Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 44

Za Su Bauta wa Jehobah Kuwa Sa’ad da Suka Yi Girma?

Za Su Bauta wa Jehobah Kuwa Sa’ad da Suka Yi Girma?

“Yesu ya yi ta ƙaruwa da hikima da tsayi, ya kuma sami farin jini a gaban Allah da kuma a gaban mutane.”​—LUK. 2:52.

WAƘA TA 134 Yara Amana Ne Daga Allah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Wane zaɓi mafi kyau ne za mu iya yi?

A YAWANCIN lokuta, zaɓin da iyaye suke yi yana shafan yaransu na dogon lokaci. Idan iyaye suka yi zaɓin da bai dace ba, hakan zai jawo wa yaransu matsaloli. Amma idan suka yi zaɓi mai kyau, za su taimaka wa yaransu su yi farin ciki a rayuwa. Wajibi ne yaran ma su yi zaɓi mai kyau. Zaɓi mafi kyau da za mu yi shi ne mu bauta wa Jehobah, Allahnmu mai ƙauna.​—Zab. 73:28.

2. Wane zaɓi mai kyau ne Yesu da iyayensa suka yi?

2 Yusufu da Maryamu sun duƙufa su taimaka wa yaransu su bauta wa Jehobah, kuma zaɓin da suka yi ya nuna cewa bauta wa Jehobah ne ya fi muhimmanci a gare su. (Luk. 2:​40, 41, 52) Yesu ma ya yi zaɓi mai kyau kuma hakan ya taimaka masa ya yi nufin Jehobah. (Mat. 4:​1-10) Sa’ad da Yesu ya yi girma, ya zama mai kirki da aminci da kuma ƙarfin zuciya. Babu shakka, dukan iyaye za su so yaransu su kasance da irin halayen nan.

3. Waɗanne tambayoyi ne za a amsa a wannan talifin?

3 Za mu tattauna waɗannan tambayoyin a wannan talifin: Wane zaɓi mai kyau ne Jehobah ya yi game da Yesu? Wane darasi ne iyaye za su iya koya daga zaɓin da Yusufu da Maryamu suka yi? Kuma wane darasi ne matasa za su iya koya daga zaɓin da Yesu ya yi?

KA KOYI DARASI DAGA JEHOBAH

4. Wane zaɓi mai kyau ne Jehobah ya yi game da Ɗansa?

4 Jehobah ya zaɓi iyaye mafi dacewa da za su haifi Yesu. (Mat. 1:​18-23; Luk. 1:​26-38) Furucin Maryamu a Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa tana ƙaunar Jehobah da kuma Kalmarsa. (Luk. 1:​46-55) Kuma yadda Yusufu ya bi ja-gorancin Jehobah ya nuna cewa yana tsoron Allah kuma yana so ya faranta masa rai.​—Mat. 1:24.

5-6. Mene ne Jehobah ya bari Ɗansa ya fuskanta?

5 Ka lura cewa Jehobah bai zaɓi iyaye masu arziki don su haifi Yesu ba. Hadayar da Yusufu da Maryamu suka miƙa bayan an haifi Yesu ya nuna cewa su talakawa ne. (Luk. 2:24) Wataƙila Yusufu yana da ƙaramin shago kusa da gidansa inda yake aikin kafinta. Da alama cewa ba su da kuɗi da kuma kayayyaki sosai, musamman da yake suna da aƙalla yara bakwai.​—Mat. 13:​55, 56.

6 Jehobah ya kāre Yesu daga wasu haɗarurruka, amma bai kāre shi daga dukan ƙalubale ba. (Mat. 2:​13-15) Alal misali, wasu cikin dangin Yesu ba su yarda da koyarwarsa ba. Ka yi la’akari da yadda Yesu ya ji sa’ad da wasu cikin danginsa ba su yarda cewa shi ne Almasihu ba. (Mar. 3:21; Yoh. 7:5) Kuma wataƙila Yusufu ya rasu sa’ad da Yesu yake matashi, kuma hakan ya sa shi baƙin ciki sosai. Da yake Yesu ne ɗan fari, wataƙila ya soma aikin da Yusufu yake yi. (Mar. 6:3) Yayin da yake girma, ya soma koyan yadda zai biya bukatun iyalin. Wataƙila yana aiki tuƙuru don ya biya bukatunsu. Saboda haka, ya san yadda mutum yake gajiya bayan ya dawo daga aiki.

