Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 45

Ku Ci-gaba da Nuna wa Juna Ƙauna Marar Canjawa

Ku Ci-gaba da Nuna wa Juna Ƙauna Marar Canjawa

“Ku nuna wa juna ƙauna marar canjawa da jinƙai.”​—ZAK. 7:9.

WAƘA TA 107 Mu Yi Koyi da Allah a Nuna Ƙauna

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Waɗanne dalilai masu kyau ne muke da su na nuna ƙauna marar canjawa?

AKWAI dalilai da yawa da suka sa ya kamata mu nuna wa juna ƙauna marar canjawa. Waɗanne dalilai ke nan? Ka yi la’akari da yadda waɗannan karin magana daga Littafi Mai Tsarki suka ba da amsar: “Kada ka bar ƙauna da aminci su rabu da kai. . . . Ta haka za ka sami farin jini da alheri, a gaban Allah da kuma a gaban mutum.” “Mutumin kirki yakan sami ladan kirkinsa.” “Duk wanda ya nemi adalci da ƙauna, zai sami rai a yalwace.”​—K. Mag. 3:​3, 4; 11:17; 21:21. *

2 Ayoyin nan sun ambata dalilai uku da suka sa ya kamata mu nuna ƙauna marar canjawa. Na farko, nuna ƙauna marar canjawa zai sai mu kasance da daraja a idon Jehobah. Na biyu, idan muka nuna ƙauna marar canjawa za mu amfana. Alal misali, za mu ƙulla abokantaka da wasu. Na uku, za mu sami albarku da yawa har da rai na har abada. Babu shakka, muna da dalilai masu kyau na bin wannan umurnin cewa: “Ku nuna alheri [ƙauna marar canjawa] da tausayi ga junanku.”​—Zak. 7:9.

3. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 A wannan talifin, za mu tattauna amsoshin tambayoyi huɗu. Waye ne ya kamata mu nuna wa ƙauna marar canjawa? Me za mu iya koya daga littafin Rut game da nuna ƙauna marar canjawa? Ta yaya za mu iya nuna irin ƙaunar nan a yau? Ta yaya waɗanda suke nuna ƙauna marar canjawa suke amfana?

WAYE NE YA KAMATA MU NUNA WA ƘAUNA MARAR CANJAWA?

4. Ta yaya za mu iya nuna ƙauna marar canjawa kamar Jehobah? (Markus 10:​29, 30)

4 A talifin da ya gabata, mun koyi cewa Jehobah yana nuna ƙauna marar canjawa ga waɗanda suke ƙaunar sa kuma suke bauta masa. (Dan. 9:4) A matsayin “ ’ya’ya waɗanda Allah yake ƙauna,” ya kamata mu “ɗauki misali daga wurin Allah.” (Afis. 5:1) Saboda haka, ya kamata mu riƙa nuna wa ’yan’uwanmu ƙauna marar canjawa.​—Karanta Markus 10:​29, 30.

5-6. Me kalmar nan aminci take nufi?

5 Yayin da muke daɗa sanin abin da ake nufi da ƙauna marar canjawa, za mu daɗa sanin yadda za mu riƙa nuna irin wannan ƙaunar ga ’yan’uwanmu. Don mu daɗa fahimtar abin da ƙauna marar canjawa take nufi, bari mu ga bambancin da ke tsakanin ta da aminci. Ga wani misali.

 6 A yau, idan mutum ya daɗe yana yi ma wani kamfani aiki, za a iya ce da shi ma’aikaci mai aminci. Amma, mai yiwuwa a duk shekarun da ya yi yana aikin, bai taɓa haɗuwa da masu kamfanin ba. Wataƙila ba ya son sharuɗan kamfanin ko kuma kamfanin da kansa ba. Amma yana son albashin da ake ba shi. Saboda haka, zai ci gaba da yin aikin har sai ya yi ritaya, ko kuma ya sami aikin da ya fi wannan.

7-8. (a) Me yake sa mutum ya nuna ƙauna marar canjawa? (b) Me ya sa za mu tattauna wasu ayoyi a littafin Rut?

