Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 42

Mene ne Jehobah Zai Sa Ka Zama?

Mene ne Jehobah Zai Sa Ka Zama?

“Allah . . . ne yake sa ku yi niyya ku kuma yi aiki bisa ga kyakkyawan nufinsa.”​—FILIB. 2:13.

WAƘA TA 104 Allah Yana Ba Mu Ruhunsa Mai Tsarki

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne Jehobah zai yi don ya cika nufinsa?

JEHOBAH zai zama dukan abin da yake bukata don ya cika nufinsa. Alal misali, Jehobah ya zama Malami da Uba Mai Ban-ƙarfafa da kuma Mai Shelar Labari Mai Daɗi, da dai sauransu. (Isha. 48:17; 2 Kor. 7:6; Gal. 3:8) Duk da haka, a wasu lokuta yana yin amfani da ’yan Adam don ya cika nufinsa. (Mat. 24:14; 28:​19, 20; 2 Kor. 1:​3, 4) Ƙari ga haka, Jehobah zai iya ba mu hikima da kuma ƙarfin da muke bukata don ya cika nufinsa. Wannan ɗaya ne cikin ma’anar sunan Jehobah, kamar yadda marubuta da yawa suka ce.

2. (a) Me ya sa a wasu lokuta muke shakka ko Jehobah yana amfani da mu? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 Dukanmu muna so Jehobah ya riƙa amfani da mu, amma wasu suna iya yin shakka cewa Jehobah yana amfani da su. Me ya sa? Domin suna ganin cewa ba za su iya yin abubuwa da yawa ba domin shekarunsu ko yanayinsu ko kuma ba su da baiwa. Akasin haka, wasu suna iya gamsuwa da abin da suke yi wa Jehobah a yanzu kuma suna ganin ba sa bukatar samun ci gaba. A wannan talifin, za mu tattauna yadda Jehobah zai taimaka mana mu cika nufinsa. Bayan haka, za mu tattauna labaran Littafi Mai Tsarki don mu ga yadda Jehobah ya ba bayinsa maza da mata ƙarfi da kuma marmarin cika nufinsa. A ƙarshe, za mu ga yadda za mu bari Jehobah ya riƙa yin amfani da mu.

YADDA JEHOBAH YAKE TAIMAKA MANA

3. Kamar yadda Filibiyawa 2:13 ta nuna, ta yaya Jehobah zai taimaka mana mu yi abin da muke marmari?

3 Karanta Filibiyawa 2:13. * Jehobah yana iya sa mu yi marmarin cika nufinsa. Ta yaya zai yi hakan? Alal misali, wataƙila mun ji cewa wani a ikilisiya yana bukatar taimako kuma ana bukatar yin wani aiki. Ko ƙila dattawa sun karanta wata wasiƙa daga reshen ofishi da aka bayyana cewa ana bukatar taimako a wani yanki. Wannan yana iya sa mu tambayi kanmu, ‘A wace hanya ce zan iya taimaka?’ Ko kuma wataƙila an ba mu wani aiki mai wuya kuma muna shakka cewa za mu iya yin aikin. Ko ƙila bayan mun karanta wata aya a Littafi Mai Tsarki, sai muka tambayi kanmu, ‘Ta yaya zan yi amfani da wannan ayar don in taimaka wa mutane?’ Jehobah ba zai tilasa mana mu yi abin da yake so ba. Amma idan ya ga cewa muna tunanin ƙara ƙwazo a hidimarsa, zai taimaka mana mu yi abin da muke tunani a kai.

