Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Rika Fadin Gaskiya

Ka Rika Fadin Gaskiya

“Ku faɗa wa juna gaskiya.”​—ZAK. 8:​16, Littafi Mai Tsarki.

WAƘOƘI: 56, 124

1, 2. Mene ne ya fi kasancewa da mugun sakamako ga ’yan Adam, wane ne ya jawo hakan?

WASU abubuwan da aka ƙirƙiro kamar waya da wutar lantarki da motoci da kuma firiji suna sa mutane jin daɗin rayuwa. Amma wasu kamar bindigogi da bama-bamai da ake binnewa a ƙasa da sigari da kuma makamin nukiliya da dai sauransu suna jawo haɗari ga rayuwa. Duk da haka, da akwai abin da ya fi dukan waɗannan abubuwan daɗewa da kuma haɗari. Me ke nan? Ƙarya ce! Wato faɗin wani abu da mutum ya san cewa ba gaskiya ba ne domin ya yaudari wani. Wane ne ya fara yin ƙarya? Yesu Kristi ya kira shi “Shaiɗan” da “Uban ƙarya.” (Karanta Yohanna 8:44.) A wane lokaci ne Shaiɗan ya yi ƙarya ta farko?

2 Ya yi hakan a lambun Adnin shekaru dubbai da suka shige. A lokacin, Adamu da Hauwa’u suna jin daɗin rayuwa a cikin Aljanna da Mahaliccinsu ya saka su. Allah ya gaya musu cewa za su mutu idan sun ci daga “itace mai kawo sanin nagarta da mugunta.” Ko da yake Shaiɗan ya san da haka, amma ya yi amfani da maciji don yin magana da Hauwa’u cewa: “Ko kaɗan, ba za ku mutu ba [ƙarya na farko]. Gama Allah ya sani cewa a ranar da kuka ci daga ’ya’yan itacen nan, idanunku za su buɗe. Za ku kuwa zama kamar Allah, masu sanin nagarta da mugunta.”​—Far. 2:​15-17; 3:​1-5.

3. Me ya sa aka ce Shaiɗan ya yi mugun ƙarya, wane mugun sakamako ne hakan ya jawo?

3 Wannan mugun ƙarya ne domin Shaiɗan ya san cewa Hauwa’u za ta mutu idan ta gaskata da shi kuma ta ci ’ya’yan itacen. Adamu da Hauwa’u sun yi wa Jehobah rashin biyayya kuma daga baya suka mutu. (Far. 3:6; 5:5) Ban da haka, domin zunubin Adamu, “mutuwa ta bi ta shiga dukan ’yan Adam.” Hakika, “mutuwa ta yi mulki a kan mutane . . . , har ma ta yi iko a kan waɗanda zunubansu ba na karya doka ba ne kamar yadda na Adam ya kasance.” (Rom. 5:​12, 14) Hakan ya sa mun zama ajizai kuma ba ma rayuwa har abada yadda Allah ya so mu yi. Maimakon haka, muna rayuwa shekara “saba’in ne, ko tamanin, in mun sami ƙarfi.” Duk da haka, “fama ne tare da wahala” ake yi a rayuwa. (Zab. 90:10) Dukan waɗannan abubuwa suna faruwa ne domin ƙaryar da Shaiɗan ya yi!

4. (a) Waɗanne tambayoyi ne muke bukatar mu amsa? (b) Wane ne aka ce zai iya zama abokin Jehobah a littafin Zabura 15:​1, 2?

4 Sa’ad da Yesu yake magana game da Shaiɗan, ya ce: “Ba ruwansa da gaskiya, domin babu gaskiya a cikinsa.” Har ila, Shaiɗan ba ya faɗin gaskiya domin ya ci gaba da ‘ruɗin dukan duniya’ da ƙaryace-ƙaryacensa. (R. Yar. 12:9) Amma, ba ma son Iblis ya yaudare mu. Saboda haka, bari mu tattauna tambayoyi uku: Ta yaya Shaiɗan yake yaudarar mutane? Me ya sa mutane suke ƙarya? Kuma ta yaya za mu riƙa “faɗin gaskiya” a kowane lokaci don kada mu ɓata abokantakarmu da Jehobah, kamar Adamu da Hauwa’u?​—Karanta Zabura 15:​1, 2.

