Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 43

Mu Bauta wa Jehobah da Dukan Zuciyarmu

Mu Bauta wa Jehobah da Dukan Zuciyarmu

“Yahweh ne Allah mai bukatar cikakkiyar ƙauna.”​—NAH. 1:2.

WAƘA TA 51 Mun Yi Alkawarin Zama Bayin Allah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Me ya sa Jehobah ya cancanci mu bauta masa kaɗai?

JEHOBAH ya cancanci mu bauta masa kaɗai domin shi ne Mahaliccinmu kuma Shi ya ba mu rai. (R. Yar. 4:11) Amma muna iya fuskantar wata matsala. Ko da yake muna ƙaunar Jehobah kuma muna daraja shi, wasu abubuwa za su iya janye hankulanmu daga bauta masa shi kaɗai. Ya kamata mu fahimci yadda hakan zai iya faruwa. Amma bari mu fara tattauna abin da bauta wa Jehobah shi kaɗai yake nufi.

2. Kamar yadda Fitowa 34:14 ta nuna, me za mu yi idan muna bauta wa Jehobah kaɗai?

2 A Littafi Mai Tsarki, kasancewa da cikakkiyar ƙauna ga Jehobah yana da alaƙa da bauta masa shi kaɗai. Idan muna da cikakkiyar ƙauna ga Jehobah, za mu bauta wa shi kaɗai. Ba za mu yarda wani abu ko mutum ya fi muhimmanci a gare mu ba.​—Karanta Fitowa 34:14.

3. Me ya sa muke da dalilai masu kyau na bauta wa Jehobah?

3 Muna da dalilai masu kyau na bauta wa Jehobah. Mun koyi abubuwa da dama game da shi kuma muna son halayensa sosai. Muna son abubuwan da yake so kuma mun tsani abubuwan da ba ya so. Mun fahimci nufinsa a gare mu kuma mun yarda da hakan. Muna matuƙar farin ciki cewa ya ba mu zarafin zama aminansa. (Zab. 25:14) Kowane abu da muka koya game da Mahaliccinmu yana sa mu daɗa kusantar sa.​—Yaƙ. 4:8.

4. (a) Mene ne Shaiɗan yake amfani da shi don ya raunana ƙaunarmu ga Jehobah? (b) Me za mu tattauna a wannan talifin?

4 Shaiɗan Iblis ne yake mulki a kan wannan duniyar, kuma yana yin amfani da ita wajen sa mu yi sha’awar abubuwan da ke wannan duniyar. (Afis. 2:​1-3; 1 Yoh. 5:19) Maƙasudinsa shi ne ya raba hankalinmu don kada mu bauta wa Jehobah shi kaɗai. Bari mu tattauna abubuwa biyu da yake yin amfani da su don ya cim ma burinsa. Na ɗaya, yana jarraba mu mu nemi arziki ruwa a jallo, na biyu, yana jarraba mu mu zaɓi nishaɗin da bai dace ba.

KU GUJI SON KUƊI

5. Me ya sa muke bukatar mu guji son kuɗi?

5 Dukanmu muna bukatar isashen abinci da sutura mai kyau da kuma gidan da ya dace. Amma ya kamata mu yi hankali don kada mu soma son kuɗi. Mutane da yawa a yau suna “son kuɗi” da abin duniya. (2 Tim. 3:2) Yesu ya san cewa mabiyansa za su iya fuskantar wannan jarrabawar, shi ya sa ya shawarce su cewa: “Ba wanda zai iya bauta wa shugabanni biyu, ko dai ya ƙi ɗaya ya so ɗaya, ko ya yi wa ɗayan aminci ya rena ɗayan. Ba dama ku sa ranku ga bin Allah ku kuma sa ga bin kuɗi duk gaba ɗaya.” (Mat. 6:24) Babu shakka, duk mutumin da ke bauta wa Jehobah kuma yake yin amfani da dukan ƙarfinsa wajen neman yin arziki yana bauta wa shugabanni biyu. Ba shi da cikakkiyar ƙauna ga Jehobah.

