Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ku Dogara ga Kristi, Mai Mana Ja-goranci

Ku Dogara ga Kristi, Mai Mana Ja-goranci

“Shugaba ɗaya gare ku, wato Almasihu.”​—MAT. 23:10.

WAƘOƘI: 16, 14

1, 2. Wane ƙalubale ne Yoshuwa ya fuskanta bayan mutuwar Musa?

JEHOBAH ya gaya wa Yoshuwa cewa: “Bawana Musa ya mutu. Sai ka shirya yanzu, kai da dukan jama’ar Isra’ila, ku ƙetare Kogin Yodan zuwa cikin ƙasar da nake ba ku.” (Yosh. 1:​1, 2) Wannan canji ne na farat ɗaya ga Yoshuwa wanda ya yi shekara kusan 40 yana taimaka wa Musa!

2 Domin Musa ya daɗe sosai yana wa Isra’ilawa ja-goranci, wataƙila Yoshuwa ya yi tunani ko mutanen za su amince da shi a matsayin shugabansu. (M. Sha. 34:​8, 10-12) Wani littafin bincike ya yi bayani game da littafin Yoshuwa 1:​1, 2 cewa: “A zamanin dā da kuma a yau, lokaci mafi wuya da kuma haɗari ga al’umma shi ne sa’ad da aka yi sabon sarki.”

3, 4. Ta yaya Allah ya albarkaci Yoshuwa don ya dogara gare shi, kuma wace tambaya ce za mu iya yi?

3 Ya kamata Yoshuwa ya damu sosai, amma ya dogara ga Jehobah kuma ya yi saurin bin ja-gorancinsa. (Yosh. 1:​9-11) Allah ya albarkaci Yoshuwa don ya dogara da shi. Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya nuna, Jehobah ya yi amfani da mala’ika don ya ja-goranci Yoshuwa da kuma Isra’ilawa. Da alama cewa wannan mala’ikan Ɗan fari ne na Allah, wanda ake kira Kalma.​—Fit. 23:​20-23; Yoh. 1:1.

4 Jehobah ya taimaka wa Isra’ilawa su bi ja-gorancin sabon shugabansu, Yoshuwa. A zamaninmu, ana canje-canje sosai, kuma mukan yi tunani, ‘Yayin da ƙungiyar Jehobah ke samun ci gaba sosai, shin ya kamata mu dogara da Shugabanmu Yesu?’ (Karanta Matiyu 23:10.) Za mu bincika yadda Jehobah ya yi wa mutanensa ja-goranci a lokacin da aka yi canje-canje a dā.

YA JA-GORANCI MUTANEN ALLAH ZUWA ƘASAR KAN’ANA

5. Mene ne Yoshuwa ya gani a kusa da Yeriko? (Ka duba hoton da ke shafi na 22.)

5 Yoshuwa ya ga abin mamaki ba da daɗewa ba da Isra’ilawa suka ƙetare Yodan. Ya haɗu da wani mutum mai ɗauke da takobi sa’ad da ya kusan Yeriko. Da yake Yoshuwa bai san mutumin ba, sai ya tambaye shi: “Kai ɗaya daga cikin sojojinmu ne, ko kai na abokan gābanmu ne?” Yoshuwa ya yi mamaki da mutumin ya bayyana kansa cewa shi “sarkin yaƙin rundunar Yahweh ne” kuma yana shirye ya kāre mutanen Allah. (Karanta Yoshuwa 5:​13-15.) A wasu ayoyi, an ce Jehobah ya yi magana kai tsaye da Yoshuwa. Amma kamar yadda Allah yake yi a dā, ya yi amfani ne da mala’ika don ya yi wa Yoshuwa magana.​—Fit. 3:​2-4; Yosh. 4:​1, 15; 5:​2, 9; A. M. 7:38; Gal. 3:19.

6-8. (a) Me ya sa ’yan Adam za su yi tunani cewa wasu umurnin Jehobah ba su dace ba? (b) Ta yaya muka san cewa umurnin ya dace kuma an ba da umurnin a lokacin da ya kamata? (Ka duba ƙarin bayani.)

