Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

1918​—Shekara Dari da ta Shige

1918​—Shekara Dari da ta Shige

An soma Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Janairu, 1918, da cewa: “Mene ne zai faru a shekara ta 1918?” Duk da cewa ana kan tabka Yaƙin Duniya na Ɗaya a Turai, abubuwa da suka faru a somawar shekarar, sun ba da alama cewa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da kuma duniya gabaki ɗaya za su cim ma abubuwa da yawa.

AN YI TARON ZAMAN LAFIYA

A ranar 8 ga Janairu, 1918, shugaban ƙasar Amirka mai suna Woodrow Wilson ya yi jawabi a wani Taron Majalisa da aka yi a Amirka kuma ya lissafa abubuwa 14 da yake gani za su taimaka a “sami zaman lafiya.” Ya ba da shawara cewa al’ummai su riƙa tattaunawa da kuma sasantawa. Ƙari ga haka, ya ce su rage ƙera makamai kuma “su riƙa yin hulɗa da juna da zai amfani dukan ƙasashe.” Daga baya an yi amfani da shawarwarinsa don a kafa Tsohuwar Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Yarjejeniyar da aka yi a Versailles wadda ta sa aka daina Yaƙin Duniya na Ɗaya.

AN YI NASARA A KAN ABOKAN GĀBA

Duk da tashin hankali da aka yi a shekara ta 1917, * an ga alama cewa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki za su kasance da kwanciyar hankali. Me ya sa? Domin abubuwan da suka faru a taron shekara-shekara na Watch Tower Bible and Tract Society.

A taron da aka yi a ranar 5 ga Janairu, 1918, ’yan’uwa da yawa masu ja-goranci da aka sallame su daga Bethel sun yi kulle-kulle don su ƙwace ƙungiyar Jehobah. Ɗan’uwa Richard H. Barber wani mai kula mai ziyara ne ya buɗe taron da addu’a. Bayan an ba da rahoto game da ayyukan da aka yi a shekarar da ta shige, sai aka yi zaɓen darektoci da ake yi kowace shekara. Ɗan’uwa Barber ya zaɓi Joseph Rutherford da kuma wasu ’yan’uwa guda shida don su zama darektoci. Sai wani lauya da ke goyon bayan ’yan adawar ya zaɓi mutane guda bakwai, har da mazan da aka sallama daga Bethel, amma ba su yi nasara ba. Jama’a mafi yawa suka zaɓi Ɗan’uwa Rutherford da kuma wasu ’yan’uwa shida masu aminci don su zama darektoci a ƙungiyar.

’Yan’uwa da yawa da suka halarci taron nan sun ce “wannan shi ne taro da aka fi yin nasara da suka taɓa halarta.” Amma farin cikinsu bai jima ba.

YADDA MUTANE SUKA ƊAUKI LITTAFIN THE FINISHED MYSTERY

Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun ɗau watanni suna rarraba littafin nan The Finished Mystery. Kuma masu zuciyar kirki sun amince da koyarwar Littafi Mai Tsarki da ke cikin wannan littafin.

Ɗan’uwa E. F. Crist wanda yake hidimar mai kula mai ziyara a Kanada, ya ce akwai wasu ma’aurata da suka karanta littafin The Finished Mystery kuma suka karɓi gaskiya cikin makonni biyar kawai. Ya ce: “Ma’auratan masu ibada ne sosai kuma suna samun ci gaba.”

Wani mutumin da ya karɓi littafin ya karanta shi kuma ya gaya ma abokansa abin da ke ciki. Abin da ya koya ya “burge shi sosai.” Ya ce: “Ina wucewa ta Third Avenue, sai na ji wani abu ya buge ni a kafaɗa. Na ɗauka bulo ne, amma na yi mamaki cewa littafin ‘The Finished Mystery’ ne. Sai na taho da shi gida kuma na karanta. . . . Na gano cewa wani malamin addini . . . ne cikin fushi ya jefo littafin ta tagarsa. . . . Wannan abin da ya yi ya sa mutane da yawa sun koyi gaskiya. . . . A yanzu muna bauta wa Allah.”

