Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Rika Koyar da Gaskiya

Ka Rika Koyar da Gaskiya

“Ya Yahweh, . . . ƙwayar maganarka gaskiya ce.”​—ZAB. 119:​159, 160.

WAƘOƘI: 29, 53

1, 2. (a) Wane aiki ne Yesu ya fi ɗauka da muhimmanci, kuma me ya sa? (b) Me za mu yi don mu yi nasara a matsayin “abokan aiki na Allah”?

YESU KRISTI kafinta ne kuma daga baya ya zama malami. (Mar. 6:3; Rom. 15:8) Ya ƙware a yin waɗannan ayyuka sosai. Da yake shi kafinta ne, ya koyi yin amfani da kayan aikinsa don ya ƙera abubuwa da katako. A matsayinsa na mai yin wa’azi, ya yi amfani da iliminsa na Nassosi don ya taimaka wa mutane su san Kalmar Allah sosai. (Mat. 7:28; Luk. 24:​32, 45) A lokacin da Yesu ya kai shekara 30, ya bar yin aikin kafinta domin ya san cewa yin wa’azi shi ne aiki mafi muhimmanci. Ya ce yin wa’azi game da Mulkin Allah yana cikin dalilan da suka sa Allah ya turo shi duniya. (Mat. 20:28; Luk. 3:23; 4:43) Yesu ya sa yin wa’azi game da Mulkin Allah ya zama abu na farko a rayuwarsa, kuma ya so wasu ma su yi wa’azi tare da shi.​—Mat. 9:​35-38.

2 Da yawa daga cikinmu ba kafintoci ba ne, amma mu masu wa’azi game da Mulkin Allah ne. Wannan aikin yana da muhimmanci sosai shi ya sa Allah yake goyon bayan aikin kuma ake kiran mu “abokan aiki na Allah.” (1 Kor. 3:9; 2 Kor. 6:4) Mun san cewa ‘ƙwayar maganar [Jehobah] gaskiya ce.’ (Zab. 119:​159, 160) Don haka, mu tabbatar da cewa muna “koyar da kalmar gaskiya daidai” a hidimarmu. (Karanta 2 Timoti 2:15.) Muna bukatar mu riƙa koyan yin amfani da Kalmar Allah yadda ya dace. Littafi Mai Tsarki ne asali abin da muke amfani da shi don koya wa mutane game da Jehobah da Yesu da kuma Mulkin Allah. Don mu yi nasara a wa’azi, ƙungiyar Jehobah ta yi mana tanadin abubuwan da muke bukatar mu riƙa amfani da su don koyarwa. Muna kiran su Kayan Aiki don Koyarwa.

3. Mene ne muke bukatar mu mai da wa hankali sa’ad da muke wa’azi, kuma ta yaya littafin Ayyukan Manzanni 13:48 zai taimaka mana mu yi hakan?

3 Kana iya yin mamakin dalilin da ya sa ake kiran sa da wannan sunan. Yin wa’azi yana nufin yin shelar wani saƙo, amma koyarwa tana nufin bayyana wa mutum abin da saƙon yake nufi har sai mutumin ya fahimta sosai kuma abin da ya koya ya motsa shi ya ɗauki mataki. Da yake ƙarshe ya kusa sosai, muna bukatar mu mai da hankali ga soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma koya wa mutane gaskiya game da Jehobah. Hakan yana nufin cewa muna bukatar mu mai da hankali ga neman mutanen da za su bauta wa Allah.​—Karanta Ayyukan Manzanni 13:​44-48.

4. Ta yaya za mu san mutane masu zuciyar kirki, kuma ta yaya za mu neme su?

4 Ta yaya za mu san waɗanda suke da zuciyar kirki? Kamar yadda yake a ƙarni na farko, hanya ɗaya da za mu iya sanin su ita ce ta wajen yi musu wa’azi. Saboda haka, muna bukatar mu yi abin da Yesu ya umurci almajiransa cewa: “Duk gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mutumin kirki.” (Mat. 10:11) Babu shakka, mutane marasa gaskiya da masu fahariya da kuma waɗanda ba sa so su san Allah ba za su saurare mu ba. Waɗanda suke da zuciyar kirki da tawali’u kuma suke so su koya game da Allah muke nema. Muna iya kwatanta yadda muke neman masu zuciyar kirki da abin da wataƙila Yesu ya yi a lokacin da yake aikin kafinta. Da farko, yana bukatar ya nemi katakon da ya dace don ya ƙera kujera ko ƙofa ko karkiya ko kuma wani abu dabam. A yau ma, muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu almajirantar da mutane masu zuciyar kirki.​—Mat. 28:​19, 20.

