Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ku Kasance da Kwanciyar Rai Idan Yanayinku Ya Canja

Ku Kasance da Kwanciyar Rai Idan Yanayinku Ya Canja

“Na haƙura na kwantar da raina.”​—ZAB. 131:2.

WAƘOƘI: 128, 129

1, 2. (a) Ta yaya canjin yanayi zai iya shafan mu? (Ka duba hoton da ke shafin nan.) (b) Wane ra’ayi ne Zabura ta 131 ta ce zai sa mu kasance da kwanciyar rai?

AKWAI wani ɗan’uwa mai suna Lloyd da matarsa Alexandra da aka ce su koma yin hidimar majagaba bayan sun yi hidima fiye da shekara 25 a Bethel. Ma’auratan sun yi baƙin ciki sosai domin sun daɗe suna yin hidimar. Lloyd ya ce: “Bethel da kuma hidimar da nake yi sun zama min jiki. Na fahimci dalilan da suka sa aka yi canje-canjen, amma duk da haka, ba na jin daɗi a wasu lokuta.” A wasu lokuta Lloyd yana farin ciki, a wasu kuma yana yin baƙin ciki sosai.

2 Muna fuskantar canje-canje a rayuwarmu da ba mu yi zato ba, kuma hakan na iya tayar mana da hankali. (K. Mag. 12:25) Yana ma iya yi mana wuya mu amince da canje-canjen. Me zai taimaka mana mu ‘haƙura mu kwantar da ranmu’? (Karanta Zabura 131:​1-3.) Bari mu tattauna yadda wasu bayin Jehobah a zamanin dā da kuma a zamaninmu suka ci gaba da kasancewa da kwanciyar rai duk da cewa yanayinsu ya canja.

KU SHAIDA “SALAMA” WADDA ALLAH KE BAYARWA

3. Ta yaya yanayin Yusufu ya canja farat ɗaya?

3 Ka yi la’akari da labarin Yusufu. Shi ɗan wajen shekara 17 ne sa’ad da ’yan’uwansa suka sayar da shi ya zama bawa domin suna kishin sa. Yusufu ne mahaifinsa ya fi so a cikin ’ya’yansa. (Far. 37:​2-4, 23-28) Yusufu ya sha azaba a ƙasar Masar har wajen shekara 13. Da farko shi bawa ne, amma daga baya, aka saka shi a kurkuku. Yana nesa da mahaifinsa Yakubu wanda ke ƙaunarsa sosai. Mene ne ya taimaka wa Yusufu kada ya karaya?

4. (a) Mene ne Yusufu ya yi sa’ad da yake kurkuku? (b) Ta yaya Jehobah ya amsa addu’o’insa?

4 Babu shakka, sa’ad da Yusufu yake shan wahala a kurkuku, ya mai da hankali a kan albarkun da Jehobah ya yi masa. (Far. 39:21; Zab. 105:​17-19) Wataƙila ya yi tunani a kan mafarkan da ya yi sa’ad da yake ƙarami kuma hakan ya tabbatar masa da cewa Jehobah yana tare da shi. (Far. 37:​5-11) Mai yiwuwa, yana yawan gaya wa Jehobah dukan abubuwan da ke nauyaya masa zuciya. (Zab. 145:18) Kuma Jehobah ya amsa addu’ar Yusufu ta wajen sa ya kasance da tabbaci cewa zai taimaka masa ko da mene ne ya faru.​—A. M. 7:​9, 10. *

5. Ta yaya “salama” wadda Allah ke bayarwa take taimaka mana mu ci gaba da bauta wa Allah?

5 Kome tsananin yanayinmu a yau, za mu iya kasancewa da “salama” wadda za ta tsare zukatanmu da tunaninmu. (Karanta Filibiyawa 4:​6, 7.) Idan muna fuskantar matsaloli kuma mun yi addu’a ga Jehobah, salamarsa za ta iya ƙarfafa mu mu ci gaba da bauta masa kuma zai taimaka mana kada mu karaya. Bari mu tattauna wasu misalai a zamaninmu da suka nuna hakan.

