Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

Jehobah Ya Albarkace Ni Sosai Don Zabin da Na Yi

Jehobah Ya Albarkace Ni Sosai Don Zabin da Na Yi

Wata rana a shekara ta 1939, mun tashi da tsakar dare kuma muka yi tafiya da mota fiye da awa guda zuwa wani ƙaramin birnin Joplin da ke kudu maso yammacin jihar Missouri a Amirka. Da muka isa wuri, sai muka soma saka warƙoƙi a ƙarƙashin kowace ƙofa da ke yankin. Bayan haka, muka shiga mota don mu je mu sami sauran ’yan’uwanmu. A lokacin, gari ya ɗan waye, amma me ya sa muka fita yin wa’azi kafin gari ya waye kuma muka bar yankin nan da nan? Zan gaya muku an jima.

INA farin ciki cewa iyayena Fred da Edna Molohan masu ibada ne sosai. Sun soma bauta wa Jehobah shekara 20 kafin a haife ni a shekara ta 1934. Ina godiya don sun koyar da ni in zama mai son ibada sosai. Muna zama a ƙaramin garin Parsons da ke kudu maso gabas a jihar Kansas. Muna cikin ikilisiya da kusan dukan ’yan’uwan shafaffu ne. Muna halartan taron ikilisiya a kai a kai kuma muna yi wa mutane wa’azi game da Kalmar Allah. Mukan yi wa’azi a kan titi a ranar Asabar da rana, yanzu muna kiran sa yin wa’azi ga jama’a. A wasu lokuta mukan gaji sosai, amma idan muka gama, mahaifinmu yakan saya mana ƙanƙara mai zaki kuma hakan yana sa mu farin ciki sosai.

Yankin da ikilisiyarmu ke wa’azi a ciki yana da girma sosai. Domin ya haɗa da ƙananan garuruwa da kuma gonaki da yawa da ke ƙauyuka kusa da mu. Maimakon wasu manoma su ba mu kuɗi don littattafanmu, sukan ba mu kayan lambu da ƙwai ko kuma kaji. Tun da yake mahaifinmu ya riga ya ba da gudummawa don littattafan, mukan ci waɗannan abubuwan.

YIN WA’AZI

Iyayena sun samo garmaho da suke saka faifai da ke ɗauke da jawabi a wa’azi. Ban iya amfani da garmahon ba don ni ƙaramin yaro ne sosai a lokacin, amma ina jin daɗin taimaka wa iyayena saka jawaban Ɗan’uwan Rutherford sa’ad da suka koma ziyara ko kuma suke nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane.

Ni da iyayena a gaban motarmu mai lasifika

Mahaifina ya saka lasifika a motarmu kirar ford na shekara ta 1936. Wannan motar ta taimaka mana sosai a wa’azi. Mukan soma da saka sauti don mu jawo hankalin mutane. Bayan haka, sai mu sa wani jawabin Littafi Mai Tsarki. Idan jawabin ya ƙare, mukan ba mutane masu son saƙonmu littattafai.

A ƙaramin garin Cherryvale da ke Kansas, ’yan sanda sun gaya wa mahaifinmu kada ya ajiye motar a wurin da mutane suke shaƙatawa a garin. Don mutane da yawa suna hutawa a wurin a ranar Lahadi, amma yana iya ajiyewa a waje. Saboda haka, mahaifinmu ya ajiye motar yadda za ta fuskanci wurin shaƙatawar don mutane su ji saƙon da kyau. Nakan yi farin ciki kasancewa da mahaifinmu da kuma yayana Jerry a lokacin da muke yin wannan wa’azin.

Kafin shekara ta 1940, muna yin wa’azi na musamman a wuraren da mutane ba sa son jin saƙonmu. Kamar yadda muka yi a Joplin da ke jihar Missouri, mukan tashi da tsakar dare kuma mu saka warƙoƙi ko kuma ƙasidu a ƙarƙashin ƙofar gidajen mutane. Bayan haka, sai mu fita daga birnin kuma mu taru don mu ga ko akwai mutumin da ’yan sanda suka kama.

