TARIHI
“Jehobah Bai Mance da Ni Ba”
AN HAIFE ni a Orealla, wani ƙauyen da ke da mutane wajen 2,000, a ƙasar Guyana da ke Kudancin Amirka. Ƙauyen yana tsibiri kuma da jirgin ruwa ko kuma jirgin sama ne kaɗai ake zuwa wurin.
An haife ni a shekara ta 1983. Ina da ƙoshin lafiya sa’ad da nake yaro, amma sa’ad da na kai shekara goma, sai jikina ya soma yi mini ciwo sosai. Bayan wajen shekara biyu, na tashi da safe wata rana kuma ban iya tafiya ba. Na yi ƙoƙari sosai in ɗaga ƙafafuna amma na kasa. Tun daga ranar, ban sake tafiya ba. Rashin lafiya ya hana ni girma. A yau, jikina kamar na ƙaramin yaro ne.
Bayan na yi watanni da yawa ban fita ba don rashin lafiya, sai wasu Shaidun Jehobah biyu suka ziyarce ni. Idan baƙi suka zo, nakan ɓoye, amma a ranar, na yarda matan su tattauna da ni. Abin da suka gaya mini game da aljanna ya tuna mini abin da na ji sa’ad da nake wajen ɗan shekara biyar. A lokacin, wani mai wa’azi a ƙasar waje mai suna Jethro daga Suriname, yakan zo ƙauyenmu sau ɗaya a wata don ya yi nazari da mahaifina. Jethro ya nuna mini alheri sosai. Ina son shi ƙwarai. Ban da haka, kakana yakan kai ni taron Shaidun Jehobah da ake yi a ƙauyenmu. Saboda haka, sa’ad da Florence ɗaya daga cikin Shaidun ta tambaye ni ko zan so a yi nazari da ni, na ce e.
Florence da mijinta Justus sun dawo kuma suka soma nazari da ni. Sun koya mini yin karatu, da suka lura cewa ban iya ba. Bayan wani lokaci, sai na iya karatu. Wata rana, ma’auratan sun gaya mini cewa an tura su yin hidima a Suriname. Abin taƙaici, babu Shaidu a Orealla da za su ci gaba da yin nazari da ni. Amma na yi farin ciki cewa Jehobah bai mance da ni ba.
Nan ba daɗewa ba, wani majagaba mai suna Floyd ya zo Orealla kuma sa’ad da yake wa’azi gida-gida sai ya haɗu da ni. Sa’ad da ya tambaye ni ko zan so in yi nazarin Littafi Mai Tsarki, sai na yi murmushi. Ya ce: “Me ya sa kake murmushi?” Na gaya masa cewa na kammala nazarin ƙasidar nan Menene Allah Yake Bukata a Garemu? kuma na soma nazarin littafin nan Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada. * Na bayyana masa dalilin ya sa muka daina nazarin. Floyd ya kammala nazarin littafin da ni, amma shi ma an tura shi hidima a wani wuri. Kuma hakan ya sake sa babu wanda ke nazari da ni.
A shekara ta 2004, an turo ɗan’uwa Granville da Joshua da suke hidimar majagaba na musamman zuwa Orealla. Sun yi wa’azi gida-gida kuma suka haɗu da ni. Sa’ad da suka tambaye ni ko zan so a yi nazari da ni, sai na yi murmushi. Na gaya musu cewa su sake yin nazarin littafin nan Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada da ni. Ina so in ga ko abin da za su koya mini daidai ne da na malamina na dā. Granville ya gaya mini cewa ana taro a ƙauyenmu. Duk da cewa, na yi wajen shekara goma ba na fita daga gida, na so in halarci taron. Sai Granville ya ɗauke ni ya zaunar da ni a keken guragu kuma ya tura ni zuwa Majami’ar Mulki.
Da shigewar lokaci, Granville ya ce in gaya wa dattawa su ba ni aiki a Makarantar Hidima ta Allah. Ya ce: “Kai gurgu ne, amma za ka iya yin magana. Wata rana za ka yi jawabi ga jama’a. Hakan zai faru.” Kalmominsa sun ƙarfafa ni sosai.
Sai na soma fita wa’azi da Granville. Amma saboda yadda hanyar ƙauyen take, ba na iya amfani da keken guragu na. Sai na gaya wa Granville ya riƙa tura ni a baro. Hakan ya taimaka sosai. Na yi baftisma a watan Afrilu 2005. Ba da daɗewa ba, sai ’yan’uwan suka koya mini yadda zan riƙa kula da littattafan ikilisiya da kuma sauti a Majami’ar Mulki.
A shekara ta 2007, mahaifina ya yi hatsarin jirgin ruwa kuma ya rasu. Hakan ya sa iyalinmu baƙin ciki sosai. Granville ya yi addu’a tare da mu kuma ya karanta mana wasu ayoyi daga Littafi Mai Tsarki don ya ƙarfafa mu. Shekaru biyu bayan haka, wani abin baƙin ciki ya sake faruwa. Granville ya yi hatsarin jirgin ruwa kuma shi ma ya rasu.
Hakan ya sa ikilisiyarmu ba ta da dattawa sai bawa mai hidima guda. Mutuwar Granville ta yi mini zafi sosai domin shi abokina ne na ƙwarai. Ya taimaka mini in ƙulla dangantaka da Jehobah kuma ya biya bukatuna. Bayan mutuwarsa, an ce in karanta Hasumiyar Tsaro a taro. Na karanta sakin layi guda biyu, amma sai na soma kuka kuma na kāsa riƙe kaina. Hakan ya sa na sauko daga dakalin magana.
Na soma warwarewa sa’ad da ’yan’uwa daga wata ikilisiya suka soma zuwa don su taimaka mana a Orealla. Ban da haka, an turo Kojo ya yi hidimar majagaba na musamman a yankin. Na yi farin ciki sosai cewa mahaifiyata da ƙanena sun soma nazari kuma suka yi baftisma. Kuma a watan Maris 2015, an naɗa ni bawa mai hidima. Baya wani lokaci, na ba da jawabina na farko. A ranar, na yi farin ciki don na tuna abin da Granville ya gaya mini shekaru da suka shige cewa: “Wata rana za ka yi jawabi ga jama’a. Babu shakka, hakan zai faru.”
Ta shirye-shiryen JW, ina jin labarin ’yan’uwa da suke irin yanayina. Amma duk da haka, sun cim ma abubuwa da yawa kuma suna farin ciki. Ni ma zan iya daɗa ƙwazo. Ina son in yi iya ƙoƙarina a hidimata ga Jehobah. Saboda haka, sai na soma hidimar majagaba na kullum. Kuma a watan Satumba 2019, na sami wani albishiri! A wannan watan, an gaya mini cewa an naɗa ni dattijo a ikilisiyarmu da ke da masu shela wajen 40.
Ina matuƙar godiya ga ’yan’uwan da suka yi nazari da ni kuma suka taimaka su ɗauke ni zuwa wa’azi. Amma mafi muhimmanci, ina godiya ga Jehobah domin bai mance da ni ba.
^ sakin layi na 8 Shaidun Jehobah ne suka wallafa, amma an daina buga shi.