Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 48

Ka Mai da Hankali ga Nan Gaba

Ka Mai da Hankali ga Nan Gaba

“Bari idanunka su duba gaba sosai.”​—K. MAG. 4:25.

WAƘA TA 77 Haske a Duniya Mai Duhu

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Ta yaya za mu bi shawarar da ke Karin Magana 4:25? Ka ba da misali.

KA YI tunani a kan waɗannan misalan: Wata ’yar’uwa tsohuwa tana tunanin abubuwa masu kyau da suka faru a dā. Duk da cewa tana fuskantar matsaloli yanzu, ta ci gaba da yin iya ƙoƙarinta a hidimar Jehobah. (1 Kor. 15:58) A kowace rana, tana tunanin yadda ita da iyalinta da abokanta za su kasance tare a sabuwar duniya. Wata ’yar’uwa kuma ta tuna yadda wata a ikilisiya ta ɓata mata rai, amma ta gafarta mata kuma ta mance da batun. (Kol. 3:13) Wani ɗan’uwa ya tuna kurakuren da ya yi a dā, amma ya mai da hankali ga yin iya ƙoƙarinsa a hidimarsa.​—Zab. 51:10.

2 Wace alaƙa ce ke yanayin waɗannan Kiristoci? Dukansu sun tuna abubuwan da suka faru da su a dā, amma ba su ci gaba da mai da hankali a kansu ba. A maimakon haka, sun ‘bari idanunsu su duba gaba sosai.’​—Karanta Karin Magana 4:25.

3. Me ya sa muke bukatar mu mai da hankali ga nan gaba?

3 Me ya sa yake da muhimmanci mu mai da hankali ga nan gaba? Mutumin da yake kallon baya sa’ad da yake tafiya zai faɗi. Hakazalika, ba za mu bauta wa Jehobah da kyau ba idan muka fi mai da hankali ga abubuwan da muka yi a dā ko kuma da suka faru da mu.​—Luk. 9:62.

4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

4 A wannan talifin, za mu tattauna abubuwa uku da za su iya sa mu fi mai da hankali ga abubuwan da suka faru a dā. Su ne: (1) so rayuwarmu ta kasance yadda take a dā, (2) riƙe mutum a zuciya, da kuma (3) yawan baƙin ciki don kuskuren da muka yi a dā. Za mu ga yadda ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana mu guji mai da hankali ga abin da ya “riga ya wuce,” amma mu mai da hankali ga “abin da yake gaba.”​—Filib. 3:13.

SON RAYUWARMU TA KASANCE YADDA TAKE A DĀ

Mene ne zai iya hana mu tunanin abubuwan da za mu ji daɗinsa a nan gaba? (Ka duba sakin layi na 5, 9, 13) *

5. Mene ne Mai-Wa’azi 7:10 ta ce kada mu yi?

5 Karanta Mai-Wa’azi 7:10. Ka lura cewa wannan ayar ba ta ce bai dace mu ce: ‘Me ya sa kwanakin dā suke da kyau?’ Muna yawan tunawa da abubuwa masu kyau da suka faru da mu, kuma yadda Jehobah ya yi mu ke nan. Amma ayar ta ce: “Kada ka ce, ‘Me ya sa kwanakin dā sun fi na yanzu?’” Bai kamata mu riƙa gwada rayuwarmu ta dā da na yanzu ba, kuma mu kammala cewa ba abin da yake da kyau yanzu. Wani juyin Littafi Mai Tsarki kuma ya ce: “Kada ka tambaya, Don me kwanakin dā sun fi na yanzu kyau? Gama ba da hikima kake binciken wannan ba.”

Wane kuskure ne Isra’ilawa suka yi bayan sun bar Masar? (Ka duba sakin layi na 6)

6. Me ya sa bai dace mu riƙa tunani a kan irin rayuwar da muka yi a dā ba? Ka ba da misali.

6 Me ya sa ba zai dace mu riƙa tunanin cewa rayuwarmu a dā ta fi na yanzu ba? Irin wannan tunanin zai sa mu fi mai da hankali ga abubuwa masu kyau da suka faru da mu a dā, kuma mu mance da matsalolin da muka fuskanta. Ka yi la’akari da abin da ya faru da Isra’ilawa a zamanin dā. Bayan sun bar ƙasar Masar, sun yi saurin mance irin wahalar da suka sha a ƙasar. Amma suka mai da hankali ga abinci masu kyau da suke ci a ƙasar. Suka ce: “Mun tuna yadda a ƙasar Masar muka ci kifi kyauta. Mun kuma tuna da su kakamba, da kabewa, da albasa mai ganye da mai ƙwaya, da tafarnuwa.” (L. Ƙid. 11:5) Amma gaskiya ne cewa “kyauta” ce suke ci waɗannan abubuwan? A’a. Isra’ilawan sun sha wahala sosai domin a lokacin su bayi ne a ƙasar Masar. (Fit. 1:​13, 14; 3:​6-9) Daga baya, sun mance da wahalolin da suka sha kuma suka so rayuwarsu ta kasance yadda take a dā. Sun mai da hankali ga abubuwan da suka ji daɗinsa a dā maimakon abin da Jehobah ya yi musu. Hakan ya ɓata wa Jehobah rai.​—L. Ƙid. 11:10.