7 Don haka, bambancin da ke tsakanin aminci da ƙauna marar canjawa kamar yadda  sakin layi na 6 ya nuna shi ne dalilin da ya sa mutum yake nuna su. A Littafi Mai Tsarki, me ya sa bayin Allah suka nuna ƙauna marar canjawa? Waɗanda suka nuna ƙauna marar canjawa ba su yi hakan don an sa su dole ba ne, amma da son ransu suka yi. Ka yi la’akari da misalin Dauda. Zuciyarsa ta motsa shi ya nuna wa Jonatan ƙauna marar canjawa, duk da cewa mahaifin Jonatan ya so ya kashe shi. Shekaru da yawa bayan Jonatan ya mutu, Dauda ya ci gaba da nuna ƙauna marar canjawa ga ɗan Jonatan Mefiboshet.​—1 Sam. 20:​9, 14, 15; 2 Sam. 4:4; 8:15; 9:​1, 6, 7.

8 Za mu iya koyan abubuwa da yawa game da ƙauna marar canjawa ta wajen nazarin wasu ayoyin da ke littafin Rut. Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga mutanen da aka ambata a littafin? Ta yaya za mu yi amfani da darussan a ikilisiyarmu? *

ME ZA MU IYA KOYA A LITTAFIN RUT GAME DA NUNA ƘAUNA MARAR CANJAWA?

9. Me ya sa Naomi ta ɗauka cewa Jehobah ne ya jawo mata matsaloli?

9 Littafin Rut yana ɗauke da labarin Naomi, da surukuwarta Rut, da kuma wani mutum mai suna Bowaz, dangin mijin Naomi. Domin rashin abinci, Naomi da mijinta da kuma ’ya’yansu maza biyu sun bar ƙasar Isra’ila suka je Mowab. A wurin, mijin Naomi ya mutu. ’Ya’yanta biyun sun yi aure, amma daga baya su ma suka mutu. (Rut 1:​3-5; 2:1) Hakan ya sa Naomi ta yi sanyin gwiwa sosai har ta soma tunanin cewa Jehobah ne yake jawo mata matsalolin. Ka lura da abin da ta faɗa game da Allah, ta ce: “Yahweh ne ya jawo mini wahalar nan.” “Mai Iko Duka ya sa rayuwata ta zama da ɗaci.” Ta kuma ce: “Yahweh ya sa na sha wahala, kuma Mai Iko Duka ne ya yi mini wannan masifa.”​—Rut 1:​13, 20, 21.

10. Mene ne Jehobah ya yi domin abin da Naomi ta faɗa?

10 Mene ne Jehobah ya yi don abin da Naomi ta faɗa? Bai daina taimakon ta ba, a maimakon haka, ya ji tausayin ta. Ya san cewa “zalumci yakan maida mai-hikima wawa.” (M. Wa. 7:​7, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Duk da haka, Naomi ta bukaci taimako don ta gane cewa Allah yana tare da ita. Ta yaya Allah ya taimake ta? (1 Sam. 2:8) Ya sa Rut ta nuna wa Naomi ƙauna marar canjawa. Da son ranta, Rut ta taimaka mata ta daina sanyin gwiwa, kuma ta san cewa Jehobah yana ƙaunar ta. Mene ne misalin Rut ya koya mana?

11. Me ya sa ’yan’uwa masu alheri suke ƙoƙarin su taimaka ma waɗanda suka yi sanyin gwiwa?

11Ƙauna marar canjawa tana sa mu taimaka ma waɗanda suka yi sanyin gwiwa. Kamar yadda Rut ta manne wa Naomi, ’yan’uwa a ikilisiya ma suna taimaka ma waɗanda suka yi sanyin gwiwa. Suna ƙaunar ’yan’uwansu sosai kuma suna so su yi iya ƙoƙarinsu don su taimaka musu. (K. Mag. 12:25; 24:10) Hakan ya jitu da umurnin da Manzo Bulus ya bayar cewa: “Ku ƙarfafa waɗanda ba su da ƙarfin zuciya, ku taimaki marasa ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa.”​—1 Tas. 5:14.

