Yusufu Dan Arimathiya ya Kasance da Gaba Gadi
YUSUFU ƊAN ARIMATHIYA ya ga cewa bai zai iya kasancewa da gaba gaɗin zuwa gaban gwamnan Romawa ba don an san Bilatus Ba-bunti da taurin kai. Duk da haka, kafin a binne Yesu a hanyar da ta dace, sai wani ya je wurin Bilatus ya nemi izinin ɗaukan gawar Yesu. Amma daga baya abin da ya faru ba abin da Yusufu ya zata zai faru ba. Da suka je, Bilatus ya ba su izinin ɗaukar gawar nan da na bayan da ya tabbata cewa Yesu ya rasu. Da aka ba Yusufu wannan izinin, sai ya yi sauri ya je wurin da aka kashe Yesu ko da yake har ila yana baƙin cikin mutuwar Yesu.—Mar. 15:42-45.
-
Waye ne Yusufu ɗan Arimathiya?
-
Wace dangantaka ke tsakaninsa da Yesu?
-
Kuma me ya sa za mu bincika labarinsa?
ƊAN MAJALISA
Littafin Linjilar Markus ya kira Yusufu “ba’sarauci cikin majilisa.” Wannan yana nufin cewa yana da iko a gwamnati da kuma addini. (Mar. 15:1, 43) Ban da haka ma, Yusufu shugaba ne shi ya sa gwamna Bilatus ya ba shi izinin ɗaukan gawar Yesu. Kuma shi mai kuɗi ne sosai.—Mat. 27:57.
Shin kana da gaba gaɗin nuna cewa Yesu ne Sarkinka?
’Yan majalisa suna gāba da Yesu kuma suka ƙulla su kashe shi. Amma an kira Yusufu “nagarin mutum, mai-adalci.” (Luk. 23:50) Shi ba kamar sauran ’yan majalisa ba domin shi mai kirki ne kuma yana bin dokokin Allah. Ban da haka ma, “yana sauraron mulkin Allah” kuma wannan dalilin ne ya sa ya zama almajirin Yesu. (Mar. 15:43; Mat. 27:57) Kuma wataƙila don yana son gaskiya da adalci ne ya sa ya so koyarwar Yesu.
ALMAJIRI A ƁOYE
Littafin Yohanna 19:38 ya ce Yusufu “almajirin Yesu ne, amma daga ɓoye saboda tsoron Yahudawa.” Me ya sa Yusufu yake tsoro? Ya san cewa Yahudawa ba sa son koyarwar Yesu kuma suna koran duk wani da ya ba da gaskiya ga Yesu. (Yoh. 7:45-49; 9:22) Kuma idan aka kori mutum daga haikali, Yahudawa za su tsani mutumin su zage shi kuma su daina tarayya da shi. Wannan dalilin ne ya sa Yusufu ya ƙi gaya wa mutane cewa shi almajirin Yesu ne. Domin idan ya yi hakan, za a ƙwace matsayin da yake da shi.
Ba Yusufu ba ne kawai ya kasance cikin wannan yanayin. Littafin Yohanna 12:42 ya ce, “har cikin hakimai mutane da yawa suka ba da gaskiya gareshi [Yesu], amma saboda Farisawa ba su shaida shi ba, domin ka da a fitar da su daga cikin majami’a.” Wani kuma da yanayinsa ya yi daidai da na Yusufu shi ne Nikodimu wani ɗan majalisa.—Yoh. 3:1-10; 7:50-52.
Ko da yake Yusufu almajirin Yesu ne, amma bai taɓa nuna hakan a gaban jama’a ba. Hakan matsala ce babba domin Yesu ya ce: “Ko wane ne . . . da za ya shaida ni a gaban mutane, shi zan shaida a gaban Ubana wanda ke cikin sama kuma. Amma dukan wanda za ya yi musun sanina a gaban mutane, shi zan yi musunsa a gaban Ubana wanda ke cikin sama.” (Mat. 10:32, 33) Yusufu bai yi musun sanin Yesu ba, amma bai kasance da gaba gaɗin nuna kansa a gaban mutane ba. Kai kuma fa?
Abin da Yusufu ya yi yana da kyau domin Littafi Mai Tsarki ya ce shi bai goyi bayan ƙullin da aka yi ma Yesu ba. (Luk. 23:51) Wasu suna ganin cewa Yusufu ba ya nan sa’ad da ake wulaƙanta Yesu. Ko da
mene ne yanayin, Yusufu bai yi farin ciki da irin wannan rashin adalci da aka yi musu ba, amma ba abin da zai yi don ya hana su hakan.YA KASANCE DA ƘARFIN HALI
Amma a lokacin da Yesu ya mutu, wataƙila Yusufu ya daina jin tsoro kuma ya soma goyon bayan mabiyan Yesu. Abin da aka faɗa a Markus 15:43 ya nuna hakan. Wurin ya ce: ‘Ya shiga wurin Bilatus da gaba gaɗi, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.’