Ban da malamin addinin nan, da akwai wasu ma da suka yi fushi haka. A ranar 12 ga Fabrairu, 1918, hukumomin Kanada sun hana mutane karanta littafin da kuma rarraba shi. Sun ce littafin na ɗauke da kalaman da za su sa mutane yin tawaye da kuma ƙin saka hannu a yaƙi. Ba da daɗewa ba, hukumomi a Amirka suka hana mutane karanta littafin da kuma rarraba shi. Hukumomi sun je Bethel da kuma wasu ofisoshinmu da ke New York da Pennsylvania da kuma Kalifoniya don su tuhumi ’yan’uwa da ke ja-goranci a ƙungiyar Jehobah. A ranar 14 ga Maris, 1918, U.S. Department of Justice, wato Ma’aikatar Shari’a na Amurka ta hana buga littafin nan The Finished Mystery. A cewar ta, buga da kuma rarraba litafin nan zai hana mutane zuwa yaƙi kuma hakan taka doka ce.

AN SAKA ’YAN’UWA A KURKUKU!

A ranar 7 ga Mayu, 1918, Ma’aikatar Shari’a na Amurka ta ba da izini a kama Ɗan’uwa Giovanni DeCecca da George Fisher da Alexander Macmillan da Robert Martin da Frederick Robison da Joseph Rutherford da William Van Amburgh da kuma Clayton Woodworth. An tuhume su da laifin “taka doka da sa mutane yin tawaye da kuma ƙin shiga soja.” An soma yi musu shari’a a ranar 3 ga Yuni, 1918, amma da alama cewa an riga an yanke musu hukunci kafin ma a soma shari’ar. Me ya sa?

Lauyan Ba’amirke ya ce ’yan’uwan sun karya dokar da ake kira Espionage Act, wato dokar da ta hana yaɗa jita-jita. A ranar 16 ga Mayu, 1918, Majalisa ta ƙi amincewa a yi gyara ga dokar wadda za ta kāre mutanen da suka wallafa “abubuwan da gaskiya ne ko da suna da dalilai masu kyau na yin hakan.” Sun mai da hankali musamman ga littafin nan The Finished Mystery a muhawwararsu. A rahoto da ke ofishin Majalisar Amirka, an ce game da littafin: “Wani misalin littafin da ke yaɗa jita-jita mafi haɗari shi ne littafin nan ‘The Finished Mystery’ . . . Abin da Littafin nan ke yi kawai shi ne sa sojoji su ƙi bin umurni . . . har ma da sa mutane ƙin shiga soja.”

A ranar 20 ga Yuni, 1918, lauyoyi sun kama ’yan’uwan nan takwas da laifi. Washegari, sai alƙali ya yanke hukunci, ya ce: “Jita-jitar da waɗannan mutane suke yaɗawa . . . ta fi rundunar Jamus haɗari. . . . Don haka, ya kamata a yanke musu hukunci mai tsanani.” Bayan makonnin biyu, aka tura ’yan’uwan guda takwas kurkukun da ke birnin Atlanta a jihar Georgia. An yanke musu hukuncin shekara goma zuwa ashirin a kurkuku.

AN CI GABA DA YIN WA’AZI

A wannan lokacin, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun fuskanci tsanantawa sosai. Ma’aikatan Sashen Binciken Laifi da ake kira FBI sun bincika ayyukan ’yan’uwan kuma suka rubuta rahotanni da yawa game da su. Waɗannan rahotanni sun nuna cewa ’yan’uwanmu sun ƙudiri niyyar ci gaba da yin wa’azi.

A wata wasiƙa da aka rubuta wa Ma’aikatan Sashen Binciken Laifi, mai tura wasiƙa a birnin Orlando da ke jihar Florida, ya rubuta cewa: “[Ɗaliban Littafi Mai Tsarki] suna zuwa gida-gida wa’azi a dukan garin kuma yawanci suna yin hakan daddare. . . . Sun ƙuduri niyyar ci gaba da yin wa’azi duk da cewa ana tsananta musu sosai.”

