Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 41

Ku Kasance da Aminci a Lokacin Kunci Mai Girma

Ku Kasance da Aminci a Lokacin Kunci Mai Girma

“Ku ƙaunaci Yahweh, dukanku masu ƙaunarsa! Yahweh yana kiyaye masu aminci.”​—ZAB. 31:23.

WAƘA TA 129 Za Mu Riƙa Jimrewa

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. (a) Wace sanarwa ce za a yi nan ba daɗewa ba? (b) Waɗanne tambayoyi ne muke bukatar amsoshinsu?

KA YI tunani cewa shugabannin duniya sun fito kuma suka yi sanarwar da aka annabta za a yi cewa an sami “zaman lafiya da salama.” Suna iya yin da’awa cewa ba a taɓa samun kwanciyar hankali kamar haka ba. Al’ummai za su so su sa mu soma tunani cewa sun magance matsalolin ʼyan Adam. Amma ba za su iya dakatar da abin da zai biyo baya ba! Me ya sa? Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa “halaka za ta auko musu, . . . ba kuwa hanyar tsira.”​—1 Tas. 5:3.

2 Da akwai tambayoyi masu muhimmanci da muke bukatar mu san amsoshinsu: Mene ne zai faru a lokacin ƙunci mai girma? Mene ne Jehobah zai so mu yi a lokacin? Kuma ta yaya za mu kasance a shirye domin mu riƙe amincinmu a lokacin ƙunci mai girma?​—Mat. 24:21.

MENE NE ZAI FARU A LOKACIN ƘUNCI MAI GIRMA?

3. Kamar yadda Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 17:​5, 15-18 suka nuna, ta yaya Allah zai halaka Babila Babba?

3 Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 17:​5, 15-18. Za a halaka Babila Babba! Kamar yadda aka ambata ɗazu, al’ummai ba za su iya dakatar da abin da zai faru ba. Me ya sa? Domin ‘Allah ya nufe su su aikata nufinsa.’ Wane nufi ke nan? Su halaka dukan addinan ƙarya har da waɗanda suke da’awa cewa su Kiristoci ne. Allah zai sa “Ƙahoni goma” na jar “dabbar” su aikata nufinsa. Ƙahoni nan suna wakiltar dukan gwamnatocin da suke goyon bayan “dabbar,” wato Majalisar Ɗinkin Duniya. (R. Yar. 17:​3, 11-13; 18:8) Sa’ad da waɗanda gwamnatoci suka kai wa addinan ƙarya hari, wannan shi ne zai nuna cewa ƙunci mai girma ya soma. Wannan mawuyacin yanayin zai shafi kowa a duniya.

4. (a) Waɗanne dalilai ne gwamnatoci za su ba da na kai wa addinan ƙarya hari? (b) Mene ne mabiyan addinan za su yi?

4 Ba mu san dalilai da gwamnatoci za su bayar na kai wa Babila Babba hari ba. Wataƙila suna iya cewa addinan ƙarya suna sa mutanen kasa kasancewa da kwanciyar rai kuma su ce addinan suna yawan saka hannu a batutuwan siyasa. Ko kuma wataƙila su ce ƙungiyoyin addinan ƙarya sun tara dukiyoyi da yawa. (R. Yar. 18:​3, 7) Sa’ad da gwamnatoci suka kai wa addinan ƙarya hari, wataƙila ba za su halaka dukan mabiya addinan ba. Kamar dai, addinan ne za a halaka. Da zarar an kawar da waɗannan addinan, mabiyansu za su ga cewa malamansu sun ci amanarsu, don haka za su nisanta kansu daga addinan.

5. Wane alkawari ne Jehobah ya yi game da ƙunci mai girma, kuma me ya sa?

5 Littafi Mai Tsarki bai faɗi yawan kwanaki da za a yi ana halaka Babila Babba ba, amma mun san cewa zai ɗau ɗan ƙanƙanin lokaci ne. (R. Yar. 18:​10, 21) Jehobah ya yi alkawari cewa zai “rage kwanakin” ƙunci mai girma kuma ba za a halaka addinin gaskiya ba. (Mar. 13:​19, 20) Amma mene ne Jehobah zai so mu yi daga lokacin da aka soma ƙunci mai girma har zuwa lokacin yaƙin Armageddon?

