Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ɗan’uwa Joseph F. Rutherford da wasu ’yan’uwa a lokacin da suka ziyarci Turai

1920​—Shekaru Dari da Suka Shige

1920​—Shekaru Dari da Suka Shige

DAGA shekara ta 1920, bayin Jehobah sun saka ƙwazo sosai don su yi aikin da ke gabansu. Shi ya sa suka zaɓi jigon nan a shekara ta 1920: “UBANGIJI shi ne ƙarfina da waƙata.”​—Zab. 118:​14, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.

Jehobah ya ƙarfafa waɗannan bayinsa da suke son wa’azi. A wannan shekarar, adadin majagaba ya ƙaru daga 225 zuwa 350. Kuma masu shela fiye da 8,000 sun tura rahoton hidimarsu a lokaci na farko zuwa hedkwatarmu. Jehobah ya albarkace su sosai domin ya sa mutane sun saurare su.

SUN NUNA ƘWAZO SOSAI

A ranar 21 ga Maris, 1920, Ɗan’uwa Joseph F. Rutherford wanda shi ne ke ja-goranci a aikin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki a lokacin ya yi jawabi mai jigo “Millions Now Living Will Never Die.” (Miliyoyin Mutane da Suke Rayuwa Yanzu Ba Za Su Taɓa Mutuwa Ba.) Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun yi iya ƙoƙarinsu don su gayyaci mutane su saurari jawabin. Sun yi hayar gidan wasan kwaikwayo mafi girma a birnin New York kuma sun rarraba takardun gayyata guda 320,000.

Jaridar da ta yi tallar jawabin nan “Millions Now Living Will Never Die”

Mutane sun zo sosai fiye da yadda ɗaliban suka yi zato. Mutane fiye da 5,000 sun cika gidan wasan kuma aka gaya wa sauran mutane 7,000 su koma domin babu wurin zama. Hasumiyar Tsaro ta kira taron “taro da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka fi yin nasara.”

Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun yi suna sosai don shelar wannan jawabin. A lokacin, ba su fahimci ba cewa ya kamata su yi shelar Mulkin Allah a faɗin duniya. Duk da haka, suna da ƙwazo sosai. Wata ’yar’uwa mai suna Ida Olmstead wadda ta soma halartan taro a shekara ta 1902, ta ce: “Mun san cewa dukan ’yan Adam za su sami albarka a nan gaba, kuma ba mu fasa yin shelar wannan albishiri ga waɗanda muka haɗu da su a wa’azi ba.”

MUN SOMA BUGA LITTATTAFAI

Don a tabbata cewa ’yan’uwa suna samun abin da zai sa su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah, ’yan’uwa a Bethel sun soma buga wasu cikin littattafanmu da kansu. Sun saya wata maɗaba’a kuma suka kafa ta a wani gidan haya a 35 Myrtle Avenue da ke Brooklyn, kuma wurin ba shi da nisa daga Bethel.

’Yan’uwa Leo Pelle da Walter Kessler sun soma hidima a Bethel a Janairu 1920. Walter ya ce: “Sa’ad da muka isa, mai kula da sashen buga littattafai ya kalle mu kuma ya ce, ‘Muna da awa ɗaya da minti talatin kafin mu je hutu.’ Sai ya ce mu ɗauko wasu kwalayen littattafai.”

Leo ya faɗi abin da ya faru washegari, ya ce: “An ce mu wanke bangwayen da ke ginin ƙasa na benen. Ban taɓa share wuri mai datti kamar wannan ba. Amma aikin Jehobah ne, shi ya sa yin wannan aikin ya sa mu farin ciki.”

Injin buga Littattafai da aka buga Hasumiyar Tsaro da shi

A cikin ’yan makonni, ’yan’uwa masu ƙwazo da suka ba da kansu sun soma buga Hasumiyar Tsaro. An buga Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Fabrairu, 1920, guda dubu sattin a injin buga littattafai da ke hawa na farko a gidan benen. Ban da haka, an kafa wani injin buga littattafai a gidan kuma ’yan’uwan suka sa masa suna Battleship. Bayan haka, mun soma buga mujallar The Golden Age na 14 ga Afrilu, 1920, a maɗaba’armu. Hakika, Jehobah ya albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcen waɗannan ’yan’uwa masu ƙwazo.

