Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Karfafa Bangaskiyarka a Kan Abin da Kake Begensa

Ka Karfafa Bangaskiyarka a Kan Abin da Kake Begensa

“Bangaskiya fa ainihin abin da muke begensa ne.”​—IBRAN. 11:1.

WAƘOƘI: 81, 134

1, 2. (a) Ta yaya begen da Kiristoci suke da shi ya bambanta da na wasu mutane? (b) Waɗanne tambayoyi masu muhimmanci ne za mu tattauna yanzu?

KIRISTOCI na gaskiya suna da abubuwa masu kyau da suke ɗokinsu. Ko da mu shafaffu ne ko kuma “waɗansu tumaki,” dukanmu muna sa ran ganin yadda Allah zai cika nufinsa ga ‘yan Adam da kuma yadda zai tsarkake sunansa. (Yoh. 10:16; Mat. 6:​9, 10) Waɗannan abubuwan ne suka fi muhimmanci a gare mu. Ƙari ga haka, muna ɗokin yin rayuwa har abada ko a “sababbin sammai” ko kuma a “sabuwar duniya.” (2 Bit. 3:13) Amma kafin wannan lokacin, muna ɗokin ganin yadda Jehobah zai ci gaba da yi wa mutanensa ja-gora da kuma tallafa musu a wannan kwanaki na ƙarshe.

2 Mutane da yawa a wannan duniyar suna da bege, amma ba su da tabbaci a kan abin da suke begensa. Alal misali, masu yin caca suna iya sa rai cewa za su ci cacan amma ba su da tabbacin hakan. Amma bangaskiya ta ainihi “abin da muke begensa ne.” Hakan yana nufin cewa waɗanda suke da bangaskiya sun tabbata cewa Jehobah zai cika alkawuransa. (Ibran. 11:⁠1) Amma, kana iya yin tunani, ta yaya za ka ƙara tabbata da wannan begen? Me ya sa ya kamata ka kasance da bangaskiya sosai a kan abin da kake begensa?

3. Me ya sa Kiristoci suke da tabbaci cewa Allah zai cika alkawuransa?

3 Ba a haifi dukanmu da bangaskiya ba, saboda haka, wajibi ne mu koyi kasancewa da wannan halin. Don mu iya yin hakan, muna bukatar mu bar ruhu mai tsarki ya yi mana ja-gora. (Gal. 5:22) Littafi Mai Tsarki bai ce Jehobah yana da bangaskiya ko kuma yana bukatar ya kasance da bangaskiya ba. Domin Jehobah shi ne Allah maɗaukaki, ba abin da zai hana shi cika nufinsa. Ubanmu na sama yana da tabbacin cewa zai cika alkawuransa shi ya sa a gare shi kamar ya riga ya cika su. Don haka ya ce waɗannan alƙawuran “sun tabbata!” (Karanta Ru’ya ta Yohanna 21:​3-6.) Wannan shi ne dalilin da ya sa Kiristoci suka tabbata cewa Jehobah “Allah mai-aminci” ne wanda yake cika alkawuransa.​—⁠K. Sha. 7:⁠9.

BAYIN ALLAH A DĀ DA SUKE DA BANGASKIYA SOSAI

4. Wane bege ne bayin Allah na dā suka kasance da shi?

4 Littafin Ibraniyawa sura 11 ta ambata sunayen mata da maza guda 16 da suke da bangaskiya sosai. Marubucin wannan littafin ya ce waɗannan mutanen da kuma wasu su ne waɗanda “aka ba da shaida a kansu ta wurin bangaskiyarsu.” (Ibran. 11:39) Dukansu sun tabbata cewa Allah zai kawo ‘zuriyar’ da aka ce zai ƙuje Shaiɗan kuma ya cika nufin Jehobah. (Far. 3:15) Waɗannan masu amincin sun mutu kafin Yesu Kristi, wato ‘zuriyar’ da aka ce zai zo ya sa mutane su soma kasancewa da begen yin rayuwa a sama. (Gal. 3:16) Amma, alkawarin da Jehobah ya yi zai sa a ta da su daga mutuwa kuma su soma rayuwa a cikin aljanna a duniya.​—⁠Zab. 37:11; Isha. 26:19; Hos. 13:⁠14.

5, 6. Mene ne Ibrahim da iyalinsa suke begen ganinsa, kuma ta yaya suka kasance da bangaskiya sosai? (Ka duba hoton da ke shafi na 21.)

