Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 41

Yadda Za Ka Taimaki Dalibi Ya Yi Baftisma​—Sashe na Daya

Yadda Za Ka Taimaki Dalibi Ya Yi Baftisma​—Sashe na Daya

“Kun nuna cewa ku wasiƙa ce ta Almasihu wadda take sakamakon hidimarmu.”​—2 KOR. 3:3.

WAƘA TA 78 “Mu Riƙa Koya wa Mutane Maganar Allah”

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

Dukan ’yan’uwa a ikilisiya suna farin ciki sosai sa’ad da suka ga wata ɗalibarsu tana yin baftisma. (Ka duba sakin layi na 1)

1. Ta yaya littafin 2 Korintiyawa 3:​1-3 ya taimaka mana mu riƙa godiya don damar da muke da shi na nazari da ɗalibai har su yi baftisma? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

YAYA kake ji sa’ad da ka ga wani ɗalibi a ikilisiyarku ya yi baftisma? Babu shakka, hakan na sa ka farin ciki sosai. (Mat. 28:19) Kuma idan kai ne ka yi nazari da ɗalibin, za ka yi matuƙar farin ciki a ranar da ya yi baftisma! (1 Tas. 2:​19, 20) Ɗalibai da ba su daɗe da baftisma ba “wasiƙun shaida ne” ga waɗanda suka yi nazari da su da kuma dukan ʼyan’uwa a ikilisiya.​—Karanta 2 Korintiyawa 3:​1-3.

2. (a) Wace tambaya mai muhimmanci ce muke bukatar mu tattauna, kuma me ya sa? (b) Mene ne yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutum yake nufi? (Ka duba ƙarin bayani.)

2 Muna farin ciki ganin cewa cikin shekaru huɗu da suka shige, muna nazari * kowane wata da mutane wajen 10,000,000 a faɗin duniya. Kuma a waɗannan shekarun, mutane fiye da 280,000 suna yin baftisma kowace shekara. Ta yaya za mu taimaka wa waɗannan miliyoyin mutane da muke nazari da su su yi baftisma? Har ila, Jehobah yana ba mutane damar zama shaidunsa. Shi ya sa muke bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu taimaka musu su cancanci yin baftisma nan da nan domin lokaci yana ƙurewa!​—1 Kor. 7:29a; 1 Bit. 4:7.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin game da yin nazari?

3 Domin yana da muhimmanci mu taimaka wa mutane su yi baftisma yanzu, an gaya wa ofisoshinmu su yi binciken abin da za su iya yi don a taimaka wa ɗalibai su cancanci yin baftisma. A wannan talifin da kuma na gaba, za mu ga abin da za mu iya koya daga majagaba da masu wa’azi a ƙasar waje da masu kula da da’ira da suka ƙware a yin wa’azi. * (K. Mag. 11:14; 15:22) Sun bayyana abin da malamai da ɗalibai za su iya yi don su yi nasara. A wannan talifin, za mu tattauna abubuwa biyar da kowane ɗalibi zai yi don ya cancanci yin baftisma.

KU RIƘA NAZARI KOWANE MAKO

Ka tambayi ɗalibin ko zai so ku zauna don ku tattauna Littafi Mai Tsarki (Ka duba sakin layi na 4-6)

4. Me muke bukatar mu sani game da tattaunawa kawai da mutane a bakin ƙofarsu?

4 ’Yan’uwanmu da yawa suna gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki yayin da suke tattaunawa da mutane a bakin ƙofarsu. Ko da yake yin hakan yana da kyau don sa mutane su so tattauna Littafi Mai Tsarki, a yawancin lokaci ba a tattaunawa sosai kuma ba a kowane mako ba ne ake yin hakan. Don a ci gaba da tattaunawa, wasu ’yan’uwa sukan tambayi mutumin ya ba su lambar wayarsa, kuma su riƙa kiransa ko tura masa saƙo game da wani batu a Littafi Mai Tsarki. Suna iya ci gaba da yin hakan na watanni ba tare da yin nazarin Littafi Mai Tsarki ba. Amma, ɗalibin * zai sami ci gaba kuma ya yi alkawarin bauta wa Jehobah da yin baftisma idan ba a yi nazarin Kalmar Allah da shi ba? A’a.