“Aikin Jehobah ne, shi ya sa yin wannan aikin ya sa mu farin ciki”

“BARI MU YI ZAMAN LAFIYA”

Bayin Jehobah masu aminci suna jin daɗin aikin da suke yi da kuma yin cuɗanya da ’yan’uwa. Wasu Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun bar ƙungiyar Jehobah a lokacin da ake fuskantar matsaloli a shekara ta 1917 zuwa 1919. Mene ne za a yi don a taimaka musu?

Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Afrilu, 1920, tana ɗauke da talifi mai jigo: “Let Us Dwell in Peace” (Bari Mu Yi Zaman Lafiya.) A talifin, an gaya musu cewa: “Muna da tabbaci . . . cewa duk wanda yake da ruhun Ubangiji . . . zai manta abin da ya faru, . . . don a kasance da haɗin kai.”

Mutane da yawa sun bi wannan umurnin. Wasu ma’aurata sun ce: “Gaskiya ne cewa a shekarun da suka shige, mun yi zaman kashe wando yayin da wasu suke yin wa’azi. . . . Mun ƙuduri niyya cewa za mu riƙa wa’azi da ƙwazo.” Waɗannan ’yan’uwan suna da aiki da yawa da za su yi a nan gaba.

AN RARRABA MUJALLAR “ZG”

A ranar 21 ga Yuni, 1920, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun soma rarraba littafin nan The Finished Mystery * da ke da laƙabin nan “ZG.” Akwai littattafan nan da yawa da ba a rarraba ba domin a shekara ta 1918, hukuma ta hana a rarraba su.

An gaya wa dukan masu shela su saka hannu wajen rarraba wannan littafin, ba majagaba kaɗai ba. An gaya wa dukan waɗanda suka yi baftisma su yi wannan aikin da farin ciki. Kuma an ƙarfafa ’yan’uwan su saka ƙwazo a rarraba wannan littafin. Wani ɗan’uwa mai suna Edmund Hooper ya tuna cewa wannan ne lokaci na farko da ’yan’uwa da yawa suka yi wa’azi gida-gida. Ya daɗa cewa: “Mun soma fahimtar abin da yin wa’azi a faɗin duniya ya ƙunsa.”

AN SAKE TSARA AIKINMU A TURAI

Sadawa da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki yana da wuya a ƙasashe da yawa a lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya, kuma Ɗan’uwa Rutherford yana so ya ƙarfafa waɗannan ’yan’uwan kuma ya sake tsara yadda ake wa’azi. Saboda haka, a ranar 12 ga Agusta, 1920, Ɗan’uwa Rutherford da ’yan’uwa huɗu suka yi tafiya zuwa Ingila da kuma ƙasashe da yawa.

Ɗan’uwa Rutherford a ƙasar Masar

Sa’ad da Ɗan’uwa Rutherford ya ziyarci Birtaniya, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun yi taron yanki guda uku da kuma jawabi ga jama’a guda 12. Kuma an ce aƙalla mutane 50,000 ne suka halarci taron. Da ake taƙaita abin da ya faru a cikin Hasumiyar Tsaro, an ce: “Yan’uwan sun sami ƙarfafawa sosai. Sun yi cuɗanya da kuma aiki da juna sosai kuma hakan ya sa su farin ciki.” A birnin Paris, Ɗan’uwa Rutherford ya sake ba da jawabin nan “Millions Now Living Will Never Die.” (Miliyoyin Mutane da Suke Rayuwa Yanzu Ba Za Su Taɓa Mutuwa Ba.) Majami’ar ta cika maƙil sa’ad da ya soma jawabin kuma mutane ɗari uku sun nemi ƙarin bayani.

