Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 40

Mene ne Tuban Gaske Yake Nufi?

Mene ne Tuban Gaske Yake Nufi?

Na “zo don in kira . . . masu zunubi su tuba.”​—LUK. 5:32.

WAƘA TA 36 Mu Riƙa Kāre Zuciyarmu

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Ta yaya wasu sarakuna guda biyu suka bambanta, kuma waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

BARI mu tattauna misalan sarakuna guda biyu da suka yi rayuwa a zamanin dā. Ɗaya ya yi sarauta a kan ƙabilu goma na Isra’ila, ɗayan kuma ya yi sarauta a kan ƙabilu biyu na Yahuda. Ko da yake sun yi rayuwa a zamani dabam-dabam, sun yi abubuwa da dama da suke da alaƙa da juna. Sarakuna biyun sun yi ma Jehobah tawaye, kuma sun sa mutanensa su yi masa rashin biyayya. Dukansu biyu masu kisa ne. Amma akwai bambanci tsakanin sarakuna biyun nan. Ɗaya ya ci gaba da aikata mugunta har ya mutu, ɗayan kuma ya tuba kuma Jehobah ya gafarta masa zunubansa. Waɗanne sarakuna ke nan?

2 Sarakunan su ne Sarki Ahab na Isra’ila da Sarki Manasse na Yahuda. Bambanci da ke tsakanin sarakuna biyun nan zai koya mana darasi mai kyau game da tuba. (A. M. 17:30; Rom. 3:23) Mene ne tuba, kuma ta yaya mutum zai yi hakan? Muna bukatar mu san amsar domin muna so Jehobah ya gafarta mana idan muka yi zunubi. Don mu sami amsar, za mu tattauna rayuwar sarakuna biyun nan kuma mu ga abin da za mu koya daga misalinsu. Za mu kuma bincika abin da Yesu ya koya mana game da tuba.

ABIN DA ZA MU IYA KOYA DAGA MISALIN SARKI AHAB

3. Wane irin sarki ne Ahab?

3 Ahab ne sarki na bakwai a masarautar ƙabilu goma na Isra’ila. Ya auri Jezebel ’yar sarkin Sidon, wato ƙasar da ke arewa da Isra’ila. Mai yiwuwa ƙasar Isra’ila ta sami arziki sosai saboda auren, amma auren ya sa mutanen Isra’ila sun daɗa yin zunubi ga Jehobah. Jezebel tana bauta ma Ba’al, kuma ta sa Sarki Ahab ya ɗaukaka wannan addini mai ƙazanta da ya ƙunshi karuwanci a haikali da kuma yin hadayu da yara. A lokacin da Jezebel ce sarauniya, ta sa rayuwar annabawan Jehobah cikin haɗari. Ta sa an kashe da yawa daga cikinsu. (1 Sar. 18:13) Ahab ma “ya aikata mugunta a idon Yahweh fiye da kowane mutumin da ya taɓa mulki kafin shi.” (1 Sar. 16:30) Jehobah ya ga muguntar da Ahab da Jezebel suke yi. Saboda jinƙansa, Jehobah ya aiki annabi Iliya ya gargaɗi mutanensa su daina muguntar da suke yi kafin lokaci ya ƙure. Amma Ahab da Jezebel sun ƙi saurara.

4. Wane hukunci ne Jehobah ya ce zai yi wa Ahab, kuma mene ne Ahab ya yi?

4 A ƙarshe, haƙurin Jehobah ya ƙure. Ya aiki Iliya ya gaya wa Ahab da Jezebel yadda zai hukunta su. Jehobah ya ce zai hallaka iyalinsu gabaki ɗaya. Kalmomin Iliya sun sa Ahab baƙin ciki! Abin mamaki, sai wannan sarki mai girman kai “ya ƙasƙantar da kansa.”​—1 Sar. 21:​19-29.

Sarki Ahab bai tuba da gaske ba, shi ya sa ya sa annabin Allah a kurkuku (Ka duba sakin layi na 5-6) *

5-6. Me ya nuna cewa Ahab bai tuba da gaske ba?