5. Mene ne muke bukatar mu sani game da Kayan Aiki don Koyarwa? Ka ba da misali. (Ka duba hoton da ke shafi na 11.)

5 A cikin akwatin kayan aiki, kowane abu na da amfaninsa. Alal misali, ka yi tunanin akwatin kayan aikin kafinta da Yesu ya yi amfani da shi. Yana bukatar abin gwada katako da zarto da alƙalami da abin huɗa katako da kuma abin sifanta shi da dai sauransu. Haka yake da Kayan Aiki don Koyarwa domin kowane littafi da bidiyo da ke cikinsa na da manufa. Saboda haka, bari mu ga yadda za mu riƙa yin amfani da su.

TANADODI DON GABATAR DA KANMU

6, 7. (a) A wace hanya ce ka yi amfani da takardar gayyata? (b) Wace manufa biyu ce takardar gayyatar take da ita?

6 Katin JW. Waɗannan ƙananan katuna ne da muke amfani da su don mu gabatar da kanmu kuma mu taimaka wa mutane su shiga dandalinmu. A dandalin, za su koyi abubuwa da yawa game da mu kuma za su iya cika fom don a yi nazari da su. Fiye da mutane 400,000 sun cika fom a dandalin jw.org don a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su kuma mutane da yawa suna cika fom kowace rana! Kai ma kana iya riƙe katin nan don ka ba mutane idan ka sami damar tattaunawa da su yayin da kake ayyukanka na yau da kullum.

7 Takardar Gayyata. Ko da yake muna yawan kiran ta takardar gayyata zuwa taro, wannan takardar tana da manufa biyu. A ciki, an rubuta cewa: “Muna gayyatar ka ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah.” Bayan haka, an bukaci mutumin ya zaɓi ko zai yi nazarin Littafi Mai Tsarki “a taronmu” “ko tare da wani.” Saboda haka, wannan takardar ba gabatar da mu kaɗai take yi ba amma tana gayyatar “waɗanda suka san cewa suna bukatar ƙulla dangantaka da Allah” su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mu. (Mat. 5:​3, New World Translation.) Babu shakka, muna gayyatar mutane su halarci taronmu ko suna so a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su ko a’a. Idan suka halarci taron, za su koyi abubuwa da yawa game da Allah.