Fostar da ke tallar jawabi da aka yi a majami’ar Royal Albert a Landan

A makonni na gaba, wasu ’yan’uwa sun ziyarci birnin Athens da Alƙahira da kuma Urushalima. Don a sake ziyartar waɗanda suke son saƙonmu a waɗannan wuraren, Ɗan’uwa Rutherford ya buɗe sabon reshen ofishi a garin Ramallah, kusa da Urushalima. Sai ya koma Turai kuma ya sa aka kafa ofishi a wurin kuma ya shirya a riƙa buga littattafanmu.

FALLASA RASHIN ADALCI

A watan Satumba 1920, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun fito da mujallar The Golden Age na 27 da ta fallasa yadda aka tsananta musu a shekara ta 1918. ’Yan’uwa sun yi aiki dare da rana da injin buga littattafai da suka kira Battleship don su buga fiye da kofofi miliyan huɗu na mujallar.

Hoton Emma Martin da ’yan sanda suka ɗauka

Waɗanda suka karanta wannan mujallar sun ji labarin rashin adalci da aka yi wa ’Yar’uwa Emma Martin. ’Yar’uwar majagaba ce a birnin San Bernardino a jihar Kalifoniya. A ranar 17 ga Maris, 1918, ita da ’yan’uwa uku, wato E. Hamm da E. J. Sonnenburg da kuma E. A. Stevens sun halarci taron da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka yi.

Akwai wani mutum da ya halarci taron, amma ba don yana so ya koya game da Jehobah ba. Daga baya, ya faɗi a kotu cewa: “Wani lauya ne ya ce . . . in je taron. Na je ne don in samu shaida.” Ya samu abin da yake nema, wato littafin nan The Finished Mystery. Bayan ’yan kwanaki, sai aka kama ’Yar’uwar Martin da ’yan’uwa ukun. An tuhume su da laifin taka dokar da ta haramta rarraba littafin.

An sami ’yan’uwan da laifi kuma aka yanke musu hukuncin yin shekara uku a kurkuku. Sun ɗaukaka ƙara, amma damarsu ta ƙare a ranar 17 ga Mayu, 1920, sai aka tura su kurkuku. Amma ba da daɗewa ba, yanayinsu ya canja.

A ranar 20 ga Yuni, 1920, Ɗan’uwa Rutherford ya ba da labarinsu a taron yanki da aka yi a birnin San Francisco. Masu sauraro sun yi fushi don rashin adalci da aka yi ma waɗannan ’yan’uwa. Saboda haka, suka tura wa shugaban ƙasar Amirka wasiƙa. Sun ce: “Muna ganin cewa . . . tuhumar Malama Martin, rashin adalci ne . . . abin da hukumomi suka yi bai dace ba . . . Sun yi amfani da ikonsu don . . . su sa ta faɗa cikin tarko . . . Kuma suka yi amfani da wannan zarafin don su sa Malama Martin cikin kurkuku. A ganinmu abin da suka yi . . . rashin adalci ne.”

Washegari, shugaban ƙasar, Woodrow Wilson ya canja hukuncin da aka yanke wa ’Yar’uwa Martin da ’Yan’uwa Hamm da Sonnenburg da kuma Stevens kuma ya ce a sake su daga kurkuku.

A ƙarshen shekara ta 1920, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun fuskanci abubuwa da yawa da suka sa su farin ciki. Sun ci gaba da faɗaɗa aikin da suke yi a hedkwatarmu, kuma sun ci gaba da sanar cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai cire matsalolin ’yan Adam. (Mat. 24:14) Za su ma fi yin wa’azi da ƙwazo a shekara ta 1921.

^ sakin layi na 18 Littafin nan The Finished Mystery ne littafi na bakwai na kundin nan Studies in the Scriptures. Littafin nan The Finished Mystery da ke da laƙabin nan “ZG” ne Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Maris, 1918. Harufan nan “Z” tana nufin mujallar Zion’s Watch Tower, “G” kuma tana nufin bakwai, wato littafi na bakwai.