KU CI GABA DA BAUTA WA JEHOBAH

6. Bayan mun guji saka hannu a ayyukan addinan ƙarya, mene ne muke bukatar mu yi?

6 Kamar yadda muka tattauna a talifin da ya gabata, Jehobah yana so bayinsa su guji addinan ƙarya. Ba kawai guje wa saka hannu a ayyukan addinan ƙarya muke bukatar mu yi ba, amma muna bukatar mu ƙuduri niyyar bauta wa Jehobah. Ka yi la’akari da hanyoyi biyu da za mu iya yin hakan.

Kada mu taɓa daina halartan taro, har a mawuyacin yanayi (Ka duba sakin layi na 7) *

7. (a) Ta yaya za mu ci gaba da bin ƙa’idodin Jehobah? (b) Ta yaya Ibraniyawa 10:​24, 25 suka nanata muhimmanci yin taro tare da ’yan’uwa, musamman ma a yanzu?

7 Na farko, muna bukatar mu riƙa bin ƙa’idodin Jehobah da ƙarfin zuciya. Ba za mu taɓa amincewa da ɗabi’un mutanen duniya ba. Alal misali, ba ma amincewa da lalata, har da luwaɗi da kuma auren jinsi ɗaya. (Mat. 19:​4, 5; Rom. 1:​26, 27) Na biyu, muna bukatar mu ci gaba da bauta wa Jehobah tare da ’yan’uwanmu Kiristoci. Muna yin hakan a duk inda muka sami dama, ko a Majami’ar Mulki ko a gidajen ’yan’uwa ko kuma a ɓoye. Ko da mene ne ya faru, ba za mu daina yin taro tare da ’yan’uwanmu ba. Hakika muna bukatar mu ‘ƙara yin haka yayin da muke ganin cewa ranar nan tana matsowa kusa.’​—Karanta Ibraniyawa 10:​24, 25.

8. Ta yaya saƙon da muke wa’azinsa zai canja a nan gaba?

8 A lokacin ƙunci mai girma, saƙon da muke wa’azi zai canja. A yanzu, muna wa’azin bishara game da Mulkin Allah kuma muna ƙoƙarin almajirtar da mutane. Amma a lokacin, za mu yi wa’azi ba tare da yin ɓoye-ɓoye ba. Saƙon zai zama kamar “manyan ƙanƙara.” (R. Yar. 16:21) Wataƙila za mu yi wa’azi cewa nan ba da daɗewa ba za a halaka duniyar Shaiɗan. Da shigewar lokaci, za mu san kowane irin saƙo ne za mu yi wa’azinsa da kuma yadda za su yi hakan. Shin za mu riƙa yin wa’azi yadda muke yi fiye da shekara ɗari don mu cim ma hidimarmu? Ko kuma za mu yi amfani da wata dabara dabam ne? Muna bukatar mu jira mu gani. Ko da ta yaya ne muka yi wa’azi, za mu sami damar yin shelar huƙuncin Allah kai tsaye!​—Ezek. 2:​3-5.

9. Mene ne wataƙila al’ummai za su yi don saƙon da muke wa’azi a kai, amma wane tabbaci ne muke bukatar mu kasance da shi?

9 Kamar dai saƙon da muke wa’azinsa zai ɓata wa al’ummai rai sosai kuma za su so su hana mu yin wa’azi gabaki ɗaya. Kamar yadda muke dogara ga Jehobah don ya taimaka mana a wa’azi a yanzu, za mu bukaci taimakonsa a nan gaba. Muna bukatar mu kasance da tabbaci cewa Allah zai ba mu ƙarfin cika nufinsa.​—Mik. 3:8.

KU YI SHIRI DON HARIN DA ZA A KAWO WA BAYIN ALLAH

10. Kamar yadda aka annabta a Luka 21:​25-28, mene ne yawancin ’yan Adam za su yi domin abubuwan da za su faru a ƙunci mai girma?