4. Ta yaya Jehobah zai ba mu ƙarfin cika nufinsa?

4 Ban da haka, Jehobah zai iya ba mu ƙarfin cika nufinsa. (Isha. 40:29) Ta yaya? Zai iya ba mu ruhu mai tsarki don ya taimaka mana mu kyautata baiwar da muke da shi. (Fit. 35:​30-35) Ta ƙungiyarsa, Jehobah yana koya mana yadda za mu yi wasu ayyuka. Idan ba ka san yadda za ka yi wani aiki ba, ka nemi taimako. Ban da haka, kada ka ji kunyar roƙon Jehobah ya ba ka “cikakken iko.” (2 Kor. 4:7; Luk. 11:13) Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da labaran maza da mata da Jehobah ya ba su ƙarfi da kuma marmarin cika nufinsa. Yayin da muke tattauna waɗannan labaran, ka yi tunanin yadda Jehobah zai yi amfani da kai don ka yi irin abubuwan da waɗannan mutanen suka yi.

ABIN DA JEHOBAH YA TAIMAKA WA MAZAJE SU ZAMA

5. Mene ne muka koya game da yadda Jehobah ya yi amfani da Musa da kuma lokacin da ya yi hakan?

5 Jehobah ya yi amfani da Musa don ya ceci Isra’ilawa. Amma a wane lokaci ne Jehobah ya yi amfani da shi? Bai yi hakan a lokacin da Musa yake ganin cewa yana a shirye ya ceci Isra’ilawa ba, wato bayan an “koya wa Musa dukan hikimar Masarawa.” (A. M. 7:​22-25) Amma Jehobah ya yi amfani da Musa bayan ya taimaka masa ya zama mai sauƙin kai. (A. M. 7:​30, 34-36) Ya ba Musa ƙarfin zuciya don ya je gaban sarkin mafi iko a ƙasar Masar. (Fit. 9:​13-19) Mene ne muka koya game da yadda Jehobah ya yi amfani da Musa da kuma lokacin da ya yi hakan? Jehobah yana yin amfani da mutanen da suke yin koyi da halayensa kuma suke dogara gare shi.​—Filib. 4:13.

6. Mene ne muka koya daga yadda Jehobah ya yi amfani da Barzillai don ya taimaka wa Sarki Dauda?

6 Bayan shekaru da yawa, Jehobah ya yi amfani da Barzillai don ya taimaka wa Sarki Dauda. Dauda da mutanensa sun ‘ji yunwa da gajiya da ƙishin ruwa’ domin sun guje wa Absalom ɗan Dauda. Barzillai wanda shi tsoho ne da kuma wasu sun saka ransu cikin haɗari don su taimaka wa Dauda da mutanensa. Barzillai bai yi tunanin cewa Jehobah ba zai iya yin amfani da shi ba domin shekarunsa. A maimakon haka, ya yi amfani da abubuwan da yake da su don ya taimaka wa bayin Allah da suke da bukata. (2 Sam. 17:​27-29) Wane darasi ne za mu iya koya? Duk da shekarunmu, Jehobah zai iya yin amfani da mu don ya taimaka wa ’yan’uwanmu Kiristoci a faɗin duniya da suke da bukata. (K. Mag. 3:​27, 28; 19:17) Wataƙila ba za mu iya taimaka musu da kanmu ba, amma za ka iya ba da gudummawar kuɗi don a yi amfani da shi wajen ba da agaji.​—2 Kor. 8:​14, 15; 9:11.

7. Ta yaya Jehobah ya yi amfani da Simeyon, kuma me ya sa hakan yake da ban-ƙarfafa?

7 Jehobah ya yi wa wani tsoho mai aminci da ke zama a Urushalima mai suna Simeyon alkawari cewa kafin ya mutu, zai ga Almasihu. Hakika, da yake ya yi shekaru da yawa yana jiran zuwan Almasihu, wannan alkawarin ya ƙarfafa shi sosai. Ya sami albarka domin ya nuna bangaskiya kuma ya jimre. Wata rana, “ruhu mai tsarki” ya sa ya je haikali. A wurin, ya ga Yesu sa’ad da yake jariri, kuma Jehobah ya yi amfani Simeyon wajen annabta cewa yaron ne zai zama Kristi. (Luk. 2:​25-35) Ko da yake wataƙila Simeyon bai ga hidimar da Yesu ya yi a duniya ba, amma ya yi farin ciki don gatan da aka ba shi, kuma a nan gaba zai sami gata fiye da hakan! A sabuwar duniya, wannan mutum mai aminci zai ga yadda sarautar Yesu za ta sa ’yan Adam su sami albarka. (Far. 22:18) Mu ma za mu iya nuna godiya don gatar da Jehobah ya ba mu a hidimarsa.