6 Mala’ikan ya gaya wa Yoshuwa abin da za su yi don su ci birnin Yeriko. Da farko, kamar dai wasu umurnin ba su dace ba. Alal misali, Jehobah ya ba da umurni cewa a yi wa dukan mazajen kaciya. Hakan yana nufin cewa ba za su iya yin yaƙi ba har sai bayan wasu kwanaki. Ya dace kuwa a yi ma waɗannan mazajen kaciya a wannan lokacin?​—Far. 34:​24, 25; Yosh. 5:​2, 8.

7 Wataƙila waɗannan sojojin sun yi tunanin yadda za su kāre iyalinsu idan abokan gābansu suka kawo musu hari. Amma farat ɗaya, suka ji labari cewa an “kulle ƙofofin Yeriko daga ciki da kuma waje.” (Yosh. 6:1) Babu shakka cewa wannan labarin ya ƙarfafa Isra’ilawa su ci gaba da bin ja-gorancin Allah.

8 Ƙari ga haka, an umurci Isra’ilawa kada su kai wa mutanen Yeriko hari. Maimakon haka, su zagaya birnin sau ɗaya kowace rana har kwanaki shida. Amma a rana ta bakwai, za su zagaya birnin sau bakwai. Wataƙila sojojin sun ce ai wannan wawanci ne. Wasu cikinsu za su ce, ‘Wannan ɓata lokaci ne!’ Amma Shugaban Isra’ila da ba a gani ya san abin da yake yi. Bin umurnin Jehobah ya ƙarfafa bangaskiyar Isra’ilawa kuma ba su yi faɗa kai tsaye da sojojin Yeriko ba.​—Yosh. 6:​2-5; Ibran. 11:30. *

9. Me ya sa ya dace mu bi ja-gorancin ƙungiyar Allah? Ka ba da misali.

9 Mene ne muka koya daga wannan labarin? A wasu lokuta, ƙungiyar Jehobah takan yi wasu canje-canje da ba mu fahimci dalilin ba. Alal misali, wataƙila da farko muna ganin bai dace ba a yi amfani da na’ura don nazari ko sa’ad da muke wa’azi ko kuma a taro. Amma yanzu mai yiwuwa mun ga amfanin waɗannan abubuwa. Ƙari ga haka, yin amfani da na’ura ya ƙarfafa bangaskiyarmu sa’ad da muka ga sakamakon da aka samu. Kuma hakan ya ƙara sa mu kasance da haɗin kai.

YADDA KRISTI YA YI JA-GORANCI A ƘARNI NA FARKO

10. Wane ne ainihi ya sa a yi taro mai muhimmanci da hukumar ta yi a Urushalima?

10 Bayan wajen shekara 13 da Koneliyus ya zama Kirista, wasu Kiristoci Yahudawa suna ganin ya dace a riƙa kaciya. (A. M. 15:​1, 2) Sa’ad da ’yan’uwa suka soma jayayya a kan wannan batun a birnin Antakiya, sai aka ce Bulus ya je ya tuntuɓi hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a ƙarni na farko a Urushalima. Amma wane ne ya ba da wannan umurnin? Bulus ya ce: “Allah ne ya nuna mini a cikin ru’uya cewa in tafi.” Hakika, Kristi ne ya sa hukumar ta sasanta wannan batun.​—Gal. 2:​1-3.

Yesu ne shugaban ikilisiyar Kirista a ƙarni na farko (Ka duba sakin layi na 10, 11)

11. (a) Mene ne wasu Kiristoci Yahudawa har ila suka gaskata game da kaciya? (b) Ta yaya Bulus ya nuna cewa ya goyi bayan dattawa da ke Urushalima? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)

11 Kristi ya ja-goranci hukumar ta bayyana sarai cewa Yahudawa da ba Kiristoci ba ba sa bukatar su yi kaciya. (A. M. 15:​19, 20) Amma bayan shekaru da yawa da hukumar ta yanke wannan shawarar, Yahudawa da yawa masu bauta wa Allah sun ci gaba da yi wa yaransu kaciya. Sa’ad da dattawa a Urushalima suka ji jita-jita da ake yi game da Bulus cewa ba ya bin Dokar da aka ba da ta hannun Musa, sun ce ya yi wani abu da zai nuna cewa yana bin Dokar. * (A. M. 21:​20-26) Sun gaya masa ya ɗauki maza huɗu su je haikali don mutane su ga cewa yana “kiyaye Koyarwar Musa.” Bulus bai karya wata doka ba, Yahudawan ne ba su fahimci batun kaciya ba. Don haka, su ne suke da laifi. Amma Bulus ya fahimci cewa dattawan suna so dukan Kiristoci su kasance da haɗin kai, shi ya sa ya bi umurninsu. Muna iya yin tunani, ‘Me ya sa Yesu ya bar wannan batun kaciya ya ci gaba da tayar da ƙura, ko da yake mutuwarsa ta kawar da Dokar da aka ba da ta hannun Musa?’​—Kol. 2:​13, 14.

