za su ba ka shawara mai kyau. (K. Mag. 20:18) Yin hakan yana da kyau kafin ka yanke shawarar canja aikinka da ƙaura zuwa wani wuri da kuma zaɓan irin ilimin da kake so ka samu don ka sami biyan bukatunka kuma ka ci gaba da bauta wa Jehobah.
9. Ta yaya za mu amfana idan mu masu gaskiya ne?
9 Ka bincika muradinka. Jehobah ya damu da dalilan da suka sa muke yanke wasu shawarwari. (K. Mag. 16:2) Yana so mu yi gaskiya a dukan abu. Saboda haka, idan muka yanke shawara, ya kamata mu gaya wa kanmu da kuma mutane gaskiya game da dalilin da ya sa muka yi hakan. Idan ba mu yi haka ba, zai iya yi mana wuya mu cika alkawarin da muka yi. Alal misali, wani ɗan’uwa matashi yana iya yanke shawarar yin hidimar majagaba. Amma bayan wani lokaci, sai ya soma yi masa wuya ya cika awoyinsa kuma ba ya jin daɗin hidimarsa sosai. Wataƙila ya yi tunani cewa dalilin da ya sa yake yin hidimar shi ne don yana so ya faranta ran Jehobah. Amma zai iya yiwu cewa ya yi hakan ne domin ya so ya faranta ran iyayensa kuma yana so su yi alfahari da shi.
10. Me muke bukata idan muna so mu yi canje-canje?
10 Ka yi la’akari da misalin wani ɗalibin Littafi Mai Tsarki da ya so ya daina shan sigari. Ya yi wajen mako ɗaya ko biyu bai sha sigari ba, amma bayan haka, sai ya sake komawa gidan jiya. Daga baya, ya daina shan sigari gabaki ɗaya! Ƙaunarsa ga Jehobah da kuma so ya faranta masa rai ne ya taimaka masa ya daina shan sigari.—Kol. 1:10; 3:23.
11. Me ya sa ya dace mu yanke takamaiman shawara?
11 Ka yanke takamaiman shawara. Idan ka yanke takamaiman shawara, zai fi kasance maka da sauƙi ka aiwatar da ita. Alal misali, wataƙila ka yanke shawara cewa za ka riƙa karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai. Amma idan ba ka da tsarin ayyuka, zai yi maka wuya ka cim ma burinka. * Ko kuma zai yiwu dattawan ikilisiya sun yanke shawara cewa suna so su riƙa ziyartar ʼyan’uwa a kai a kai, amma an ɗan jima kuma ba su yi ba. Idan suna so su yi nasara, suna iya yin waɗannan tambayoyi: “Mun bincika sunayen ʼyan’uwan da za su fi bukatar ziyarar ƙarfafawa? Mun tsai da shawara a kan lokacin da za mu ziyarce su?”
12. Mene ne za mu bukaci yi, kuma me ya sa?
12 Ka nuna sanin yakamata. Babu waninmu da ke da lokaci da kuzarin cim ma dukan abubuwan da yake so ya yi. Saboda haka, ka kasance da sanin yakamata. Idan zai yiwu, za ka iya canja shawarar da ta fi ƙarfinka. (M. Wa. 3:6) Amma me za ka yi idan ka sake duba shawarar, ka yi gyare-gyaren da ya kamata amma duk da haka, kana gani ba za ka iya aiwatar da ita ba? Ka yi la’akari da matakai biyar da za su iya taimaka maka ka gama abin da ka fara.
MATAKAN DA ZA SU TAIMAKA MUKU KU CIM MA MAƘASUDANKU
13. Ta yaya za ka sami ƙarfin aiwatar da shawarar da ka yanke?
13 Ka roƙi Allah ya ba ka ƙarfi. Allah zai iya ba ka ƙarfi ka aiwatar da shawarar da ka yanke. (Filib. 2:13) Ka roƙi Jehobah ya ba ka ruhunsa mai tsarki don ka sami ƙarfin da kake bukata. Ka ci gaba da yin addu’a ko da kana ganin ba a amsa addu’ar ba tukun. Kamar yadda Yesu ya ce: “Ku yi ta roƙo za a ba ku [ruhu mai tsarki].”—Luk. 11:9, 13.
14. Ta yaya ƙa’idar da ke Karin Magana 21:5 za ta taimaka maka ka aiwatar da shawararka?
14 Ka yi shiri. (Karanta Karin Magana 21:5.) Idan kana so ka gama kowane abu da ka soma, kana bukatar shiri. Bayan haka, ka bi shirin da ka yi. Hakazalika, idan ka yanke wata shawara, ka rubuta hanyoyin da kake so ka cim ma shawarar. Idan ka rarraba wani babban aikin da kake so ka cim ma cikin ƙanana sassa, hakan zai taimaka maka ka san abin da ka riga ka cim ma. Bulus ya ƙarfafa Korintiyawa cewa “a kowace ranar farko ta mako,” su ajiye abin da za su bayar, maimakon su jira sai ya zo kafin su soma tattara gudummawar. (1 Kor. 16:2) Rarraba aikin cikin ƙananan sassa zai kuma taimaka maka don kada ka gaji.
