Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kalmar Allah Tana da Iko

Kalmar Allah Tana da Iko

“Maganar Allah rayayyiya ce, mai ƙarfin aiki.”​—IBRAN. 4:12, Littafi Mai Tsarki.

WAƘOƘI: 114, 113

1. Me ya sa muke da tabbaci cewa Kalmar Allah tana da iko? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

SHAIDUN JEHOBAH sun tabbata cewa Kalmar Allah, wato saƙon da ya ba mutane “rayayyiya ce, mai ƙarfin aiki” kuma. (Ibran. 4:​12, LMT) Mutane da yawa a cikinmu mun shaida cewa Littafi Mai Tsarki yana da ikon canja rayuwar mutane. Wasu cikinmu a dā ɓarayi ne da masu shan ƙwaya da kuma masu yin lalata. Wasu kuma sun yi suna ko kuɗi a wannan zamanin amma suka ga cewa akwai wani abu da suka rasa a rayuwarsu. (M. Wa. 2:​3-11) Kuma wasu a dā ba su da bege amma yanzu suna da shi domin Littafi Mai Tsarki ya gyara rayuwarsu. Wataƙila kana jin daɗin karanta labarai da yawa da suke fitowa a jerin talifofin Hasumiyar Tsaro mai jigo “Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane.” Kuma ka fahimta cewa ko da mutum ya zama Mashaidin Jehobah, yana bukatar ya ci gaba da ƙarfafa dangantakarsa da Jehobah ta wurin karanta Littafi Mai Tsarki.

2. Ta yaya Kalmar Allah ta kasance da iko a ƙarni na farko?

2 Ba abin mamaki ba ne cewa da yawa daga cikinmu sun gyara rayuwarsu sa’ad da suka yi nazarin Kalmar Allah. Waɗannan labaran sun tuna mana da ’yan’uwanmu shafaffu da suke da begen zuwa sama. (Karanta 1 Korintiyawa 6:​9-11.) Bayan da manzo Bulus ya lissafta mutanen da ba za su shiga Mulkin Allah ba, sai ya ce: ‘Waɗansu ma a cikinku dā haka kuke.’ Amma da taimakon Littafi Mai Tsarki da kuma ruhu mai tsarki, sun gyara rayuwarsu. Wasu ma bayan da suka zama Kiristoci ne suka yi ƙoƙari sosai don su daina wasu halaye. Littafi Mai Tsarki ya ba da labarin wani Kirista shafaffe da aka masa yankan zumunci, bayan haka aka dawo da shi. (1 Kor. 5:​1-5; 2 Kor. 2:​5-8) Muna farin ciki cewa ’yan’uwanmu sun iya gyara rayuwarsu da taimakon Littafi Mai Tsarki, ko ba haka ba?

3. Me za mu tattauna a wannan talifin?

3 Da yake Kalmar Allah tana da iko sosai, muna bukatar mu yi amfani da ita da kyau. (2 Tim. 2:15) A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu yi amfani da Kalmar Allah da kyau (1) a rayuwarmu, (2) sa’ad da muke wa’azi, da kuma (3) sa’ad da muke ba da jawabi. Abubuwan da za mu koya za su taimaka mana mu riƙa ƙauna da kuma godiya ga Jehobah wanda yake koyar da mu don mu amfana.​—Isha. 48:17.

A RAYUWARMU

4. (a) Me muke bukata mu yi idan muna son mu amfana daga Kalmar Allah? (b) Yaushe kake karatun Littafi Mai Tsarki?

4 Idan muna son mu amfana daga Kalmar Allah, ya kamata mu yi ƙoƙari mu riƙa karanta ta kowace rana. (Josh. 1:8) Ko da yake muna da ayyuka da yawa da muke yi, zai dace mu nemi lokaci mu riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana. (Karanta Afisawa 5:​15, 16.) Wasu sun nemi lokacin da ya dace da su don su riƙa karatun Littafi Mai Tsarki, wasu suna yinsa da safe wasu kuma da rana ko kuma yamma. Kuma suna da ra’ayin wani marubucin zabura wanda ya ce: “Ina ƙaunar shari’arka ba misali! Abin tunawa ne a gareni dukan yini.”​—Zab. 119:97.

5, 6. (a) Me ya sa yin bimbini yake da muhimmanci? (b) Ta yaya za mu yi bimbini da kyau? (c) Ta yaya za mu amfana sa’ad da muke karanta da kuma bimbini a kan Kalmar Allah?