A wannan lokacin, wani fannin wa’azi da muka ji daɗinsa sosai shi ne yin shela da fosta. Don mu yi shelar Mulki, mukan rataye fosta a wuya kuma mu riƙa tafiya a layi a gefen hanya. Na tuna cewa akwai lokacin da ’yan’uwa suka zo garinmu kuma suka yi hakan. Sun rataye fosta da aka rubuta “Religion Is a Snare and a Racket,” wato “Addini Tarko ne da kuma Hayaniya.” Sun yi tafiya na mil ɗaya a garin kuma suka dawo gidanmu. Mun yi farin ciki cewa babu wanda ya tsananta musu kuma mutane da yawa sun so su san abin da yake faruwa.

TARON YANKI A DĀ

Mukan yi tafiya daga jihar Kansas zuwa jihar Texas don halarta manyan taro. A lokacin, mahaifinmu yana aiki da wani kamfanin jirgin ƙasa, saboda haka mukan yi tafiya a jirgi zuwa manyan taro ba tare da biyan ko sisi ba. Muna yin amfani da wannan zarafin don mu ziyarci danginmu. Yayan mahaifiyarmu mai suna Fred Wismar da matarsa Eulalie suna zama a birnin Temple da ke jihar Texas. Kawunmu Fred ya koyi gaskiya bayan shekara ta 1900 sa’ad da yake matashi. Sai ya yi baftisma kuma ya koya wa ’yan’uwansa har da mahaifiyarmu abin da ya koya. ’Yan’uwa da suke yankunan da ke tsakiyar Texas sun san shi sosai don akwai lokacin da ya yi hidimar mai kula da da’ira. Shi mutumi ne mai fara’a da alheri da kuma ƙwazo. Babu shakka, ya kafa mini misali mai kyau a lokacin da nake matashi.

A shekara ta 1941, mun yi tafiya a jirgin ƙasa zuwa birnin St. Louis da ke jihar Missouri don mu halarci babban taro. An gaya wa dukan matasa su zauna a wani wuri da aka keɓe musu don su saurari jawabin Ɗan’uwa Rutherford mai jigo “Children of the King” (“Yaran Sarkin.”) Da ya gama jawabin, mun yi mamaki da Ɗan’uwa Rutherford da mataimakansa suka ba kowannenmu kyautar sabon littafi mai jigo Children. Yara fiye da 15,000 ne suka sami wannan albarka daga wurin Jehobah.

A watan Afrilu 1943 mun halarci wani babban taro mai jigo “Call to Action” a birnin Coffeyville da ke jihar Kansas. A taron ne aka sanar da cewa za a soma wata makaranta da ake kira Makarantar Hidima ta Allah a dukan ikilisiyoyi. Mun kuma karɓi sabuwar ƙasida mai darussa 52 da za a yi amfani da ita a makarantar. A wannan shekarar ne na yi jawabina na farko. Ba zan taɓa manta wannan taron ba don a wurin ne na yi baftisma tare da wasu a cikin ruwan tafki mai sanyi sosai da ke wata gona a kusa da wurin taron.

INA SON IN YI HIDIMA A BETHEL

Na gama makarantar sakandare a 1951 kuma na bukaci in tsai da shawarar abin da zan yi da rayuwata. Yayana Jerry ya yi hidima a Bethel. Saboda haka, ni ma na so in je Bethel, sai na tura fom zuwa Bethel da ke Brooklyn. Ba da daɗewa ba, aka gayyace ni zuwa Bethel kuma na soma hidima a ranar 10 ga Maris, 1952. Wannan zaɓin ya taimaka mini in bauta wa Allah da aminci.