5 Ko da yake Ahab ya ƙasƙantar da kansa a wannan lokacin, abubuwan da ya yi daga baya sun nuna cewa bai tuba da gaske ba. Bai yi ƙoƙarin dakatar da bautar Ba’al a masarautarsa ba. Kuma bai ɗaukaka bauta ta gaskiya ba. Akwai ƙarin abubuwa da Ahab ya yi da suka nuna cewa bai tuba da gaske ba.

6 Bayan wani lokaci, sai Sarki Ahab ya gaya wa Sarki Jehoshaphat na Yahuda cewa ya zo su je su yaƙi Suriyawa. Jehoshaphat sarkin kirki ne, kuma ya dogara ga Jehobah. Sai ya gaya wa Ahab cewa su tambayi wani annabin Jehobah abin da za su yi kafin su je yaƙin. Da farko Ahab bai yarda ba, kuma ya ce: “Akwai wanin da za mu iya neman nufin Yahweh ta wurinsa, sunansa Mikaya ɗan Imala. Amma ba na sonsa, saboda ba ya annabci mai kyau a kaina, sai dai masifa.” A ƙarshe, sun tuntuɓi annabi Mikaya. Gaskiyar Ahab ne, domin annabin ya yi annabci marar kyau a kan Ahab! Maimakon ya roƙi Jehobah ya gafarta masa, Ahab ya saka annabin a kurkuku. (1 Sar. 22:​7-9, 23, 27) Ko da yake sarkin ya saka annabin a kurkuku, bai iya hana annabcin cika ba. A yaƙin da aka yi, sai aka kashe Ahab.​—1 Sar. 22:​34-38.

7. Bayan Ahab ya mutu, yaya Jehobah ya kwatanta shi?

7 Bayan Ahab ya mutu, Jehobah ya nuna yadda ya ɗauke shi. Da Sarki Jehoshaphat mai aminci ya koma gida, Jehobah ya aiki annabi Yehu ya tsawata masa domin ya haɗa kai da mugun Sarki Ahab. Annabin ya ce masa: ‘Daidai ne ka taimaki mugaye, ka kuma yi abokantaka da waɗanda suke ƙin Yahweh?’ (2 Tar. 19:​1, 2) Ka yi tunanin wannan: Da a ce Ahab ya yi tuban gaske, da annabin ba zai ce da shi mugun mutum wanda ya tsani Jehobah ba. Don haka, ko da yake Ahab ya yi da-na-sani don kurakuran da ya yi, bai tuba da gaske ba.

8. Mene ne za mu iya koya game da tuba daga misalin Ahab?

8 Me za mu iya koya daga misalin Ahab? A lokacin da Ahab ya ji masifar da za ta auko ma iyalinsa, sai ya ƙasƙantar da kansa. Hakan abu ne mai kyau. Amma abubuwan da ya yi daga baya sun nuna cewa bai tuba da gaske ba. Don haka, tuba ba ya nufin ba da haƙuri kawai don kurakuran da muka yi. Bari mu tattauna wani misali kuma da zai nuna mana abin da tuban gaske ya ƙunsa.

ABIN DA ZA MU IYA KOYA DAGA MISALIN SARKI MANASSE

9. Wane irin sarki ne Manasse?

9 Bayan wajen shekaru ɗari biyu, Manasse ya zama sarkin Yahuda. Mai yiwuwa ya fi Ahab mugunta! Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya aikata mugunta sosai a idon Yahweh, wanda ya sa Yahweh ya yi fushi sosai.” (2 Tar. 33:​1-9) Ya gina bagadai ga allolin ƙarya, ya ma saka gunki a haikalin Jehobah! Da alama gunkin yana wakiltar bauta da ake yi da lalata. Ya yi duba da dabo da kuma sihiri. Ƙari ga haka, Manasse “ya kakkashe marasa laifi da yawa.” Ya kakkashe mutane da yawa, har “ya miƙa ’ya’yansa maza hadaya ta ƙonawa” ga allolin ƙarya.​—2 Sar. 21:​6, 7, 10, 11, 16.