Yadda wasu a Lawudikiya suka ɗauki kansu . . . da kuma yadda Jehobah da Yesu suka ɗauke su (Ka duba sakin layi na 6)

6. Wane darasi ne muka koya daga shawarar da Yesu ya ba ikilisiyar Lawudikiya?

6 A kusan ƙarshen ƙarni na farko bayan haihuwar Yesu, ʼyan’uwan da ke ikilisiyar Lawudikiya sun yi fahariya cewa: ‘Muna da arziki, muna da dukiya, ba ma bukatar kome.’ Amma a wurin Jehobah da kuma Yesu, su ‘abin tausayi [ne], matalauta, tsiraru, makafi kuma.’ Yesu ya yi musu gargaɗi ba domin suna da arziki ba, amma domin sun bari arziki ya raunana dangantakarsu da Jehobah. (R. Yar. 3:​14-17) Idan mun lura cewa mun soma son kuɗi, ya kamata mu ɗauki mataki nan da nan don mu daidaita ra’ayinmu. (1 Tim. 6:​7, 8) Idan ba haka ba, hankalinmu zai rabu biyu kuma Jehobah ba zai amince da ibadarmu ba. Jehobah yana “bukatar cikakkiyar ƙauna.” (M. Sha. 4:24) Me zai iya sa mu soma son kuɗi fiye da kima?

7-9. Wane darasi ne muka koya daga labarin wani dattijo mai suna David?

7 Ku yi la’akari da misalin wani dattijo mai suna David a Amirka. Ya ce yana aiki tuƙuru a wurin aikinsu. Saboda haka, sai aka ƙara masa matsayi a wurin aiki kuma ya yi suna sosai a ƙasar. David ya ce: “A lokacin, na yi tunani cewa ƙarin matsayin da na samu ya nuna cewa Jehobah yana mini albarka.” Amma hakan gaskiya ne kuwa?

8 David ya soma lura cewa aikinsa ya soma raunana abokantakarsa da Jehobah. Ya ce: “Na lura cewa idan ina taron ikilisiya ko wa’azi, ina yawan yin tunani a kan matsaloli da ke faruwa a wurin aikina. Albashin da ake biya na yana da yawa, amma ina gajiya sosai kuma na soma fuskantar matsaloli a aurena.”

9 David ya lura cewa yana bukatar ya binciki kansa. Ya ce: “Na duƙufa yin canje-canje.” David ya so ya yi gyara ga tsarin ayyukansa kuma ya nuna wa shugaban aikinsa sabon tsarin ayyukan da ya shirya wa kansa. A sakamakon haka, aka sallame shi daga aiki! Yaya David ya ji sa’ad da hakan ya faru? Ya ce: “Washegari, na cika fom ɗin majagaba na ɗan lokaci. Sai shi da matarsa suka soma aikin shara don su biya bukatunsu. Bayan ɗan lokaci, sai ya soma hidimar majagaba na kullum, kuma daga baya, matarsa ma ta zama majagaba. Ma’auratan nan sun yarda su yi aikin da mutane da yawa suka raina, amma ba aikin ne abu mafi muhimmanci a rayuwarsu ba. Ko da yake kuɗin da suke samu ya ragu sosai, amma a kowane wata, suna samun isashen kuɗin biyan bukatunsu. Suna so su nuna cikakkiyar ƙauna ga Jehobah kuma sun lura cewa yana kula da mutanen da suka saka Mulkinsa farko a rayuwarsu.​—Mat. 6:​31-33.

10. Ta yaya za mu iya kiyaye zuciyarmu?

10 Muna bukatar mu kiyaye zuciyarmu ko da mu masu arziki ne ko a’a. Ta yaya za mu yi hakan? Kada ka so abin duniya kuma kada ka yarda aikinka ya fi ibadarka ga Jehobah muhimmanci. Me zai taimaka maka ka san cewa hakan ya soma faruwa? Wasu tambayoyin da za ku iya yi wa kanku su ne: ‘Ina yawan yin tunani game da aikina sa’ad da nake wa’azi ko taro? Ina yawan yin tunani a kan yadda zan yi arziki a nan gaba? Shin ni da matata muna yawan samun saɓani saboda kuɗi? Zan iya yin aikin da mutane suka raina idan aikin zai sa in sami isashen lokacin bauta wa Jehobah?’ (1 Tim. 6:​9-12) Sa’ad da muke tunani a kan waɗannan tambayoyin, wajibi ne mu tuna cewa Jehobah yana ƙaunar mu kuma ya yi alkawarin nan ga mutanen da ke ƙaunar sa: “Har abada ba zan bar ka ba.” Shi ya sa manzo Bulus ya ce: “Ku yi nesa da halin son kuɗi.”​—Ibran. 13:​5, 6.

