Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Onésime da Géraldine

Jehobah Yana wa Wadanda Suka Koma Kasarsu Albarka

Jehobah Yana wa Wadanda Suka Koma Kasarsu Albarka

ʼYAN’UWA da yawa da suka je ƙasashen Turai don neman abin biyan bukata sun koma ƙasarsu yanzu. Ƙaunarsu ga Jehobah da kuma maƙwabtansu ne ya motsa su su ƙaura zuwa wuraren da ake bukatar masu shela sosai. (Mat. 22:​37-39) Wace sadaukarwa ce suka yi, kuma wace albarka ce suka samu? Don mu sami amsoshin tambayoyin nan, bari mu mai da hankali ga abin da ya faru a ƙasar Kamaru da ke yammacin Afirka.

“SUN KOMA WURAREN DA SUKA DACE”

A shekara ta 1998, wani ɗan’uwa mai suna Onésime daga Kamaru ya koma wata ƙasa. Ya yi shekara 14 a ƙasar da ya koma. Wata rana sa’ad da suke taron ikilisiya, mai jawabin ya yi amfani da wani kwatanci game da wa’azi. Mai jawabin ya ce: “Idan mutane biyu suna kama kifi a wurare dabam-dabam, amma ɗayan ya fi kama kifi. Babu shakka, wancan ɗin zai koma wurin da ɗayan yake kama kifi sosai.”

Wannan kwatancin ya sa Onésime ya soma tunanin koma ƙasarsu, don ya taimaka wa mutanen da ke so a yi nazari da su. Amma yana da wasu ƙalubale. Shin zai iya sake zama a ƙasarsu bayan ya yi shekaru da yawa a ƙasar waje? Onésime ya je ya yi wata shida a Kamaru don ya san ko zai iya zama a wurin. A shekara ta 2012, sai ya koma Kamaru da zama.

Onésime ya ce: “Na ɗan yi fama da zafi da kuma yanayin garin. Na sake koyan yadda ake zama a kan benci a Majami’ar Mulki.” Ya faɗa da fara’a cewa: “Sannu a hankali, sai na soma sabawa da zama a kan benci.”

A shekara ta 2013, Onésime ya auri wata mai suna Géraldine da ta dawo Kamaru bayan ta yi shekara tara a Faransa. Waɗanne albarku ne ma’auratan nan suka samu domin sun mai da hankali ga biɗan al’amuran Mulkin Allah? Onésime ya ce: “Ni da matata mun halarci Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki kuma muka soma hidima a Bethel. A shekarar da ta wuce, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki guda 20 a ikilisiyarmu sun yi baftisma. A yanzu, na ga cewa ina wurin da ya dace in yi wa’azi.” (Mar. 1:​17, 18) Matarsa ta ce: “Na sami albarka sosai fiye da yadda nake zato.”

YADDA MUKE FARIN CIKI DON ALMAJIRTARWA

Judith da Sam-Castel

Judith ta koma Amirka amma tana so ta daɗa yin ƙwazo a hidimarta. Ta ce: “A duk lokacin da na je ziyara a Kamaru, ina zub da hawaye sa’ad da zan koma domin na bar ɗalibai da yawa da na soma nazari da su.” Amma, Judith ta yi jinkirin koma Kamaru. Tana da aikin da ake biyanta albashi mai tsoka kuma hakan na taimaka mata ta biya kuɗin jinyar babanta a Kamaru. Duk da haka, Judith ta dogara ga Jehobah kuma ta ƙaura. Ta ce a Kamaru, babu wasu abubuwa da ake da su a ƙasar waje. Ta yi addu’a ga Jehobah don ya taimaka mata ta saba da yanayin wurin kuma wani mai kula da da’ira da matarsa sun ƙarfafa ta.

Sa’ad da Judith take tunawa da yanayinsu bayan sun dawo Kamaru, ta ce: “A cikin shekara uku, na taimaka wa mutane huɗu su yi baftisma.” Sai Judith ta soma hidimar majagaba na musamman. A yau, ita da maigidanta Sam-Castel suna hidimar mai kula da da’ira. Me ya faru da mahaifin Judith? Ita da maigidanta sun samo wani asibiti a ƙasar waje da suka yarda su yi wa mahaifinta tiyata kyauta. Kuma mahaifin ya samu sauƙi.

JEHOBAH YA TAIMAKA MANA

Caroline da Victor

Wani ɗan’uwa mai suna Victor ya ƙaura zuwa Kanada. Bayan ya karanta wani talifi a Hasumiyar Tsaro game da jami’a, sai ya soma tunani sosai game da makarantar da yake zuwa. Ya daina zuwa makarantar kuma ya soma koyon sana’a. Ya ce: “Hakan ya sa in samu aiki nan da nan kuma na soma hidimar majagaba da nake son yi da daɗewa.” Bayan haka, Victor ya auri Caroline kuma suka ziyarci Kamaru. Da suka ziyarci reshen ofishi da ke Kamaru, wasu ’yan’uwa suka ƙarfafa su su yi tunanin yin hidima a Kamaru. Victor ya ce, “Ba mu ga dalilin da zai hana mu yin hakan ba, kuma tun da yake mun sauƙaƙa salon rayuwarmu, muna iya soma wannan hidimar.” Ko da yake Caroline ba ta da ƙoshin lafiya sosai, sun tsai da shawara su ƙaura.