Na so in yi aiki a wurin da ake buga littattafai don in riƙa taimaka wajen buga mujallunmu, amma ban sami wannan gatar ba. An ce in yi aikin ba da abinci kuma daga baya na soma aiki a wurin dafa abinci. Na ji daɗin yin wannan aiki kuma na koyi abubuwa da yawa. A wurin dafa abincin, wasu cikinmu na aiki da safe a wasu lokuta, wasu kuma da rana. Hakan yana sa in sami lokacin yin nazari a laburaren da ke Bethel. Hakan ya taimaka mini in ƙarfafa bangaskiyata da kuma dangantakata da Jehobah. Kuma na ƙara ƙuduri niyyar in bauta wa Jehobah a Bethel muddar raina. Yayana Jerry ya bar Bethel a 1949 kuma ya auri Patricia, amma wurin da suke ba shi da nisa daga Bethel da ke Brooklyn. Sun taimaka mini kuma sun ƙarfafa ni sa’ad da na soma hidima a Bethel.

Ba da daɗewa ba da na zo Bethel, sai aka soma neman masu hidima a Bethel da za a riƙa tura yin jawabai. Akan tura ’yan’uwan da aka zaɓa su je yin jawabi a ikilisiyoyi masu nisan mil 200 daga Brooklyn. Bayan hakan sai su fita yin wa’azi da ’yan’uwa a ikilisiyar. Ni ma an zaɓe ni, sai na soma yin jawabi kuma a lokacin ana yin jawabi awa guɗa. Nakan je waɗannan ikilisiyoyin a jirgin ƙasa. Na tuna wata ranar Lahadi da rana da ake sanyin sosai a shekara ta 1954. Na shiga jirgin da zai koma birnin New York kuma ya kamata in kai Bethel da yamma. Amma da muke hanya sai aka soma ƙanƙara da iska sosai. Hakan ya ɓata jirgin, kuma ban isa birnin New York da wuri ba sai da ƙarfe biyar na asuba a ranar Litinin. Na shiga mota daga tashar jirgin zuwa Brooklyn kuma na koma wurin aiki nan da nan. Ko da yake na ɗan makara kuma na gaji domin ban yi barci daddare ba, amma farin cikin yin hidima tare da ikilisiya da kuma haɗuwa da ’yan’uwa da yawa sun sa ban damu da wahalar da na sha ba.

Muna shirin tattaunawa a tashar rediyo na WBBR

A lokacin da na soma hidima a Bethel, an gayyace ni in soma yin shirye-shiryen nazarin Littafi Mai Tsarki da ake yi kowane mako a tashar rediyo na WBBR. A lokacin, tashar tana hawa na biyu a ginin 124 Columbia Heights. Aikina shi ne yin kwaikwayon ɗaya cikin mutanen da suke shirye-shirye na nazarin Littafi Mai Tsarki da ake yi kowane mako. Ɗan’uwa A. H. Macmillan da ya daɗe yana hidima a Bethel, yakan gudanar da waɗannan shirye-shiryen a kai a kai. Muna kiransa Ɗan’uwa Mac kuma ya kafa wa matasa a Bethel misali mai kyau domin ya kasance da aminci duk da cewa ya fuskanci matsaloli da yawa.

Mukan rarraba warƙar shirye-shiryen tashar WBBR don mutane su saurara

An canja aikina a 1958 kuma na soma aiki da waɗanda suka sauke karatu daga Makarantar Gilead. Nakan taimaka wa waɗannan ’yan’uwa masu ƙwazo su sami takardar izinin shiga ƙasar da aka tura su da kuma shirya yadda za su tafi ƙasashen. Yin tafiya a jirgin sama yana da tsada sosai a lokacin. Saboda haka, kaɗan ne kawai suke tafiya a jirgin sama. Yawancin da suke zuwa Afirka da Asiya suna hakan da jirgin ruwa. Amma bayan wasu shekaru sai farashin tafiya a jirgin sama ya sauka kuma yawancin masu wa’azi a ƙasar waje suka soma tafiya da jirgin sama.