10 Karanta Luka 21:​25-28. A lokacin ƙunci mai girma, mutane za su yi mamaki sosai sa’ad da suka ga dukan abubuwan da suke zato za su kasance har abada sun halaka. Za su ji tsoro sosai kuma za su damu cewa za a halaka su a wannan mawuyacin lokaci da ba a taɓa yin irinsa ba. (Zaf. 1:​14, 15) A wannan lokaci, rayuwa za ta yi wuya har ga mutanen Jehobah. Da yake mun ƙi saka hannu a harkokin duniya, muna iya shan wahala. Wataƙila za mu ci gaba da yin rayuwa ba tare da wasu abubuwa da muke bukata ba.

11. (a) Me ya sa za a mai da hankali ga Shaidun Jehobah? (b) Me ya sa bai kamata mu ji tsoron ƙunci mai girma ba?

11 Mutanen da aka halaka addininsu za su yi fushi sosai domin Shaidun Jehobah sun ci gaba da yin ibadarsu. Hakika za su nuna wa kowa cewa suna fushi sosai, kuma ƙila za su nuna hakan a dandalin sada zumunta na Intane. Al’ummai da kuma shugabansu Shaiɗan, za su tsane mu sosai domin addininmu ne kaɗai ba a halaka ba. Ba za su cim ma burinsu na halaka dukan addinan da suke duniya ba. Don haka, za su mai da hankali a kanmu. A wannan lokacin ne al’ummai za su zama Gog na ƙasar Magog. * Za su haɗa kai don su kai wa mutanen Jehobah hari da dukan ƙarfinsu. (Ezek. 38:​2, 14-16) Za mu iya damuwa a wannan lokacin musamman domin ba mu san yadda abubuwa za su kasance ba. Amma abu ɗaya da muke da tabbaci shi ne: Ba ma bukatar mu ji tsoron ƙunci mai girma. Jehobah zai ba mu umurnan da za su ceci rayukanmu. (Zab. 34:19) Za mu ‘shirya kanmu sosai domin cetonmu ya yi kusa.’ *

12. Ta yaya “bawan nan mai aminci, mai hikima” yake shirya mu domin abubuwan da za su faru a nan gaba?

12 “Bawan nan mai aminci, mai hikima” yana shirya mu domin mu kasance da aminci a lokacin ƙunci mai girma. (Mat. 24:45) Ya yi hakan a hanyoyi da yawa. Ka yi la’akari da misali guda, wato taron yanki da muka halarta a shekara ta 2016 zuwa 2018. A jawaban da aka yi a taron, an ƙarfafa mu mu ci gaba da kyautata halayenmu yayin da ranar Jehobah take kusatowa. Bari mu ɗan tattauna waɗannan halayen.

KU CI GABA DA KASANCEWA DA AMINCI DA JIMIRI DA KUMA ƘARFIN ZUCIYA

Ka yi shiri yanzu don ka tsira a lokacin ƙunci mai girma (Ka duba sakin layi na 13-16) *

13. Ta yaya za mu ƙarfafa amincinmu ga Jehobah, kuma me ya sa muke bukatar yin hakan a yanzu?

13 Aminci: Jigon taron yanki na 2016 shi ne, “Ka Riƙe Aminci ga Jehobah!” Wannan taron ya koya mana cewa idan muna da dangantaka mai kyau da Jehobah, za mu riƙe amincinmu a gare shi. An tunasar da mu cewa za mu iya kusantar Jehobah ta addu’a da kuma yin nazarin Kalmarsa sosai. Yin hakan zai ba mu ƙarfin jimre dukan matsalolin da muke fuskanta. Yayin da ake gab da halaka duniyar Shaiɗan, za a jarraba amincinmu ga Allah da kuma Mulkinsa. Kuma mai yiwuwa mutane za su ci gaba da yi mana ba’a. (2 Bit. 3:​3, 4) Dalili ɗaya da zai sa hakan ya faru shi ne domin ba ma goyon bayan duniyar Shaiɗan. Muna bukatar mu ƙarfafa amincinmu a yanzu domin mu riƙe aminci a lokacin ƙunci mai girma.