12. Me ya sa wataƙila Kristi bai sasanta batun kaciya da sauri ba?

12 Yakan ɗauki lokaci kafin a saba da wani sabon umurni. Wasu Yahudawa suna bukatar isashen lokaci kafin su canja ra’ayinsu. (Yoh. 16:12) Ya yi ma wasu wuya su fahimci cewa mutum ba ya bukatar yin kaciya kafin ya ƙulla dangantaka na musamman da Allah. (Far. 17:​9-12) Wasu kuma suna jin tsoro cewa ’yan’uwansu Yahuduwa za su tsananta musu idan ba su yi abubuwan da suke yi ba. (Gal. 6:12) Da shigewar lokaci, Kristi ya ba da ƙarin bayani ta wurin wasiƙu da Bulus ya rubuta.​—Rom. 2:​28, 29; Gal. 3:​23-25.

KRISTI YANA JA-GORANCI HAR A YAU

13. Mene ne zai taimaka mana mu goyi bayan ja-gorancin Kristi a yau?

13 Har ila Kristi ne shugaban ikilisiyar Kirista a yau. Saboda haka, idan ba mu fahimci dalilin da ya sa ƙungiyar Jehobah ta yi wani canji ba, ya kamata mu yi tunani yadda Kristi ya ja-goranci mutanen Allah a dā. A zamanin Yoshuwa ko kuma a ƙarni na farko, Kristi ya ba da umurni da ya kāre mutanen Allah gabaki ɗaya. Hakan ya ƙarfafa bangaskiyarsu kuma ya sa su kasance da haɗin kai.​—Ibran. 13:8.

14-16. Ta yaya umurnin “bawan nan mai aminci, mai hikima,” ya nuna cewa Kristi yana so ya taimaka mana mu ƙarfafa bangaskiyarmu?

14 A yau “bawan nan mai aminci, mai hikima,” yana ba mu umurni a lokacin da ya dace kuma hakan ya nuna cewa Yesu yana kula da mu. (Mat. 24:45) Marc wanda yake da yara huɗu ya ce: “Shaiɗan yana ƙoƙari ya ɓata ikilisiyoyi ta wajen jawo matsaloli a iyalai. Da yake ana ƙarfafa iyalai su riƙa yin ibada ta iyali a kowane mako, ana gaya wa magidanta su kāre iyalansu!”

15 Za mu fahimci cewa Kristi yana son ya taimaka mana mu ƙarfafa bangaskiyarmu sa’ad da muka ga yadda yake mana ja-goranci. Alal misali, wani dattijo mai suna Patrick ya ce: “A lokacin da aka fara wannan shirin, wasu suna ganin bai kamata a riƙa haɗuwa a ƙananan rukunoni don yin taron fita wa’azi a ranar Asabar da Lahadi ba. Amma wannan canjin ya nuna yadda Yesu yake kula da kowa a ikilisiya. ’Yan’uwa da suke jin kunya ko kuma waɗanda ba sa fita wa’azi suna ganin cewa yanzu ana daraja su kuma suna da amfani. Wannan ya ƙarfafa su su kasance da ƙwazo a wa’azi.”

16 Kristi ya kuma taimaka mana mu mai da hankali ga yin wa’azi, don shi ne aiki mafi muhimmanci da ake yi a duniya. (Karanta Markus 13:10.) Wani ɗan’uwa mai suna André da bai daɗe da zama dattijo ba, yana ƙoƙari ya bi duk wani umurni daga ƙungiyar Jehobah. Ya ce: “Yadda aka rage masu hidima a ofisoshinmu ya tuna mana cewa yanzu ya fi muhimmanci a mai da hankali ga yin wa’azi.”