Ina shirya difloma kafin bikin sauke karatu na makarantar Gilead

TAFIYE-TAFIYE ZUWA MANYAN TARO

A shekara ta 1960, an ce in shirya wa ’yan’uwan da za su je taron ƙasashe a shekara ta 1961 jirgin sama daga Amirka zuwa Turai. Na bi jirgin da muka yi hayar sa daga New York zuwa birnin Hamburg da ke Jamus don in halarci taron. Bayan taron, ni da ’yan’uwa uku a Bethel muka yi hayar mota daga Jamus zuwa Italiya. Mun ziyarci ofishinmu da ke Roma, daga wajen muka je Faransa kuma muka haye Dutsen Pyrenees muka shiga Sifen inda gwamnati ta saka wa aikinmu takunkumi. Ban da haka, mun ba ’yan’uwanmu da ke Barceloniya wasu littattafan da aka ƙunsa kamar kyauta. Mun yi farin ciki sosai da muka haɗu da ’yan’uwan! Sai muka shiga mota zuwa Amsterdam wurin da muka shiga jirgin sama don mu koma New York.

Bayan shekara ɗaya, an gaya mini in shirya tafiye-tafiye don ’yan’uwa 583 da za su halarci taron ƙasashe dabam-dabam da za a yi a faɗin duniya. An yi wannan taro mai jigo “Everlasting Good News” a shekara ta 1963 kuma ’yan’uwan za su halarci taro a Turai da Asiya da kuma Fasifik ta Kudu. Daga wajen za su je Hawaii da Pasadena da kuma Kalifoniya. Ƙari ga haka, za su ziyarci Lebanon da Urdun don su yi yawon buɗe ido na musamman a wasu ƙasashen da aka ambata a Littafi Mai Tsarki. Ban da shirya tafiye-tafiye da jirgin sama, mun samo wa dukan waɗannan ’yan’uwa takardar izinin shiga waɗannan ƙasashen.

NA SAMI ABOKIYAR TAFIYA

Shekara ta 1963 tana da muhimmanci sosai a gare ni. Na auri Lila Rogers ’yar jihar Missouri a ranar 29 ga Yuni, ta soma hidima a Bethel shekara uku kafin lokacin. Bayan mako guda da aure, ni da matata Lila muka soma tafiye-tafiye da ya kai mu Girka da Masar da kuma Lebanon. Daga wajen muka shiga jirgi daga birnin Beirut zuwa ƙaramin tashar jirgin sama da ke Jordan. Gwamnati ta saka takunkumi a aikinmu. Don haka, ba ta ba Shaidun Jehobah bizan shiga ƙasar ba. Saboda haka, ba mu san abin da zai faru ba sa’ad da muka isa. Amma mun yi farin ciki sosai sa’ad da muka ga ’yan’uwa suna tsaye a kan wani ginin da ke tashar jirgin saman da babban fosta da aka rubuta “Marabanku Shaidun Jehobah”! Mun yi farin ciki sosai da kuma ziyarci wasu ƙasashe da aka ambata a Littafi Mai Tsarki. Mun ga wuraren da Ibrahim da Ishaƙu da Yakubu suka zauna. Ƙari ga haka, mun ga wuraren da Yesu da manzanninsa suka yi wa’azi da wurin da aka soma yaɗa Kiristanci zuwa iyakar duniya.​—A. M. 13:47.

Matata Lila ta yi shekara 55 tana taimaka mini a dukan hidimarmu. Mun ziyarci Sifen da Portugal sau da yawa sa’ad da gwamnatocin ƙasashen ta saka wa aikinmu takunkumi. Mun ƙarfafa ’yan’uwan kuma muka kai musu littattafai da wasu abubuwa. Ƙari ga haka, mun ziyarci wasu ’yan’uwanmu da suke kurkuku a birnin Cádiz da ke Sifen. Na yi farin ciki cewa na yi musu jawabin da ya ƙarfafa su.

