Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ɗan’uwa Rutherford yana jawabi a taron yanki a Cedar Point, Ohio, a shekara ta 1919

1919​—Shekara Dari da Suka Shige

1919​—Shekara Dari da Suka Shige

A shekara ta 1919, an kammala Yaƙin Duniya na Ɗaya da aka yi fiye da shekara huɗu ana yi. A ranar 18 ga Janairu, 1919, an yi taron Paris Peace Conference (Taron Samar da Salama ta Paris). Ɗaya daga cikin abubuwan da taron ya cim ma shi ne yadda ya kawo ƙarshen yaƙin da wasu ƙasashe suke yi da ƙasar Jamus. An saka hannu a yarjejeniyar a ranar 28 ga Yuni, 1919.

A taron, an kafa ƙungiyar nan Tsohuwar Majalisar Ɗinkin Duniya. An kafa ta ne don a “sa ƙasashe dabam-dabam su sami haɗin kai kuma su zauna cikin lumana.” Addinai da yawa sun goyi bayan Ƙungiyar. Majalisar da Ke Haɗa Kan Cocin Kristi a Amirka ta ce “ƙungiyar Mulkin Allah ne a duniya.” Majalisar ta nuna goyon bayanta ta wajen aika mutane zuwa taron Paris Peace Conference. Ɗaya daga cikin mutanen da suka halarci taron ya ce “taron sabon yayi ne a tarihin ʼyan Adam.”

Babu shakka, an shiga sabon yayi, amma ba shi da alaƙa da mutanen da suka sa hannu a wannan yarjejeniyar. A shekara ta 1919, an shiga sabon yayi a wa’azin bishara ta Mulkin Allah sa’ad da Jehobah ya ƙarfafa mutanensa su daɗa ƙwazo a yin wa’azi. Amma da farko, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suna bukatar su yi wasu canje-canje na musamman.

SHAWARA MAI WUYAR YANKEWA

Joseph F. Rutherford

An zaɓi ranar 4 ga Janairu, 1919, don a yi zaɓen darektan Watch Tower Bible and Tract Society. A lokacin, an saka Ɗan’uwa Joseph F. Rutherford da ke kula da aikinmu da kuma wasu ʼyan’uwa bakwai a kurkuku a Atlanta, Georgia, Amirka. Sai wata tambaya ta taso, Shin a sake zaɓan ʼyan’uwan don su ci gaba da kula da aikinmu ne? Ko kuma a zaɓi wasu ʼyan’uwa dabam?

Evander J. Coward

Yayin da Ɗan’uwa Rutherford yake cikin kurkuku, ya damu sosai game da aikinmu. Ya san cewa wasu sun gwammace a zaɓi wani dabam ya yi ja-goranci. Saboda haka, sai ya rubuta wasiƙa ga mutanen da suka yi taro cewa a zaɓi Ɗan’uwa Evander J. Coward ya zama shugaba. Ɗan’uwa Rutherford ya ce Ɗan’uwa Coward “natsatse ne” kuma “yana da aminci ga Ubangiji.” Amma wasu sun gwammace a ɗage zaɓen zuwa watanni shida. Lauyoyin da ke taimaka musu a kurkuku sun yarda da shawarar. Yayin da ake wannan taron, wasu ʼyan’uwa sun yi fushi sosai.

Richard H. Barber

Ɗan’uwa Richard H. Barber ya ce an ɗauki wani mataki don a sasanta matsalar. Wani ɗan’uwa da ya halarci taron ya tashi tsaye ya ce: “Ni ba lauya ba ne, amma na san abin da kasancewa da aminci yake nufi. Aminci shi ne abin da Allah yake bukata. Hanya mafi muhimmanci da za mu nuna amincinmu ga Allah shi ne mu sake zaɓan Ɗan’uwa Rutherford a matsayin mai ja-goranci.”​—Zab. 18:25.

Alexander H. Macmillan

Ɗan’uwa A. H. Macmillan wanda shi ma yake kurkuku ya ce, washegari sai Ɗan’uwa Rutherford ya ƙwanƙwasa ƙofar kurkukun da Macmillan yake ciki kuma ya ce: “Miƙo hannunka.” Sai Ɗan’uwa Rutherford ya miƙa masa wasiƙa. Ɗan’uwa Macmillan ya ga saƙon kuma nan da nan ya fahimci abin da yake nufi. An rubuta a wasiƙar cewa: “RUTHERFORD WISE VAN BARBER ANDERSON BULLY AND SPILL DIRECTOR FIRST THREE OFFICERS LOVE TO ALL.” Saƙon yana nufin cewa an sake zaɓen dukan darektocin kuma har ila, Joseph Rutherford da William Van Amburgh suna riƙe da matsayinsu. Saboda haka, Ɗan’uwa Rutherford zai ci gaba da yin ja-goranci.

AN SAKO SU!

Sa’ad da ʼyan’uwan suke cikin kurkuku, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki masu aminci sun nemi goyon bayan jama’a don a sako ʼyan’uwan daga kurkuku. Waɗannan ʼyan’uwan sun sami fiye da mutane 700,000 da suka saka hannu a wasiƙun don su nuna goyon bayansu. Amma a ranar Laraba, 26 ga Maris 1919, an sako Ɗan’uwa Rutherford da sauran ʼyan’uwan kafin ma a tura wa hukuma wasiƙun.

A jawabin da Ɗan’uwa Rutherford ya yi sa’ad da ake marabtar sa, ya ce: “Ina da tabbaci cewa abubuwan nan da suka faru suna shirya mu ne don abubuwan da za su faru a nan gaba. . . . Famar da kuka yi ba don a sako ʼyan’uwanku daga kurkuku ba ne. Ba ainihin dalilin ke nan ba. . . . Kun yi fama ne musamman don ku ɗaukaka Jehobah, kuma ku da kuka yi hakan kun sami babbar lada.”