5 Littafin Ibraniyawa 11:13 ta yi magana game da wasu daga cikin bayin Allah na dā cewa: “Dukan waɗannan suka mutu cikin bangaskiya, ba su rigaya sun amshi alkawarai ba, amma daga nesa suka tsinkaye su, suka yi masu maraba.” Ibrahim yana ɗaya daga cikin waɗannan mutanen. Shin ya kasance da begen yin rayuwa a lokacin da wannan ‘zuriyar’ yake sarauta ne? Yesu ya ba da amsar wannan tambayar sa’ad da ya gaya wa maƙiyansa cewa: “Ubanku Ibrahim ya yi murna da ganin ranata; har ya gan ta, zuciyarsa ta yi fari kuma.” (Yoh. 8:56) Hakazalika, Saratu da Ishaƙu da Yakubu da kuma wasu mutane sun kasance da bege a kan Mulkin da zai yi sarauta a nan gaba, “wanda mai-sifansa da mai-aikinsa Allah ne.”​—⁠Ibran. 11:​8-11.

6 Ta yaya Ibrahim da iyalinsa suka kasance da bangaskiya sosai? Wataƙila sun koyi game da Allah daga wurin tsofaffi masu aminci, ko ta wurin wahayin da Allah ya saukar musu ko kuma sun karanta tabbatattun rubuce-rubuce na dā. Ƙari ga haka, ba su manta da abin da suka karanta ba amma sun ɗauki alkawuran Allah da ƙa’idodinsa da tamani kuma sun yi bimbini a kansu. Domin sun tabbata da begensu, waɗannan maza da mata sun kasance da aminci ko a lokacin da suke shan wahala ko ake tsananta musu.

7. Waɗanne abubuwa ne Jehobah ya yi mana tanadinsu don mu ƙarfafa bangaskiyarmu, kuma mene ne za mu yi da su?

7 Jehobah ya yi mana tanadin Kalmarsa Littafi Mai Tsarki don ya taimaka mana mu ƙarfafa bangaskiyarmu. Idan muna so mu riƙa farin ciki kuma mu yi nasara a rayuwa, wajibi ne mu riƙa karanta Kalmar Allah a kai a kai. (Zab. 1:​1-3; karanta Ayyukan Manzanni 17:11.) Kamar bayin Allah a dā, muna bukatar mu riƙa yin bimbini a kan alkawuran Allah kuma muna bin ƙa’idodinsa. Jehobah yana ba mu abinci a kan kari ta wurin abubuwan da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” yake mana tanadinsu. (Mat. 24:45) Idan muka ɗauki waɗannan abubuwan da Jehobah yake tanadinsu da tamani, za mu zama kamar bayinsa na dā masu bangaskiya sosai da suka tabbata da begensu cewa Mulkin Allah zai soma sarauta bisa dukan duniya.

8. Ta yaya addu’a za ta ƙarfafa bangaskiyarmu?

8 Yin addu’a ya taimaka wa bayin Jehobah a dā su ƙarfafa bangaskiyarsu. Kuma sa’ad da suka ga cewa Allah ya amsa addu’o’insu, hakan ya ƙara ƙarfafa bangaskiyarsu. (Neh. 1:​4, 11; Zab. 34:​4, 15, 17; Dan. 9:​19-21) Mu ma muna iya gaya wa Jehobah dukan abubuwan da ke damun mu don mun san cewa zai saurare mu kuma ya ba mu ƙarfin jimrewa. Sa’ad da Jehobah ya amsa addu’o’inmu, hakan yana ƙarfafa bangaskiyarmu. (Karanta 1 Yohanna 5:​14, 15.) Tun da bangaskiya tana cikin ‘ya’yan ruhu, muna bukatar mu ci gaba da ‘roƙon’ Allah ya ba mu ruhunsa kamar yadda Yesu ya umurce mu mu yi.​—⁠Luk. 11:​9, 13.

9. Ban da yin addu’a don kanmu, su wane ne kuma ya kamata mu riƙa yin addu’a a madadinsu?

9 Bai kamata mu riƙa roƙon Jehobah ya taimaka mana kawai ba. Amma mu riƙa gode masa kuma mu riƙa yabonsa kullum don “ayyuka masu-ban al’ajabi” da ya yi da suka “fi gaban lissafi.” (Zab. 40:⁠5) Ban da haka, ya kamata addu’armu ta nuna cewa muna “tunawa da waɗanda ke kurkuku, kamar tare [muke] ɗaure.” Ƙari ga haka, mu riƙa yin addu’a don ‘yan’uwanmu da ke faɗin duniya musamman ‘waɗanda suke shugabannanmu.’ Ganin yadda Jehobah yake amsa addu’o’inmu yana sa mu farin ciki sosai!​—⁠Ibran. 13:​3, 7.