KU ROƘI JEHOBAH DON KU KASANCE DA KWANCIYAR RAI

6, 7. Ta yaya yin addu’a kai tsaye zai iya sa mu kasance da salama? Ka ba da misali.

6 Ryan da matarsa Juliette sun yi baƙin ciki sosai sa’ad da aka sanar da su cewa su daina hidimar majagaba na musamman. Ryan ya ce: “Mun miƙa damuwarmu ga Jehobah ba tare da ɓata lokaci ba. Mun san cewa wannan dama ce na nuna cewa mun dogara da shi. Da yake mutane da yawa a ikilisiyarmu sababbi ne, mun roƙi Jehobah ya taimaka mana mu kafa musu misali mai kyau na nuna bangaskiya.”

7 Ta yaya Jehobah ya amsa addu’ar Ryan? Ya ce: “Da zarar mun kammala addu’ar, mun daina alhini da kuma tunanin da bai dace ba. Salamar da Allah ke bayarwa ta tsare zukatanmu da hankulanmu. Mun fahimci cewa Jehobah zai ci gaba da yin amfani da mu idan mun kasance da ra’ayi mai kyau.”

8-10. (a) Ta yaya ruhun Allah zai iya taimaka mana mu daina yin alhini? (b) A waɗanne hanyoyi ne Jehobah zai iya taimaka mana idan mun mai da hankali ga bauta masa?

8 Ruhun Allah zai iya kwantar mana da hankali, ƙari ga haka, zai iya sa mu tuna nassosin da za su iya taimaka mana mu fahimci abubuwan da suka fi muhimmanci a rayuwa. (Karanta Yohanna 14:​26, 27.) Ku yi la’akari da misalin Philip da matarsa Mary da sun taɓa yin hidima na kusan shekara 25 a Bethel. A cikin wata huɗu, mahaifiyarsa da na matarsa sun rasu kuma wani danginsu ma ya rasu. Ƙari ga haka, mahaifin matarsa ya soma fama da ciwon mantuwa.

9 Philip ya ce: “Na yi tsammani cewa ina jimrewa, amma na lura cewa akwai abin da ba na yi. Sai na ga littafin Kolosiyawa 1:11 a wani talifin Hasumiyar Tsaro na nazari. Gaskiya ne cewa ina jimrewa, amma ba na yin hakan sosai. Ina bukatar in jimre ‘matuƙa cikin haƙuri da farin ciki.’ Wannan ayar ta tuna mini cewa ba yanayina ba ne ya kamata ya riƙa sa ni farin ciki ko baƙin ciki a rayuwa ba, amma yadda ruhun Allah yake shafan rayuwata ne.”

10 Da yake Philip da matarsa sun mai da hankali a kan bautarsu ga Jehobah, ya albarkace su a hanyoyi da yawa. Ba da daɗewa ba da barin Bethel, sun sami ɗalibai da suka yarda a yi nazari da su fiye da sau ɗaya a mako. Mary ta ce: “Ɗaliban nan sun sa ni farin ciki kuma hanya ce da Jehobah yake gaya mana cewa kome zai yi daidai.”

TASHI IN TAIMAKE KA

Ta yaya za mu iya yin koyi da misalin Yusufu ko da wane irin yanayi muke fuskanta? (Ka duba sakin layi na 11-13.)

11, 12. (a) Wane mataki ne Yusufu ya ɗauka don Jehobah ya albarkace shi? (b) Ta yaya aka albarkace shi don jimirinsa?

11 Idan yanayinmu ya canja farat ɗaya, muna iya soma alhini ainun a kan matsalolinmu. Wataƙila hakan ya faru da Yusufu. Amma maimakon ya damu ainun, ya ci gaba da yin iya ƙoƙarinsa duk da yanayinsa kuma Jehobah ya albarkace shi. Ko da yake Yusufu yana kurkuku, ya sa ƙwazo wajen yin aikin da shugaban masu gadi ya ba shi, kamar yadda ya yi sa’ad da yake aiki da Fotifa.​—Far. 39:​21-23.