5 Ban da karanta Littafi Mai Tsarki ma, ya kamata mu riƙa bimbini a kan abin da muke karantawa. (Zab. 1:​1-3) Sai mun yi hakan ne za mu iya samun hikimar Allah kuma mu yi amfani da ita. Ko da muna da Littafi Mai Tsarki ko kuma muna karanta wa ta waya, makasudinmu shi ne mu riƙa amfani da abin da muke karantawa.

6 Ta yaya za mu riƙa bimbini da kyau? Wasu suna ɗan dakatawa bayan sun karanta Littafi Mai Tsarki kuma su yi tambayoyi kamar su: ‘Me wannan nassin yake koya min game da Jehobah? Ta yaya nake amfani da wannan nassin a rayuwata yanzu? A waɗanne hanyoyi ne kuma zan yi amfani da wannan nassin a rayuwarta?’ Idan muka yi bimbini a kan Kalmar Allah, za mu sami ƙarfin yin amfani da shawarar a rayuwarmu. Babu shakka, yin hakan zai taimaka mana a rayuwarmu.​—2 Kor. 10:​4, 5.

SA’AD DA KAKE WA’AZI

7. Ta yaya za mu yi amfani da Kalmar Allah sa’ad da muke wa’azi?

7 Me zai taimaka mana mu yi amfani da Kalmar Allah da kyau sa’ad da muke wa’azi? Abu na farko da za mu yi shi ne mu riƙa karanta wa mutane sa’ad da muke wa’azi da kuma nazari. Wani ɗan’uwa ya ce, “A ce kana wa’azi tare da Jehobah, kai kaɗai ne za ka riƙa magana ko kuma za ka bar shi ya yi wa’azi?” Abin da ɗan’uwan yake nufi shi ne: Idan muka karanta wa mutane Littafi Mai Tsarki, muna barin Jehobah ya yi wa mutane wa’azi. Idan muka karanta nassin da ya dace, mutane za su amfana sosai fiye da abin da za mu gaya musu da baki. (1 Tas. 2:13) Don haka, zai dace ka tambayi kanka, ‘Ina neman zarafi don in riƙa karanta Littafi Mai Tsarki ga mutanen nake musu wa’azi?’

8. Me ya sa ba zai dace mu riƙa karanta nassosi kawai ba sa’ad da muke wa’azi?

8 Ba zai dace kawai mu riƙa karanta wa mutane Littafi Mai Tsarki ba. Me ya sa? Dalilin shi ne mutane da yawa ba sa fahimtar Littafi Mai Tsarki. Haka yake da wasu Kiristoci a ƙarni na farko da wasu ma a yau. (Rom. 10:2) Don haka, bai kamata mu ɗauka cewa mutanen da muke musu wa’azi suna fahimtar duk wani nassin da muka karanta musu ba. Muna bukatar mu maimaita kalmomi ko kuma furucin da muke so mu yi amfani da shi kuma mu taimaka musu su san ma’anarsu. Yin hakan zai taimaka wa mutane su san Kalmar Allah kuma abin da suka koya zai ratsa zukatansu.​—Karanta Luka 24:32.

9. Ta yaya abin da muke faɗa kafin mu karanta Littafi Mai Tsarki zai sa mutane su daraja Littafi Mai Tsarki? Ka ba da misali.

9 Abin da za mu faɗa kafin mu karanta Littafi Mai Tsarki zai sa mutane su riƙa daraja shi. Alal misali, za mu iya ce, “Bari mu ga abin da Mahaliccinmu ya faɗa game da wannan batun.” Idan muna ma wani da ba Kirista ba wa’azi, za mu iya ce, “Bari mu ga abin da Nassosi Masu Tsarki suka faɗa.” Ko kuma idan muna magana da wani da bai damu da addini ba, za mu iya tambayarsa, “Ka taɓa jin wannan karin maganar kuwa?” Idan muna la’akari cewa kowane mutum yana da ra’ayinsa da addininsa, hakan zai taimaka mana mu yi gabatarwar da za ta ratsa zuciyarsu.​—1 Kor. 9:​22, 23.

10. (a) Ka ba da labarin wani ɗan’uwa. (b) Wane labari kake da shi na yadda ka taɓa shaida ikon Kalmar Allah sa’ad da kake wa’azi?

