Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 45

Yadda Za Mu Taimaka wa Mutane Su Bi Umurnan Kristi

Yadda Za Mu Taimaka wa Mutane Su Bi Umurnan Kristi

“Ku je ku sa . . . su zama almajiraina . . . , ku kuma koya musu su yi biyayya da dukan abubuwan da na umarce ku.”​—MAT. 28:​19, 20.

WAƘA TA 89 Mu Ji, Mu Yi Biyayya Don Mu Sami Albarka

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Kamar yadda aka nuna a Matiyu 28:​18-20, wane umurni ne Yesu ya bayar?

DA AKA ta da Yesu daga mutuwa, ya bayyana ga mabiyansa da suka taru a Galili. Yana da wani abu mai muhimmanci da yake so ya gaya musu. Wane abu ke nan? Abin da ya faɗa yana cikin Matiyu 28:​18-20.​—Karanta.

2. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

2 Umurnin da Yesu ya ba da ya shafi bayin Jehobah a yau. Saboda haka, za mu tattauna tambayoyi uku da suke da alaƙa da aikin da Yesu ya ba mu. Na farko, me kuma ya kamata mu yi ban da koya wa mutane abin da Allah yake bukata a gare mu? Na biyu, ta yaya dukan masu shela a ikilisiya za su taimaka wa ɗalibai su sami ci gaba? Na uku, ta yaya za mu taimaka wa ’yan’uwa da suka daina yin wa’azi da halartan taro su soma yin hakan?

KA KOYA MUSU SU BI UMURNIN YESU

3. Wane abu mai muhimmanci ne Yesu ya faɗa a umurninsa?

3 Umurnan Yesu na da sauƙin fahimta. Wajibi ne mu koya wa mutane umurnan. Amma bai kamata mu mance da wani batu mai muhimmanci ba. Yesu bai ce: ‘Ku koya musu dukan abubuwan da na umurce ku’ ba. Maimakon haka, ya ce: ‘Ku koya musu su yi biyayya da dukan abubuwan da na umarce ku.’ Don mu bi umurnin Yesu, muna bukatar mu koya wa ɗalibinmu abin da zai yi da kuma yadda zai yi hakan. (A. M. 8:31) Me ya sa?

4. Wane misali ne ya nuna yadda za mu koya wa wani ya bi umurnin Yesu?

4 Ta yaya za mu koya wa mutum ya yi “biyayya” da umurnin Yesu? Misali na gaba zai taimaka mana mu fahimci abin da muke bukatar mu yi. Ta yaya direba zai koya wa mutumin da ke koyon tuƙi yadda zai bi dokokin hanya? Zai fara koya masa dokokin hanya a makaranta. Amma ba dukan abin da yake bukatar ya yi ke nan ba. Ya kamata malamin ya kasance cikin mota da ɗalibin sa’ad da yake tuƙi don ya riƙa nuna masa yadda ake bin dokokin hanya kuma ɗalibin ya yi amfani da abin da yake koya. Mene ne muka koya daga wannan misalin?

5. (a) Kamar yadda Yohanna 14:15 da 1 Yohanna 2:3 suka nuna, mene ne muke bukatar mu koya wa ɗalibanmu? (b) Ka ba da misalan yadda za mu iya yi wa ɗalibanmu ja-goranci.

5 Muna koya wa mutane abin da Allah yake bukata a gare mu sa’ad da muke yin nazari da su. Me kuma muke bukatar mu yi? Muna bukatar mu koya wa ɗalibanmu su yi amfani da abin da suke koya. (Karanta Yohanna 14:15; 1 Yohanna 2:3.) Ta ayyukanmu, za mu iya nuna wa ɗalibanmu yadda za su riƙa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a makaranta da wajen aiki da kuma sa’ad da suke shaƙatawa. Muna iya ba da labarin yadda bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki suka kāre mu ko kuma yadda suka taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau. Sa’ad da muke tare da ɗalibanmu, muna iya yin addu’a cewa Jehobah ya yi musu ja-goranci da ruhunsa.​—Yoh. 16:13.

6. Mene ne koya wa mutane su bi umurnin Yesu ya ƙunsa?

6 Mene ne koya wa mutane su bi umurnin Yesu ya ƙunsa? Muna bukatar mu taimaka wa ɗalibanmu su so yin wa’azi. Wasu ɗalibai suna iya jin tsoron yin wa’azi. Muna bukatar mu riƙa haƙuri da su sa’ad da muke taimaka musu su fahimci koyarwar Littafi Mai Tsarki sosai kuma su ƙarfafa bangaskiyarsu. Hakan zai ratsa zuciyarsu kuma ya motsa su su yi wa’azi. Me kuma muke bukatar mu yi don mu taimaka wa ɗalibanmu su so yi wa mutane wa’azi?