Iyaye, ku shirya yaranku don matsalolin da za su fuskanta ta wajen koya musu bin shawarar da ke Kalmar Allah (Ka duba sakin layi na 7) *

7. (a) Waɗanne tambayoyi ne za su taimaka wa iyaye su reni yaransu? (b) Ta yaya Karin Magana 2:​1-6 za su taimaka wa ma’auratan su koyar da yaransu?

7 Idan ku ma’aurata ne da ke son ku haifi yara, ku tambayi kanku: ‘Mu mutane ne masu sauƙin kai da ke ƙaunar Jehobah da kuma Kalmarsa? Shin Jehobah zai zaɓe mu mu kula da jariri da ke da daraja kamar Yesu?’ (Zab. 127:​3, 4) Idan kun riga kun haifi yara, ku tambayi kanku: ‘Ina koya wa yaranmu amfanin yin aiki tuƙuru?’ (M. Wa. 3:​12, 13) ‘Ina yin iya ƙoƙarina don in kāre yarana daga mugayen abubuwan da za su fuskanta a wannan duniyar Shaiɗan?’ (K. Mag. 22:3) Gaskiya ne cewa ba za ku iya kāre yaranku daga dukan matsalolin da za su fuskanta ba. Amma za ku iya shirya su don matsalolin da za su fuskanta ta wajen koya musu yadda za su riƙa bin ƙa’idodin da ke Kalmar Allah. (Karanta Karin Magana 2:​1-6.) Alal misali, idan wani danginku ya daina bauta wa Jehobah, ku taimaka wa yaranku su san muhimmancin kasancewa da aminci ga Jehobah. (Zab. 31:23) Ko kuma idan wani naku ya rasu, ku nuna wa yaranku ayoyin Littafi Mai Tsarki da za su ta’azantar da su.​—2 Kor. 1:​3, 4; 2 Tim. 3:16.

KU KOYI DARASI DAGA YUSUFU DA MARYAMU

8. Kamar yadda Maimaitawar Shari’a 6:​6, 7 suka nuna, mene ne Yusufu da Maryamu suka yi?

8 Yusufu da Maryamu sun taimaka wa Yesu ya sami amincewar Allah domin sun bi ja-gorancin da Jehobah ya ba su. (Karanta Maimaitawar Shari’a 6:​6, 7.) Yusufu da Maryamu suna ƙaunar Jehobah sosai, kuma abin da ya fi muhimmanci a gare su shi ne su taimaka wa yaransu ma su ƙaunaci Jehobah.

9. Wane zaɓi mai kyau ne Yusufu da Maryamu suka yi?

9 Yusufu da Maryamu da kuma yaransu sun zaɓi su riƙa bauta wa Jehobah a kai a kai. Babu shakka, suna halartar taro kowane mako a majami’ar da ke Nazarat, da kuma Idin Ƙetarewa kowace shekara a Urushalima. (Luk. 2:41; 4:16) Wataƙila sun yi amfani da zarafin nan don su koya wa Yesu da kuma ƙannensa game da tarihin mutanen Jehobah. Mai yiwuwa, suna tsayawa su duba wuraren da aka ambata a Littafi Mai Tsarki. Sa’ad da suka sami yara da yawa, bai kasance musu da sauƙi su ci gaba da yin abubuwan nan ba. Amma sun sami albarka don ayyukansu! Da yake Yusufu da Maryamu sun saka ibadarsu farko, iyalinsu gabaki ɗaya sun kusaci Jehobah.

10. Waɗanne darussa ne iyaye Kiristoci za su iya koya daga Yusufu da Maryamu?

10 Mene ne iyaye masu tsoron Allah za su iya koya daga wajen Yusufu da Maryamu? Abu mafi muhimmanci shi ne ku riƙa koya wa yaranku cewa kuna ƙaunar Jehobah sosai ta furucinku da ayyukanku. Ku san cewa kyauta mafi kyau da za ku ba su ita ce taimaka musu su ƙaunaci Jehobah. Kuma abu mafi muhimmanci da za ku koya musu shi ne yadda za su riƙa nazari da addu’a da halartan taro da kuma wa’azi. (1 Tim. 6:6) Babu shakka, wajibi ne ku biya bukatun yaranku. (1 Tim. 5:8) Amma ku tuna cewa dangantaka mai kyau da Jehobah ne zai sa yaranku su tsira a yaƙin Armageddon kuma su shiga aljanna, ba wadatarsu ba. *​—Ezek. 7:19; 1 Tim. 4:8.