Victor da Caroline sun soma hidimar majagaba na kullum don su taimaka wa mutane da suke son su koya game da Jehobah. Sun tara kuɗaɗe da yawa don kada su soma aiki da zarar sun ƙaura. Bayan haka, sun yi aiki a Kanada na ’yan watanni, kuma suka koma Kamaru don su ci gaba da hidimarsu. Wace albarka ce suka samu? Sun halarci Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki, sun yi hidimar majagaba na musamman kuma yanzu suna aikin gine-gine. Victor ya ce, “Don mun bar yin rayuwa da muka saba, mun dogara ga Jehobah kuma ya kula da mu.”

MUN YI FARIN CIKIN TAIMAKA WA MUTANE SU BAUTA WA JEHOBAH

Stéphanie da Alain

A shekara ta 2002, wani ɗan’uwa mai suna Alain da ke makarantar jami’a a Jamus ya karanta warƙar nan Matasa​Me Za Ku Yi da Rayuwarku? Abin da ya karanta ya motsa shi ya kafa sababbin maƙasudai. A shekara ta 2006, ya halarci Makarantar Koyar da Masu Hidima kuma aka tura shi hidima a ƙasarsu Kamaru.

A ƙasar, Alain ya sami aiki na ɗan lokaci. Daga baya, ya sami aikin da ake biyan sa albashi mai tsoka, amma ya lura cewa aikin zai hana shi yin hidima da ƙwazo. Saboda haka, da aka gayyace shi yin hidimar majagaba na musamman, ya amince ya yi hidimar. Shugaban aikinsu ya so ya ƙara masa albashi, amma Alain ya tsaya a kan shawarar da ya yanke. Daga baya, Alain ya auri Stéphanie, wadda ta yi shekaru da yawa a Faransa. Waɗanne ƙalubale ne Stéphanie ta fuskanta sa’ad da ta ƙaura zuwa Kamaru?

Stéphanie ta ce: “Na ɗan soma rashin lafiya, kuma akwai wasu abubuwa da ke damuna idan na ci su. Sai na samo magani, kuma hakan ya sa na sami sauƙi.” Ma’auratan sun sami albarka don sun ci gaba da hidimarsu. Alain ya ce: “Sa’ad da muka je wani ƙauye da ake kira Katé don yin wa’azi, mun samu mutane da yawa da suke son nazarin Littafi Mai Tsarki. Daga baya mun soma nazari da su ta waya. Maza biyu cikin waɗannan ɗalibanmu sun yi baftisma, kuma aka kafa rukuni a ƙauyen.” Stéphanie ta daɗa cewa: “Babu abin da ya fi sa mutum farin ciki kamar taimaka wa mutane su soma bauta wa Jehobah. Yin hidima a nan ya sa mun shaida irin wannan farin ciki sau da yawa.” A yau, Alain da Stéphanie suna hidimar mai kula da da’ira.

“MUN YI ABIN DA YA KAMATA MU YI”

Léonce da Gisèle

Gisèle ta yi baftisma sa’ad da ta je makarantar likitoci a Italiya. Tana son yadda ma’aurata majagaba da suka yi nazari da ita suka sauƙaƙa rayuwarsu, hakan ya sa ta so daɗa ƙwazo a wa’azi. Sai Gisèle ta soma hidimar majagaba na kullum sa’ad da take gab da sauƙe karatu.

Gisèle tana son ta koma Kamaru don ta bauta wa Jehobah sosai, amma akwai wasu abubuwan da ke damunta. Ta ce, “Hakan yana nufin zan yi watsi da damar zama ’yar ƙasar Italiya kuma ba zan kasance da abokaina da iyalina da suke Italiya ba.” Duk da haka, Gisèle ta koma Kamaru a watan Mayu 2016. Daga baya, ta auri wani ɗan’uwa mai suna Léonce, kuma reshen ofishinmu da ke Kamaru ya tura su hidima a garin Ayos da ake bukatar masu shela sosai.

Waɗanne matsaloli ne suka fuskanta a garin Ayos? Gisèle ta ce: “A yawancin lokuta, muna yin makonni da yawa ba mu da wutan lantarki. Don haka, a yawancin lokuta, ba mu iya yin cajin wayoyinmu. Na koyi yin girki da itace, muna tura baro, mu kuma yi amfani da tocila daddare don mu je ɗiban ruwa sa’ad da babu mutane da yawa a kogi.” Mene ne ya taimaka wa ma’auratan su jimre? Gisèle ta ce: “Ruhun Jehobah ya taimaka mana mu jimre. Ƙari ga haka, ni da maigidana muna taimaka wa juna, kuma iyalanmu da abokanmu suna ƙarfafa mu kuma suna taimaka mana da kuɗi a wasu lokuta.”

Gisèle tana farin ciki kuwa cewa ta koma ƙasarsu? Ta ce: “Ƙwarai kuwa! Da farko mun fuskanci matsaloli kuma a wasu lokuta mukan yi sanyin gwiwa, amma muddin muka shawo kan waɗannan abubuwa, ni da maigidana muna ganin mun yi abin da ya kamata mu yi. Mun dogara ga Jehobah kuma mun kusace shi sosai.” Léonce da Gisèle sun Halarci Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki, kuma yanzu suna hidimar majagaba na musamman na ɗan lokaci.

Kamar masu kamun kifi da suka kasance da ƙarfin zuciya duk da matsaloli, waɗanda suka koma ƙasarsu sun yi sadaukarwa don su taimaka wa mutane da suke son saƙonmu. Babu shakka, Jehobah zai tuna da waɗannan masu shela masu ƙwazo don ƙaunar da suka nuna masa. (Neh. 5:19; Ibran. 6:10) Idan kana zama a ƙasar waje kuma ana bukatar masu shela a ƙasarku, za ka so ka koma ne? Idan ka yi hakan, Jehobah zai albarkace ka.​—K. Mag. 10:22.