Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yadda Za Ka Gyara Dangantakarka da Jehobah

Yadda Za Ka Gyara Dangantakarka da Jehobah

A KOWACE shekara, ana dawo da ’yan’uwa da yawa da aka yi musu yankan zumunci. Ka yi tunanin yadda hakan yake sa a yi “murna sosai a sama.” (Luk. 15:​7, 10) Idan kana cikin waɗanda aka dawo da su ikilisiya, ka kasance da tabbaci cewa Yesu da mala’iku da kuma Jehobah suna farin ciki cewa ka sake zama memban ikilisiya. Amma yayin da kake ƙoƙarin gyara dangantakarka da Jehobah, za ka iya fuskantar wasu ƙalubale. Waɗanne ƙalubale ne za ka iya fuskanta, kuma mene ne zai taimaka maka?

WAƊANNE ƘALUBALE NE ZA KA IYA FUSKANTA?

’Yan’uwa da yawa sukan ci gaba da yin sanyin gwiwa bayan sun dawo cikin ikilisiya. Idan kana cikinsu, wataƙila za ka iya fahimtar yadda Sarki Dauda ya ji. Duk da cewa Jehobah ya gafarta masa zunubansa, ya ce: “Zunubaina sun sha ƙarfina.” (Zab. 40:12; 65:3) Bayan mutum ya komo ga Jehobah, zai iya yin shekaru da yawa yana jin kunya don abin da ya yi, ko kuma zuciyarsa za ta ci gaba da damunsa. Wata ’yar’uwa mai suna Isabelle da aka yi mata yankan zumunci na fiye da shekaru 20. * Ta ce: “Ya yi mini wuya in yarda cewa Jehobah ya gafarta mini.” Idan ka yi sanyin gwiwa, dangantakarka da Jehobah za ta iya sake yin sanyi. (K. Mag. 24:10) Ka yi ƙoƙari don kada hakan ya faru da kai.

Wasu suna damuwa domin suna ganin cewa ba za su iya yin abubuwan da ya kamata su yi, don su gyara dangantakarsu da Jehobah ba. Bayan an dawo da wani ɗan’uwa mai suna Antoine ikilisiya, ya ce: “Na ji kamar na manta abubuwa da yawa da na koya da kuma abubuwan da nake yi a matsayin Kirista kafin a yi mini yankan zumunci.” Irin wannan tunanin yana sa wasu ’yan’uwa su kasa yin ayyukan ibada da dukan zuciyarsu.

Alal misali, idan guguwa ta rusa gidan mutum, mutumin zai iya yin sanyin gwiwa idan ya yi tunanin lokaci da aikin da yake bukatar ya yi kafin ya sake gina gidan. Idan dangantakarka da Jehobah ta lalace domin wani zunubi mai tsanani da ka yi, za ka iya ji kamar aikin da kake bukatar ka yi don ka gyara dangantakar ya fi ƙarfinka. Amma Jehobah da ’yan’uwanka za su taimake ka.

Jehobah ya ce mana: “Ku zo mu shirya tsakaninmu.” (Isha. 1:18) Ka yi aiki tuƙuru don ka ‘shirya tsakaninka’ da Jehobah. Jehobah yana ƙaunar ka domin ka ɗauki wannan matakin. Ka yi tunanin wannan: Yadda ka komo ga Jehobah zai ba shi damar nuna cewa Iblis maƙaryaci ne!​—K. Mag. 27:11.

Komowa ga Jehobah ya sa ka kusace shi kuma ya yi alkawari cewa shi ma zai kusace ka. (Yak. 4:8) Yana da kyau mutane su ga cewa ka komo ikilisiya, amma akwai abubuwan da kake bukata ka yi fiye da hakan. Kana bukata ka ƙoƙarta ka daɗa ƙaunar Jehobah, Ubanka na sama da kuma amininka. Ta yaya za ka yi hakan?