AMFANIN BIN JA-GORANCIN KRISTI

17, 18. Me ya sa ya kamata mu mai da hankali ga hanyoyin da muke amfana don bin canje-canje da ƙungiyar Jehobah take yi?

17 Bin ja-gorancin Sarkinmu, Yesu Kristi zai taimaka mana a yanzu da kuma a nan gaba. Saboda haka, bari mu mai da hankali ga yadda muke amfana don muna goyon bayan canje-canjen da ake yi kwanan nan. Kuna iya tattauna yadda canje-canjen da aka yi ga yadda ake yin taro a tsakiyar mako ko kuma wa’azi ya taimaka wa iyalinku.

Kana taimaka wa iyalinka da kuma wasu su bi ja-gorancin ƙungiyar Jehobah? (Ka duba sakin layi na 17, 18)

18 Idan muka tuna cewa bin umurnin da ƙungiyar Jehobah take bayarwa yana kawo sakamako mai kyau, zai yi mana sauƙi mu bi umurnin kuma za mu yi farin ciki. Alal misali, muna farin ciki cewa muna rage yawan kuɗin da muke kashewa domin ba mu buga littattafai da yawa kamar dā. Kuma yin amfani da na’ura yana sa ya kasance da sauƙi mu yi wa mutane da yawa wa’azi. Saboda haka, zai fi kyau mu riƙa amfani da na’ura sosai a hidimarmu ga Jehobah. Ta yin hakan, muna goyon bayan Kristi wanda yake so mu mai da hankali ga yadda muke amfani da gudummawa da ake bayarwa.

19. Me ya sa ya kamata mu bi ja-gorancin Kristi?

19 Idan muka bi ja-gorancin Kristi, za mu taimaka wa ’yan’uwanmu su ƙarfafa bangaskiyarsu kuma su kasance da haɗin kai. André ya yi furucin nan game da canje-canje da aka yi kwanan nan da suka shafi waɗanda suke hidima a Bethel. Ya ce: “Halin kirki da masu hidima a Bethel a dā suka nuna ya ƙarfafa ni kuma ina daraja su. Suna bin ja-gorancin Jehobah ta wajen yin farin ciki a kowace irin hidima da aka ce su yi.”

KU KASANCE DA BANGASKIYA KUMA KU DOGARA GA SHUGABANMU

20, 21. (a) Me ya sa ya dace mu dogara ga Kristi Shugabanmu? (b) Wace tambaya ce za mu tattauna a talifi na gaba?

20 Ba da daɗewa ba, Shugabanmu Yesu Kristi zai ‘ci nasara’ kuma zai “aikata ayyukan ban mamaki!” (R. Yar. 6:2; Zab. 45:4) Amma, a yanzu yana shirya mu don yin rayuwa a sabuwar duniya da kuma aikin da za mu yi a wurin. A lokacin, kowannenmu zai koyar da waɗanda aka ta da daga mutuwa kuma mu sa duniya ta zama aljanna.

21 Muddin mun dogara ga Shugabanmu ko da mene ne ya faru, zai sa mu shiga cikin sabuwar duniya. (Karanta Zabura 46:​1-3.) A yau, mukan yi fama da canje-canje, musamman idan hakan ya shafe mu a hanyar da ba mu yi zato ba. Ta yaya za mu kasance da kwanciyar rai da kuma bangaskiya ga Jehobah idan hakan ya faru? Za mu tattauna wannan tambayar a talifi na gaba.

^ sakin layi na 8 Masu tonon ƙasa sun sami hatsi mai yawa a birnin Yeriko. Hakan ya nuna cewa sojojin Isra’ilawa sun kewaye birnin Yeriko na ɗan lokaci ne kafin su halaka shi kuma abincin mutanen Yeriko bai ƙare ba. Da yake Jehobah bai yarda Isra’ilawa su kwashi ganima a Yeriko ba, lokacin da suka kai wa ƙasar hari ya dace domin lokacin girbi ne kuma akwai hatsi sosai a gonaki.​—Yosh. 5:​10-12.

^ sakin layi na 11 Ka duba akwatin nan “Bulus Ya Fuskanci Gwaji da Tawali’u” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Afrilu, 2003, shafi na 18.