14. (a) Mene ne zai faru da ’yan’uwan da ke ja-goranci a ƙungiyar Jehobah? (b) Me ya sa muke bukatar mu kasance da aminci a wannan lokacin?

14 A lokacin ƙunci mai girma, za a sami canji a ’yan’uwan da suke yin ja-goranci a ƙungiyar Jehobah a duniya. Dukan shafaffun da ke duniya za su je sama don su saka hannu a yaƙin Armageddon. (Mat. 24:31; R. Yar. 2:​26, 27) Hakan yana nufin cewa Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ba za su kasance tare da mu a duniya ba. Amma taro mai girma za su kasance da tsari. ’Yan’uwa da suka ƙware waɗanda su waɗansu tumaki ne za su yi ja-goranci. Muna bukatar mu nuna amincinmu ta wajen goyon bayan waɗannan ’yan’uwa da kuma bin umurnan da Allah ya ba su. Yin hakan ne zai sa mu tsira!

15. Ta yaya za mu ƙarfafa jimirinmu, kuma me ya sa yake da muhimmanci mu yi hakan yanzu?

15 Jimiri: Jigon taron yanki na 2017 shi ne, “Kar Ka Gaji!” Taron ya taimaka mana mu ƙarfafa kanmu don jimre jarrabawa. Mun koyi cewa muna bukatar mu nuna jimiri har a lokacin da muke fuskantar mawuyacin yanayi. Muna iya ƙarfafa jimirinmu ta wajen dogara ga Jehobah. (Rom. 12:12) Kada mu manta alkawarin da Yesu ya yi, ya ce: ‘Amma wanda ya jimre har zuwa ƙarshe, zai tsira.’ (Mat. 24:13) Wannan alkawarin yana nufin cewa wajibi ne mu jimre ko da wace irin jarrabawa ce muka fuskanta. Ta jimre matsaloli a yanzu, za mu sami ƙarfin gwiwa kafin a soma ƙunci mai girma.

16. Mene ne zai sa mu kasance da ƙarfin zuciya, kuma ta yaya za mu ƙara kasancewa da ƙarfin zuciya a yanzu?

16 Ƙarfin zuciya: Jigon taron yanki na 2018 shi ne “Ku Zama Masu Ƙarfin Zuciya”! Jawaban da aka yi a taron sun tuna mana cewa baiwar da muke da su ba za su iya sa mu kasance da ƙarfin zuciya ba. Kamar yadda muke bukatar mu dogara ga Jehobah don mu jimre matsaloli, dole ne mu dogara ga Jehobah don mu kasance da ƙarfin zuciya. Ta yaya za mu daɗa dogara ga Jehobah? Ta wajen karanta Kalmarsa kowace rana da kuma yin tuna sosai a kan yadda Jehobah ya ceci bayinsa a zamanin dā. (Zab. 68:20; 2 Bit. 2:9) Sa’ad da al’ummai suka kawo mana hari a lokacin ƙunci mai girma, za mu bukaci kasancewa da ƙarfin zuciya kuma mu dogara ga Jehobah sosai. (Zab. 112:​7, 8; Ibran. 13:6) Idan muka dogara ga Jehobah a yanzu, za mu sami ƙarfin zuciyar da muke bukata sa’ad da Gog ya kawo mana hari. *

KA YI DOƘIN SAMUN CETO

Yesu da rundunarsa na sama za su yi yaƙin Armageddon don su halaka maƙiyan Allah! (Ka duba sakin layi na 17)

17. Me ya sa bai kamata mu ji tsoron yaƙin Armageddon ba? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

17 Kamar yadda aka ambata a talifin da ya gabata, an haifi yawancinmu a kwanaki na ƙarshe. Kuma muna da begen tsira a lokacin ƙunci mai girma. Yaƙin Armageddon shi ne zai kawo ƙarshen wannan zamanin. Amma ba ma bukatar mu ji tsoro. Me ya sa? Domin wannan yaƙin Allah ne. (K. Mag. 1:33; Ezek. 38:​18-20; Zak. 14:3) Sa’ad da Jehobah ya ba da umurni, Yesu zai ja-goranci rundunar Allah a yaƙin. Shafaffu da aka ta da zuwa sama za su kasance tare da shi kuma dubban mala’iku ma za su kasance da shi. Za su haɗa ƙarfi da ƙarfe su yaƙi Shaiɗan da aljanunsa da kuma magoya bayansa a duniya.​—Dan. 12:1; R. Yar. 6:2; 17:14.