15. Me kake bukatar ka yi bayan ka yi shiri?
15 Idan ka rubuta abin da kake so ka yi, zai fi maka sauƙi ka yi shi. (1 Kor. 14:40) Alal misali, an umurci rukunin dattawa cewa su zaɓi dattijon da zai riƙa rubuta shawarar da suke yankewa da dattijon da zai aiwatar da shawarar da kuma ranar da za a kammala ta. Yana kasance wa dattawan da ke bin wannan shawarar sauƙi su aiwatar da shawarar da suka yanke. (1 Kor. 9:26) Kai ma kana iya bin shawarar nan a rayuwarka ta yau da kullum. Alal misali, za ka iya shirya tsarin ayyukan da za ka cim ma kowace rana kuma ka kasa shi yadda kake so ka aiwatar da shi. Hakan zai iya taimaka maka ka gama abin da ka soma kuma ka cim ma abubuwa da yawa a ƙanƙanin lokaci.
16. Me kake bukata don ka aiwatar da shawararka, kuma ta yaya Romawa 12:11 ta goyi bayan hakan?
16 Ka ƙoƙarta. Kana bukatar ka ƙoƙarta don ka bi shawarar da ka yanke kuma ka gama abin da ka fara. (Karanta Romawa 12:11.) Bulus ya ce wa Timoti ya “ci gaba,” kuma ya “nace” don ya zama ƙwararren malami. Hakazalika, za mu iya bin shawarar nan a dukan abin da muke so mu yi a hidimar Allah.—1 Tim. 4:13, 16.
17. Ta yaya Afisawa 5:15, 16 za su taimaka mana mu aiwatar da shawararmu?
17 Ka yi amfani da lokacinka yadda ya dace. (Karanta Afisawa 5:15, 16.) Ka ƙayyade lokacin da za ka aiwatar da shawararka kuma ka ƙoƙarta ka yi hakan. Kada ka ce kana jiran lokacin da ya fi dacewa kafin ka aiwatar da shawararka domin da kyar za ka sami irin wannan lokacin. (M. Wa. 11:4) Ka mai da hankali don kada abubuwa marar muhimmanci su cinye lokacinka da kuma ƙarfin da kake bukata don yin abubuwa mafi muhimmanci. (Filib. 1:10) Idan zai yiwu, ka nemi lokacin da mutane ba za su raba hankalinka ba. Ka gaya musu cewa ba ka so a dame ka. Ka kashe wayarka kuma ka karanta saƙonnin imel da na dandalin sada zumunta bayan ka gama abin da kake yi. *
18-19. Mene ne zai taimaka maka ka aiwatar da shawararka ko da ka fuskanci ƙalubale?
18 Ka yi tunani a kan sakamakon. Sakamakon shawarar da ka yanke yana kamar yin tafiya mai nisa. Idan kana so ka kai wurin da za ka je, dole ne ka ci gaba da yin tafiya ko da an rufe hanya kuma kana bukatar ka bi wata hanya. Hakazalika, idan mun mai da hankali a kan sakamakon shawararmu, ba za mu fid da rai ba ko da mun fuskanci matsaloli.—Gal. 6:9.
19 Yanke shawarwari masu kyau na da wuya kuma aiwatar da su na cike da ƙalubale. Amma da taimakon Jehobah, za ka sami hikima da kuma ƙarfin gama abin da ka fara.
WAƘA TA 65 Mu Riƙa Samun Ci Gaba!
^ sakin layi na 5 Kana yin da-na-sani don wasu shawarwarin da ka taɓa yankewa? Ko a wasu lokuta, kana fama ka yanke shawara mai kyau kuma ka aiwatar da shawarar? Wannan talifin zai taimaka maka ka magance ƙalubalen kuma ka gama abin da ka fara.
^ sakin layi na 11 Idan kana bukatar taimaka don ka riƙa karanta Littafi Mai Tsarki, za ka iya yin amfani da tsarin ayyukan da ke jw.org®. Ka duba ƙarƙashin LITTATTAFAI > LITTATTAFAI DA ƘASIDU.
^ sakin layi na 17 Don samun ƙarin shawarwari a kan yadda za ka yi amfani da lokacinka, ka duba talifin nan “20 Ways to Create More Time” a Awake! ɗin Afrilu 2010.