8. Me ya sa yake da muhimmanci mutane su halarci taronmu ko da sau ɗaya ne? Ka ba da misali.

8 Yana da muhimmanci mu ci gaba da gayyatar mutane zuwa taronmu ko da sau ɗaya ne za su halarta. Me sa ya? Domin za su ga bambanci tsakanin abubuwan da Shaidun Jehobah suke koyarwa game da Allah da kuma abubuwan da addinan ƙarya suke koyarwa. (Isha. 65:13) Wani ɗan’uwa mai suna Ray a Amirka da matarsa Linda sun lura da wannan bambanci shekaru da yawa da suka shige. A lokacin, sun yanke shawara cewa za su soma zuwa coci. Sun gaskata da Allah kuma suna so su koya game da shi. Don haka, sai suka soma zuwa dukan coci da ke birnin da suke da zama ɗaya bayan ɗaya. A birnin, da akwai coci da yawa da kuma ɗariku dabam-dabam. Da farko, ma’auratan sun yanke shawarar cewa kafin su zama memban wani coci, suna bukatar su ga abu biyu. Na farko, suna bukatar su koyi wani abu sa’ad da suka halarci cocin, na biyu kuma suna so su ga cewa tufafin membobin cocin ya dace da mutanen da ke da’awar bauta wa Allah. Bayan shekaru da yawa, sun je dukan coci da ke birnin, amma ba su yi nasara ba. Ma’auratan ba su koyi kome ba, kuma ’yan cocin ba su da tarbi’a ko kaɗan. Bayan sun halarci coci na ƙarshe, sai Linda ta tafi wajen aiki, maigidanta Ray kuma ya koma gida. Da yake hanya zuwa gida, sai ya ga Majami’ar Mulki kuma ya ce wa kansa, ‘Me zai hana ni shiga don in ga abin da suke yi?’ Babu shakka, ya yi farin ciki don abin da ya gani! Kowa a Majami’ar yana da fara’a kuma ya yi shiga mai kyau. Ray ya zauna a kujerar gaba kuma ya ji daɗin taron! Wannan ya tuna mana da abin da manzo Bulus ya faɗa game da mutumin da ya halarci taro a lokaci na farko kuma ya ce: “Lallai Allah yana cikinku.” (1 Kor. 14:​23-25) Bayan haka, Ray ya soma halartan taro kowane Lahadi, daga baya ya soma halartan na tsakiyar mako. Matarsa Linda ma ta soma halartan taron, sai suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma suka yi baftisma a lokacin da sun riga sun kai shekara 70.

ABUBUWA DON SOMA TATTAUNAWA

9, 10. (a) Me ya sa warƙoƙinmu suke da sauƙin yin wa’azi da su? (b) Ka bayyana yadda za mu iya yin amfani da warƙar nan Mene ne Mulkin Allah?

9 Warƙoƙi. Muna da warƙoƙi guda takwas da suke da sauƙin yin amfani da su don soma tattaunawa da mutane. Tun daga lokacin da aka fitar da su a shekara ta 2013, an buga wajen kofi biliyan biyar! Abin ƙayatarwa game da waɗannan warƙoƙi shi ne, idan mutum ya koyi yin amfani da guda ɗaya a wa’azi, zai iya yin amfani da dukansu. Ta yaya za ka iya yin amfani da warƙoƙin don ka soma tattaunawa da mutane?

10 Kana iya zaɓa ka yi amfani da warƙar nan Mene ne Mulkin Allah? Ka nuna wa mutumin tambayar da ke gaban warƙar kuma ka tambaye shi: “Ka taɓa yin tunanin ko mene ne Mulkin Allah? Shin za ka ce . . . ?” Bayan haka, sai ka tambayi mutumin wanne ne ya zaɓa a cikin amsoshi ukun. Ba tare da gaya masa ko amsarsa daidai ne ko a’a ba, ka buɗe sashen nan “Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce” a cikin warƙar kuma ka karanta Daniyel 2:44 da kuma Ishaya 9:6. Idan zai yiwu ka ci gaba da tattaunawa da mutumin. A ƙarshe, ka yi tambayar da ke sashen nan “Ka Yi Tunani a Kan Wannan Tambayar”: “Ya rayuwa za ta kasance a ƙarƙashin Mulkin Allah?” Kana iya amsa wannan tambayar idan ka koma ziyara. Idan kun sake haɗuwa, kana iya nuna masa darasi na 7 na ƙasidar nan Albishiri Daga Allah!, wanda ɗaya ne daga cikin littattafan da muke amfani da su don yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane.

ABUBUWAN DA KE SA MUTANE SU SO KALMAR ALLAH

11. Me ya sa ake wallafa mujallunmu, kuma me muke bukatar mu sani game da su?

11 Mujallu. Hasumiyar Tsaro da kuma Awake! su ne mujallu da aka fi wallafawa da kuma fassarawa a duniya! Domin mutane a ko’ina suna karanta waɗannan mujallun, ana zaɓan jigon da mutane a ko’ina za su so. Muna bukatar mu yi amfani da waɗannan mujallun don mu taimaka wa mutane su san abin da ya fi muhimmanci a rayuwa. Amma don mu iya yin amfani da mujallun nan, muna bukatar mu san mutanen da aka wallafa wa mujallun.

12. (a) Don su waye ne ake wallafa Awake! kuma me ya sa? (b) Wane sakamako ka samu sa’ad da ka yi amfani da mujallar?