Abin farin ciki ne cewa iyaye da yawa suna yanke wa iyalinsu shawarwari masu kyau! (Ka duba sakin layi na 11) *

11. (a) Ta yaya shawarar da ke 1 Timoti 6:​17-19 za ta taimaka wa iyaye su yi zaɓi mai kyau sa’ad da suke renon yaransu? (b) Waɗanne maƙasudai ne za ku iya kafa wa kanku a matsayin iyali, kuma waɗanne albarku ne za ku samu? (Ka duba akwatin nan “Waɗanne Maƙasudai Ne Za Ka Kafa?”)

11 Abin farin ciki ne ganin cewa iyaye Kiristoci da yawa suna taimaka wa yaransu su kusaci Jehobah. Suna bauta wa Jehobah tare a kai a kai. Suna halartar taron ikilisiya da taron da’ira, kuma suna wa’azi. Wasu iyalai ma suna wa’azi a yankunan da ba a yawan wa’azi. Wasu kuma suna zuwa Bethel don yawon buɗe ido ko kuma su taimaka a aikin gine-gine da muke yi. Iyalan da suka yi waɗannan ayyukan za su kashe kuɗi kuma za su fuskanci wasu matsaloli. Amma Jehobah zai albarkace su sosai. (Karanta 1 Timoti 6:​17-19.) Yaran da irin iyayen nan suka rene su suna yawan ci gaba da ayyukan nan masu kyau kuma ba sa yin da-na-sani!​—K. Mag. 10:22.

KU KOYA DAGA YESU

12. Mene ne Yesu ya bukaci ya yi sa’ad da yake girma?

12 Jehobah yana yin zaɓi mai kyau a kowane lokaci, kuma iyayen Yesu a duniya ma sun tsai da shawarwari masu kyau. Amma sa’ad da Yesu ya yi girma, ya bukaci ya yanke wa kansa shawara. (Gal. 6:5) Yesu ma yana da ’yancin yin zaɓi kamar dukanmu. Da ya zaɓi ya yi abin da yake so ba nufin Allah ba. Maimakon haka, ya zaɓi ya kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. (Yoh. 8:29) Ta yaya misalinsa zai iya taimaka wa matasa a yau?

Matasa, kada ku yi banza da ja-gorancin iyayenku (Ka duba sakin layi na 13) *

13. Wane zaɓi mai kyau ne Yesu ya yi sa’ad da yake matashi?

13 Yesu ya yi wa iyayensa biyayya sa’ad da yake matashi. Bai taɓa rena iyayensa ba don yana ganin cewa ya fi su ilimi. Maimakon haka, “ya ɗinga biyayya” a gare su. (Luk. 2:51) Babu shakka cewa Yesu ya ɗauki hakkinsa a matsayin ɗa na fari da muhimmanci. Ya yi aiki tuƙuru don ya koyi aikin kafinta daga wurin Yusufu don ya sami kuɗin taimaka wa iyayensa.

14. Ta yaya muka san cewa Yesu ya san Kalmar Allah sosai?

14 Mai yiwuwa, iyayen Yesu sun gaya masa yadda aka haife shi a hanya ta mu’ujiza da kuma abin da mazannin Allah suka faɗa game da shi. (Luk. 2:​8-19, 25-38) Yesu bai gamsu kawai da abin da aka gaya masa ba, amma ya yi nazari don ya tabbata da hakan. Ta yaya muka san cewa Yesu ya yi nazarin Kalmar Allah sosai? Domin sa’ad da yake ƙarami, malamai a Urushalima suna “mamakin ganewarsa da yadda yake ba da amsoshi.” (Luk. 2:​46, 47) Kuma sa’ad da Yesu yake ɗan shekara 12, ya riga ya tabbatar wa kansa cewa Jehobah ne Ubansa.​—Luk. 2:​42, 43, 49.

15. Ta yaya Yesu ya nuna cewa ya zaɓi ya yi nufin Jehobah?

15 Sa’ad da Yesu ya san nufin Jehobah a gare shi, ya yanke shawarar yin hakan. (Yoh. 6:38) Ya san cewa mutane da yawa za su tsane shi, kuma babu shakka, hakan ya ɗan sa shi baƙin ciki. Duk da haka, ya zaɓi ya yi biyayya ga Jehobah. A lokacin da Yesu ya yi baftisma a shekara ta 29, ya mai da dukan hankalinsa ga yin nufin Jehobah. (Ibran. 10:​5-7) Yesu ya ci gaba da yin nufin Jehobah har a lokacin da yake a kan gungumen azaba.​—Yoh. 19:30.