7. Mene ne ya taimaka ma wata ’yar’uwa ta guji so rayuwarta ta kasance yadda take a dā?

7 Ta yaya za mu guji so rayuwarmu ta kasance yadda take a dā? Ka yi la’akari da labarin wata ’yar’uwa da ta soma yin hidima a Bethel da ke Brooklyn a shekara ta 1945. Wasu shekaru bayan haka, ta auri wani da ke hidima a Bethel kuma suka yi shekaru da yawa suna hidima tare. Amma a shekara ta 1976, mijinta ya soma rashin lafiya sosai. Ta ce a lokacin da ya gano cewa mutuwarsa ta kusa, ya ba ta shawarwari masu kyau da za su taimaka mata ta jimre bayan rasuwarsa. Ya ce mata: “Mun ji daɗin aurenmu sosai. Mutane da yawa ba su sami irin wannan damar ba.” Ya ƙara da cewa: “Ba za ki manta da abubuwan da muka yi tare ba, amma kada ki ci gaba da tunani a kansu. Da shigewar lokaci, za ki rage baƙin ciki. Kada ki yi sanyin gwiwa don abin da ya faru da ke. Amma ki yi farin ciki don yadda muka ji daɗin bauta wa Jehobah tare. . . . Tuna abubuwa masu kyau da suka faru da mu, kyauta ce daga Allah.” Hakika, wannan shawara ce mai kyau!

8. Ta yaya wata ’yar’uwa ta amfana daga yin tunanin abubuwan da za su faru a nan gaba?

8 Yar’uwar ta bi shawarar da magidanta ya ba ta. Ta bauta wa Jehobah da aminci har mutuwarta a lokacin da take ’yar shekara 92. ʼYan shekaru kafin ta mutu, ta ce: “Idan na yi tunanin shekara 63 da na yi ina bauta wa Jehobah a hidima ta cikakken lokaci, zan iya cewa na sami gamsuwa a rayuwata.” Me ya sa? Ta ce: “Muna farin ciki sosai domin muna cikin iyalin da ke da begen yin rayuwa tare a aljanna, kuma a lokacin, za mu riƙa bauta wa Mahaliccinmu Jehobah, har abada.” * Za mu iya koyan darasi sosai daga wannan ’yar’uwa da ta mai da hankali ga abubuwan da Jehobah ya yi alkawari cewa zai yi a nan gaba!

RIƘE MUTUM A ZUCIYA

9. Kamar yadda Littafin Firistoci 19:18 ya nuna, a wane lokaci ne zai iya yi mana wuya mu guji riƙe mutum a zuciya?

9 Karanta Littafin Firistoci 19:18. A wasu lokuta, yana yi mana wuya sosai mu gafarta wa wani a ikilisiya ko abokinmu ko kuma wani danginmu da ya ɓata mana rai. Alal misali, wata ’yar’uwa ta zargi wata ’yar’uwa cewa ta saci kuɗinta. Daga baya, ’yar’uwar da aka sace wa kuɗin ta ba wa ’yar’uwar da take zargi haƙuri. Amma ’yar’uwar ba ta haƙura ba kuma ta ci gaba da yin tunani a kan batun. Ka taɓa samun kanka a irin wannan yanayin? Ko da hakan bai taɓa faruwa da kai ba, yawancinmu muna ganin cewa ba za mu taɓa gafarta wa wani da ya ɓata mana rai ba.

10. Mene ne zai iya taimaka mana idan muka kasa gafartawa?

10 Mene ne zai iya taimaka mana idan muka kasa gafartawa? Da farko, ka tuna cewa Jehobah yana ganin dukan abubuwan da ke faruwa. Ya san dukan abubuwan da muke fuskanta, har da rashin adalci da aka mana. (Ibran. 4:13) Ba ya farin ciki idan muna shan wahala. (Isha. 63:9) Kuma ya yi alkawari cewa zai magance dukan baƙin cikin da muke yi don an yi mana rashin adalci.​—R. Yar. 21:​3, 4.

