Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Mutane suna bukatar su saurari gargaɗi cewa hukuncin Allah tana nan tafe!

Hukuncin Allah​—Yana Ba da Isashen Gargadi Kuwa?

Hukuncin Allah​—Yana Ba da Isashen Gargadi Kuwa?

WANI mai duba yanayin gajimare yana duba wata taswira, sai ya lura cewa mahaukaciyar guguwa tana nan tafe. Ya yi iya ƙoƙarinsa don ya gargaɗar da mutane kafin lokacin ya ƙure musu. Ya yi hakan ne domin ya damu da mutanen.

Hakazalika, Jehobah yana faɗakar da mazaunan duniya game da wata “guguwa” da za ta fi kowane irin guguwa haɗari. Ta yaya yake yin hakan? Me ya sa muka tabbata cewa Jehobah yana ba mutane isashen lokaci don su ɗauki mataki? Don mu sami amsar, bari mu fara tattauna wasu gargaɗi da Jehobah ya bayar a dā.

LOKUTAN DA ALLAH YA YI GARGAƊI

A dā, Jehobah ya yi gargaɗi game da “guguwa” dabam-dabam ko kuma hukunci da zai yi wa mutane da suka taka dokarsa da ganga. (K. Mag. 10:25; Irm. 30:23) A kowannensu, Jehobah ya sanar da mutanen tun da wuri, kuma ya umurce su cewa su yi canje-canjen da suka jitu da nufinsa. (2 Sar. 17:​12-15; Neh. 9:​29, 30) Sau da yawa, Jehobah ya sa mutane su tuba ta wurin yin amfani da bayinsa masu aminci don ya sanar da hukuncinsa kuma ya sa mutane su ga cewa suna bukatar su ɗau mataki nan da nan.​—Amos 3:7.

Nuhu yana cikin mutanen da Allah ya yi amfani da su don ya sanar da hukuncinsa. Ya yi shekaru da yawa yana yi wa mutane masu lalata da mugunta gargaɗi game da ambaliyar ruwa da ake gab da yi. (Far. 6:​9-13, 17) Nuhu ya kuma gaya musu abin da suke bukatar su yi don su tsira. Ya yi wa’azi har aka kira shi “mai wa’azin adalci.”​—2 Bit. 2:5.

Duk da ƙoƙarce-ƙoƙarcen da Nuhu ya yi, mutanen zamaninsa sun ƙi bin saƙon Allah. Sun nuna cewa ba su da bangaskiya ko kaɗan. Hakan ya sa suka mutu sa’ad da ambaliyar ruwa “ta zo ta kwashe su duka.” (Mat. 24:39; Ibran. 11:7) Sa’ad da hakan ya kusan faruwa, ba za su iya cewa Allah bai yi musu gargaɗi ba.

A wasu lokuta, Jehobah ya yi wa mutane gargaɗi jim kaɗan kafin ya kawo hukuncinsa. Duk da haka, ya tabbata cewa ya ba su isashen lokaci don su ɗauki mataki. Alal misali, ya yi wa mutanen Masar gargaɗi tun da wuri kafin ya tura musu Annoba Goma. Sa’ad da za a yi annoba ta bakwai, Jehobah ya tura Musa da Haruna zuwa wurin Fir’auna da bayinsa cewa zai sa a yi ƙanƙara mai tsananin gaske. Tun da yake zai sa a yi ƙanƙarar washegari, shin Allah ya ba su isashen lokaci don su nemi mafaka kuma su tsira daga wannan ƙanƙarar? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowane dattijon Fir’auna wanda ya ji tsoron maganar Yahweh, ya sa bayinsa da shanunsa su gudu zuwa cikin rumfa. Amma duk wanda bai kula da maganar Yahweh ba, ya bar bayinsa da shanunsa a waje.” (Fit. 9:​18-21) A bayyane yake cewa Jehobah ya ba da gargaɗi tun da wuri don kada mutanen da suka saurare shi su sha wahala.

Hakazalika, an gargaɗi Fir’auna da bayinsa jim kaɗan kafin a soma annoba ta goma, amma sun ƙi bin gargaɗin. (Fit. 4:​22, 23) A sakamako, dukan ’ya’yansu na fari suka mutu. (Fit. 11:​4-10; 12:29) Musa ya yi wa Isra’ilawa gargaɗi game da annoba ta goma da ke nan tafe kuma ya gaya musu yadda za su ceci iyalansu. (Fit. 12:​21-28) Mutane nawa ne suka bi wannan gargaɗin? An kiyasta cewa mutane miliyan uku har da Isra’ilawa da “mutane masu yawa waɗanda su ba Isra’ilawa ba” ne suka tsira daga hukuncin Allah kuma suka bar Masar.​—Fit. 12:38.

Kamar yadda waɗannan misalan suka nuna, Jehobah yana ba mutane isashen lokaci don ya tabbatar da cewa sun sami damar bin gargaɗinsa. (M. Sha. 32:4) Me ya sa Allah yake yin hakan? Manzo Bitrus ya bayyana cewa Jehobah ba ya son “wani ya halaka, sai dai kowa ya zo ya tuba.” (2 Bit. 3:9) Hakika, Allah ya damu da mutane sosai. Saboda haka, yana son mutanen su tuba kuma su riƙa bin umurnansa kafin ya hukunta mugaye.​—Isha. 48:​17, 18; Rom. 2:4.

YADDA MUTANE SUKE BIN GARGAƊIN ALLAH A YAU

Yau, mutane suna bukatar su saurari saƙon da ake sanarwa da gaggawa a dukan duniya. A lokacin da Yesu yake duniya, ya gargaɗi mutane cewa za a hallaka zamaninmu a lokacin “azaba mai zafi.” (Mat. 24:21) Yesu ya yi wani annabci da ya taimaka wa mabiyansa su san abubuwa da za su faru sa’ad da lokacin yake kusatowa. Ya ambata abubuwa masu muhimmanci da za su faru da muke gani a yau.​—Mat. 24:​3-12; Luk. 21:​10-13.

Don a cika wannan annabcin, Jehobah yana gayyatar mutane su goyi bayan Mulkinsa. Yana so mutanen da suka yi masa biyayya su more rayuwa a yanzu kuma su mori albarkun da ya yi alkawari a nan gaba. (2 Bit. 3:13) Jehobah yana son ya taimaka wa mutane su gaskata da alkawuran da ya yi. Yana yin hakan ne ta wajen sa su ji saƙon da zai sa su sami ceto. Wannan saƙon shi ne “labari mai daɗi na mulkin sama” wanda Yesu ya annabta cewa za a yi wa’azinsa ga “dukan al’umma.” (Mat. 24:14) Allah yana yin amfani da bayinsa masu aminci wajen ba da wannan “shaida,” ko kuma yin wa’azi a ƙasashe kusan 240. Jehobah yana son mutane da yawa su saurari wannan saƙon kuma su tsira wa hukuncinsa da ke nan tafe.​—Zaf. 1:​14, 15; 2:​2, 3.

Abubuwan da muka tattauna sun nuna cewa a koyaushe, Jehobah yana ba mutane isashen lokaci don su bi gargaɗinsa. Saboda haka, abin da ya fi muhimmanci shi ne: Mutane za su bi gargaɗin Allah a yanzu da akwai ɗan sauran lokaci da ya rage kuwa? Bari dukanmu a matsayin bayin Allah mu ci gaba da taimaka wa mutane da yawa don su tsira.