HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Satumba 2017

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari na 23 ga Oktoba zuwa 26 ga Nuwamba, 2017.

Ka Rika Kame Kanka

Ta yaya misalan da ke Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu kasance da wannan halin kuma mu rika nuna shi? Me ya sa Kiristoci suke son kasancewa ka halin kame kai?

Ka Yi Koyi da Halin Jehobah na Nuna Tausayi

Akwai lokacin da Jehobah ya fada wa Musa sunansa da kuma halayensa don ya san shi sosai. Daya daga cikin halayen da Jehobah ya ambata shi ne tausayi. Wane irin hali ne, kuma me ya sa muke son mu kasance da irin wannan halin?

TARIHI

Na Sami Albarka a Yin Aiki da Mutanen da Suka Manyanta

Dan’uwa David Sinclair ya tuna yadda ya yi farin cikin don gatan yin aiki da ’yan’uwa masu aminci na shekara 61 a Bethel da ke Brooklyn.

“Maganar Ubangiji Za ta Tsaya Har Abada”

Har ila, Littafi Mai Tsarki ne aka fi sayarwa bayan da aka gama fassarawa duk da cewa an yi canje-canje a yaruka da siyasa kuma an tsananta ma wadanda suka fassara shi.

Kalmar Allah Tana da Iko

Mutane da yawa sun canja halinsu sa’ad da suka soma nazarin Kalmar Allah. Mene ne muke bukatar mu yi idan muna son mu amfana daga Kalmar Allah?

“Ka Yi Karfin Hali . . . Ka Kama Aikin”

Me ya sa muke bukatar mu kasance da karfin hali, kuma ta yaya za kasance da wannan hali?