KA ZAƁI NISHAƊINKA DA KYAU

11. Ta yaya nishaɗi zai iya ɓata mu?

11 Jehobah yana so mu ji daɗin rayuwa kuma nishaɗi zai iya sa mu yi hakan. Kalmar Allah ta ce “babu abin da ya fi kyau ga ’yan Adam fiye da su ci, su sha, su kuma ji daɗin aikinsu.” (M. Wa. 2:24) Amma, nishaɗi da yawa da ake yi a yau suna iya ɓata mu. A wace hanya? Suna ɓata ɗabi’un mutane kuma suna sa su so abubuwan da Jehobah ya haramta a Kalmarsa.

Waye ne yake shirya nishaɗinka? (Ka duba sakin layi na 11-14) *

12. Kamar yadda 1 Korintiyawa 10:​21, 22 suka nuna, me ya sa muke bukatar mu zaɓi nishaɗi mai kyau?

12 Da yake muna so mu nuna wa Jehobah cikakkiyar ƙauna, ba zai yiwu mu “ci abinci a teburin” Jehobah mu kuma “ci a na aljanu” ba. (Karanta 1 Korintiyawa 10:​21, 22.) Idan mun ci abinci tare da wani, hakan yana nuna cewa shi abokinmu ne. Hakazalika, idan muka zaɓi nishaɗin da ake ɗaukaka mugunta da sihiri da lalata ko kuma wasu halaye na wannan duniyar, muna cin abincin da maƙiyan Allah suka dafa. A sakamakon haka, muna jawo wa kanmu lahani kuma muna ɓata abotarmu da Jehobah.

13-14. Kamar yadda Yaƙub 1:​14, 15 suka nuna, me ya sa ya kamata mu mai da hankali a kan irin nishaɗin da muke yi? Ka ba da misali.

13 Ku yi la’akari da yadda nishaɗi yake kamar abinci. Sa’ad da muke cin abinci, za mu iya zaɓan wanda za mu saka a bakinmu. Amma da zarar mun haɗiye abincin, zai narke a cikinmu kuma ya shiga jininmu. Abinci mai kyau zai iya gina mana jiki kuma abinci marar kyau zai iya sa mu yi rashin lafiya. Wataƙila abincin ba zai sa mu rashin lafiya nan da nan ba, sai an ɗan jima kaɗan.

14 Hakazalika, yayin da muke zaɓan nishaɗi, za mu iya zaɓan abubuwa da za mu yarda su shiga zuciyarmu. Amma bayan haka, abubuwan da muka yarda su shiga zuciyarmu za su iya jawo mana la’ani. Nishaɗi mai kyau zai iya sa mu farin ciki amma nishaɗi marar kyau zai jawo mana la’ani. (Karanta Yaƙub 1:​14, 15.) Wataƙila ba za mu shaida sakamako marar kyau na nishaɗin da muka yi nan da nan ba. Amma daga baya, zai shafe mu. Shi ya sa Jehobah ya gargaɗe mu cewa: “Kada ku ruɗi kanku, ai ba ya yiwuwa a yi wa Allah wayo. Duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba. Gama idan mutum ya shuka ta biyan sha’awar jiki, zai kai shi girbin mutuwa.” (Gal. 6:​7, 8) Saboda haka, yana da muhimmanci sosai mu nisanta kanmu daga nishaɗin da ke ɗaukaka abubuwan da Jehobah ba ya so.​—Zab. 97:10.

15. Wane tanadi ne Jehobah ya yi mana don mu ji daɗin rayuwa?

15 Bayin Jehobah da yawa suna jin daɗin kallon Tashar JW kuma tashar tana ɗauke da abubuwa masu ban-ƙarfafa. Wata ʼyar’uwa mai suna Marilyn ta ce: “Tashar JW ta taimaka mini in kasance da ra’ayin da ya dace kuma ba na tace abin da zan kalla. A duk lokacin da na kaɗaita ko na yi sanyin gwiwa, ina kallon jawabi ko Ibadar Safiya mai ban-ƙarfafa. Shirye-shiryen suna sa in kusaci Jehobah da ƙungiyarsa. Tashar JW ta canja rayuwata gabaki ɗaya.” Kuna amfana daga tanadin da Jehobah ya yi mana kuwa? Ban da shirye-shiryen da ake yi kowane wata a Tashar JW, ana saka sababbin sauti da bidiyoyi da kuma waƙoƙi masu daɗi da za ku iya morewa a duk lokacin da kuke so.