Abubuwan da suka faru sa’ad da ake yin shari’a a kan ʼyan’uwan nan sun nuna cewa Jehobah yana goyan bayansu. A ranar 14 ga Mayu, 1919, kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci cewa: “Ba a yi adalci . . . a hukuncin da aka yanke a kan ʼyan’uwan ba, kuma don haka, an canja hukuncin da aka yi musu.” An tuhumi ʼyan’uwan da laifofi masu tsanani, kuma da a ce an gafarce su ko kuma an sauƙaƙa hukuncinsu, da an rubuta hakan a takardun shari’a da aka buɗe musu. Amma an soke laifofin. A sakamakon haka, Ɗan’uwa Judge Rutherford ya ci gaba da samun ’yancin kāre mutanen Jehobah a Kotun Ƙoli na Amirka kuma ya yi hakan sau da yawa bayan an sako shi daga kurkuku.

SUN DUƘUFA YIN WA’AZI

Ɗan’uwa Macmillan ya tuna abin da ya faru, ya ce: “Ba za mu zauna haka kawai muna jiran Ubangiji ya zo ya kai mu sama ba. Mun fahimci cewa muna bukatar mu ɗauki mataki don mu san ainihin nufin Ubangiji.”

Amma bai kasance wa ʼyan’uwan da ke hedkwatarmu sauƙi su sake soma aikin da suka ɗan jima ba su yi ba. Me ya sa? Domin a lokacin da suke cikin kurkuku, kayan buga littattafai da suke amfani da su sun lalace. Wannan lamarin ya sa ʼyan’uwan sanyin gwiwa, kuma wasu cikinsu sun yi zato cewa an daina yin wa’azin bishara ke nan.

Har ila, akwai mutanen da ke son wa’azin da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suke yi kuwa? Don a sami amsa ga tambayar, Ɗan’uwa Rutherford ya tsai da shawarar yin jawabi ga jama’a. Ya ce za a gayyato mutane. Ɗan’uwa Macmillan ya ce: “Idan babu mutumin da ya zo taron, to mun kammala wa’azinmu ke nan.”

Tallar da aka yi a jarida game da jawabin Ɗan’uwa Rutherford mai jigo “The Hope for Distressed Humanity” a Los Angeles, Kalifoniya, a shekara ta 1919

Sai a ranar Lahadi, 4 ga Mayu, 1919, duk da cewa Ɗan’uwa Rutherford yana rashin lafiya sosai, ya yi jawabi mai jigo “The Hope for Distressed Humanity (Bege ga Mutane da Suka Rikice).” An yi taron a Los Angeles, Kalifoniya. Wajen mutane 3,500 sun halarci jawabin kuma da yawa sun koma gida domin ba su sami wurin zama ba. Mutane 1,500 sun halarci taron washegari. Wannan taron ya nuna cewa har ila, mutane suna son wa’azinmu!

Abin da ʼyan’uwan suka yi bayan haka ya shafi yadda Shaidun Jehobah suke yin wa’azi har yau.

MUN YI SHIRIN SAMUN ƘARUWA

An sanar a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Agusta, 1919, cewa za a yi taron yanki a Cedar Point Ohio a farkon watan Satumba. Wani ɗan Missouri da ke nazarin Littafi Mai Tsarki, mai suna Clarence B. Beaty ya ce kowa yana so ya je taron. ʼYan’uwa maza da mata fiye da 6,000 sun hallara, kuma adadin ya wuce yadda muka yi tsammani. Ƙari ga haka, mutane fiye da 200 sun yi baftisma a Tafkin Erie.

Mujallar The Golden Age na farko ta ranar 1 ga Oktoba, 1919

A ranar 5 ga Satumba, 1919, wato rana ta biyar na taron, Ɗan’uwa Rutherford ya sanar da fitowar sabuwar mujalla mai jigo The Golden Age. * Mujallar “za ta riƙa ɗaukan labarai da ɗumi-ɗuminsu, kuma za ta nuna dalilan da ke Nassosi da suka sa abubuwan suke faruwa.”

An ƙarfafa dukan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki su riƙa yin amfani da wannan mujallar wajen yin wa’azi da himma. A wata wasiƙa da aka rubuta da ta bayyana yadda za a tsara aikinmu, an ce: “Bari kowane ɗan’uwa da ya yi baftisma ya tuna cewa gata ne ya yi wa’azi, kuma ya yi wa’azin da himma sosai ga mazaunan duniya.” Mutane da yawa sun amince da wannan gayyatar! Daga lokacin zuwa watan Disamba, masu shelar Mulkin Allah da ƙwazo sun karɓi sama da mujallu 50,000.

ʼYan’uwa a Brooklyn, New York, ɗauke da mujallar The Golden Age a motarsu

A ƙarshen shekara ta 1919, mutanen Jehobah sun sake tsara ayyukansu. Ƙari ga haka, annabce-annabce da yawa game da kwanaki na ƙarshe sun cika. Annabcin da ke Malakai 3:​1-4 ya gama cika, an saki bayin Jehobah daga ƙunshin “Babila Babba,” kuma Yesu ya naɗa “bawan nan mai aminci, mai hikima.” * (Mal. 3:​1-4; R. Yar. 18:​2, 4; Mat. 24:45) Yanzu, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun kasance a shirye su cim ma aikin da Jehobah yake so su yi.

^ sakin layi na 22 An canja sunan mujallar zuwa Consolation a shekara ta 1937 kuma an sake canjawa zuwa Awake! a 1946.

^ sakin layi na 24 Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2013, shafuffuka na 10-12 da 21-23 da na Maris 2016, shafuffuka na 29-31.