16. Wane darasi ne yara za su iya koya daga wajen Yesu?

16 Ku yi biyayya ga iyayenku. Iyayenku ma suna kamar Yusufu da Maryamu domin su ajizai ne. Duk da haka, Jehobah ya zaɓe su su kāre ku, su koyar da ku kuma su yi muku ja-goranci. Idan kun bi shawararsu kuma kun yi musu biyayya, za ku “sami zaman lafiya.”​—Afis. 6:​1-4.

17. Kamar yadda Yoshuwa 24:15 ta nuna, wace shawara ce matasa suke bukatar su yanke wa kansu?

17 Ku zaɓi wanda za ku bauta wa. Kana bukatar ka san Jehobah da nufinsa da kuma yadda za ka yi shi. (Rom. 12:2) Hakan zai taimaka maka ka yanke shawara mafi muhimmanci a rayuwarka, wato bauta wa Jehobah. (Karanta Yoshuwa 24:15; M. Wa. 12:1) Idan kana karanta Littafi Mai Tsarki da kuma nazari a kai a kai, za ka ƙaunaci Jehobah sosai kuma bangaskiyarka za ta daɗa ƙarfi.

18. Wace shawara ce ya wajaba matasa su yanke, kuma wane sakamako ne za su samu?

18 Ka sa yin nufin Jehobah ya zama abu na farko. Mutane a duniyar Shaiɗan suna ganin cewa za mu yi farin ciki idan muka yi amfani da iyawarmu don mu amfani kanmu. Amma gaskiyar ita ce, mutanen da suka mai da hankali ga abin duniya suna “jawo wa kansu baƙin ciki iri-iri masu zafi.” (1 Tim. 6:​9, 10) Akasin haka, idan muka yi biyayya ga Jehobah kuma muka sa yin nufinsa a kan gaba, za mu yi farin ciki kuma za mu yi “nasara.”​—Yosh. 1:8.

WANE ZAƁI NE ZA KA YI?

19. Mene ne ya wajaba iyaye su sani?

19 Iyaye, ku ƙoƙarta ku taimaka wa yaranku su bauta wa Jehobah. Ku dogara da Jehobah kuma zai taimaka muku ku yanke shawarwari masu kyau. (K. Mag. 3:​5, 6) Ku san cewa ayyukanku ne za su fi rinjayar yaranku, ba furucinku ba. Saboda haka, ku yanke shawarwarin da za su taimaka musu su sami amincewar Jehobah.

20. Wace albarka ce yara za su samu idan suka bauta wa Jehobah?

20 Yara, iyayenku za su taimaka muku ku yanke shawarwari masu kyau. Amma ku ne za ku yanke shawarar faranta ran Allah. Saboda haka, ku yi koyi da Yesu kuma ku bauta wa Jehobah, Allah mai ƙauna. Idan kuka yi haka, za ku shagala da yin ayyuka masu kyau, za ku sami gamsuwa kuma za ku ji daɗin rayuwa yanzu. (1 Tim. 4:16) Kuma a nan gaba, za ku ji daɗin rayuwa yadda ba ku taɓa yi ba!

WAƘA TA 133 Mu Bauta wa Jehobah da Kuruciyarmu

^ sakin layi na 5 Iyaye suna so yaransu su riƙa farin ciki kuma su bauta wa Jehobah sa’ad da suka yi girma. Me iyaye za su iya yi don su taimaka wa yaransu su bauta wa Jehobah? Wane zaɓi ne matasa za su yi don su yi nasara? Za a amsa tambayoyin nan a wannan talifin.

^ sakin layi na 10 Ka duba littafin nan Pure Worship of Jehovah​—Restored At Last!, shafuffuka na 69-70, sakin layi na 17-18.

^ sakin layi na 65 BAYANI A KAN HOTUNA: Babu shakka, Maryamu ta taimaka wa Yesu ya ƙaunaci Jehobah. Iyaye ma a yau za su iya taimaka wa yaransu su ƙaunaci Jehobah.

^ sakin layi na 67 BAYANI A KAN HOTUNA: Yusufu yana son zuwa majami’a da iyalinsa. Zai dace magidanta su riƙa halartan taron ikilisiya da iyalinsu.

^ sakin layi na 69 BAYANI A KAN HOTUNA: Yesu ya koyi aiki daga wurin babansa Yusufu. Yara ma a yau za su iya koyan aiki daga wurin babansu.