5. Mene ne Yesu ya ce a Luka 14:​27-33 da za mu yi amfani da shi don mu taimaka wa ɗalibanmu?

5 Akwai lokacin da Yesu ya bayyana abin da zama mabiyinsa ya ƙunsa. Ya ba da kwatancin mutumin da yake so ya yi gini da kuma sarkin da yake so ya je yaƙi. Yesu ya ce mutumin da yake so ya yi ginin “zai fara zauna, ya yi lissafin abin da ginin zai ci tukuna.” Kuma sarkin “zai zauna tukuna ya duba” ko sojojinsa za su iya cin nasara. (Karanta Luka 14:​27-33.) Hakazalika, Yesu ya san cewa wanda yake so ya zama mabiyinsa yana bukatar ya yi tunani sosai game da abin da hakan ya ƙunsa. Saboda haka, muna bukatar mu ƙarfafa ɗalibanmu don mu riƙa nazari kowane mako. Ta yaya za mu iya yin hakan?

6. Mene ne za mu yi don mu soma nazari da mutane da muke tattaunawa da su?

6 Ka ƙara tsawon lokacin da kake tattaunawa da mutumin a bakin ƙofarsa. Wataƙila kana iya tattauna wasu ƙarin ayoyin Littafi Mai Tsarki da mutumin a kowane lokaci da ka kai masa ziyara. Sa’ad da mutumin ya saba tattaunawa da kai na dogon lokaci, ka tambaye shi ko kuna iya zama a wani wuri don ku ci gaba da tattaunawa. Amsar mutumin zai nuna ko nazarin Littafi Mai Tsarki yana da muhimmanci a gare shi. Daga baya, don ka taimaka wa mutumin ya samu ci gaba, kana iya tambayarsa ko zai so ku riƙa nazari sau biyu a mako. Amma yana bukatar yin wasu abubuwa, ba kawai yin nazari sau ɗaya ko biyu a mako ba.

KU YI SHIRI SOSAI KAFIN KOWANE NAZARI

Ka shirya sosai don yin nazari da ɗalibinka, kuma ka nuna masa yadda zai yi shiri (Ka duba sakin layi na 7-9)

7. Ta yaya malami zai yi shiri sosai kafin ya gudanar da kowane nazari?

7 A matsayinka na malami, kana bukatar ka yi shiri sosai kafin kowane nazari. Kana iya somawa ta wajen karanta abin da za ku yi nazarinsa da kuma nassosi. Ka fahimci muhimman darussan. Ka yi tunani a kan jigon da ƙaramin jigon da tambayoyin da nassosin da aka ce a karanta da hotunan da kuma bidiyoyi da za su bayyana batun. Sai ka yi tunanin ɗalibin da yadda za ka bayyana masa batun a hanya mai sauƙi don ya fahimce shi kuma ya yi amfani da shi a rayuwarsa.​—Neh. 8:8; K. Mag. 15:28a.

8. Mene ne furucin manzo Bulus da ke Kolosiyawa 1:​9, 10 ya koya mana game da yin addu’a a madadin ɗalibanmu?

8 Sa’ad da kake shirin, ka yi addu’a ga Jehobah game da ɗalibin da bukatunsa. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka yi amfani da Littafi Mai Tsarki don ka ratsa zuciyar ɗalibin. (Karanta Kolosiyawa 1:​9, 10.) Ka tambayi kanka ko akwai abin da zai yi wa ɗalibin wuyar fahimta ko ya amince da shi. Ka riƙa tuna cewa maƙasudinka shi ne ka taimaka masa ya cancanci yin baftisma.

9. Ta yaya malami zai taimaka wa ɗalibi ya yi shiri don nazarinsa? Ka bayyana.

9 Muna fatan cewa yin nazari a kai a kai da ɗalibin zai taimaka masa ya nuna godiya don abin da Jehobah da Yesu suka yi kuma ya so ƙara koya game da su. (Mat. 5:​3, 6) Don ɗalibin ya amfana sosai daga nazarin yana bukatar ya mai da hankali ga abubuwan da yake koya. Saboda haka, ka bayyana masa muhimmancin yin shiri kafin kowane nazari ta wajen karanta jigon da kuma yin tunanin yadda zai yi amfani da abin da ya koya. Ta yaya malamin zai taimaka masa? Ku shirya wani nazari tare don ya koya yadda ake yin hakan. * Ka nuna masa yadda zai sami amsoshin tambayoyin da kuma yadda jan layi a kan kalmomi masu muhimmanci zai taimaka masa ya tuna amsar. Sai ka ce masa ya ba da amsar da nasa kalmomin. Hakan zai taimaka maka ka san ko ya fahimci batun sosai. Akwai wani abu kuma da za ka ƙarfafa ɗalibinka ya yi.

KA KOYA MASA YA RIƘA ADDU’A DA KARANTA KALMAR ALLAH KULLUM

Ka koya wa ɗalibinka yadda zai riƙa karanta Littafi Mai Tsarki da yin addu’a (Ka duba sakin layi na 10-11)

10. Me ya sa yake da muhimmanci a riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana, kuma me ɗalibin yake bukatar ya yi don ya amfana daga karatun?

