1921—Shekaru Dari da Suka Shige
GA TAMBAYAR da Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Janairu, 1921 ta yi wa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki, ta ce: “Wane aiki ne musamman yake jiranmu a wannan shekarar?” Sai hasumiyar tsaron ta ba da amsa ta wajen yin ƙaulin Ishaya 61:1, 2, don ta tuna musu aikin da aka ba su na yin wa’azi. Nassin ya ce: “Ubangiji ya shafe ni da zan yi shelar bishara ga matalauta, . . . in yi shelar shekara ta alherin Ubangiji, da ranar sakaiya ta Allahnmu.”
MASU WA’AZI DA ƘARFIN ZUCIYA
Ƙarfin zuciya ne ya taimaka wa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki su yi wa’azi. Ƙari ga “shelar bishara,” sun bukaci su yi shelar “ranar sakaiya” ga mugaye.
Wani ɗan’uwa mai suna J. H. Hoskin wanda ya zauna a Kanada, ya yi wa’azi da ƙarfin zuciya duk da cewa an yi hamayya da shi. A farkon shekara ta 1921, ya haɗu da wani mai bishara na cocin Methodist. Ɗan’uwa Hoskin ya soma zancensa da cewa: “Bari mu tattauna Kalmar Allah ba tare da gardama ba. Kuma ko da ba mu amince da juna a kan wasu abubuwa ba, ba sai mun yi faɗa ba.” Amma hakan bai faru ba. Ɗan’uwa Hoskin ya faɗi abin da ya faru, ya ce: “Jim kaɗan bayan mun soma tattaunawa, sai ya bugi ƙofa da ƙarfi, har na ɗauka cewa gilashin ƙofar zai fashe.”
Sai mai bisharar ya yi ihu ya ce: “Me ya sa ba za ka je ka yi wa arna wa’azi ba?” Ɗan’uwa Hoskin bai tanka masa ba. Amma da ya kama hanya, sai ya gaya wa kansa cewa, ‘Ai na ɗauka da arne ne nake magana!’
Washegari da mai bisharar yake wa’azi a cocinsa, sai ya soma zagin Ɗan’uwa Hoskin. Ɗan’uwa Hoskin ya tuna da abin da ya faru, kuma ya ce: “Ya ce ni ɗan zamba ne kuma ya kamata a kashe ni.” Hakan bai sa ɗan’uwanmu ya daina yin wa’azi ba, amma ya yi wa’azi ga mutane da yawa. Ya ce: “Na ji daɗin yin wa’azi a wurin sosai. Har wasu mutane ma sukan ce mini, ‘Mun san kana aikin Allah ne,’ kuma sukan ce za su iya taimaka mini da abubuwan da nake bukata.”
YADDA AKA TAIMAKI MUTANE SU YI NAZARI DA IYALINSU KO KUMA SU KAƊAI
Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sukan wallafa tambayoyi game da Littafi Mai Tsarki da amsoshinsu a cikin mujallar da yanzu muke kiransa Awake!, don su taimaka wa mutane su daɗa fahimtar Littafi Mai Tsarki. An tsara wasu tambayoyi game da Littafi Mai Tsarki don iyaye su tattauna su da yaransu. Iyaye za su yi wa yaransu tambayoyin, sa’an nan su taimaka musu su bincika amsoshin daga Littafi Mai Tsarki. Wasu tambayoyi kamar “Littattafai nawa ne a cikin Littafi Mai Tsarki?,” sun koyar da wasu abubuwa game da tsarin Littafi Mai Tsarki. Wasu tambayoyi kuma kamar “Ya kamata kowane Kirista ya sa rai cewa za a tsananta masa?,” sun taimaka wa matasa su riƙa yin wa’azi da ƙarfin zuciya.
Akwai kuma tambayoyi game da Littafi Mai Tsarki da amsoshin da aka shirya don waɗanda suka fahimci Littafi Mai Tsarki sosai. An saka amsoshin a cikin kundi na farko na littafin nan Studies in the Scriptures. Mutane da yawa sun amfana daga tambayoyin. Amma daga baya, an yi sanarwa cewa za a daina wallafa tambayoyin. Me ya sa aka daina wallafa tambayoyin?
WANI SABON LITTAFI!
’Yan’uwa da suke ja-goranci sun gano cewa mutane za su fi amfana idan aka koya musu batutuwa ɗaya bayan ɗaya. Don haka, an wallafa littafin nan The Harp of God a watan Nuwamba, 1921. An ba waɗanda suka karɓi littafin damar bin tsarin nazari da za su iya yi da kansu. Wannan tsarin bincike ya taimaka wa mutane su koyi game da alkawarin da Allah ya yi na ba wa ’yan Adam rai na har abada. Yaya ake yin nazari da littafin?
Idan mutum ya karɓi littafin, za a haɗa masa da wani ƙaramin kati da zai nuna masa inda zai karanta a cikin littafin. Bayan mako ɗaya, sai a aika masa wani kati kuma da ke ɗauke da tambayoyi a kan abin da ya karanta. A ƙarshen katin, zai ga wurin da zai karanta a mako na gaba.
Kowane mako har tsawon makonni 12, ikilisiyar da ke kusa da ɗalibin za ta riƙa tura masa kati. A yawancin lokuta, tsofaffi da waɗanda ba za su iya zuwa wa’azi gida-gida ba ne suke rarraba katin. Alal misali, wata ’yar’uwa mai suna Anna K. Gardner daga garin Millvale, a Pennsylvania na ƙasar Amirka, ta ce: “Sa’ad da aka fitar da littafin nan The Harp of God, ’yar’uwata mai suna Thayle wadda gurguwa ce, ta sami damar aika wa mutane katunan da ke ɗauke da tambayoyi kowane mako.” Idan mutum ya gama nazari da katin, sai wani daga ikilisiya da ke kusa da shi ya ziyarce shi don ya taimaka masa ya daɗa fahimtar Littafi Mai Tsarki.
AIKIN DA KE GABA
A ƙarshen shekarar, Ɗan’uwa J. F. Rutherford ya rubuta wasiƙa ga dukan ikilisiyoyi. A cikin wasiƙar, ya ce: “A wannan shekarar ne aka fi yin wa’azi, kuma wa’azin ya taimaka wa mutane sosai.” Sai ya daɗa da cewa: “Da sauran aiki sosai da ya kamata a yi. Ku ƙarfafa wasu su ma su saka hannu a wannan hidima mai albarka.” A bayyane yake cewa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun bi wannan shawarar, domin a 1922, sun yi wa’azin Mulkin Allah yadda ba a taɓa yi ba.