12 Ana wallafa mujallar Awake! ne domin mutanen da ba su san Littafi Mai Tsarki ba. Wataƙila ba su san kome game da koyarwa Kirista ba ko kuma ba su yarda da addini ba, ko kuma wataƙila ba su san cewa da akwai abubuwa a Littafi Mai Tsarki da za su iya yin amfani da su a rayuwarsu ba. Dalili mafi muhimmanci da ya sa ake wallafa Awake! shi ne don a tabbatar wa mai karatu da cewa Allah yana wanzuwa. (Rom. 1:20; Ibran. 11:6) Ƙari ga haka, ana so a taimaka wa mai karatu ya kasance da bangaskiya cewa Littafi Mai Tsarki “ainihin . .  kalmar Allah” ne. (1 Tas. 2:13) Jigo uku da ke shafin farko a mujallar Awake! na 2018 su ne: “The Way of Happiness” da “12 Secrets of Successful Families” da kuma “Help for Those Who Grieve.”

13. (a) Don su waye ne ake wallafa Hasumiyar Tsaro na wa’azi? (b) Me ka shaida sa’ad da ka yi amfani da mujallar?

13 Abin da ya sa ake wallafa Hasumiyar Tsaro na wa’azi shi ne don a bayyana koyarwar Kalmar Allah ga mutanen da suke daraja Littafi Mai Tsarki. Wataƙila sun san wasu abubuwa game da Littafi Mai Tsarki amma ba su fahimci ainihin abin da yake koyarwa ba. (Rom. 10:2; 1 Tim. 2:​3, 4) Jigo guda uku da ke shafi na farko na mujallar Hasumiyar Tsaro ta 2018, su ne: “Littafi Mai Tsarki Yana da Amfani a Yau?” da “Mene ne Zai Faru a Nan Gaba?” da kuma “Allah Ya Damu da Kai Kuwa?

ABUBUWAN DA KE SA MUTANE SU ƊAUKI MATAKI

14. (a) Me ya sa aka yi bidiyoyin nan guda huɗu? (b) Me ka shaida sa’ad da ka yi amfani da bidiyoyin a wa’azi?

14 Bidiyoyi. A zamanin Yesu, kayan aikin kafintoci ba masu amfani da lantarki ba ne. Amma a yau, kafintoci suna amfani da kayan aikin da ke amfani da lantarki kamar su zarto da abin washi da dai sauransu. Ƙari ga littattafan da ake bugawa, yanzu muna da bidiyoyi kuma huɗu daga cikinsu suna cikin kayan aiki don koyarwa: Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? da Yaya Ake Gudanar da Nazarin Littafi Mai Tsarki? da Me Ake Yi a Majami’ar Mulki? da kuma Su Wane ne Shaidun Jehobah? Wasu cikinsu sun fi dacewa a ziyara ta farko, wasu kuma a koma ziyara. Waɗannan bidiyoyin za su iya motsa mutane su so yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma halartan taro.

15. Ka ba da misalin yadda kallon ɗaya daga cikin bidiyoyinmu a yarensu ya shafi mutane.

15 Alal misali, wata ’yar’uwa ta haɗu da wata mata da ta ƙauro daga yankin Micronesia kuma tana yaren Yapese. ’Yar’uwar ta nuna mata bidiyon nan Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? a yaren Yapese. Da ta soma nuna mata bidiyon sai matar ta ce: “Wannan yarenmu ne. Abin mamaki! Daga yadda mutumin yake magana na san cewa daga tsibirinmu yake. Yarenmu yake yi!” Bayan haka, sai ta ce za ta karanta dukan talifofi na yarenta da ke dandalin jw.org kuma za ta kalli bidiyoyin. (Gwada Ayyukan Manzanni 2:​8, 11.) Ka yi la’akari da wani misali. Wata ’yar’uwa a Amirka ta tura wa ɗan yayanta da ke zama a ƙasar waje adireshin da zai iya kallon bidiyo a yarensu. Bayan ya kalli bidiyon, sai ya turo mata saƙon imel cewa: “Wurin nan da aka ce wani mugu ne ke mulkin duniya ya ja hankalina sosai. Na cika fom don a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni.” Mutumin yana zama a inda aka saka wa aikinmu takunkumi.