8. Ta yaya Jehobah zai yi amfani da mu kamar Barnaba?

8 A ƙarni na farko, wani mutum mai karimci mai suna Yusufu ya amince Jehobah ya yi amfani da shi. (A. M. 4:​36, 37) Mazannin Yesu sun kira shi Barnaba, wato “Mai Ƙarfafa Zuciya,” wataƙila sun yi hakan ne domin Yusufu ya iya ƙarfafa mutane sosai. Alal misali, sa’ad da Shawulu ya zama Kirista, ’yan’uwa da yawa sun ji tsoron yin cuɗanya da shi domin sun san cewa a dā yana azabtar da Kiristoci. Amma Barnaba ya ƙarfafa Shawulu kuma ya taimaka masa. Hakika, Shawulu ya yi farin ciki don taimakon da ya samu. (A. M. 9:​21, 26-28) Daga baya, dattawan da ke Urushalima sun so su ƙarfafa ’yan’uwan da ke zama a Antakiya da ke Suriya. Waye ne suka tura? Barnaba ne! Hakika, sun yi zaɓi mai kyau. Littafi Mai Tsarki ya ce Barnaba “ya gargaɗe su duka su tsaya da bangaskiya cikin Ubangiji da dukan zuciyarsu.” (A. M. 11:​22-24) A yau ma, Jehobah yana iya taimaka mana mu ƙarfafa ’yan’uwanmu Kiristoci. Alal misali, yana iya yin amfani da mu don ya ƙarfafa waɗanda aka yi musu rasuwa. Ko ya motsa mu mu ziyarci ’yan’uwan da ke rashin lafiya ko baƙin ciki ko kuma mu kira su a waya don mu ƙarfafa su. Za ka yarda Jehobah ya yi amfani da kai yadda ya yi amfani da Barnaba kuwa?​—1 Tas. 5:14.

9. Mene ne muka koya daga yadda Jehobah ya taimaka wa Vasily ya zama dattijon da ya ƙware?

9 Jehobah ya taimaka ma wani ɗan’uwa mai suna Vasily don ya zama dattijon da ya ƙware sosai. A lokacin da Vasily ya soma hidima a matsayin dattijo, shi ɗan shekara 26 ne. Ya ji tsoro domin yana tunanin cewa ba zai iya taimaka wa ’yan’uwa a ikilisiya su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah ba, musamman ma ’yan’uwan da ke fama da matsalolin rayuwa. Amma ya sami taimako daga dattawan da suka ƙware kuma halartar Makarantar Hidima ta Mulki ta taimaka masa sosai. Vasily ya yi ƙoƙari sosai don ya kyautata hidimarsa. Alal misali, ya lissafta maƙasudan da yake so ya cim ma. Kuma da zarar ya cim ma ɗaya daga cikinsu, hakan yana sa shi gaba gaɗi. Ya ce: “Abin da a dā ya tsorata ni yana sa ni farin ciki a yanzu. Sa’ad da Jehobah ya taimaka mini in sami nassin da ya dace da zan iya yin amfani da shi don in ƙarfafa ’yan’uwa a ikilisiya, hakan yana sa in gamsu sosai.” ’Yan’uwa, idan kuka ba da kanku don Jehobah ya yi amfani da ku kamar Vasily, zai taimaka muku ku yi wasu ayyuka a ikilisiya.