Wataƙila Yusufu yana nan sa’ad da Yesu ya mutu. Babu shakka, ya riga Bilatus ji game da rasuwar Yesu. Amma a lokacin da Yusufu ya nemi izini a ba shi gawar Yesu, gwamnan “ya yi mamaki, da jin [Yesu] ya rigaya ya mutu.” (Mar. 15:44) Shin da yake wataƙila Yusufu ya ga mutuwar wulaƙanci da Yesu ya yi ne ya sa ya sake tunani kuma ya tsai da shawarar fitowa a fili ya nuna cewa shi mabiyin Yesu ne? Wataƙila hakan ne ya sa shi ya ɗauki wannan matakin kuma yanzu zai nuna wa jama’a cewa shi mabiyin Yesu ne.
YUSUFU YA BINNE YESU
A dokar Yahudawa an umurci mutane su riƙa binne waɗanda aka yanke musu hukuncin kisa kafin yamma. (K. Sha. 21:22, 23) Al’adar Romawa kuma ita ce su bar gawar waɗanda aka kashe a kan gungume su ruɓe ko kuma a jefar da gawarsu cikin wani babban rami. Amma ba abin da Yusufu yake so ya yi da gawar Yesu ba ne. Yusufu yana da wurin bizina kusa da wurin da aka kashe Yesu. Ba a taɓa yin amfani da maƙabartar ba kuma hakan ya nuna cewa ya ƙaura ne daga Arimathiya * zuwa Urushalima ba daɗewa ba, shi ya sa ya sayi wurin don su riƙa binne ’yan iyalinsa da suka rasu. (Luk. 23:53; Yoh. 19:41) Yadda aka bizine Yesu a filin Yusufu ya nuna cewa Yusufu mai karimci ne kuma hakan ya cika annabci game da Almasihu cewa za a binne shi “tare da mawadaci.”—Isha. 53:5, 8, 9.
Da akwai wani abu da ya fi dangantakarka da Jehobah muhimmanci?
Duka Linjila huɗu sun ba da labari cewa da aka sauke gawar Yesu daga kan gungumen, Yusufu ya sa aka rufe Yesu da likkafani mai kyau kuma aka binne shi a wurin bizina da ya saya. (Mat. 27:59-61; Mar. 15:46, 47; Luk. 23:53, 55; Yoh. 19:38-40) Nikodimu ne kaɗai aka ambata ya taimaka wa Yusufu kuma ya kawo turare. Da yake waɗannan maza biyu masu matsayi ne sosai, ba zai zama su biyu ne kaɗai suka ɗauki gawar Yesu ba. Wataƙila sun sa bayinsu ne su ɗauki gawar kuma suka binne. Duk da haka, ya kamata a yaba musu don abin da suka yi. Saboda a al’adarsu wanda ya taɓa gawa zai tsabtace kansa kwanaki bakwai, don idan ba su yi hakan ba kome da suka taɓa ba zai kasance marar tsarki. (Lit. Lis. 19:11; Hag. 2:13) Ƙari ga haka, zai sa ba za su yi kusa da mutane ba a makon Idin Ketarewa kuma ba za su yi bikin gabaki ɗaya ba. (Lit. Lis. 9:6) Abokan aikin Yusufu za su yi masa ba’a domin shi ya shirya a yi jana’izar Yesu. Amma a wannan lokacin, yana shirye ya fuskanci sakamakon binne Yesu yadda ya dace da kuma nuna kansa a fili cewa shi almajirin Kristi ne.
ƘARSHEN LABARIN YUSUFU
Bayan jana’izar Yesu, ba a sake ambata Yusufu na Arimathiya a cikin Littafi Mai Tsarki ba. Kuma babu shakka, hakan zai sa mu yi wannan tambayar: Mene ne ya faru da shi? Gaskiya, ba mu sani ba. Amma, saboda abubuwan da aka ambata ɗazu, babu shakka cewa ya nuna kansa a fili cewa shi Kirista ne. Ballantana ma, a lokacin da Yusufu ya ga aka tsananta wa Yesu ne ya sa ya kasance da bangaskiya da kuma gaba gaɗi. Hakan abu ne mai kyau.
Ya kamata wannan labarin ya sa dukanmu yin wannan tambayar: Shin da akwai wani abu wataƙila matsayi ko sana’a ko dukiya ko iyali ko kuma samun ’yanci da ya fi muhimmanci a kan dangantakarmu da Jehobah?
^ sakin layi na 18 Wataƙila Arimathiya ne Ramah, wurin da ake kira Rentis (Rantis) a yau. Wannan wurin garin Sama’ila ne da ke da nisan kilomita 35 daga arewa masu gabashin Urushalima.—1 Sam. 1:19, 20.