YADDA SHAIƊAN YAKE YAUDARAR MUTANE

5. Ta yaya Shaiɗan yake yaudarar mutane a yau?

5 Manzo Bulus ya san cewa za mu iya yin iya ƙoƙarinmu don “kada Shaiɗan ya sami dama ya ruɗe mu, saboda mun san dabarunsa sarai.” (2 Kor. 2:11) Mun san cewa Shaiɗan ne yake mulkin dukan duniya, har da addinin ƙarya da gwamnatoci da kuma ’yan kasuwa masu haɗama. (1 Yoh. 5:19) Saboda haka, ba abin mamaki ba ne cewa Shaiɗan da aljanunsa suna rinjayar masu iko su riƙa yin “ƙarya.” (1 Tim. 4:​1, 2) Alal misali, wasu masu kasuwanci suna ƙarya a tallar da suke yi don su sayar da kayansu masu lahani ko kuma su ruɗi mutane don su karɓi kuɗinsu.

6, 7. (a) Me ya sa shugabannin addinai da suke ƙarya suke da laifi sosai? (b) Waɗanne ƙaryace-ƙaryace ne ka ji shugabannin addinai suke yi?

6 Me ya sa shugabannin addinai da suke ƙarya suke da laifi sosai? Domin mutanen da suke gaskata da ƙaryace-ƙaryacensu kuma suke yin abin da Allah ba ya so ba za su sami rai na har abada ba. (Hos. 4:9) Yesu ya san cewa shugabannin addinai a zamaninsa sun yaudari mutane. Shi ya sa ya gaya musu cewa: “Kaitonku malaman Koyarwar Musa da Farisiyawa, munafukai! Gama kukan ƙetare teku, kukan kai ƙasashe masu nisa domin samun mai tuba ɗaya. Idan kuwa kuka samu, sai ku mai da shi ɗan gidan wuta [halaka ta har abada] fiye da ku sau biyu.” (Mat. 23:15) Yesu ya ce waɗannan shugabannin addinan ƙarya suna kamar ubansu Shaiɗan domin shi “mai kisa ne.”​—Yoh. 8:44.

7 A yau ma, da akwai shugabannin addinai da yawa. Ana iya kiran su fastoci ko firistoci ko malamai da dai sauransu. Kamar Farisawa a dā, suna “danne gaskiya” da ke cikin Kalmar Allah kuma “sun mai da gaskiyar Allah ta zama ƙarya.” (Rom. 1:​18, 25) Suna koyar da ƙarya cewa Allah zai ƙona mutane a wuta. Ƙari ga haka, suna koyar da cewa kurwa ba ta mutuwa da kuma cewa idan mutum ya mutu, za a sake haifan sa. Ban da haka, suna koyar da cewa Allah yana amincewa da daudanci da kuma auren jinsi ɗaya.

8. Wace ƙarya ce ’yan siyasa za su yi nan ba da daɗewa ba, kuma wane ra’ayi ne ya kamata mu kasance da shi?

8 ’Yan siyasa ma masu ƙarya suna yaudarar mutane. Wani mugun ƙarya da za su tabka nan ba da daɗewa ba shi ne cewa sun kawo “zaman lafiya da salama” a duniya, amma “halaka za ta auko musu” farat ɗaya. Saboda haka, bai kamata mu riƙa gaskata da waɗannan shugabanni ’yan siyasa ba. Ƙarya ne kawai suke yi cewa duniya za ta gyaru. Gaskiyar ita ce, mun san “cewa Ranar Ubangiji za ta zo kamar zuwan ɓarawo da dare.”​—1 Tas. 5:​1-4.

ABIN DA YA SA MUTANE SUKE ƘARYA

9, 10. (a) Me ya sa mutane suke ƙarya, kuma mene ne sakamakon hakan? (b) Me ya kamata mu riƙa tunawa game da Jehobah?

9 A yau, ba masu iko kaɗai ba ne suke yin ƙarya ba, amma mutane a ko’ina suna yin ƙarya. A cikin wani talifi mai jigo “Why We Lie” (Abin da Ya Sa Muke Ƙarya), wanda Y. Bhattacharjee ya wallafa, an ce: “Ƙarya ta zama halin da ’yan Adam suka saba da shi.” Wato, mutane suna ganin ya dace a riƙa yin ƙarya. Mutane sukan yi ƙarya don su kāre kansu ko kuma su ɗaukaka kansu. Suna ƙarya don su ɓoye kuskurensu ko kuma muguntar da suka yi. Ƙari ga haka, suna ƙarya don su sami kuɗi ko kuma su sami riba. Kamar yadda aka faɗa a talifin, akwai mutanen da suke ganin “ba laifi ba ne su yi wa baƙi ko abokan aikinsu ko abokansu ko kuma danginsu ƙarya.”