ABIN DA JEHOBAH YA TAIMAKA WA MATA SU ZAMA

10. Mene ne Abigail ta yi, kuma wane darasi ne ka koya daga misalinta?

10 Akwai lokacin da Sarki Saul ya so ya kashe Dauda da mutanensa, kuma suna bukatar taimako domin sun koma zama a jeji. Saboda haka, sai Dauda ya roƙi wani Ba’isra’ile mai arziki, mai suna Nabal cewa ya ba su abinci. Sun yi haka ne domin sun ɗan jima suna kāre tumakin Nabal a cikin jeji. Amma Nabal ya ƙi ya taimaka musu. Hakan ya sa Dauda fushi sosai kuma ya so ya kashe dukan mazan da ke gidan Nabal. (1 Sam. 25:​3-13, 22) Amma matar Nabal kyakkyawa mai suna Abigail tana da basira sosai. Cike da ƙarfin zuciya, ta rusuna a gaban Dauda kuma ta roƙe shi cewa kada ya rama muguntar da aka yi masa. Ta shawarce shi cewa ya dogara ga Jehobah don ya taimaka masa. Yadda Abigail ta nuna sauƙin kai da basira ya ratsa zuciyar Dauda. Don haka, ya ce Jehobah ne ya aiko ta. (1 Sam. 25:​23-28, 32-34) Abigail tana da halayen da suka sa Jehobah ya yi amfani da ita. Hakazalika, Jehobah zai yi amfani da ’yan’uwa mata da suke da basira da kuma sanin yakamata don su taimaka wa iyalinsu da kuma ’yan’uwa a ikilisiya.​—K. Mag. 24:3; Tit. 2:​3-5.

11. Mene ne ’ya’yan Shallum suka yi, kuma su waye ne a yau suke yin koyi da su?

11 Bayan ƙarnuka da yawa, ’ya’yan Shallum mata suna cikin waɗanda Jehobah ya yi amfani da su wajen gyara ganuwar Urushalima. (Neh. 2:20; 3:12) Duk da cewa mahaifinsu yarima ne, sun yarda su yi aiki mai wuya. (Neh. 4:​15-18) Ba sa kamar mutanen Tekowa da suka “ƙi su sa hannu cikin aikin.” (Neh. 3:5) Ka yi tunani a kan irin farin cikin da ʼyan matan nan suka yi sa’ad da aka kammala aikin cikin kwanaki 52! (Neh. 6:15) A zamaninmu ma, ʼyan’uwa mata suna farin cikin taimaka wajen yin tsarkakkiyar hidima, wato gina wuraren ibada da kuma gyara su. Ƙwarewarsu da himmarsu suna taimaka wajen sa a cim ma aikin.

12. A wace hanya ce Jehobah zai iya yin amfani da mu, yadda ya yi da Tabita?

12 Jehobah ya motsa Tabita ta “ba da kanta ɗungum cikin yin aikin kirki, da kuma yin sadaka,” musamman ga gwauraye. (A. M. 9:36) Saboda yawan alherinta, mutane sun yi kuka sosai sa’ad da ta rasu. Amma sun cika da farin ciki a lokacin da manzo Bitrus ya tayar da ita daga mutuwa. (A. M. 9:​39-41) Wane darasi ne muka koya daga Tabita? Ko da mu yara ne ko manya, maza ko mata, za mu iya taimaka wa ʼyan’uwanmu.​—Ibran. 13:16.

13. A wace hanya ce Jehobah ya yi amfani da wata ʼyar’uwa mai suna Ruth, kuma mene ne ta ce?

13 Akwai wata ʼyar’uwa mai suna Ruth da ta so ta zama mai wa’azi a ƙasashen waje. ʼYar’uwar nan tana jin kunya. A lokacin da take ƙarama, tana zuwa gidajen mutane da himma ta rarraba musu warƙoƙi. Ta ce: “Ina jin daɗin yin wa’azi sosai.” Amma yin wa’azi gida-gida game da Mulkin Allah yana mata wuya sosai. Duk da cewa Ruth tana jin kunya, ta zama majagaba na kullum sa’ad da take ʼyar shekara 18. A shekara ta 1946, ta halarci Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead. Bayan sun sauke karatu, ta yi hidima a tsibirin Hawaii da ƙasar Jafan. Jehobah ya yi amfani da ita sosai wajen yaɗa bishara a waɗannan ƙasashen. Sa’ad da Ruth ta yi wajen shekara 80 tana yin wa’azi, ta ce: “Jehobah yana ƙarfafa ni sosai. Ya taimaka mini in daina jin kunyar yin wa’azi. Ina da tabbaci cewa Jehobah zai iya yin amfani da kowane mutum da ya dogara gare shi.”