Idan muna saurarar ’yan’uwa da suka yi sanyin gwiwa, hakan zai iya ƙarfafa su (Ka duba sakin layi na 12)

12. A yawancin lokuta, wace hanya ce mafi kyau na taimaka ma ’yan’uwa da suka yi sanyin gwiwa?

12 A yawancin lokuta, hanya mafi kyau da za ka iya taimaka ma wanda ya yi sanyin gwiwa ita ce ta wurin saurarar sa, da kuma tabbatar masa cewa kana ƙaunar shi. Jehobah yana farin ciki yayin da yake ganin yadda kake ƙoƙari ka taimaki bayinsa masu aminci. (Zab. 41:1) Littafin Karin Magana 19:17 ta ce: “Mai yi wa . . . talaka kirki, kamar ya ba Yahweh rance ne, Yahweh kuwa zai sāka masa.”

Rut ta manne wa Naomi surukuwarta, amma Orfa ta koma ƙasar Mowab. Rut ta gaya wa Naomi cewa: “Duk inda kika tafi, nan zan tafi” (Ka duba sakin layi na 13)

13. Ta yaya Rut ta yi dabam da Orfa, kuma ta yaya ta nuna ƙauna marar canjawa? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)

13 Yin tunani a kan abin da ya faru da Naomi bayan maigidanta da ’ya’yanta biyu suka mutu zai taimaka mana mu daɗa fahimtar yadda za mu nuna ƙauna marar canjawa. Da ta ji cewa Jehobah ya juya hankalinsa ga mutanensa, kuma “ya ba su abinci mai yawa,” sai ta yanke shawarar komawa gida. (Rut 1:6) Matan yaranta sun soma tafiyar tare da ita. Amma da suke tafiyar, Naomi ta gaya wa matan su koma Mowab. Me suka yi? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Orfa ta sumbaci mamar mijinta ta yi mata ban kwana, amma Rut ta manne mata.” (Rut 1:​7-14) Orfa ta yi abin da Naomi ta gaya mata ta yi kuma ta koma Mowab. Amma Rut ta ƙi yin abin da Naomi ta faɗa. Da a ce ta so, da ta koma gida, amma saboda tana ƙaunar ta, ta yanke shawarar manne wa Naomi don ta taimaka mata. (Rut 1:​16, 17) Rut ta manne wa Naomi ba don an tilasta mata ba, amma da son ranta. Rut ta nuna ƙauna marar canjawa. Wane darasi ne za mu iya koya daga wannan labarin?

14. (a) A yau, mene ne ’yan’uwa da suke ƙaunar juna suke yi? (b) Kamar yadda Ibraniyawa 13:16 ta nuna, wace irin sadaukarwa ce take sa Jehobah farin ciki?

14Idan muna da ƙauna marar canjawa, za mu yi iya ƙoƙarinmu mu taimaki mutane. A yau ma, ’yan’uwanmu suna nuna ƙauna marar canjawa ga junansu har da waɗanda ba su taɓa gani ba. Alal misali, a duk lokacin da suka ji cewa bala’i ya auko, suna yin iya ƙoƙarinsu su taimaka. Idan suka ji cewa wani ɗan’uwa yana da bukata, nan da nan za su yi ƙoƙari su san bukatarsa, kuma su taimaka masa a hanyoyin da suka dace. Kamar yadda ’yan’uwa suka yi a Makidoniya a ƙarni na farko, ’yan’uwa a yau suna yin fiye da abin da ake bukata su yi. Suna sadaukarwa don su bayar fiye da abin da suke da shi don su taimaka ma ’yan’uwansu mabukata. (2 Kor. 8:3) Hakika, hakan yana sa Jehobah farin ciki sosai!​—Karanta Ibraniyawa 13:16.

TA YAYA ZA MU IYA NUNA IRIN ƘAUNAR NAN A YAU?

15-16. Ta yaya Rut ta nuna cewa ba za ta daina taimaka wa Naomi ba?

15 Za mu iya koyan darussa da yawa daga yin nazarin yadda Rut ta taimaka wa Naomi. Bari mu tattauna wasu daga cikin darussan.

