HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Oktoba 2016

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 28 ga Nuwamba zuwa 25 ga Disamba, 2016.

TARIHI

Na Yi Kokarin Bin Misalai Masu Kyau

Idan kiristocin da suka manyanta suka karfafa wasu, hakan zai taimaka musu su kafa makasudai masu kyau. Thomas McLain ya ba da labarin yadda misalan wasu ya taimaka masa da kuma yadda shi ma ya taimaka wa wasu.

“Kada Ku Daina Yi wa Baki Alheri”

Ta yaya Allah yake daukan baki? Mene ne za ka iya yi don ka taimaka wa wadanda suka fito daga wata kasa su saki jiki a cikin ikilisiya?

Ku Karfafa Abotarku da Jehobah Sa’ad da Kuke Hidima a Inda Ake Wani Yare

Ya kamata mu kāre dangantakarmu da na iyalinmu da Jehobah. Haka shi ne abu mafi muhimanci ga dukan Kiristoci. Amma idan kana wa’azi a inda ake wani yare za ka fuskanci matsalar yin hakan.

Kai Mai Hikima Ne?

Mene ne bambancin da ke sakanin hikima da ilimi da kuma fahimi? Sanin bambancin zai amfane mu sosai.

Ka Karfafa Bangaskiyarka a Kan Abin da Kake Begensa

Za mu iya koyan darasi daga misalan mutanen dā da na yanzu da suka kasance da bangaskiya. Ta yaya za ka ci gaba da karfafa bangaskiyarka?

Ka Kasance da Tabbaci a Kan Alkawuran da Jehobah Ya Yi

Mene ne bangaskiya? Mafi muhimmanci kuma, ta yaya za ka nuna cewa kana da bangaskiya?

Ka Sani?

Wane ‘yanci ne Romawa suka ba wa Yahudawa a karni na farko? Da gaske ne cewa a zamanin dā wani zai iya shuka zawa a gonar wani?