Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“Ka Yi Karfin Hali . . . Ka Kama Aikin”

“Ka Yi Karfin Hali . . . Ka Kama Aikin”

“Ka yi ƙarfin hali, ka dage sosai, ka kama aikin, kada ka ji tsoro, kada kuwa ka karai, gama Ubangiji . . . yana tare da kai.”​—1 LABA. 28:20, Littafi Mai Tsarki.

WAƘOƘI: 60, 29

1, 2. (a) Wane aiki mai muhimmanci ne aka ba Sulemanu? (b) Me ya sa Dauda ya damu da Sulemanu?

AN BA Sulemanu hakkin kula da aikin gini mafi muhimmanci da ake yi a lokacin, wato haikalin da ke Urushalima. Ginin zai “zama mai-daraja ƙwarai da gaske, mashahuri maɗaukaki a cikin dukan duniya.” Abin da ya fi muhimmanci shi ne cewa haikalin zai zama “gidan Ubangiji Allah.” Kuma Jehobah ya ba da umurni cewa Sulemanu ne zai kula da aikin.​—1 Laba. 22:​1, 5, 9-11.

2 Sarki Dauda ya tabbata cewa Allah zai taimaka wa Sulemanu a wannan aikin, ga shi Sulemanu “ƙarami ne” kuma ba shi da wayo sosai. Shin zai kasance da ƙarfin zuciyar yin wannan aikin gina haikali? Da yake Sulemanu matashi ne kuma ba shi wayo sosai, hakan zai hana shi yin aikin ne? Don ya yi nasara, yana bukatar ya kasance da ƙarfin hali kuma ya kama aiki.

3. Ta yaya Sulemanu ya koya kasancewa da ƙarfin hali daga mahaifinsa?

3 Wataƙila Sulemanu ya ji labarin yadda mahaifinsa ya kasance da ƙarfin hali, don sa’ad da yake matashi, Dauda ya kashe dabbobi da suka ɗauke tumakin mahaifinsa. (1 Sam. 17:​34, 35) Ƙari ga haka, ya nuna ƙarfin hali sosai sa’ad da ya yi faɗa da wani gwarzon soja. Hakika, da taimakon Allah Dauda ya yi amfani da dutse don ya kashe Goliyat.​—1 Sam. 17:​45, 49, 50.

4. Me ya sa Sulemanu yake bukatar ya kasance da ƙarfin hali?

4 Saboda haka, Dauda ne ya dace ya ƙarfafa Sulemanu ya kasance da ƙarfin hali kuma ya gina haikalin! (Karanta 1 Labarbaru 28:20.) Idan Sulemanu bai kasance da ƙarfin hali ba, tsoro zai hana shi soma aikin. Kuma hakan zai yi muni sosai.

5. Me ya sa muke bukatar mu kasance da ƙarfin hali?

5 Kamar Sulemanu, muna bukatar taimako daga Jehobah don mu kasance da ƙarfin hali kuma mu cim ma aikin. Saboda haka, bari mu bincika misalan wasu da suka kasance da ƙarfin hali a dā. Hakan zai taimaka mana mu yi tunani a kan yadda za mu kasance da ƙarfin hali don mu cim ma aikinmu.

MISALAN MUTANE MASU ƘARFIN HALI

6. Mene ne ya burge ka game da ƙarfin hali da Yusufu ya nuna?

6 Yusufu ya kasance da ƙarfin hali sa’ad da matar Fotifar ta so ya yi lalata da ita. Ya san cewa zai shiga cikin masifa sosai idan ya ƙi. Duk da haka, maimakon ya faɗa cikin jarabar, ya nuna ƙarfin hali kuma ya ɗauki matakin ya dace.​—Far. 39:​10, 12.

7. Ka faɗa yadda Rahab ta nuna ƙarfin hali. (Ka duba hoton da ke shafi na 28.)

7 Rahab ma wata ce da ta nuna ƙarfin hali. Sa’ad da Isra’ilawa masu leƙen asiri suka je gidanta a Yariko, da ta ji tsoro kuma ta ƙi taimaka musu. Amma da yake ta dogara ga Jehobah, ta kasance da ƙarfin hali kuma ta ɓoye mutane biyun kuma ta taimaka musu su tsira. (Josh. 2:​4, 5, 9, 12-16) Rahab ta gaskata cewa Jehobah ne Allah na gaskiya, kuma ta kasance da tabbaci cewa zai sa Isra’ilawa su ci nasara. Ba ta ji tsoron mutane ba, har ma da sarkin Yariko da mutanensa. Maimakon haka, ta ɗauki matakin da ya sa aka cece ta da iyalinta.​—Josh. 6:​22, 23.