16-17. Me ya sa ya wajaba mu yi la’akari da yawan lokacin da muke yi muna nishaɗi, kuma ta yaya za mu yi hakan?

16 Ya kamata mu yi hankali da irin nishaɗin da muke yi da kuma yawan lokacin da muke yi muna yinsa. Idan ba haka ba, za mu yi amfani da yawancin lokacinmu muna yin nishaɗi maimakon bauta wa Jehobah. Yana da wuya mutane da yawa su yi nishaɗi daidai-wa-daida. Wata ʼyar’uwa ʼyar shekara 18 mai suna Abigail ta ce: “Kallon talabijin bayan na daɗe ina yin aiki yana kwantar mini da hankali. Amma idan ban yi hankali ba, zan iya yin sa’o’i ina kallon talabijin.” Wani ɗan’uwa matashi mai suna Samuel ya ce: “A wasu lokuta, ina yin sa’o’i da yawa ina kallon gajerun bidiyoyi a Intane. Ina somawa da guda kuma kafin in sani, na riga na yi wajen sa’o’i uku ko huɗu ina kallo.”

17 Me zai taimaka maka ka rage yawan lokacin da kake yin nishaɗi? Mataki na farko shi ne sanin yawan sa’o’in da kake yi kana nishaɗi. Zai dace ka rubuta a kalandarka yawan sa’o’in da kake yi kana kallon talabijin da yin amfani da Intane da zuwa bukukuwa da kuma yin wasannin bidiyo. Idan ka lura cewa kana ɓata lokaci sosai a waɗannan abubuwan, ka shirya wa kanka tsarin ayyuka. Ka fara ƙayyade lokaci don yin abubuwa masu muhimmanci, sai ka yi amfani da sauran lokacin a yin nishaɗi. Bayan haka, ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka bi tsarin ayyukan. Hakan zai taimaka maka ka sami lokaci da kuma ƙarfin yin nazarin Littafi Mai Tsarki da ibada ta iyali da shirya taro, da kuma bauta wa Jehobah ta yin wa’azi da koyarwa. A sakamakon haka, ba za ka yi da-na-sani ba don yadda ka yi amfani da lokacinka.

KA CI GABA DA BAUTA WA JEHOBAH DA DUKAN ZUCIYARKA

18-19. Ta yaya za mu nuna cewa muna bauta wa Jehobah kaɗai?

18 Bayan manzo Bitrus ya rubuta game da duniyar Shaiɗan da kuma sababbin sammai da sabuwar duniya, sai ya ce: “ ’Yan’uwa waɗanda nake ƙauna, da yake kuna marmarin zuwan ranar, sai ku yi iyakacin ƙoƙarinku ku yi zamanku a gaban Allah ba tare da wani abin zargi ko tabo ba. Ku yi zama a gabansa da salama.” (2 Bit. 3:14) Idan mun bi wannan shawarar, muka yi iya ƙoƙarinmu don mu kasance da ɗabi’a mai kyau kuma muka bauta wa Jehobah yadda ya dace, za mu nuna cewa muna bauta wa masa shi kaɗai.

19 Shaiɗan da duniyarsa za su ci gaba da matsa mana mu canja ra’ayinmu. (Luk. 4:13) Amma ko da wane ƙalubale ne muka fuskanta, ba za mu yarda wani abu ko wani halitta ya hana mu bauta wa Jehobah kaɗai ba. Mun duƙufa cewa za mu ba Jehobah abin da shi kaɗai ne ya cancanta, wato cikakkiyar ƙaunarmu!

WAƘA TA 30 Jehobah Ubana, Allahna da Abokina

^ sakin layi na 5 Muna son bauta wa Jehobah. Amma shi kaɗai ne muke bauta wa kuwa? Zaɓin da muke yi zai nuna ko amsar e ce ko a’a. Yanzu za mu tattauna fannoni biyu na rayuwa da za mu nuna ko muna bauta wa Jehobah kaɗai.

^ sakin layi na 53 BAYANI A KAN HOTO: Ba za mu so mu ci abincin da aka shirya a wuri marar tsabta ba. Hakazalika, ba zai dace mu kalli bidiyoyin da ake nuna mugunta da sihiri ko kuma lalata ba.