Mu da Jerry Molohan da matarsa Patricia sa’ad da za mu taron “Peace on Earth” a shekara ta 1969

Tun daga shekara ta 1963, na soma taimakawa wajen shirya wa ’yan’uwa yawon buɗe ido a lokacin taron ƙasashe. Muna kai su Afirka da Ostareliya da Amirka ta Tsakiya da ta Kudu da Turai da Asiya da Hawaii da New Zealand da kuma Puerto Rico. Ni da matata mun ji daɗin halartan taro da yawa da ba za mu taɓa mantawa ba, har da wanda aka yi a shekara 1989 a birnin Warsaw da ke ƙasar Poland. ’Yan’uwa da yawa daga ƙasar Rasha sun halarci wannan babban taro, kuma wannan ne taronsu na farko! Mun haɗu da ’yan’uwa da aka tsare a kurkuku a ƙasar Rasha ta dā don imaninsu.

Wata hidimar da na ji daɗinsa sosai ita ce ziyarar ofisoshinmu don in ƙarfafa waɗanda suke hidima a Bethel da kuma masu wa’azi a ƙasar waje. Ofishi na ƙarshe da muka kai wa ziyara shi ne Koriya ta Kudu. A ƙasar mun haɗu da ’yan’uwa 50 da suke kurkuku a birnin Suwon. Waɗannan ’yan’uwan ba su fid da rai ba kuma suna jiran lokacin da za a ɗage takunkumin da gwamnati ta saka wa aikinsu. Haɗuwa da su ya ƙarfafa mu sosai!​—Rom. 1:​11, 12.

ƘARUWA DA NA SHAIDA TANA SA NI FARIN CIKI

Na ga yadda Jehobah ya albarkaci mutanensa sosai. Sa’ad da na yi baftisma a 1943, akwai masu shela 100,000 a faɗin duniya. Yanzu muna da masu shela fiye da 8,000,000 da ke bauta wa Jehobah a ƙasashe 240. Aiki tuƙuru da waɗanda suka sauke karatu a Gilead suka yi ya taimaka sosai. Na yi farin cikin yin aiki tare da waɗannan masu wa’azi a ƙasar waje da kuma taimaka musu su tafi ƙasashen za su yi hidima!

Na yi farin ciki cewa sa’ad da nake matashi na zaɓi in faɗaɗa hidimata ta wurin yin hidima a Bethel. Jehobah ya albarkace ni sosai a waɗannan shekarun. Ban da abubuwan da muka ji daɗinsu a hidimarmu a Bethel, ni da matata mun ji daɗin yin wa’azi da ’yan’uwan da ke ikilisiyoyi da yawa a Brooklyn kuma mun yi abokai da yawa.

Ina hidima a Bethel har yanzu kuma matata tana taimaka mini a kowace rana. Ko da yake na wuce shekara 84, har ila ina farin ciki cewa ina taimakawa a sashen rubuta wasiƙu.

Ni da matata Lila a yau

Ina farin ciki kasancewa cikin ƙungiyar Jehobah da kuma ganin bambancin da ke tsakanin waɗanda suke bauta wa Jehobah da waɗanda ba sa bauta masa. Ƙari ga haka, mun ƙara fahimtar abin da ke cikin Malakai 3:18 cewa: “Za ku sāke ganin bambanci tsakanin mai adalci da mugu, kuma tsakanin wanda yake bauta wa Allah da wanda ba ya bauta masa.” A kowace rana muna ganin yadda duniyar Shaiɗan take taɓarɓarewa, mutane ba su da bege kuma ba sa farin ciki. Amma waɗanda suke ƙaunar Jehobah da kuma bauta masa suna farin ciki ko a mawuyacin lokaci kuma suna da bege cewa abubuwa za su gyaru a nan gaba. Gata ce babba, mu riƙa wa’azi game da Mulkin Allah! (Mat. 24:14) Muna ɗokin ganin ranar da Mulkin Allah zai halaka mugaye a wannan duniyar kuma ya mayar da ita aljanna. A lokacin kowa a duniya zai kasance da ƙoshin lafiya kuma ya yi rayuwa har abada.