8. Ta yaya yadda Yesu ya kasance da ƙarfin hali ya taimaka wa manzannin?

8 Manzannin Yesu ma sun kafa misali mai kyau na kasancewa da ƙarfin hali. Don sun ga yadda Yesu ya nuna ƙarfin hali. (Mat. 8:​28-32; Yoh. 2:​13-17; 18:​3-5) Wannan misalin ya taimaka musu su kasance da ƙarfin hali. Saboda haka, sa’ad da Saddukiyawa suka hana su koyarwa game da Yesu, manzannin sun ƙi yin hakan.​—A. M. 5:​17, 18, 27-29.

9. Ta yaya 2 Timotawus 1:7 ta taimaka mana mu san inda ake bukatar a kasance da ƙarfin hali?

9 Yusufu da Rahab da Yesu da kuma manzannin sun ƙuduri aniya su yi abin da ya dace. Sun nuna ƙarfin hali ba don su nuna iya yi ba, amma don sun dogara ga Jehobah ne. A wasu lokuta da muke bukatar mu kasance da ƙarfin hali, wajibi ne mu ma mu dogara ga Jehobah ba kanmu ba. (Karanta 2 Timotawus 1:7.) Bari mu bincika wurare biyu da muke bukatar mu kasance da ƙarfin hali, a iyalinmu da kuma ikilisiya.

YANAYIN DA MUKE BUKATAR MU KASANCE DA ƘARFIN HALI

10. Me ya sa Kiristoci suke bukatar su kasance da ƙarfin hali?

10 Matasa suna fuskantar yanayi da yawa da ya kamata su nuna ƙarfin hali a bautarsu ga Jehobah. Ya kamata su bi misalin Sulemanu wanda ya kasance da ƙarfin hali sa’ad da ya tsai da shawarwari masu kyau don ya kammala gina haikalin. Ko da yake ya kamata iyaye su ja-goranci matasa, matasan ne ya kamata su tsai da shawarwari masu muhimmanci. (Mis. 27:11) Suna bukatar su kasance da ƙarfin hali don su tsai da shawarwari da suka dace game da abokan kirki da nishaɗi. Ƙari ga haka, suna bukatar ƙarfin hali don su zama da ɗabi’a mai kyau har da lokacin da suke so su yi baftisma. Kuma waɗannan shawarwarin da suka tsai da yana ɓata wa Shaiɗan rai da yake yana zargin Allah.

11, 12. (a) Ta yaya Musa ya kafa misali mai kyau na kasancewa da ƙarfin hali? (b) Ta yaya matasa za su yi koyi da Musa?

11 Wajibi ne matasa su tsai da shawara a kan abin da za su yi a rayuwarsu. A wasu ƙasashe, ana matsa wa matasa su je jami’a don su sami aikin da za a riƙa biyan su albashi mai tsoka. Idan ka samu kanka a irin wannan yanayin, ka tuna da misalin Musa. ’Yar Fir’auna ce ta yi renonsa, saboda haka yana da sauƙi ya kafa makasudin zama mai arziki ko wani mai suna. Ban da haka ma, ya fuskanci matsi sosai daga iyalinsa a Masar da malamansa da kuma wasu masu ba da shawara! Amma Musa ya kasance da ƙarfin zuciya kuma ya tsai da shawarar bauta wa Jehobah. Bayan da ya bar ƙasar Masar da dukiyarta, ya dogara ga Jehobah sosai. (Ibran. 11:​24-26) Jehobah ya albarkaci Musa sosai kuma zai daɗa masa albarka a nan gaba.

12 Hakazalika, Jehobah zai albarkaci matasa da suka kafa makasudai kuma suka saka batutuwan Mulkin Allah a kan gaba. Zai biya bukatun iyalansu. A ƙarni na farko, Timothawus ya mai da hankali ga bauta wa Allah, kai ma za ka iya yin hakan. *​—Karanta Filibiyawa 2:​19-22.

Shin ka ƙuduri aniya ka kasance da ƙarfin hali a dukan fannonin rayuwarka? (Ka duba sakin layi na 13-17)

13. Ta yaya kasancewa da ƙarfin hali ya taimaka ma wata matashiya ta cim ma makasudinta?

13 Wata ’yar’uwa da ke jihar Alabama a Amirka ta kasance da ƙarfin hali don ta kafa makasudai. Ta ce: “Sa’ad da nake girma, ni mai jin kunya ce sosai. Da kyar nake yi wa ’yan’uwa magana a Majami’ar Mulki, ballantana ma in ƙwanƙwasa ƙofar mutane da ban sani ba a wa’azi.” Amma da taimakon iyayenta da wasu a ikilisiya, wannan matashiyar ta cim ma makasudinta na zama majagaba na kullum. Ta ce: “Mutanen duniya suna matsa wa mutane su je jami’a, su yi suna, su zama masu kuɗi da kuma tara abin duniya. Sau da yawa, yawancin mutane ba sa cim ma waɗannan makasudan amma sukan jawo ma kansu baƙin ciki da wahala. Amma bauta wa Jehobah yana sa ni farin ciki da samun gamsuwa.”