Wani kanar da ke aiki a Sashen Yaƙi, ya tura wa Ma’aikatan Sashen Binciken Laifi rahoto game da ayyukan Ɗan’uwa Frederick W. Franz wanda daga baya ya zama memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu. Kanar ɗin ya ce: “F. W. Franz . . . ya saka ƙwazo wajen sayar da dubban kundin littafin nan ‘The Finished Mystery’.”

Ɗan’uwa Charles Fekel wanda daga baya ya zama memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu, ya fuskanci tsanantawa sosai. Hukumomi sun tsare shi don yana rarraba littafin The Finished Mystery kuma hukumomin sun karanta wasiƙun da ake tura masa. An tura shi kurkuku na wata ɗaya a birnin Baltimore a jihar Maryland kuma sun ce shi “Maƙiyi ne ɗan Austriya.” Yayin da yake yi wa waɗanda ke tuhumarsa wa’azi, ya tuna furucin Bulus a littafin 1 Korintiyawa 9:​16, cewa: “Kaitona kuma idan ba na yin aikin shelar nan!” *

Ƙari ga ƙwazo da suke yi a wa’azi, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun yi ƙoƙarin rubuta wasiƙu don a saki ’yan’uwan da ke kurkuku a birnin Atlanta. ’Yar’uwa Anna K. Gardner ta ce: “Koyaushe muna ƙoƙarin mu taimaka. A lokacin da aka saka ’yan’uwan a kurkuku, abin da muke yi shi ne neman mutanen da za su goyi bayanmu ta wajen saka mana hannu a takardu. Mukan je gida-gida kuma mun sami dubban mutane da suka saka mana hannu! Mukan gaya wa mutanen da muka je wurinsu cewa waɗannan ’yan’uwan Kiristoci ne na gaske da aka saka a kurkuku ba tare da sun yi laifin kome ba.”

TARON YANKI

A wannan mawuyacin yanayi, ana yin manyan taro sau da yawa don a ƙarfafa ’yan’uwa. Hasumiyar Tsaro ta ce: “An yi fiye da manyan taro arba’in . . . a wannan shekarar . . . An sami rahotanni masu kyau daga waɗannan manyan taro. A dā ana kammala dukan taron yanki ciki watanni biyu ko uku, amma yanzu kowane wata ake yin taron.”

Duk da haka, masu zuciyar kirki suna saurara saƙon mulki. A wani babban taro da aka yi a birnin Cleveland da ke jihar Ohio, wajen mutane 1,200 ne suka halarta kuma mutane 42 suka yi baftisma, a cikinsu har da wani ɗan yaro “da ke son bauta wa Allah kuma abin da yaron nan ya yi zai kunyatar da manya.”

SAI ME?

Yayin da shekara ta 1918 ta kusan ƙarewa, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki ba su san abin da zai faru da su a nan gaba ba. An sayar da wasu gine-ginen da ke Brooklyn kuma aka ƙaurar da hedkwata zuwa birnin Pittsburgh da ke jihar Pennsylvania. Sa’ad da ’yan’uwan da ke ja-goranci suke kurkuku, an ce za a yi taron shekara-shekara a ranar 4 ga Janairu, 1919. Me zai faru?

’Yan’uwanmu sun ci gaba da yin ƙwazo a wa’azi. Sun kasance da tabbaci cewa za su yi nasara, shi ya sa jigon shekara ta 1919, ya ce: “Babu kayan yaƙin da aka ƙera domin a yaƙe ki wanda zai yi nasara.” (Isha. 54:17) Hakan ya shirya su don abin da zai faru a gaba. Zai ƙarfafa bangaskiyarsu kuma zai shirya su don aikin da za su yi.

^ sakin layi na 6 Ka duba talifin nan “One Hundred Years Ago​—1917” a littafin 2017 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafuffuka na 172-176.

^ sakin layi na 22 Ka duba labarin Charles Fekel, mai jigo: “Joys Through Perseverance in Good Work,” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Maris, 1969.