10. Wane horo ne Jehobah ya yi wa Manasse, kuma mene ne sarkin ya yi?

10 Kamar Ahab, Manasse ma ya ƙi gargaɗin da Jehobah ya yi masa ta wajen bayinsa. A ƙarshe, “Yahweh ya sa manyan sojojin Assuriya suka kama Manasse. Suka sa masa zobe a hanci, suka ɗaura shi da sarƙoƙin ƙarfe suka kai shi Babila.” Sa’ad da yake kurkuku, da alama Manasse ya yi tunani sosai a kan abubuwan da ya yi. ‘Ya ƙasƙantar da kansa sosai ya yi kuka ga Allah na kakanninsa.’ Ƙari ga haka, “ya nemi fuskar Yahweh,” wato ya roƙi Jehobah ya gafarta masa. Hakika, Manasse ya yi ta yin addu’a ga Jehobah. Wannan mugun mutumin ya soma canjawa. Sai ya soma ɗaukan Jehobah a matsayin Allahnsa, kuma ya yi addu’a a gare shi babu fasawa.​—2 Tar. 33:​10-13.

Da yake Sarki Manasse ya tuba da gaske, ya yi ƙoƙarin dakatar da bautar ƙarya (Ka duba sakin layi na 11) *

11. Bisa ga 2 Tarihi 33:​15, 16, ta yaya Manasse ya nuna cewa ya tuba da gaske?

11 A ƙarshe, Jehobah ya amsa addu’ar Manasse. Ya ga cewa Manasse ya tuba da gaske. Saboda abubuwan da Manasse ya faɗa a addu’arsa, Jehobah ya ji roƙonsa, kuma ya sake mayar da shi sarki. Manasse ya yi iya ƙoƙarinsa don ya nuna cewa ya tuba da gaske. Ya yi abin da Ahab bai yi ba. Ya canja halayensa, ya yi ƙoƙarin dakatar da bauta ta ƙarya kuma ya ɗaukaka bauta da gaskiya. (Karanta 2 Tarihi 33:​15, 16.) Manasse ya bukaci ƙarfin zuciya da bangaskiya kafin ya iya yin hakan, domin kafin ya tuba ya yi shekaru da yawa yana yin abubuwa marasa kyau. Kuma hakan ya shafi iyalinsa da fadawansa da kuma al’umman Isra’ila gabaki ɗaya. Amma yanzu da ya tsufa, Manasse ya yi ƙoƙarin gyara halayen mutane. Da alama, Manasse ne ya koya wa Yosiya, jikansa game da Jehobah, wanda daga baya ya zama sarkin kirki.

12. Mene ne za mu iya koya game da tuba daga misalin Manasse?

12 Wane darasi ne misalin Manasse ya koya mana? Ya ƙasƙantar da kansa, ya yi addu’a, kuma ya roƙi Jehobah ya nuna masa jinƙai. Ƙari ga haka, ya canja halayensa. Ya yi ƙoƙarin dakatar da bauta ta ƙarya, ya bauta ma Jehobah kuma ya taimaka ma wasu su yi hakan. Labarin Manasse zai iya taimaka ma waɗanda suka yi zunubi mai tsanani. Labarin ya tabbatar mana cewa Jehobah “mai alheri ne kuma mai yin gafara” ne. (Zab. 86:5) Jehobah zai gafarta ma waɗanda suka tuba da gaske.

13. Ka ba da kwatancin da ya koya mana abu mai muhimmanci game da tuba?

13 Manasse bai yi da-na-sani kawai saboda zunubinsa ba. Hakan ya nuna abin da ya kamata mu yi idan mun tuba da gaske. Ga wani misali: A ce ka je ka sayi kosai, amma a maimakon kosai, sai mai kosan ta ba ka wake. Shin za ka karɓa waken? Idan mai kosan ta gaya maka cewa abu mafi muhimmanci da aka yi kosan da shi shi ne wake fa? Hakika ba za ka karɓa ba! Haka ma, Jehobah yana bukatar masu zunubi su tuba da gaske. Idan mutum ya yi nadama don kuskuren da ya yi, hakan yana da kyau. Hakan yana ɗaya daga cikin abubuwa masu muhimmanci da Jehobah yake so mutumin ya yi. Amma ba shi ke nan ba. Me kuma Jehobah yake bukatar mutumin ya yi? Kwatancin da Yesu ya bayar ya ba da amsar.