10 Mene ne sakamakon dukan waɗannan ƙaryace-ƙaryacen da mutane suke yi? Mutane ba sa amincewa da juna kuma hakan yakan ɓata dangantaka. Alal misali, ka yi tunanin yadda miji zai ji sa’ad da ya san cewa matarsa ta ci amanarsa kuma ta yi masa ƙarya don ta ɓoye abin da ta yi. Ko kuma magidanci da yake wulaƙanta matarsa da yaransa a gida, amma a gaban mutane sai ya yi kamar shi mai kirki ne. Ya kamata mu tuna cewa irin waɗannan mutanen suna iya yaudarar ’yan Adam, amma ba za su iya yaudarar Jehobah ba. Me ya sa? Domin “kome da kome yana nan a buɗe a fili” a gabansa.​—Ibran. 4:13.

11. Mene ne mugun misalin Hananiya da Safiratu ya koya mana? (Ka duba hoton da ke shafi na 6.)

11 A cikin Littafi Mai Tsarki an ambata yadda Shaiɗan ya sa wasu ma’aurata a ƙarni na farko su yi ƙarya. Hananiya da Safiratu sun ƙulla a zuciyarsu su yaudari manzannin Yesu. Sun sayar da filinsu kuma suka kawo ma manzannin wani sashe na kuɗin. Suna so su burge mutane a ikilisiyar, saboda haka, suka gaya wa manzannin cewa sun ba da dukan kuɗin da suka sayar da filin. Amma Jehobah ya san cewa ƙarya suke yi kuma ya hukunta su.​—A. M. 5:​1-10.

12. Mene ne zai faru da masu ƙaryace-ƙaryace, kuma me ya sa?

12 Yaya Jehobah yake ji game da mutanen da suke ƙarya? Dukan mutanen da suke ƙaryace-ƙaryace da suka ƙi tuba za su ƙare a “tafkin wuta mai ƙuna” kamar Shaiɗan. Hakan yana nufi cewa za a halaka su har abada. (R. Yar. 20:10; 21:8; Zab. 5:6) Me ya sa? Domin Jehobah yana ɗaukan waɗannan masu ƙaryace-ƙaryace a matsayin waɗanda suke ƙazantar da kansu.​—R. Yar. 22:15.

13. Mene ne muka sani game da Jehobah, kuma me hakan zai motsa mu mu yi?

13 Mun san cewa Jehobah “ba mutum ba ne, da zai yi ƙarya!” Hakika, “ba zai yiwu Allah ya yi” ƙarya ba. (L. Ƙid. 23:19; Ibran. 6:18) Jehobah “ya ƙi . . . harshe mai faɗin ƙarya.” (K. Mag. 6:​16, 17) Idan muna so mu faranta ransa, wajibi ne mu riƙa faɗin gaskiya a kowane lokaci. Shi ya sa ba ma “yi wa juna ƙarya.”​—Kol. 3:9.

MUNA FAƊIN “GASKIYA”

14. (a) Ta yaya muka bambanta da waɗanda suke bin addinan ƙarya? (b) Ka bayyana ƙa’idar da ke Luka 6:45.

14 A wace hanya ɗaya ce Kiristoci na gaske suka bambanta da mabiyan addinan ƙarya? Hanyar ita ce don muna faɗin gaskiya. (Karanta Zakariya 8:​16, 17.) Bulus ya bayyana: ‘Mu nuna cewa mu masu hidimar Allah ne, . . . ta saƙonmu ta gaskiya.’ (2 Kor. 6:​4, 7) Kuma Yesu ya ce: “Abin da yake cikin zuciya, ai, shi yake fitowa a baki.” (Luk. 6:45) Hakan yana nufin cewa mutumin kirki zai riƙa faɗin gaskiya a kowane lokaci. Zai gaya wa baƙi ko abokan aikinsa ko abokai ko kuma ’yan gidansu gaskiya. Bari mu tattauna wasu misalan yadda za mu nuna cewa muna ƙoƙari mu riƙa faɗin gaskiya a dukan abubuwa.

Wace irin rayuwa ce wannan ’yar’uwa matashiya take yi? (Ka duba sakin layi na 15, 16)

15. (a) Me ya sa bai kamata mu riƙa bin salon rayuwar da bai dace ba? (b) Mene ne zai taimaka wa matasa su guji faɗawa cikin matsi? (Ka duba ƙarin bayani.)