10 Ban da nazari da malamin, ɗalibin zai amfana idan yana yin wasu abubuwa kowace rana da kansa. Yana bukatar ya riƙa tattaunawa da Jehobah. Ta yaya? Ta wajen saurarar Jehobah da kuma yi masa magana. Zai saurari Allah ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana. (Yosh. 1:8; Zab. 1:​1-3) Ka nuna masa yadda zai yi amfani da “Tsarin Karanta Littafi Mai Tsarki” da ke jw.org. * Ka taimaka masa ya amfana daga abin da yake karantawa. Ka ƙarfafa shi ya yi bimbini a kan abin da Littafi Mai Tsarki yake koya masa game da Jehobah da kuma yadda zai yi amfani da abin da yake koya a rayuwarsa.​—A. M. 17:11; Yaƙ. 1:25.

11. Ta yaya ɗalibi zai koya yin addu’a da kyau, kuma me ya sa yake da muhimmanci ya riƙa addu’a ga Jehobah a kai a kai?

11 Ka ƙarfafa ɗalibinka ya riƙa addu’a kowace rana. Ka riƙa addu’a da dukan zuciyarka kafin ku soma nazari da kuma bayan kun gama, ka riƙa ambata ɗalibinka sa’ad da kake addu’ar. Yayin da yake saurarar ka, zai koyi yadda zai riƙa addu’a da dukan zuciyarsa ga Jehobah kuma ya kammala cikin sunan Yesu. (Mat. 6:9; Yoh. 15:16) Babu shakka, karanta Littafi Mai Tsarki kullum (saurarar Jehobah) da yin addu’a, (yin magana da Jehobah) za su taimaka wa ɗalibinka ya kusaci Allah! (Yaƙ. 4:8) Yin waɗannan abubuwa za su taimaka wa ɗalibinka ya yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ya cancanci yin baftisma.

KA TAIMAKA MASA YA ƘULLA DANGANTAKA DA JEHOBAH

12. Ta yaya malami zai taimaka wa ɗalibi ya ƙulla dangantaka da Jehobah?

12 Ya kamata abin da ɗalibi yake koya ya ratsa zuciyarsa. Muna so ɗalibinmu ya koya game da Jehobah. Saboda haka, wajibi ne abin da yake koya ya ratsa zuciyarsa don ya so yin amfani da abin da yake koya. Yesu ya koya wa mutane abubuwa da yawa kuma suna so ya riƙa koyar da su. Duk da haka, mutane sun bi shi ne don ya ratsa zuciyarsu. (Luk. 24:​15, 27, 32) Ɗalibinka yana bukatar ya ga Jehobah a matsayin wanda zai iya ƙulla dangantaka da shi, kuma ya ɗauke shi a matsayin Ubansa da Allahnsa da kuma Abokinsa. (Zab. 25:​4, 5) A lokacin da kuke nazari, ka sa ɗalibin ya lura da halaye masu kyau na Allah. (Fit. 34:​5, 6; 1 Bit. 5:​6, 7) A kowane batu da kuke tattaunawa, ka taimaka wa ɗalibin ya san Jehobah sosai. Ka taimaka wa ɗalibin ya fahimci halayen Jehobah, kamar su ƙauna da alheri da kuma juyayi. Yesu ya ce “doka ta farko, kuma mafi girma” ita ce “ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka.” (Mat. 22:​37, 38) Ka taimaka wa ɗalibin ya ƙaunaci Jehobah.

13. Ka ba da misalin yadda za ka taimaka wa ɗalibi ya koya game da halayen Jehobah.

13 Sa’ad da kake tattaunawa da ɗalibinka, ka bayyana masa dalilin da ya sa kake ƙaunar Jehobah. Hakan zai taimaka masa ya san cewa yana bukatar ya ƙulla dangantaka da Allah kuma ya ƙaunace shi. (Zab. 73:28) Alal misali, akwai wani furuci a littafin da kuke nazari ko nassi da ya faɗi wani abu game da ƙaunar Jehobah da hikimarsa da adalcinsa ko ikonsa? Shin hakan ya ratsa zuciyarka? Ka gaya wa ɗalibinka cewa wannan yana cikin dalilan da suka sa kake ƙaunar Jehobah. Da akwai wani abu kuma da ɗalibinka yake bukatar ya yi don ya cancanci yin baftisma.