16Kar ka gaji. A lokacin da Rut ta ce za ta bi surukuwarta zuwa Yahudiya, da farko Naomi ta ƙi. Amma Rut ta nace. Wane sakamako ne hakan ya jawo? “Da Na’omi ta gane Rut tana da niyya ta bi ta, sai ta daina ce wa Rut ta koma.”​—Rut 1:​15-18.

17. Me zai taimaka mana kar mu gaji da yin ƙoƙari mu taimaka ma ’yan’uwanmu?

17Darasi: Sai da haƙuri ne za mu iya taimaka ma waɗanda suka yi sanyin gwiwa, amma kada mu gaji da taimaka musu. Da farko, wata ’yar’uwa da take bukatar taimako, za ta iya ƙi mu taimaka mata. * Duk da haka, ƙauna marar canjawa za ta sa mu nace. (Gal. 6:2) Muna fata a ƙarshe za ta amince da taimakonmu kuma ta sami ƙarfafa.

18. Mene ne wataƙila ya sa Rut baƙin ciki?

18Kada ka yi fushi. Sa’ad da Rut da Naomi suka isa Bai’talami, Naomi ta haɗu da maƙwabtanta na dā. Sai ta gaya musu cewa: “Na bar nan cike da kome, amma ga shi Yahweh ya dawo da ni hannu wofi.” (Rut 1:21) Ka yi tunanin yadda Rut ta ji sa’ad da ta ji abin da Naomi ta faɗa! Rut ta riga ta yi iya ƙoƙarinta don ta taimaka ma Naomi. Ta riga ta yi kuka tare da ita, ta ƙarfafa ta, kuma ta yi tafiya na kwanaki da yawa tare da ita. Duk da haka, Naomi ta ce: “Yahweh ya dawo da ni hannu wofi.” Ko da yake Rut tana tsaye a wurin lokacin da Naomi take maganar, abin da ta faɗa ya yi kamar ba ta ma damu da taimakon da Rut ta yi mata ba. Mai yiwuwa, hakan ya sa Rut baƙin ciki! Duk da haka, ta manne wa Naomi.

19. Mene ne zai taimaka mana mu manne ma wadda take baƙin ciki?

19Darasi: A yau, ’yar’uwar da take cikin matsala za ta iya yi mana magana da ɓacin rai duk da cewa mun yi iya ƙoƙarinmu don mu taimaka mata. Amma ba za mu bar hakan ya sa mu fushi ba. Za mu manne ma ’yar’uwarmu da take da bukata kuma mu roƙi Jehobah ya taimaka mana mu san yadda za mu ƙarfafa ta.​—K. Mag. 17:17.

Ta yaya dattawa za su iya bin misalin Bowaz? (Ka duba sakin layi na 20-21)

20. Mene ne ya taimaka wa Rut ta ci gaba da taimakon Naomi?

20Ka ƙarfafa ’yan’uwa a lokacin da ya dace. Rut ta nuna wa Naomi ƙauna marar canjawa, amma daga baya ita ma ta bukaci ƙarfafa. Sai Jehobah ya sa Bowaz ya ƙarfafa ta. Bowaz ya gaya wa Rut cewa: “Bari Yahweh ya ba ki lada saboda abin da kika yi. Bari Ubangiji Allahn Isra’ila wanda kika zo wurinsa neman mafaka ya ba ki cikakken lada.” Waɗannan kalmomi masu daɗin ji sun ratsa zuciyar Rut sosai. Sai ta ce wa Bowaz: “Ka yi wa baiwarka magana mai ƙarfafa zuciya.” (Rut 2:​12, 13) Bowaz ya ƙarfafa Rut a lokacin da take bukatar ƙarfafa kuma hakan ya sa ta ci gaba da taimaka wa Naomi.

21. Kamar yadda Ishaya 32: 1, 2 suka nuna, mene ne dattawa da suka damu da ’yan’uwa suke yi?

21Darasi: Waɗanda suke nuna wa ’yan’uwa ƙauna marar canjawa, su ma suna bukatar ƙarfafa a wasu lokuta. Kamar yadda Bowaz ya tabbatar wa Rut cewa Jehobah yana lura da yadda take nuna alheri, a yau ma, dattawa suna yaba ma waɗanda suke taimaka wa ’yan’uwa a ikilisiya. Irin wannan ƙarfafar zai sa ’yan’uwa ba za su gaji da ba da taimako ba.​—Karanta Ishaya 32:​1, 2.