14. A waɗanne yanayi ne iyaye suke bukatar su nuna ƙarfin hali?

14 Iyaye ma suna bukatar su kasance da ƙarfin hali. Alal misali, shugaban wurin aikinku zai iya gaya maka ka riƙa yin aiki bayan an tashi aiki da ranakun da ka keɓe don yin bauta ta iyali da fita wa’azi da kuma halartan taro. Kana bukatar ka kasance da ƙarfin hali don ka ƙi yin hakan kuma ka kafa wa yaranka misali mai kyau. Ko kuma wataƙila wasu iyaye a ikilisiyarku suna barin yaransu su yi abubuwan da ba ka son yaranka su riƙa yi. Iyayen suna iya tambayarka dalilin da ya sa yaranka ba sa yin waɗannan abubuwa. Shin za ka kasance da ƙarfin hali kuma ka bayyana musu cikin basira dalilin da ya sa ba ka son yaranka su yi hakan?

15. Ta yaya Zabura 37:25 da Ibraniyawa 13:5 za su taimaka wa iyaye?

15 Iyaye suna nuna ƙarfin hali sa’ad da suka taimaka wa yaransu su kafa makasudai kuma su cim ma hakan. Alal misali, wasu iyaye sukan yi jinkirin ƙarfafa yaransu su soma hidimar majagaba ko su tafi wurin da ake bukatar masu shela sosai ko su soma hidima a Bethel ko kuma su yi a aiki a inda ake gina Majami’un Mulki da na babban taro. Wataƙila suna tsoro cewa yaransu ba za su iya kula da su ko kuma su kula da kansu a nan gaba ba. Amma, iyaye masu hikima suna kasancewa da ƙarfin hali kuma su kasance da bangaskiya cewa Jehobah zai cika alkawuransa. (Karanta Zabura 37:25; Ibraniyawa 13:5.) Ƙari ga haka, iyaye da suke da ƙarfin hali kuma suka dogara ga Jehobah suna taimaka wa yaransu su yi hakan.​—1 Sam. 1:​27, 28; 2 Tim. 3:​14, 15.

16. Ta yaya wasu iyaye suka taimaka wa yaransu su kafa makasudai a bautar Jehobah, kuma ta yaya hakan ya kasance da amfani?

16 Wasu ma’aurata a Amirka sun taimaka wa yaransu su kafa makasudai. Maigidan ya ce: “Kafin yaranmu su soma tafiya da kuma magana, mukan gaya musu cewa mutum yana farin ciki sosai idan yana hidimar majagaba da kuma taimakawa a ikilisiya. Sun yi nasara domin yaran yanzu sun kafa makasudin yin hakan. Misalin da muka kafa musu ya taimaka musu su ƙi biɗe-biɗen kayan duniyar Shaiɗan kuma su mai da hankalinsu ga bauta wa Jehobah.” Wani ɗan’uwa mai yara biyu ya ce: “Iyaye da yawa suna ƙoƙari sosai kuma suna amfani da dukiyarsu don su taimaka wa yaransu su cim ma burinsu na zama ƙwararrun ’yan wasa da biɗan nishaɗi da kuma ilimi. Amma zai fi dacewa mu yi amfani da dukiyarmu don mu taimaka wa yaranmu su cim ma makasudin da zai taimaka musu su kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Muna farin ciki sosai yadda muke ganin yaranmu suna cim ma makasudinsu.” Babu shakka, Allah zai albarkaci iyaye da suka taimaka wa yaransu su kafa makasudai masu kyau a bautar Jehobah kuma su cim ma hakan.

KASANCEWA DA ƘARFIN HALI A IKILISIYA

17. Ka ba da misalan yadda wasu suka nuna ƙarfin hali a ikilisiya.

17 Muna bukatar mu nuna ƙarfin hali a ikilisiya. Alal misali, dattawa suna bukatar su kasance da ƙarfin hali sa’ad da suke shari’a ko kuma a lokacin da suke taimaka ma waɗanda suke da ciwon ajali. Wasu dattawa suna ziyarar fursunoni don su yi nazari da su ko kuma su gudanar da taro a wurin. ’Yan’uwa mata da ba su da aure kuma fa? Yanzu suna da zarafi da yawa na nuna ƙarfin hali kuma su bauta wa Jehobah. Suna iya yin hidimar majagaba ko su ƙaura zuwa inda ake bukatar masu shela sosai, ko su yi aiki da Sashen Gine-gine ko kuma su cika fam na zuwa Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki. Wasu ma sun halarci Makarantar Gilead.