15 Idan kai matashi ne, kana iya son tsararka su amince da kai. Saboda haka, wasu matasa suna bin salon rayuwar da bai dace ba. Suna yi kamar su masu halin kirki ne sa’ad da suke tare da iyalinsu da kuma ’yan’uwa a ikilisiya. Amma suna yin wani abu dabam sa’ad da suke shafin sada zumunta na intane ko kuma sa’ad da suke tare da waɗanda ba Shaidu ba ne. Suna iya yin baƙar magana ko saka tufafin da ba su dace ba ko su saurari waƙoƙin banza. Suna iya yin maye ko shan ƙwaya ko su riƙa fita zance a ɓoye ko kuma su yi wasu ayyukan da ba su dace ba. Suna wa iyayensu da ’yan’uwa da kuma Allah ƙarya. (Zab. 26:​4, 5) Jehobah ya san sa’ad da muke da’awa cewa muna girmama shi da bakinmu kawai amma zukatanmu sun yi nesa da shi. (Mar. 7:6) Ya fi kyau mu yi abin da aka faɗa a littafin Karin Magana cewa: “Kada ka bar zuciyarka ta yi kishin mai zunubi, amma ka ƙaunaci Yahweh dukan yini.”​—K. Mag. 23:17. *

16. Me ya sa muke bukatar mu faɗi gaskiya sa’ad da muke cika fom na yin hidima?

16 Wataƙila kana son ka soma hidimar majagaba na kullum ko kuma hidima ta musamman kamar yin aiki a Bethel. Sa’ad da kake cika fom, yana da muhimmanci ka faɗi gaskiya ga dukan tambayoyi da aka yi a cikin fom ɗin da suka shafi lafiyar jikinka da nishaɗin da kake so da kuma halayenka. (Ibran. 13:18) Ƙari ga haka, idan ka yi wani abu da Jehobah ba ya so kuma ba ka gaya wa dattawa ba, kana bukatar ka nemi taimakonsu don ka yi hidima da zuciya mai tsabta.​—Rom. 9:1; Gal. 6:1.

17. Mene ne za mu yi sa’ad da masu hamayya suka yi mana tambayoyi game da ’yan’uwanmu?

17 Mene ne za ka yi idan hukuma ta saka wa aikinmu takunkumi a ƙasarku kuma an kira ka don a yi maka tambayoyi? Zai dace ne ka gaya musu kome da ka sani? Mene ne Yesu ya yi sa’ad da gwamnar Roma ya yi masa tambayoyi? Akwai lokutan da Yesu bai ce kome ba don ya bi ƙa’idar da ke cikin Nassi da ta ce, “akwai lokacin yin shiru, da lokacin yin magana.” (M. Wa. 3:​1, 7; Mat. 27:​11-14) Idan muna cikin irin wannan yanayin, muna bukatar mu kasance da basira don kada mu saka ’yan’uwa a cikin haɗari.​—K. Mag. 10:19; 11:12.

Ta yaya za ka san lokacin da za ka yi shiru da lokacin da za ka faɗa gaskiya? (Ka duba sakin layi na 17, 18)

18. Mene ne ya kamata mu yi idan dattawa suka yi mana tambayoyi game da ’yan’uwa?

18 Idan wani a cikin ikilisiya ya yi zunubi mai tsanani kuma ka san abin da ya faru fa? Wataƙila dattawa sun kira ka kuma sun yi maka tambayoyi a kan batun, da yake su ke da hakkin tsabtace ikilisiya. Mene ne za ka yi, musamman idan batun ya shafi abokinka ko kuma danginka? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai faɗin gaskiya yana shelar adalci.” (K. Mag. 12:17; 21:28) Saboda haka, ya kamata ka gaya wa dattawa gaskiya ba rabin gaskiya ba ko kuma ka ɓoye wasu abubuwa. Zai dace dattawa su san gaskiyar don su san yadda za su taimaka wa mutumin ya gyara dangantakarsa da Jehobah.​—Yaƙ. 5:​14, 15.

19. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

19 Dawuda ya yi addu’a ga Jehobah cewa: “Lallai kana so in yi gaskiya daga zuciyata.” (Zab. 51:6) Ya san cewa abin da yake cikin zuciyarsa ne ya fi muhimmanci. Kiristoci na gaske suna faɗa wa juna gaskiya a kowane lokaci. Wata hanya da za mu iya nuna cewa mun bambanta da masu bin addinan ƙarya ita ce ta wajen koya wa mutane gaskiya game da Allah. A talifi na gaba, za mu tattauna yadda za mu yi hakan.

^ sakin layi na 15 Ka duba babi na 6 mai jigo, “Ta Yaya Zan Ƙi Matsi Daga Tsarana?” a ƙasidar nan Amsoshi ga Tambayoyi 10 da Matasa Suke Yi da kuma “A Double Life​—Who Has to Know?,” a littafin nan Questions Young People Ask​—Answers That Work, Littafi na 2, babi na 16.