7. Ta yaya za mu taimaka wa ɗalibinmu ya so yin wa’azi?

7 Muna iya yi wa ɗalibinmu waɗannan tambayoyin: “Ta yaya bin koyarwar Littafi Mai Tsarki ya kyautata rayuwarka? Kana ganin yi wa mutane wa’azi yana da muhimmanci? Mene ne za ka iya yi don ka taimaka musu?” (K. Mag. 3:27; Mat. 9:​37, 38) Ka nuna wa ɗalibin warƙoƙi da ke cikin Kayan Aiki don Koyarwa domin ya zaɓi waɗanda yake ganin danginsa da abokansa ko kuma abokan aikinsa za su so. * Ka ba ɗalibin waɗannan warƙoƙin. Ka koya masa yadda zai ba mutane warƙa. Sa’ad da ɗalibin ya zama mai shela da bai yi baftisma ba, ya kamata mu fita wa’azi da shi don mu taimaka masa.​—M. Wa. 4:​9, 10; Luk. 6:40.

YADDA ’YAN’UWA A IKILISIYA ZA SU TAIMAIKA WA ƊALIBAI

8. Me ya sa yake da muhimmanci ɗalibanmu su ƙaunaci Allah da maƙwabtansu sosai? (Ka kuma duba akwatin nan “ Yadda Za Mu Taimaki Ɗalibanmu Su Ƙaunaci Allah Sosai.”)

8 Ka tuna cewa Yesu ya gaya mana mu koya wa mutane ‘su yi biyayya da dukan abubuwan’ da ya umurce mu. Hakan ya ƙunshi umurnai biyu mafi muhimmanci, kuma dukansu suna da alaƙa sosai da yin wa’azi da kuma almajirtarwa. (Mat. 22:​37-39) Wace alaƙa ke nan? Abu na musamman da ke sa mu yi wa’azi shi ne ƙaunarmu ga Allah da kuma maƙwabtanmu. Babu shakka, wasu ɗalibai suna jin tsoron yin wa’azi. Amma za mu iya tabbatar musu da cewa Jehobah zai taimaka musu su daina jin tsoron mutane. (Zab. 18:​1-3; K. Mag. 29:25) A akwatin da ke wannan talifin, an nuna matakan da za mu iya ɗauka don mu taimaka wa ɗalibinmu ya ƙaunaci Allah sosai. Ƙari ga haka, an nuna abin da ’yan’uwa a ikilisiya za su iya yi don su taimaki ɗalibai su ci gaba da nuna ƙauna.

9. A misalin da aka bayar, ta yaya ɗalibin yake koyon abubuwa masu muhimmanci?

9 Ka sake tunani game da misalin direba da ɗalibinsa. Sa’ad da ɗalibin yake tuƙi kuma malaminsa yana tare da shi, ta yaya hakan yake taimaka masa? Ɗalibin zai amfana idan ya saurari malaminsa, kuma ya lura da abin da wasu direbobi da suka ƙware suke yi. Alal misali, malamin zai iya nuna masa wani direba da ya haƙura ya bar wani direba ya shiga gabansa. Ko kuma ya nuna wa ɗalibin wani direba da ya rage hasken fitilar motarsa don kada ya kashe wa sauran direbobin ido. Irin waɗannan misalan suna koya wa ɗalibin abin da zai yi sa’ad da yake tuƙi.

10. Mene ne zai iya taimaka wa ɗalibi ya soma bauta wa Jehobah?

10 Hakazalika, ɗalibin Littafi Mai Tsarki da ya soma bauta wa Jehobah yana bukatar ya koya daga malaminsa da kuma bayin Jehobah masu aminci. Saboda haka, me zai taimaka wa ɗalibin Littafi Mai Tsarki sosai ya samu ci gaba? Halartan taronmu zai taimaka masa. Me ya sa? Domin abin da ɗalibin ya ji a taron ikilisiya zai sa ya ƙara koya game da Jehobah kuma ya ƙarfafa bangaskiyarsa. Ban da haka, zai ƙara ƙaunar Allah sosai. (A. M. 15:​30-32) Ƙari ga haka, malamin yana iya sa ɗalibin ya haɗu da ’yan’uwa da suka fuskanci irin matsalolin da yake fuskanta. Babu shakka, ɗalibin zai ga yadda ’yan’uwa suke nuna ƙauna a ikilisiya. Ka yi la’akari da misalan nan.