12 Wata rana, aka ce Yusufu ya riƙa kula da wasu maza biyu da suke hidima a fādar Fir’auna a dā. Yusufu ya mutunta musu har suka saki jiki kuma suka gaya masa mafarkan da suka yi da ke ci musu tuwo a ƙwarya. (Far. 40:​5-8) Yusufu bai san cewa wannan tattaunawar ce za ta sa ya sami ’yanci daga baya ba. Shekaru biyu bayan wannan lokacin, sai aka sako shi daga kurkuku. A ranar da aka sako Yusufu, ya zama mutum na biyu mafi matsayi a ƙasar Masar.​—Far. 41:​1, 14-16, 39-41.

13. Me za mu yi don Jehobah ya albarkace mu ko da a wane irin yanayi muke ciki?

13 Muna iya tsinci kanmu a irin yanayin Yusufu. Amma idan muka kasance da haƙuri kuma muka ɗauki mataki, Jehobah zai albarkace mu. (Zab. 37:5) A wasu lokuta, muna iya yin “shakka” kamar yadda manzo Bulus ya faɗa, amma ba za mu “fid da zuciya” ba. (2 Kor. 4:8) Idan mun mai da hankali ga hidimarmu, waɗannan kalmomin za su cika a kanmu.

KU MAI DA HANKALI GA HIDIMARKU

14-16. Ta yaya Filibus ya mai da hankali ga hidimarsa duk da cewa yanayinsa ya canja?

14 Filibus mai wa’azi ya kafa misali mai kyau wajen mai da hankali ga hidimarsa duk da cewa yanayinsa ya canja. An soma tsananta wa Kiristoci a Urushalima sosai bayan da aka kashe Istifanus. * A lokacin, Filibus bai daɗe da samun sabon aiki a hidimar Allah ba. (A. M. 6:​1-6) Amma sa’ad da sauran mabiyan Kristi suka gudu, Filibus ya je yin hidima a wani wuri dabam. Ya je Samariya wanda birni ne da mutane da yawa ba su taɓa jin bishara ba.​—Mat. 10:5; A. M. 8:​1, 5.

15 Filibus ya kasance a shirye ya je kowane wurin da ruhun Allah ya bishe shi. Saboda haka, Jehobah ya yi amfani da shi wajen yaɗa bishara a yankin da ba a taɓa yin wa’azi a ciki ba. Babu shakka, yadda bai nuna wa Samariyawa bambanci ba ya ƙarfafa su domin a lokacin, Yahudawa suna nuna musu bambanci sosai. A sakamakon haka, Samariyawa sun saurare shi da “nufi ɗaya”!​—A. M. 8:​6-8.

16 Bayan haka, ruhun Allah ya sa Filibus ya je Ashdod da Kaisariya. Waɗannan birane biyu ne da mazaunansa da yawa ba Yahudawa ba ne. (A. M. 8:​39, 40) Shekaru 20 bayan Filibus ya yi wa’azi a Samariya, sai yanayinsa ya sake canjawa. Ya kama zama a yankin domin ya yi aure kuma ya sami yara. Amma duk da cewa yanayinsa ya canja, ya mai da hankali ga hidimarsa. A sakamakon haka, Jehobah ya yi wa shi da iyalinsa albarka sosai.​—A. M. 21:​8, 9.

17, 18. Ta yaya mai da hankali ga yin wa’azi zai taimaka mana idan yanayinmu ya canja?