YADDA ZA MU GANE TUBAN GASKE

Bayan da ɗa mubazzarin ya dawo cikin hankalinsa, ya yi tafiya mai nisa ya koma gida (Ka duba sakin layi na 14-15) *

14. A kwatancin Yesu, ta yaya mubazzarin ya fara ɗaukan matakan da suka nuna ya tuba?

14 A littafin Luka 15:​11-32, Yesu ya ba da wani kwatanci mai ban ƙarfafa game da wani ɗa mubazzari. Matashin ya yi wa babansa tawaye, ya bar gida kuma ya je wani “gari mai nisa.” A garin, ya yi rayuwar iskanci. Amma da ya shiga wahala, sai ya soma tunani a kan shawarar da ya yanke. Ya tuna yadda rayuwarsa take a lokacin da yake tare da babansa. Yesu ya ce: “Matashin ya dawo cikin hankalinsa.” Sai ya yanke shawarar komawa gida don ya nemi gafarar babansa. Ya yi kyau da matashin ya gane kuskurensa, amma iyakar abin da zai yi ke nan? A’a. Dole ne ya canja halayensa!

15. Ta yaya ɗa mubazzari na kwatancin Yesu ya nuna cewa ya tuba da gaske?

15 Mubazzarin ya yi tuban gaske daga kurakuransa. Ya dawo gida daga gari mai nisa da ya je. Da ya haɗu da babansa, sai ya ce: ‘Na yi wa Allah laifi na kuma yi maka laifi. Ban isa a ƙara kirana ɗanka ba.’ (Luk. 15:21) Tuban gaske da matashin ya yi, ya nuna cewa yana so ya yi sulhu da Jehobah. Ya kuma gane cewa abin da ya yi, ya sa mahaifinsa baƙin ciki. Yanzu yana so ya yi iya ƙoƙarinsa don ya sami amincewar babansa. Har ya ce a shirye yake babansa ya ɗauke shi a matsayin lebura! (Luk. 15:19) Wannan kwatancin ba tatsuniya ce mai daɗi kawai ba. Kwatancin zai taimaka ma dattawa idan suna so su gane ko wanda ya yi zunubi mai tsanani ya tuba da gaske.

16. Me ya sa zai iya yi ma dattawa wuya su gane ko mutum ya tuba da gaske?

16 Ba zai yi ma dattawa sauƙi su gane ko wanda ya yi zunubi ya tuba da gaske ba. Me ya sa? Domin dattawa ba sa ganin abin da ke zuciyar mutane. Saboda haka, sukan yi la’akari da ayyukan mutum don su gane ko ya tuba da gaske. A wasu lokuta, mutum zai iya yin zunubi mai tsanani sosai, kuma hakan zai sa ya yi ma dattawa wuya su gane ko ya tuba da gaske.

17. (a) Wane misali ne ya nuna cewa neman gafara kawai ba ya nufin cewa mutum ya tuba da gaske? (b) Kamar yadda 2 Korintiyawa 7:11 ta bayyana, mene ne mutumin da ya tuba da gaske zai yi?

17 Ka yi la’akari da wannan misalin. A ce wani ɗan’uwa ya yi shekaru da yawa yana yin zina. Maimakon ya faɗi laifinsa domin dattawa su taimaka masa, ya ɓoye laifin daga matarsa da abokansa da kuma dattawa. A ƙarshe, asirinsa ya tonu. Da aka gaya masa laifin da ya yi, sai ya amince da laifin, har ma ya nemi gafara. Shin hakan yana nufin cewa ya tuba da gaske ne? Dattawa da suke yin shari’ar za su bukaci ɗan’uwan ya yi abubuwa fiye da nuna baƙin ciki kawai domin zunubin da ya yi. Ba wai mutumin ya yi zunubi sau ɗaya saboda kuskure ba ne, amma ya yi shekaru da yawa yana yin hakan. Mutumin bai faɗi zunubin da kansa ba, sai da aka fallasa shi. Don haka, dole ne tunaninsa, da yadda yake ji, da kuma halayensa su tabbatar ma dattawa cewa ya tuba da gaske. (Karanta 2 Korintiyawa 7:11.) Zai iya ɗauki mutumin lokaci da yawa kafin ya yi canje-canje da za su nuna cewa ya tuba da gaske. A yawancin lokuta, akan yi wa mai zunubi kamar haka yankan zumunci.​—1 Kor. 5:​11-13; 6:​9, 10.