11. Mene ne ɗalibinmu zai iya lura a ikilisiya, kuma yaya hakan zai shafe shi?

11 Wata ɗaliba da take renon yaranta ita kaɗai ta ga wata ’yar’uwa da ke cikin irin yanayinta. Yadda ’yar’uwar take kawo yaranta ƙanana taro a Majami’ar Mulki ita kaɗai ya ratsa zuciyar ɗalibar. Wani ɗalibi da yake fama ya daina shan sigari ya haɗu da wani mai shela da a dā, ya yi fama ya daina shan sigari. Sai mai shelan ya gaya wa ɗalibin yadda ƙaunarsa ga Jehobah ta sa ya bi umurnin Jehobah. (2 Kor. 7:1; 2 Kor. 4:7) Bayan ɗan’uwan ya gaya wa ɗalibin yadda ya daina shan sigari, sai ɗan’uwan ya ce: “Kai ma za ka iya daina shan sigari.” Hakan ya sa ɗalibin ya kasance da tabbaci cewa shi ma zai iya yin nasara. Wata matashiya da take nazarin Littafi Mai Tsarki ta lura cewa wata ’yar’uwa tana yawan farin ciki. Abin da matashiyar ta lura ya motsa ta ta so sanin abin da ke sa ’yar’uwar farin ciki a kowane lokaci.

12. Me ya sa muka ce kowa a ikilisiya zai iya taimaka wa ɗalibai?

12 Idan ɗalibi ya san masu shela dabam-dabam, zai koyi ma’anar bin umurnin nan na Yesu cewa a ƙaunaci Allah da kuma maƙwabta. (Yoh. 13:35; 1 Tim. 4:12) Amma, kamar yadda aka ambata ɗazu, ɗalibi zai iya koyan abubuwa daga ’yan’uwa da suka shawo kan irin matsalolin da ɗalibin yake ciki. Hakan zai taimaka wa ɗalibin ya san cewa shi ma zai ya yin canje-canjen da yake bukatar ya yi don ya zama mabiyin Yesu. (M. Sha. 30:11) Kowa a cikin ikilisiya zai iya taimaka wa ɗalibi ya sami ci gaba. (Mat. 5:16) Mene ne kake yi don ka ƙarfafa ɗalibai da suke halartan taro?

KA TAIMAKA WA WAƊANDA SUKA DAINA WA’AZI SU SOMA HAKAN

13-14. Yaya Yesu ya bi da manzanninsa da suka yi sanyin gwiwa?

13 Ya kamata mu taimaka wa ’yan’uwa da suka daina bin umurnin Yesu na yin wa’azi su soma hakan kuma. Yadda Yesu ya bi da manzanninsa da suka karaya ya taimaka mana mu san abin da za mu iya yi a yau.

14 Sa’ad da Yesu ya kusan mutuwa, “dukan almajiran suka bar shi, suka gudu.” (Mar. 14:50; Yoh. 16:32) Mene ne Yesu ya yi a wannan lokacin da manzaninsa suka yi sanyin gwiwa? Ba da daɗewa ba bayan Yesu ya tashi daga matattu, ya gaya wa wasu cikin mabiyansa cewa: “Kada ku ji tsoro, ku je ku faɗa wa ’yan’uwana [an ta da ni daga matattu].” (Mat. 28:10a) Yesu bai yasar da manzaninsa ba. Duk da cewa sun gudu sun bar shi, ya kira su “ ’yan’uwana.” Hakan ya nuna cewa Yesu yana gafarta wa mutane kuma yana nuna jin ƙai kamar Jehobah.​—2 Sar. 13:23.

15. Yaya muke ɗaukan waɗanda suka daina yin wa’azi da halartan taro?

15 Hakazalika, mun damu da waɗanda suka daina yin wa’azi da halartan taro. Su ’yan’uwanmu ne, kuma muna ƙaunar su! Har ila, muna tuna da ƙwazo da waɗannan ’yan’uwan suka nuna a dā a hidimarsu ga Jehobah. Wasu cikinsu sun yi shekaru da yawa suna yin hakan. (Ibran. 6:10) Muna kewarsu sosai! (Luk. 15:​4-7) Ta yaya za mu iya yin koyi da Yesu kuma mu nuna cewa mun damu da su?

16. Ta yaya za mu nuna cewa mun damu da ’yan’uwa da suka daina yin wa’azi da zuwa taro?

16 Ka gayyace su zuwa taro. Hanya ɗaya da Yesu ya ƙarfafa manzanninsa da suka yi sanyin gwiwa ita ce ta wajen gayyatar su zuwa taro. (Mat. 28:10b; 1 Kor. 15:6) Hakazalika a yau, za mu iya ƙarfafa waɗanda suka daina halartan taro da yin wa’azi su soma halartar taro. Mun san cewa muna bukatar mu yi hakan sau da yawa kafin su halarci taro. Babu shakka Yesu ya yi farin ciki sa’ad da mabiyansa suka amince da gayyatarsa.​—Gwada Matiyu 28:16 da Luka 15:6.