18. Ta yaya ’yan’uwa mata da suka tsufa suke nuna ƙarfin hali?

18 Muna ƙaunar ’yan’uwa mata da suka tsufa, kuma muna farin ciki suna tare da mu a ikilisiya! Wasu ba sa iya yin abin da suke yi a dā a hidimarsu ga Allah, amma har ila suna iya nuna ƙarfin hali kuma sun kama aiki. (Karanta Titus 2:​3-5.) Alal misali, ’yar’uwa da ta tsufa tana bukatar ƙarfin hali don ta yi ma wata matashiya magana game da yin ado da saka tufafi da ya dace. Ba za ta tsauta wa matashiyar game da irin kayan da ta saka ba, amma za ta ƙarfafa ta ta yi tunani a kan yadda tufafinta zai shafi wasu. (1 Tim. 2:​9, 10) Idan suka nuna ƙaunarsu a waɗannan hanyoyi, suna ƙarfafa ikilisiya.

19. (a) Ta yaya ’yan’uwa maza za su zama masu ƙarfin hali? (b) Ta yaya Filibiyawa 2:13 da Ishaya 12:2 za su taimaka wa ’yan’uwa maza su kasance da ƙarfin hali?

19 ’Yan’uwa maza da suka yi baftisma ma suna bukatar su kasance da ƙarfin hali kuma su kama aiki. ’Yan’uwa a ikilisiya za su amfana idan suna shirye su yi hidimar bayi masu hidima da dattawa. (1 Tim. 3:1) Amma wasu suna jinkirin yin hakan. Wataƙila wani ɗan’uwa ya yi kuskure a dā, kuma yanzu yana ganin bai cancanci zama bawa mai hidima ba ko kuma dattijo ba. Wani ɗan’uwa yana iya ganin cewa bai ƙware a yin wata hidima ba. Idan kana jin hakan, Jehobah zai taimaka maka ka kasance da ƙarfin hali. (Karanta Filibiyawa 2:13; Ishaya 12:2.) Ka tuna cewa akwai wani lokaci da Musa ya ga cewa bai cancanci yin wata hidima ba. (Fit. 3:11) Duk da haka, Jehobah ya taimaka masa kuma da shigewar lokaci, Musa ya kasance da ƙarfin hali don ya cim ma aikin da aka ba shi. Ɗan’uwa da ya yi baftisma yana iya kasancewa da irin wannan ƙarfin hali ta wurin yin addu’a Allah ya taimaka masa kuma yana karanta Littafi Mai Tsarki kullum. Yin bimbini a kan irin waɗannan labaran zai taimaka masa. Ƙari ga haka, zai iya gaya wa dattawa su horar da shi kuma ya riƙa taimakawa a duk inda ake bukatar yin wasu ayyuka a ikilisiya. Muna ƙarfafa dukan ’yan’uwa maza da suka yi baftisma su kasance da ƙarfin hali kuma su yi aiki tuƙuru a cikin ikilisiya!

JEHOBAH YANA TARE DA KAI

20, 21. (a) Wane tabbaci ne Dauda ya ba Sulemanu? (b) Wane tabbaci ne muke da shi?

20 Sarki Dauda ya gaya wa Sulemanu cewa Jehobah zai kasance tare da shi har ya gama gina haikalin. (1 Laba. 28:20) Babu shakka cewa Sulemanu ya yi bimbini a kan waɗannan kalami, kuma ko da yake shi matashi ne ba shi da wayo sosai, bai bar hakan ya hana shi yin aikinsa ba. Ya kasance da ƙarfin hali sosai kuma ya kama aikinsa, da taimakon Jehobah ya gama babban aikin gina haikali cikin shekara bakwai da rabi.

21 Jehobah ya taimaki Sulemanu, kuma zai taimaka mana mu kasance da ƙarfin hali don mu cim ma aikinmu a iyali da kuma ikilisiya. (Isha. 41:​10, 13) Idan muka nuna ƙarfin hali a bautar Jehobah, za mu kasance da tabbaci cewa zai albarkace mu yanzu da kuma a nan gaba. Saboda haka, “ka yi ƙarfin hali . . . ka kama aiki.”

^ sakin layi na 12 Za ka samu matakai masu kyau na kafa makasudai a talifin nan “Use Spiritual Goals to Glorify Your Creator,” da ke cikin Hasumiyar Tsaro na 15 ga Yuli, 2004 a Turanci.