11. Ta yaya za mu amfana idan muka gafarta wa mutane?

11 Muna bukatar mu tuna cewa idan muka guji riƙe mutum a zuciya za mu amfana. Daga baya, ’yar’uwar da aka zargi ta fahimci hakan. Da shigewar lokaci, ta gafarta wa wadda ta zarge ta. Ta fahimci cewa idan muka gafarta wa mutane, Jehobah ma zai gafarta mana. (Mat. 6:14) Ta san cewa abin da ’yar’uwar ta yi bai dace ba, amma ta zaɓi ta gafarta mata. A sakamakon haka, ’yar’uwar ta yi farin ciki kuma ta mai da hankali ga hidimarta ga Jehobah.

YAWAN BAƘIN CIKI DON KUSKUREN DA MUKA YI A DĀ

12. Mene ne muka koya daga 1 Yohanna 3:​19, 20?

12 Karanta 1 Yohanna 3:​19, 20. A wasu lokuta, muna iya damuwa don kuskuren da muka yi. Alal misali, wasu suna iya baƙin ciki domin abubuwan da suka yi a dā kafin su soma bauta wa Jehobah. Wasu kuma suna iya baƙin ciki don kuskuren da suka yi bayan sun yi baftisma. (Rom. 3:23) Babu shakka, muna son mu yi abin da ya dace. Amma “dukanmu mukan yi kuskure da yawa.” (Yaƙ. 3:2; Rom. 7:​21-23) Ko da yake ba ma so mu riƙa baƙin ciki don kuskuren da muka, hakan yana da amfani. Me ya sa? Domin yin hakan zai sa mu yi canje-canje a rayuwarmu kuma mu ƙuduri niyyar cewa ba za mu maimaita kuskuren ba.​—Ibran. 12:​12, 13.

13. Me ya sa muke bukatar mu guji yawan baƙin ciki don kuskurenmu?

13 Amma muna iya soma baƙin ciki fiye da kima. Wato mu ci gaba da damuwa duk da cewa mun tuba kuma Jehobah ya gafarta mana zunubanmu. Irin wannan baƙin cikin yana da lahani. (Zab. 31:10; 38:​3, 4) Ta yaya? Ka yi la’akari da misalin wata ’yar’uwa da ta yi baƙin ciki don kuskuren da ta yi a dā. Ta ce: “Aikin banza ne in saka ƙwazo a hidimata ga Jehobah domin wataƙila ba zai cece ni ba.” Da yawa cikinmu muna ji kamar wannan ’yar’uwar. Yana da muhimmanci mu guji yawan baƙin ciki don kuskuren da muka yi. Me ya sa? Domin Shaiɗan zai yi farin ciki idan muka ƙi bauta wa Jehobah, duk da cewa Jehobah ya gafarta mana zunubinmu!​—Gwada 2 Korintiyawa 2:​5-7, 11.

14. Ta yaya za mu tabbata cewa Jehobah yana so ya gafarta mana?

14 Duk da haka, muna iya tunani cewa: ‘Ta yaya zan san cewa Jehobah ya gafarta mini da gaske?’ Idan ka yi wannan tambayar, ya nuna cewa Jehobah ya gafarta maka. Shekaru da yawa da suka shige, wata Hasumiyar Tsaro ta ce: “Muna iya maimaita wani kuskure da muka yi, wataƙila domin ba mu kawar da halin kafin mu soma bauta wa Allah ba. . . . Kada ka fid da rai. Kada ka yi tunanin cewa ka yi zunubin da Allah ba zai taɓa gafarta maka ba. Shaiɗan yana so ka riƙa tunani hakan. Da yake kana baƙin ciki sa’ad da ka yi kuskure ya nuna cewa ba ka wuce kira ba, kuma Jehobah zai iya gafarta maka. Ka kasance da sauƙin kai, ka riƙa addu’a ga Allah don ya gafarta maka, ya taimaka maka ka kasance da zuciya mai kyau, kuma ka guji maimaita kuskuren. Ko da sau nawa ne yaro ya yi kuskure, yana zuwa wurin mahaifinsa don ya taimaka masa. Saboda haka, ka ci gaba da neman taimako daga wurin Jehobah kuma zai taimake ka.” *

15-16. Yaya wasu suka ji sa’ad da suka fahimci cewa Jehobah bai yasar da su ba?