LITTATTAFAI DA KE KOYAR DA GASKIYA

16. Ka bayyana manufar ƙasidun nan: (a) Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada. (b) Albishiri Daga Allah! (c) Su Wane Ne Suke Yin Nufin Jehobah a Yau?

16 Ƙasidu. Ta yaya za ka koya wa mutum gaskiya idan bai iya karatu ba ko kuma ba mu da littattafai a yarensu? Muna da abin da za ka iya yin amfani da shi. Me ke nan? Ƙasidar nan Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada. * Wata ƙasida kuma da za mu iya yin amfani da ita don nazarin Littafi Mai Tsarki ita ce Albishiri Daga Allah! Kana iya nuna wa mutum jigo guda 14 da ke bangon baya kuma ka bar shi ya zaɓi wanda yake so ku tattauna. Sai ka soma tattaunawa da mutumin daga wurin. Shin ka taɓa yin hakan sa’ad da ka koma ziyara? Ban da haka ma, muna iya yin amfani da ƙasidar nan Su Wane Ne Suke Yin Nufin Jehobah a Yau? Wannan ita ce ƙasida ta uku a cikin Kayan Aiki don Koyarwa da muke amfani da su. An tsara ƙasidar ne don a koya wa ɗalibi game da ƙungiyarmu. Don ka koyi yadda za ka riƙa yin amfani da ita a kowane nazarin Littafi Mai Tsarki, ka duba Littafin Taro don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu na Maris 2017.

17. (a) Me ya sa aka wallafa waɗannan littattafai? (b) Mene ne waɗanda suke so su yi baftisma za su yi, kuma me ya sa?

17 Littattafai. Bayan kun soma yin nazari da ƙasida, kuna iya komawa kan littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? a duk lokacin da kuka ga ya dace. Littafin zai taimaka wa ɗalibin ya san muhimman koyarwar Littafi Mai Tsarki. Bayan kun kammala nazarin kuma ɗalibin yana samun ci gaba, ka yi nazarin littafin nan da shi: Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah. Littafin zai taimaka masa ya san yadda zai riƙa yin amfani da ƙa’idodin Allah a rayuwarsa. Ka tuna cewa ko bayan baftisma, sababbin suna bukatar su ci gaba da yin nazarin har sai sun kammala yin nazarin waɗannan littattafai biyu. Hakan zai taimaka musu su ƙarfafa bangaskiyarsu.​—Karanta Kolosiyawa 2:​6, 7.

18. (a) Mene ne 1 Timoti 4:16 ya ƙarfafa mu mu yi a matsayin masu koyar da gaskiya, kuma me hakan zai cim ma? (b) Mene ne maƙasudinmu yayin da muke amfani da Kayan Aiki don Koyarwa?

18 A matsayinmu na Shaidun Jehobah, muna da hakkin koyar da “gaskiya” game da Allah, wadda za ta sa su sami rai na har abada. (Kol. 1:5; karanta 1 Timoti 4:16.) Saboda haka, an yi mana tanadin Kayan Aiki don Koyarwa da ke ɗauke da abubuwan da muke bukata. (Ka duba akwatin nan “ Kayan Aiki don Koyarwa.”) Bari mu yi iya ƙoƙarinmu don mu yi amfani da waɗannan abubuwan yadda ya dace. Kowane mai shela ne zai zaɓa wanda zai yi amfani da shi daga cikin abubuwan da aka yi mana tanadin su don wa’azi sa’ad da ya haɗu da wani. Amma ka tuna manufar mu ba kawai mu riƙa ba da littattafai ba ne kuma ba zai dace mu ba waɗanda ba sa son saƙonmu ba. Manufarmu ita ce mu almajirantar da mutane masu zuciyar kirki da suke so su koya game da Allah.​—A. M. 13:48; Mat. 28:​19, 20.

^ sakin layi na 16 Idan wani bai iya karatu ba, kana iya sa ya yi amfani da ƙasidar nan Ka Saurari Allah domin babu rubutu sosai a ciki.