17. Me ya kamata mu yi sa’ad da wani da ya daina halartan taro ya soma halarta?

17 Ka marabce su sosai. Yesu ne ya je ya sami almajiransa kuma ya yi magana da su, bai jira su zo su same shi ba. (Mat. 28:18) Mene ne za mu yi sa’ad da wani da ya daina halartan taro ya yi hakan? Ya kamata mu marabce shi da hannu biyu-biyu. Da farko, muna iya ji cewa ba mu san abin da za mu faɗa ba. Ba tare da kunyantar da shi ba, muna iya gaya masa cewa muna farin cikin ganin sa.

18. Ta yaya za mu ƙarfafa waɗanda suka daina yin wa’azi da halartan taro?

18 Ka ƙarfafa su sosai. Wataƙila mabiyan Yesu suna ganin cewa ba za su iya yin wa’azi a dukan duniya ba. Amma Yesu ya tabbatar musu da cewa: “Ina tare da ku kullum.” (Mat. 28:20) Abin da Yesu ya yi ya taimaka wa mabiyansa kuwa? E. Ba da daɗewa ba, sun shagala da “koyarwa da ba da labari mai daɗi.” (A. M. 5:42) Waɗanda suka daina wa’azi suna bukatar a ƙarfafa su. Suna iya jin tsoron soma yin wa’azi. Amma muna iya tabbatar musu cewa ba za su yi wa’azi su kaɗai ba. Idan sun shirya, muna iya fita wa’azi tare da su. Za su yi farin ciki idan muka taimaka musu sa’ad da suka soma wa’azi. Idan muka bi da waɗanda suka daina yin wa’azi da halartan taro a matsayin ’yan’uwanmu, hakan zai sa su soma wa’azi, ya kuma sa dukan ’yan’uwa farin ciki.

YA KAMATA MU KAMMALA AIKIN DA YESU YA BA MU

19. Mene ne muke so mu yi, kuma me ya sa?

19 Har tsawon wane lokaci ne za mu ci gaba da wa’azi da almajirantarwa? Sai ƙarshen zamanin nan. (Mat. 28:20) Har sai lokacin, za mu ci gaba da wa’azi da kuma almajirtarwa. Kuma mun ƙuduri niyyar yin hakan! Muna farin cikin yin amfani da lokacinmu da kuzarinmu da kuma kuɗinmu don mu nemi “waɗanda suke da zuciya ta samun rai na har abada.” (A. M. 13:​48, New World Translation) Muna bin misalin Yesu sa’ad da muka yi hakan. Yesu ya ce: ‘Abincina shi ne in yi nufin wanda ya aiko ni, in kuma gama aikinsa.’ (Yoh. 4:34; 17:4) Abin da muke so mu yi ke nan. Muna so mu kammala aikin da aka ba mu. (Yoh. 20:21) Kuma muna so kowa, har da waɗanda suka daina yin wa’azi da halartan taro su yi wannan aikin tare da mu.​—Mat. 24:13.

20. Kamar yadda 2 Korintiyawa 4:7 ta nuna, me ya sa za mu iya cim ma aikin da Yesu ya ba mu?

20 Yin gagarumin aikin da Yesu ya ba mu ba shi da sauƙi. Amma, ba mu kaɗai ba ne muke yin wannan aikin ba. Yesu ya yi alkawari cewa zai kasance tare da mu. Muna almajirtarwa a matsayinmu na “abokan aiki na Allah” da kuma Yesu. (1 Kor. 3:9; 2 Kor. 2:17) Saboda haka, za mu iya cim ma wannan aikin. Muna farin ciki cewa muna da damar yin wannan aikin da kuma taimaka wa mutane su yi hakan!​—Karanta 2 Korintiyawa 4:7.

WAƘA TA 79 Mu Koya Musu Su Kasance da Aminci

^ sakin layi na 5 Yesu ya gaya wa mabiyansa su almajirantar da mutane kuma su koya musu su yi biyayya da dukan abubuwan da ya umurce su. A wannan talifin, za a tattauna yadda za mu iya bin umurnin Yesu. An ɗauko wasu abubuwan da aka tattauna a talifin nan daga Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuli, 2004, shafuffuka na 20-24..

^ sakin layi na 7 Abin da aka tattauna a wannan talifin ya shafi maza da mata.

^ sakin layi na 67 BAYANI A KAN HOTO: ’Yar’uwa da take gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da ɗalibarta ta bayyana mata yadda za ta ƙarfafa dangantakarta da Jehobah. Daga baya, ɗalibar ta bi shawarwari uku da ’yar’uwa ta ba ta.