18. Ta yaya wanda aka yi wa yankan zumunci zai nuna cewa ya tuba da gaske, kuma wane sakamako ne hakan zai jawo?

18 Kafin wanda aka yi wa yankan zumunci ya nuna cewa ya tuba da gaske, wajibi ne ya riƙa zuwa taro a kai a kai. Ƙari ga haka, zai bi shawarar da dattawa suka ba shi na yin addu’a da nazari a kullum. Har ila, zai yi iya ƙoƙarinsa don kada ya sake shiga yanayin da zai sa shi yin zunubin. Idan ya yi iya ƙoƙarinsa don ya gyara dangantakarsa da Jehobah, Jehobah zai gafarta masa zunubansa, kuma dattawa za mayar da shi cikin ikilisiya. Sa’ad da dattawa suke ƙoƙarin sani ko mutum ya tuba da gaske, ya kamata su tuna cewa yanayin mai zunubin ya bambanta da na wani mai zunubi da suka taɓa taimaka wa.

19. Mene ne tuban gaske yake nufi? (Ezekiyel 33:​14-16)

19 Kamar yadda muka koya, wajibi ne wanda ya tuba da gaske ya canja tunaninsa da ra’ayinsa, kuma ya ɗauki matakan da za su nuna cewa ya tuba da gaske. Hakan yana nufin cewa zai daina munanan abubuwan da yake yi, kuma ya soma bin ƙa’idodin Jehobah. (Karanta Ezekiyel 33:​14-16.) Abin da ya fi muhimmanci mai zunubi ya yi shi ne ya gyara dangantakarsa da Jehobah.

KU TAIMAKA WA MASU ZUNUBI SU TUBA

20-21. Ta yaya za mu taimaka wa mutumin da ya yi zunubi mai tsanani?

20 Yesu ya bayyana wani abu mai muhimmanci game da hidimarsa sa’ad da yake duniya. Ya ce: Na “zo don in kira . . . masu zunubi su tuba.” (Luk. 5:32) Abin da ya kamata mu ma mu yi ke nan. A ce mun san cewa wani abokinmu ya yi zunubi mai tsanani. Me ya kamata mu yi?

21 Za mu sa abokinmu cikin haɗari idan ba mu gaya ma dattawa abin da ya yi ba. Balle ma ba za mu iya ɓoye zunubin ba domin Jehobah yana gani. (K. Mag. 5:​21, 22; 28:13) Za ka iya taimaka ma abokinka ta wajen tuna masa cewa dattawa za su taimaka masa. Idan abokinka ya ƙi ya gaya ma dattawa, ka gaya musu. Ta hakan za ka nuna cewa kana so ka taimaka masa, don dangantakarsa da Jehobah tana cikin haɗari!

22. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

22 Idan mutumin ya daɗe yana yin zunubi mai tsanani, kuma dattawa sun yanke shawarar yi masa yankan zumunci fa? Hakan yana nufin ba su yi masa jinƙai ba ne? A talifi na gaba, za mu tattauna yadda Jehobah yake nuna wa masu zunubi jinƙai yayin da yake yi musu horo, da kuma yadda za mu yi koyi da misalinsa.

WAƘA TA 103 Jehobah Ya Yi Tanadin Makiyaya

^ sakin layi na 5 Tuban gaske ya wuci mutum ya ba da haƙuri don laifin da ya yi. A wannan talifin, za a tattauna misalin Sarki Ahab da Sarki Manasse da ɗa mubazzari na kwatancin Yesu, don a taimaka mana mu fahimci abin da tuban gaske yake nufi. Za mu kuma ga abubuwan da dattawa za su yi la’akari da su don su san ko wanda ya yi zunubi ya tuba da gaske.

^ sakin layi na 60 BAYANI A KAN HOTO: Da fushi, Sarki Ahab ya umurci sojojinsa su saka Mikaya a kurkuku.

^ sakin layi na 62 BAYANI A KAN HOTO: Sarki Manasse ya umurci wasu ma’aikata su farfasa gumaka da ya saka a haikali.

^ sakin layi na 64 BAYANI A KAN HOTO: Ɗa mubazzarin a gajiye bayan ya yi tafiya mai nisa. Ya yi farin ciki sa’ad da ya ga gidansu daga nesa.