SUN KASANCE DA AMINCI

10. Waɗanne bayin Allah ne suka kasance da aminci, kuma mene ne ya taimaka musu su yi hakan?

10 A littafin Ibraniyawa sura 11, manzo Bulus ya ambata matsalolin da bayin Allah da yawa da ba a ambata sunansu ba suka jimre. Alal misali, manzon ya ambata mata masu bangaskiya da yaransu suka mutu amma daga baya aka ta da su daga mutuwa. Kuma ya ambata wasu da “ba su karɓi fansarsu ba, domin su [samu] tashi mafi kyau.” (Ibran. 11:35) Ko da yake ba mu san waɗanda Bulus yake magana a kansu ba, amma mu san cewa an jejjefe wasu kamar Naboth da Zakariya da duwatsu har suka mutu don sun yi biyayya ga Allah da kuma nufinsa. (1 Sar. 21:​3, 15; 2 Laba. 24:​20, 21) Daniel da abokansa suna da zarafin su “karɓi fansarsu” ta wajen kin kasancewa da aminci. Maimakon haka, sun kasance da bangaskiya cewa Jehobah zai ba su ruhu mai tsarki kuma ya taimaka musu su jimre da matsalolin da suke fuskanta.​—Ibran. 11:​33, 34; Dan. 3:​16-18, 20, 28; 6:​13, 16, 21-23.

11. Waɗanne matsaloli ne wasu annabawa suka jimre don sun kasance da bangaskiya?

11 An yi wa annabawa kamar Micaiah da Irmiya “ba’a . . . har da ɗauri” don sun kasance da bangaskiya. Wasu kuma kamar Iliya sun yi “yawo a jeji, cikin duwatsu da kogai, da kwazanzaman ƙasa.” Dukansu sun jimre domin suna da tabbacin za su samu ‘abin da suke begensa.’​—Ibran. 11:​1, 36-38; 1 Sar. 18:13; 22:​24-27; Irm. 20:​1, 2; 28:​10, 11; 32:2.

12. Wane ne ya yi fice wajen kafa misali na jimre da matsaloli, kuma mene ne ya taimaka masa ya yi hakan?

12 Bayan Bulus ya ambata maza da mata dabam-dabam da suka kasance da bangaskiya, ya ce Ubangijinmu Yesu Kristi ne ya yi fice wajen kasancewa da bangaskiya. Littafin Ibraniyawa 12:2 ta ce: “Ya jimre da [gungumen azaba, NW ] domin farin zuciya da aka sa gabansa, yana rena kunya, ya kuwa zauna ga hannun dama na al’arshen Allah.” Hakika, ya kamata mu bi misalin yadda Yesu ya kasance da bangaskiya sa’ad da ya fuskanci matsaloli masu tsanani. (Karanta Ibraniyawa 12:⁠3.) Bayin Allah a ƙarni na farko da aka kashe kamar almajiri Antibas sun kasance da aminci kamar Yesu. (R. Yoh. 2:13) Irin waɗannan Kiristocin sun riga sun samu ladarsu, ba kamar bayin Allah na dā da suke da begen yin rayuwa a wannan duniyar ba. (Ibran. 11:35) Bayan Yesu ya zama sarki a shekara ta 1914, an ta da Kiristoci shafaffu da suka mutu zuwa sama, kuma za su yi sarautar wannan duniyar tare da shi.​—⁠R. Yoh. 20:⁠4.

BAYIN ALLAH MASU BANGASKIYA A ZAMANINMU

13, 14. Waɗanne matsaloli ne Rudolf Graichen ya fuskanta, kuma mene ne ya taimaka masa?

13 Bayin Allah da yawa a zamaninmu suna bin misalin Yesu. Suna yin bimbini a kan alkawuran Allah kuma suna kasancewa da aminci sa’ad da suke fuskantar matsaloli. Alal misali, an haifi ɗan’uwa Rudolf Graichen a Jamus a shekara ta 1925. Ya tuna da hotunan labaran Littafi Mai Tsarki da aka rataye a bangon gidansu. Ya rubuta cewa: “Ɗaya daga cikin hotunan yana ɗauke da hoton “kyarketai da tumaki da ɗan akuya da damisa da ɗan maraƙi da kuma zaki, dukansu suna zaman lafiya, kuma wani ƙaramin yaro ne yake ja-gorarsu. . . . Irin waɗannan hotunan sun sa in riƙa tunanin yadda aljanna za ta kasance.” (Isha. 11:​6-9) Ko da yake ‘yan Nazi da kuma ‘yan sandan ciki na Kwamisanci na Gabashin Jamus sun yi shekaru da yawa suna tsananta wa Rudolf, ya ci gaba da kasancewa da aminci a kan begensa na yin rayuwa a aljanna.