TA YAYA WAƊANDA SUKE NUNA ƘAUNA MARAR CANJAWA SUKE AMFANA?

22-23. Ta yaya Naomi ta canja ra’ayinta, kuma me ya sa? (Zabura 136:​23, 26)

22 Bayan wani lokaci, Bowaz ya ba Rut da Naomi abinci da yawa kyauta. (Rut 2:​14-18) Mene ne Naomi ta yi da ta sami abincin? Ta ce: “Bari Yahweh ya albarkace shi. Yahweh bai daina nuna alherinsa ga masu rai da matattu ba.” (Rut 2:20a) Hakika, Naomi ta canja ra’ayinta! A dā, Naomi da hawaye ta ce: “Yahweh ya sa na sha wahala,” amma yanzu da farin ciki ta ce: “Yahweh bai daina nuna alherinsa . . . ba.” Me ya sa Naomi ta canja ra’ayinta?

23 Naomi ta soma ganin yadda Jehobah yake taimaka mata. Ta gano cewa Jehobah ne ya yi amfani da Rut don ya taimake ta yayin da take komawa Yahudiya. (Rut 1:16) Ƙari ga haka, Naomi ta gano cewa Jehobah ne ya yi amfani da Bowaz don ya taimaka mata da Rut. (Rut 2:​19, 20b) Mai yiwuwa ta gaya wa kanta cewa: ‘Ashe Jehobah bai bar ni ba. Yana tare da ni a duk wahalar da na sha!’ (Karanta Zabura 136:​23, 26.) Naomi ta yi farin ciki cewa Rut da Bowaz ba su gaji da ita ba! Dukansu sun yi murna sa’ad da Naomi ta soma farin ciki a ibadarta.

24. Me ya sa muke bukatar mu ci gaba da nuna wa ’yan’uwa ƙauna marar canjawa?

24 Wane darasi ne muka koya daga littafin Rut game da ƙauna marar canjawa? Ƙauna marar canjawa tana sa kada mu gaji da taimaka wa ’yan’uwanmu da suke baƙin ciki. Ƙari ga haka, tana sa mu yi iya ƙoƙarinmu don mu taimaka musu. Dattawa suna bukatar su riƙa ƙarfafa waɗanda suke nuna wa ’yan’uwansu ƙauna marar canjawa. Ganin yadda ’yan’uwan da ke baƙin ciki suke samun ƙarfafa yana sa mu farin ciki. (A. M. 20:35) Amma wane dalili mafi muhimmanci ne yake sa mu nuna ƙauna marar canjawa? Dalilin shi ne, muna so mu bi misalin Jehobah kuma mu faranta masa rai da yake shi “mai yawan ƙauna marar canjawa” ne.​—Fit. 34:6; Zab. 33:22.

WAƘA TA 130 Mu Riƙa Gafartawa

^ sakin layi na 5 Jehobah yana so mu nuna wa ’yan’uwanmu ƙauna marar canjawa. Za mu daɗa fahimtar abin da ƙauna marar canjawa take nufi ta wajen bincika yadda bayin Allah a dā suka nuna wannan halin. A wannan talifin, za mu tattauna abin da za mu iya koya daga misalin Rut da Naomi da kuma Bowaz.

^ sakin layi na 1 Kalmomin nan “kirki” da kuma “ƙauna” a nassosin nan suna nufin “ƙauna marar canjawa” ne a asalin yaren da aka rubuta Littafi Mai Tsarki.

^ sakin layi na 8 Don ka amfana sosai daga talifin nan, muna ƙarfafa ka ka karanta littafin Rut sura 1 da 2.

^ sakin layi na 17 Da yake muna tattauna misalin Naomi ne, mukan yi magana game da ’yan’uwa mata da suke da bukata. Amma abin da aka tattauna a talifin nan ya shafi ’yan’uwa maza ma.