KA BARI JEHOBAH YA YI AMFANI DA KAI

14. Kamar yadda Kolosiyawa 1:29 ta nuna, mene ne ya wajaba mu yi idan muna so Jehobah ya yi amfani da mu?

14 A cikin shekaru da yawa da suka wuce, Jehobah ya yi amfani da bayinsa a hanyoyi dabam-dabam. A wace hanya ce zai yi amfani da kai? Jehobah zai yi amfani da kai idan kana a shirye ka yi aiki tuƙuru. (Karanta Kolosiyawa 1:29.) Idan ka yarda Jehobah ya yi amfani da kai, zai iya sa ka zama mai yin wa’azi da ƙwazo ko ƙwararren malami ko mai ƙarfafa mutane ko wanda ya ƙware a yin aiki ko abokin kirki, ko kuma duk wani abu da yake so don ya cim ma nufinsa.

15. Kamar yadda 1 Timoti 4:​12, 15 suka nuna, me ya kamata ʼyan’uwa matasa su roƙi Jehobah ya yi musu?

15 Idan kai ɗan’uwa ne matashi, a wace hanya ce za ka iya taimakawa? A yanzu haka, ƙungiyar Jehobah tana bukatar maza masu kuzari su zama bayi masu hidima. A ikilisiyoyi da yawa, dattawa sun fi bayi masu hidima yawa. Za ku so ku yi ƙarin hidima a cikin ikilisiya kuwa? A wasu lokuta, wasu ʼyan’uwa maza suna cewa: “Na gamsu da zama mai shelan da ke da ƙwazo.” Idan kana yin irin wannan tunanin, ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka yi marmarin zama bawa mai hidima kuma ya ba ka ƙarfin yin iya ƙoƙarinka a hidimarsa. (M. Wa. 12:1) ʼYan’uwa, muna bukatar taimakonku sosai!​—Karanta 1 Timoti 4:​12, 15.

16. Me ya kamata mu roƙi Jehobah, kuma me ya sa?

16 Jehobah zai iya sa ka zama kowane abu da yake bukata don ya cim ma nufinsa. Saboda haka, ka roƙe shi ya sa ka yi marmarin yin aikinsa, kuma ya ba ka ƙarfin da kake bukata. Ko da kai tsoho ne ko matashi, ka yi amfani da lokacinka da kuzarinka da ƙwarewarka da kuma arzikinka don girmama Jehobah yanzu. (M. Wa. 9:10) Idan an ba ka ƙarin aiki a hidimar Jehobah, kada ka yi jinkirin yin aikin domin kana tunani cewa ya fi ƙarfinka. Dukanmu muna da gatan yin iya ƙoƙarinmu wajen ɗaukaka Ubanmu mai ƙauna!

WAƘA TA 127 Irin Mutumin da Ya Kamata In Zama

^ sakin layi na 5 Kana so ka ƙara ƙwazo a hidimarka ga Jehobah kuwa? Kana shakka ko har yanzu Jehobah yana ɗaukar hidimarka da muhimmanci? Ko kana ganin cewa ba ka bukatar ka ƙara ƙwazo a hidimarka? A wannan talifin, za mu tattauna hanyoyi da yawa da Jehobah yake ba mu ƙarfin da muke bukata don mu zama dukan abin da yake so don cika nufinsa.

^ sakin layi na 3 Ko da yake Bulus ya rubuta wannan wasiƙa ga Kiristoci a ƙarni na farko, dukan bayin Jehobah za su iya yin amfani da ƙa’idar.