14 Ɗan’uwa Rudolf ya fuskanci wasu matsaloli kuma. Hakan ya ƙunshi sa’ad da mahaifiyarsa ta mutu a sansanin da ke Ravensbrück don wata mummunar cutar da ake kira typhus. Ƙari ga haka, mahaifinsa bai kasance da aminci ba don ya saka hannu a wani takardan rantsuwa da ya nuna cewa shi ba Mashaidi ba ne kuma. Bayan da aka sake shi daga kurkuku, Rudolf ya yi hidimar mai kula da da’ira kuma aka gayyace shi zuwa Makarantar Gilead. Bayan ya sauke karatun, sai aka tura shi hidima a ƙasar Chile inda ya yi hidimar mai kula da da’ira. Amma matsalolinsa ba su ƙare a nan ba. Ya auri wata mai wa’azi a ƙasar waje mai suna Patsy. Kuma bayan shekara ɗaya da aurensu, sai ‘yarsu ta mutu. Bayan hakan, matarsa ma ta mutu sa’ad da take shekara 43. Rudolf ya jimre da dukan waɗannan matsalolin. Ko da yake ya tsufa kuma yana rashin lafiya, yana hidimar majagaba na kullum kuma shi dattijo ne sa’ad da tarihinsa ya fito a Hasumiyar Tsaro na 1 ga Agusta, 1997, shafuffuka na 20-25.

15. Ka ba da misalan Shaidun Jehobah a zamaninmu da suka jimre da tsanantawa?

15 Ko da yake ana tsananta wa Shaidun Jehobah sosai, sun ci gaba da yin farin ciki a ibadarsu ga Jehobah. Alal misali, an saka ‘yan’uwanmu da yawa a kurkuku a ƙasashen Eritrea da Singapore da kuma Koriya ta Kudu don sun bi umurnin Yesu cewa kada su ɗauki takobi. (Mat. 26:52) Wasu daga cikin waɗannan fursunonin su ne Isaac da Negede da Paulos kuma sun yi fiye da shekara 20 a cikin kurkukun da ke Eritrea! Waɗannan ‘yan’uwan da aka hana su kula da iyayensu da suka tsufa da kuma yin aure sun kasance da aminci duk da irin wulakancin da suke fuskanta. Akwai hotunansu a dandalinmu na jw.org. Suna fara’a ko da yake suna shan wahala. Kuma masu gadinsu suna daraja su sosai.

Kana amfana daga misalan ‘yan’uwa masu aminci a ikilisiyarku? (Ka duba sakin layi na 15, 16)

16. Ta yaya kasancewa da bangaskiya sosai zai taimaka maka?

16 Yawancin bayin Jehobah a yau ba sa fuskantar tsanantawa mai tsanani. Amma ana jaraba bangaskiyarsu a wata hanya dabam. Da yawa a cikinsu sun jimre da talauci ko kuma sun sha wahala a lokacin da ake yaƙin basasa ko kuma tsarar bala’i. Wasu sun bi misalin Musa da kuma ubanni na dā ta wajen ƙin yin suna ko kuma arziki don su bauta wa Allah. Sun yi iya ƙoƙarinsu don su guji biɗan abin duniya ko kuma bin salon rayuwa na mutanen duniya. Mene ne ya taimaka musu? Suna ƙaunar Jehobah kuma suna da bangaskiya cewa zai kawar da dukan rashin adalci kuma ya albarkaci bayinsa masu aminci da rai na har abada a sabuwar duniya.​—Karanta Zabura 37:​5, 7, 9, 29.

17. Mene ne ka ƙudura niyyar yi, kuma mene ne za a tattauna a talifi na gaba?

17 A wannan talifin, mun ga yadda yin bimbini a kan alkawuran Allah da kuma yin addu’a a kai a kai za su sa mu ƙarfafa bangaskiyarmu. Hakan kuma zai taimaka mana mu jimre da matsaloli da kuma mai da hankali ga alkawuran da Jehobah ya yi mana. Amma a talifi na gaba, za a ƙara tattauna abin da yake nufi mutum ya kasance da bangaskiya.