KA KAFA MAƘASUDAN DA ZA KA IYA CIM MA

Ka yi ƙoƙari ka kafa maƙasudai da za ka iya cim ma. Mai yiwuwa ka tuna abubuwan da ka koya game da Jehobah da kuma alkawuransa game da nan gaba. Amma yanzu, kana bukatar ka soma fita wa’azi, da halartan taro a kai a kai da kuma yin cuɗanya da ’yan’uwa. Ga wasu maƙasudan da za ka iya kafawa.

Ka riƙa yin addu’a a kai a kai. Jehobah Ubanka na sama ya san cewa idan zuciyarka tana damunka a kai a kai, zai iya yi maka wuya ka yi addu’a. (Rom. 8:26) Duk da haka, ka “nace da addu’a” kuma ka gaya wa Jehobah yadda kake so ka sake zama abokinsa. (Rom. 12:​12, Littafi Mai Tsarki) Wani ɗan’uwa mai suna Andrej ya tuna abin da ya faru da shi kuma ya ce: “Zuciyata ta dame ni ba kaɗan ba, kuma na ji kunya sosai. Amma a duk lokacin da na yi addu’a, nakan sami sauƙi da kuma kwanciyar hankali.” Idan ba ka san abin da za ka yi addu’a a kai ba, ka yi nazarin addu’ar da Sarki Dauda ya yi a Zabura ta 51 da kuma 65 bayan da ya tuba.

Ka riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Yin hakan zai sa ka ƙarfafa bangaskiyarka kuma ka daɗa ƙaunar Jehobah. (Zab. 19:​7-11) Wani ɗan’uwa mai suna Felipe ya ce: “Tun da farko, abin da ya sa bangaskiyata ta yi sanyi kuma na yi zunubi, shi ne rashin yin nazari a kai a kai. Da yake ba na so in sake yin kuskuren da na yi, sai na soma yin nazari a kai a kai.” Kai ma za ka iya yin hakan. Idan kana neman batutuwa masu kyau da za ka iya yin nazari a kai, kana iya tambayar abokinka da ya manyanta ya taimaka maka.

Ka gyara dangantakarka da ’yan’uwa. Wasu da suka dawo ikilisiya za su iya ɗauka cewa ’yan’uwa suna fushi da su. Wata ’yar’uwa mai suna Larissa ta ce: “Na ji kunya sosai, na ji kamar na ci amanar kowa a ikilisiya. Na daɗe ina jin hakan.” Ka kasance da tabbaci cewa dattawa da ’yan’uwa da suka manyanta, suna marmarin taimaka maka ka sake gyara dangantakarka da Jehobah. (Ka duba akwatin nan “ Mene ne Dattawa Za Su Iya Yi?”) Suna murna ka komo ga Jehobah, kuma suna so kai ma ka yi murna!​—K. Mag. 17:17.

Me zai taimaka maka ka daɗa kusantar ’yan’uwa a ikilisiya? Ka riƙa halartan taro da kuma fita wa’azi tare da su. Ta yaya yin hakan zai taimaka maka? Wani ɗan’uwa mai suna Felix ya ce: “Tun kafin in dawo, kowa a ikilisiya yana jira na in dawo. Hakan ya nuna mini cewa suna ƙauna ta. Sun taimaka mini in gane cewa ina da amfani a cikin ikilisiya, cewa Jehobah ya gafarta mini kuma zan iya ci gaba da bauta masa.”​—Ka duba akwatin nan “ Abin da Za Ka Iya Yi.”

KADA KA FID DA RAI!

Shaiɗan zai ci gaba da ƙoƙarin jawo maka matsaloli yayin da kake ƙoƙarin sake gyara dangantakarka da Jehobah. (Luk. 4:13) Ka shirya masa, ta wajen ƙarfafa dangantakarka da Jehobah yanzu.

Ga abin da Jehobah ya faɗa game da tumakinsa, ya ce: “Zan nemo waɗanda suka ɓata, in komo da waɗanda suka kauce, in ɗaura waɗanda suka karya, in ƙarfafa marasa ƙarfi.” (Ezek. 34:16) Jehobah ya taimaka wa ’yan’uwa da yawa su sake gyara dangantakarsu da shi. Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah yana so ya taimaka maka ka daɗa kusantar shi.

^ sakin layi na 4 An canja wasu sunaye a wannan talifin.