KA ƘARFAFA SHI YA RIƘA HALARTAN TARO

Ka ƙarfafa ɗalibinka ya soma halartan taro! (Ka duba sakin layi na 14-15)

14. Mene ne Ibraniyawa 10:​24, 25 suka gaya mana game da taron ikilisiya da zai taimaka wa ɗalibi ya samu ci gaba?

14 Dukanmu muna so ɗalibanmu su cancanci yin baftisma. Wata hanya mai muhimmanci da za mu taimaka musu ita ce mu ƙarfafa su su riƙa halartan taro. Malamai da suka ƙware sun faɗi cewa ɗalibai da suke halartan taro suna saurin samun ci gaba. (Zab. 111:1) Wasu malamai suna bayyana wa ɗalibansu cewa da akwai abubuwa da yawa da za su koya a taro da ba za su koya ba daga nazarinsu. Ka karanta Ibraniyawa 10:​24, 25 da ɗalibinka, kuma ka bayyana masa amfanin halartan taro. Ka nuna masa bidiyon nan Me Ake Yi a Majami’ar Mulki? * Ka taimaka wa ɗalibinka ya ƙuduri niyyar halartan taro kowane mako.

15. Mene ne za mu iya yi don mu ƙarfafa ɗalibinmu ya riƙa halartan taro a kai a kai?

15 Mene ne za ka iya yi idan ɗalibinka bai taɓa halarta taro ba ko ba ya halarta a kai a kai? Ka gaya masa abin da ka koya daga taron da ka halarci kwanan nan. Zai so ya halarci taron idan ya ga yadda ka ji daɗin taron. Ka ba shi Hasumiyar Tsaro ko kuma Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu da ake nazarin sa. Ka nuna masa abin da za a tattauna a taro na gaba, kuma ka tambaye shi sashen da ya fi so. Abin da ɗalibinka zai gani a taro na farko da ya halarta a Majami’ar Mulki zai fi na kowane addini da ya taɓa halarta. (1 Kor. 14:​24, 25) Zai haɗu da wasu da zai iya yin koyi da su kuma su taimaka masa ya cancanci yin baftisma.

16. Me muke bukatar mu yi don mu taimaka wa ɗalibi ya cancanci yin baftisma, kuma me za mu koya a talifi na gaba?

16 Ta yaya za mu gudanar da nazari har ɗalibin ya yi baftisma? Za mu iya taimaka wa kowane ɗalibi ya ga muhimmancin yin nazarin, ta wajen ƙarfafa shi ya riƙa nazari kowane mako kuma ya yi shiri da kyau kafin kowane nazari. Ya dace mu ƙarfafa shi ya riƙa karanta Littafi Mai Tsarki da yin addu’a kowace rana kuma ya ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah. Ya kamata mu ƙarfafa ɗalibin ya halarci taro. (Ka duba shafi na 12 a akwatin nan “ Abin da Ɗalibi Zai Yi Don Ya Cancanci Yin Baftisma.”) Amma, kamar yadda za a bayyana a talifi na gaba, akwai ƙarin abubuwa biyar da malamai za su iya yi don ɗalibansu su cancanci yin baftisma.

WAƘA TA 76 Yin Wa’azi Yana Sa Mu Murna

^ sakin layi na 5 Koyar da mutum yana nufin taimaka masa ya riƙa tunani da kuma yin abu a wata hanya. Jigonmu na shekara ta 2020 da aka ɗauko daga Matiyu 28:19 ya tuna mana muhimmancin yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. Ƙari ga haka, muna koya musu yadda za su zama almajiran Yesu. A wannan talifin da kuma na gaba, za mu koyi yadda za mu ƙware a wannan aiki mai muhimmanci sosai.

^ sakin layi na 2 MA’ANAR WASU KALMOMI: Idan kana da tsarin tattauna Littafi Mai Tsarki da wani a kai a kai, hakan yana nufin cewa kana gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki. Kana iya ba da rahoton wannan nazari idan ka nuna wa ɗalibin yadda za ku riƙa yin nazari, ka yi nazari da shi sau biyu kuma ka san cewa za ku ci gaba da nazarin.

^ sakin layi na 3 A waɗannan talifofin, da akwai wasu shawarwari game da gudanar da nazari da aka ɗauko daga jerin talifofi mai jigo “Conducting Progressive Bible Studies” da aka wallafa a Hidimarmu ta Mulki na watan Yuli 2004 zuwa Mayu 2005.

^ sakin layi na 4 Abin da ake tattaunawa a wannan talifin ya shafi ɗalibai maza da mata.

^ sakin layi na 9 Ka kalli bidiyon nan na minti huɗu mai jigo Koyar da Ɗalibanmu su Shirya Nazari. A jw.org, ka duba LABURARE > TARO DA HIDIMARMU > INGANTA YADDA MUKE KOYARWA DA KUMA WA’AZI.

^ sakin layi na 10 Ka duba KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > KAYAN NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI.

^ sakin layi na 14 A jw.org, ka duba LABURARE > BIDIYO > TARO DA HIDIMARMU > ABUBUWAN YIN WA’AZI.