17 ’Yan’uwa da yawa da suke hidima ta cikakken lokaci sun ce mai da hankali ga hidimarsu yana taimaka musu su riƙa farin ciki ko da yanayinsu ya canja. Sa’ad da wani ɗan’uwa mai suna Osborne da matarsa Polite suka daina hidima a Bethel, sun yi tsammani cewa ba da jimawa ba, za su sami aiki da kuma wurin zama. Amma Osborne ya ce: “Abin baƙin ciki, ba mu sami aiki da sauri yadda muka yi tsammani ba.” Matarsa Polite ta ce: “Mun nemi aiki har watanni uku, amma ba mu samu ba kuma ba mu yi ajiyar kuɗi ba. Bai kasance mana da sauƙi ba ko kaɗan.”

18 Mene ne ya taimaka musu su iya jimrewa? Osborne ya kammala da cewa: “Yin wa’azi tare da ’yan’uwa a cikin ikilisiya ya taimaka mana sosai mu rage yin alhini. Mun yanke shawarar yin ƙwazo sosai a wa’azi maimakon mu zauna a gida muna tausaya wa kanmu. Kuma hakan ya sa mu farin ciki matuƙa. Mun ta kai-da-kawowa muna neman aiki kuma daga baya mun yi dace.”

KU DOGARA GA JEHOBAH

19-21. (a) Mene ne zai taimaka mana mu kasance da kwanciyar rai? (b) Ta yaya za mu amfana idan ba mu karaya ba sa’ad da yanayinmu ya canja?

19 Kamar yadda wannan misalin ya nuna, idan muka bi da yanayinmu yadda ya dace kuma muka dogara ga Jehobah, za mu kasance da kwanciyar rai. (Karanta Mikah 7:7.) Za mu ga cewa yadda muke bi da matsaloli yana ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah. Polite da aka ambata ɗazu ta ce: “Barin Bethel ya sa na daɗa dogara ga Jehobah ko da abubuwa sun yi wuya sosai. Hakan ya sa dangantakata da Jehobah ta ƙara ƙarfi.”

20 Har yau, Mary da muka ambata ɗazu tana kula da mahaifinta da ya tsufa kuma tana hidimar majagaba. Ta ce: “Na koya cewa a duk lokacin da nake baƙin ciki, ina bukatar in ɗan dakata, in yi addu’a kuma in kwantar da hankalina. Dogara ga Jehobah ne darasi mafi muhimmanci da na koya kuma zan fi bukatar hakan a nan gaba.”

21 Lloyd da Alexandra ma sun ce yanayinsu da ya canja ya jarraba bangaskiyarsu a hanyar da ba su taɓa tsammani ba. Amma sun ce: “Jarrabawa tana sa mu sani ko muna da bangaskiya sosai da za ta iya sa mu jimre a lokacin da muke fuskantar matsaloli. Hakan na kyautata halinmu sosai.”

Canje-canjen da ba mu tsammani ba, zai iya sa mu sami albarka sosai! (Ka duba sakin layi na 19-21)

22. Mene ne za mu shaida idan muka bi da yanayinmu yadda ya dace?

22 A wannan mugun zamanin da muke ciki, yanayinmu yana iya canjawa farat ɗaya. Za a iya canja aikin da muke yi a hidimar Jehobah. Za mu iya yin ciwo mai tsanani ko kuma mu bukaci kula da wani a iyalinmu. Amma ko da mene ne ya faru, ka kasance da tabbaci cewa Jehobah ya damu da kai kuma zai taimaka maka a lokacin da ya dace. (Ibran. 4:16; 1 Bit. 5:​6, 7) A yanzu, ka bi da yanayinka yadda ya dace. Ka yi addu’a a gare shi kuma ka dogara gare shi gabaki ɗaya. Idan ka yi haka, za ka kasance da kwanciyar rai ko da yanayinka ya canja.

^ sakin layi na 4 Shekaru da yawa bayan an sako Yusufu daga kurkuku, ya bayyana cewa Jehobah ya sanyaya masa zuciya ta wajen ba shi ɗa. Ya ba yaron suna Manassa, domin ya ce: “Allah ya sa na manta da wahalata.”​—Far. 41:51.

^ sakin layi na 14 Ka duba talifin nan “Ka Sani?” a wannan mujallar.