15 Bayin Jehobah da yawa sun sami ƙarfafawa sa’ad da suka fahimci cewa Jehobah bai yasar da su ba. Alal misali, wasu shekaru da suka shige, wani ɗan’uwa ya sami taimako a wani talifin da ya karanta a jerin talifofin nan “Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane.” A talifin, wata ’yar’uwa ta ba da labari cewa saboda abubuwan da ta yi a dā, ya yi mata wuya ta gaskata cewa Jehobah yana ƙaunar ta. Ta kasance da wannan ra’ayin shekaru da yawa bayan ta yi baftisma. Amma sa’ad da ta yi tunani a kan hadayar Yesu, hakan ya taimaka mata ta ga cewa Jehobah yana ƙaunar ta. *

16 Ta yaya labarinta ya taimaka wa ɗan’uwan? Ya ce: “Sa’ad da nake yaro, na shaƙu da kallon hotunan batsa. A kwana-kwanan nan, na sake faɗawa cikin jarrabawar. Na nemi taimakon dattawa, kuma na soma shawo kan matsalar. Dattawa sun tabbatar mini cewa Allah yana ƙauna ta kuma yana so ya taimaka mini. Duk da haka a wasu lokuta, ina ji kamar ba ni da amfani kuma Jehobah ba ya ƙauna ta. Karanta labarin wannan ’yar’uwar ya taimaka mini sosai. Na fahimci cewa idan na ce Allah ba zai gafarta mini ba, kamar dai ina cewa hadayar Ɗansa ba za ta iya wanke zunubaina ba. Na yanka wannan fallen don in riƙa karanta shi da kuma tunani a kansa a duk lokacin da na soma ji ba ni da amfani.”

17. Ta yaya manzo Bulus ya guji yin baƙin ciki sosai don kuskurensa?

17 Irin waɗannan labaran suna tuna mana da manzo Bulus. Kafin ya zama Kirista, ya yi zunubai masu tsanani. Bulus ya tuna abubuwan da ya yi, amma bai mai da hankali a kansu ba. (1 Tim. 1:​12-15) Ya ɗauki hadaya da Yesu ya yi a matsayin kyauta da Jehobah ya ba shi. (Gal. 2:20) Saboda haka, Bulus ya guji yawan baƙin ciki don kuskurensa kuma ya mai da hankali ga yin iya ƙoƙarinsa a hidimar Jehobah.

KA RIƘA TUNANI A KAN SABUWAR DUNIYA!

Bari mu ƙuduri niyyar mai da hankali ga abubuwan da za su faru nan gaba (Ka duba sakin layi na 18-19) *

18. Mene ne muka koya a wannan talifin?

18 Mene ne muka koya daga abubuwan da muka tattauna a wannan talifin? (1) Muna yawan tunawa da abubuwa masu kyau da suka faru da mu, kuma yadda Allah ya yi mu ke nan. Amma, ko da wane irin jin daɗi muka yi, za mu fi jin daɗi a Aljanna. (2) Wasu suna iya ɓata mana rai, amma idan muka gafarta musu, hakan zai sa mu mai da hankali ga hidimar Jehobah. (3) Yin baƙin ciki sosai don kuskurenmu yana iya hana mu farin ciki a bautarmu ga Jehobah. Don haka, muna bukatar mu gaskata kamar manzo Bulus cewa Jehobah ya gafarta mana.

19. Ta yaya muka san cewa a sabuwar duniya ba za mu riƙa tuna kuskurenmu na dā ba?

19 Muna da begen yin rayuwa har abada. Kuma a sabuwar duniya, ba za mu tuna abubuwan da za su sa mu baƙin ciki ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba za a sāke tunawa da abubuwan dā ba.” (Isha. 65:17) Ka yi tunani: Wasunmu sun tsufa suna bauta wa Jehobah, a sabuwar duniya za su sake zama matasa. (Ayu. 33:25) Saboda haka, bari mu ƙuduri niyyar guje wa mai da hankali a kan yadda rayuwarmu take a dā. Amma mu mai da hankali ga abubuwan da za mu iya yi yanzu don mu kasance a sabuwar duniya!

WAƘA TA 142 Mu Jimre, Aljanna Ta Kusa

^ sakin layi na 5 Yana da kyau mu tuna abubuwan da suka faru a dā. Amma ba ma son mu mai da hankali sosai har mu daina yin iya ƙoƙarinmu a hidimarmu ga Jehobah. Ko kuma mu manta da alkawuran da Jehobah ya yi game da nan gaba. A wannan talifin, za mu tattauna abubuwa uku da ya kamata mu guje wa domin suna iya sa mu fi mai da hankali ga abubuwan da suka faru a dā.

^ sakin layi na 8 Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuli, 2004, shafuffuka na 23-29.

^ sakin layi na 14 Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Fabrairu, 1954, shafi na 123.

^ sakin layi na 15 Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Agusta, 2011, shafuffuka na 20-21.

^ sakin layi na 58 BAYANI A KAN HOTO: So rayuwarmu ta kasance yadda take a dā, da riƙe mutum a zuciya, da kuma yawan baƙin ciki don kuskurenmu, suna nan kamar kaya mai nauyi da muke ɗauke da shi da zai iya hana mu yin tafiya a hanyar rai.

^ sakin layi na 65 BAYANI A KAN HOTO: Idan muka daina jin hakan, za mu yi farin ciki kuma mu sami ƙarfi. Hakan zai sa mu iya mai da hankali ga nan gaba.