18. (a) Wane tabbaci ne Jehobah ya ba mu? (b) Me ya sa Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:​9, 13-17 suka sa ka kasance da tabbaci?

18 Jehobah ya tabbatar mana da cewa: ‘Babu kayan yaƙin da aka ƙera domin a yaƙe mu wanda zai yi nasara.’ (Isha. 54:17) Taro mai girma na bayin Jehobah masu aminci za su tsira a lokacin ƙunci mai girma! Bayan haka, za su ci gaba da bauta masa. (Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:​9, 13-17.) Littafi Mai Tsarki ya taimaka mana mu kasance da tabbaci cewa za mu sami kāriya a nan gaba! Mun san cewa Jehobah “yana kiyaye masu aminci.” (Zab. 31:23) Dukan waɗanda suke ƙaunar Jehobah da kuma yabon sa, za su yi murna sosai sa’ad da suka ga ya ɗaukaka sunansa mai tsarki.​—Ezek. 38:23.

19. Mene ne za mu more nan ba da daɗewa ba?

19 Ka yi tunanin yadda za a rubuta 2 Timoti 3:​2-5 da a ce suna magana ne game da mutanen da za su yi rayuwa a sabuwar duniya da babu Shaiɗan. (Ka duba akwatin nan “ Halayen Mutane a Lokacin.”) Ɗan’uwa George Gangas wanda ya yi hidima a matsayin memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ya ce: “Duniya za ta yi kyau sosai sa’ad da kowa yake bauta wa Jehobah a matsayin ’yan’uwa! Nan ba da daɗewa ba, za ku sami gatar yin rayuwa a sabuwar duniya. Za ku yi rayuwa har abada, yadda Jehobah ma yake rayuwa har abada.” Hakika wannan lokaci ne mai kyau sosai da muke jira!

WAƘA TA 122 Mu Tsaya Daram, Babu Tsoro!

^ sakin layi na 5 Mun san cewa nan ba da daɗewa ba, za a yi ƙunci mai girma da zai shafi dukan ’yan Adam. Mene ne zai faru da bayin Jehobah a wannan lokacin? Mene ne Jehobah zai so mu yi? Waɗanne halaye ne muke bukata yanzu don mu riƙe aminci? Za mu sami amsoshin a wannan talifin.

^ sakin layi na 11 MA’ANAR WASU KALMOMI: Wannan furuci Gog na ƙasar Magog yana nufin al’ummai da suka haɗa kai don su halaka addini na gaskiya a lokacin ƙunci mai girma.

^ sakin layi na 11 Don samun cikakken bayani game da abin da zai faru kafin Armageddon, ka duba shafi na 21 a littafin nan Mulkin Allah Yana Sarauta! Don ƙarin bayani game da harin da Gog na ƙasar Magog da kuma yadda Jehobah zai kāre mutanensa, ka duba w15 7/15, shafuffuka na 14-19 da babi na 17 da 18 na littafin nan Pure Worship of Jehovah​—Restored At Last!

^ sakin layi na 16 Taron yankin na 2019 da ke da jigo “Ƙauna Ba Ta Ƙarewa”! zai sa mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai kāre mu.​—1 Kor. 13:8.

^ sakin layi na 63 BAYANI A KAN HOTO: A lokacin ƙunci mai girma, wani rukunin Shaidu sun haɗu a daji da ƙarfin zuciya don su yi taro.

^ sakin layi na 65 BAYANI A KAN HOTO: Taro mai girma na bayin Jehobah masu aminci za su tsira a lokacin ƙunci mai girma kuma za su yi farin ciki!