10 Mutane da yawa sun gano cewa yin amfani da Kalmar Allah a wa’azi yana taimaka wa mutane sosai. Ka yi la’akari da wannan misalin. Wani ɗan’uwa ya koma don ya ziyarci wani da ya yi shekaru da yawa yana karanta mujallunmu. Amma maimakon ya ba shi mujallun kawai, sai ya karanta wani nassin da ke cikin Hasumiyar Tsaron da ya kawo masa. Ya karanta masa littafin 2 Korintiyawa 1:​3, 4, da ya ce: “Uban jiyejiyenƙai, Allah na dukan ta’aziyya; shi da ke yi mana ta’aziyya cikin dukan ƙuncinmu.” Mutumin ya ji daɗin nassin da aka karanta masa sai ya ce a sake karanta wurin. Bayan haka, sai ya ce shi da matarsa suna bukatar ta’aziyya, yanzu yana so ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki. Wannan labarin ya nuna cewa Kalmar Allah tana da iko sosai sa’ad da muke wa’azi, ko ba haka ba?​—A. M. 19:20.

SA’AD DA KAKE BA DA JAWABI

11. Wane hakki ne ’yan’uwa da suke ba da jawabi suke da shi?

11 Dukanmu muna jin daɗin halartan taron ikilisiya da manyan taro. Amma ainihin dalilin da ya sa muke zuwa taro shi ne don mu bauta ma Jehobah. Kuma muna samun ƙarfafa sosai daga abin da muke ji a taron. ’Yan’uwan da suke ba da jawabi a waɗannan taron suna ɗaukan yin hakan babban gata da kuma hakki mai muhimmanci. (Yaƙ. 3:1) Kuma suna mai da hankali su ga cewa duk abin suke faɗa daga Littafi Mai Tsarki ne. Idan aka ba ka jawabi, ta yaya za ka yi amfani da Kalmar Allah don ka ratsa zukatan mutane?

12. Ta yaya wanda yake ba da jawabi zai tabbata cewa tushen abin da yake koyarwa daga Littafi Mai Tsarki ne?

12 Ya kamata Littafi Mai Tsarki ya zama tushen koyarwarka sa’ad da kake ba da jawabi. (Yoh. 7:16) Mene ne yin hakan ya ƙunsa? Hakan yana nufin cewa za ka mai da hankali kada labari ko kwatanci ko kuma yadda kake ba da jawabin ya sa mutane su kāsa ganin cewa koyarwar Littafi Mai Tsarki ce ta fi muhimmanci. Ban da haka ma, zai dace ka san cewa karanta ayoyi da yawa ba ya nuna cewa mutum ya iya koyar da Littafi Mai Tsarki da kyau. A gaskiya, idan mutum ya yi amfani da ayoyi da yawa sa’ad da yake ba da jawabi, mutane ba za su iya tuna ko ɗaya daga cikinsu ba. Don haka, zai dace ka zaɓi ayoyi da za ka karanta da kyau kuma ka bayyana da kuma yi kwatancin da zai sa mutane su fahimci ainihin abin da wurin yake faɗa. (Neh. 8:8) Idan aka ba ka awutlayin jawabin, ka yi nazarin shi da kyau da kuma Nassosin da aka yi amfani da su. Ka yi ƙoƙari ka fahimci yadda Nassosin suka goyi bayan abin da aka faɗa a awutlayin. Bayan haka, sai ka zaɓi Nassosin da za ka yi amfani da su don ka koyar da darussan da ke cikin awutlayin. (Za ka sami ƙarin bayani game da hakan a shafuffuka na 21-23 na littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education.) Abu mafi muhimmanci shi ne ka yi addu’a don Jehobah ya taimaka maka ka bayyana Kalmarsa daidai.​—Karanta Ezra 7:10; Misalai 3:​13, 14.

13. (a) Ta yaya wata ’yar’uwa ta shaida yadda Kalmar Allah take da iko? (b) Ta yaya ka amfana sa’ad da ka halarci taro?

13 Wata ’yar’uwa a ƙasar Ostareliya ta shaida yadda Kalmar Allah take da iko sa’ad da ta halarci taro. A lokacin da take ƙarama, an yi lalata da ita, amma daga baya ta koyi Littafi Mai Tsarki kuma ta yi baftisma. Duk da haka, ta ga kamar Jehobah ba ya ƙaunarta ko kaɗan. Amma daga baya, sai ta fahimta cewa Allah yana ƙaunarta. Me ya taimaka mata ta fahimci hakan? Hakan ya faru ne bayan ta yi bimbini a kan wani nassin da aka karanta a taro kuma ta yi bincike da ya sa ta karanta wasu nassosi da suka yi magana a kan batun. * Kai kuma fa, akwai wasu nassosi da aka bayyana a taron ikilisiya ko manyan taro da ya taɓa ratsa zuciyarka?​—Neh. 8:12.

14. Ta yaya za mu nuna muna daraja da kuma ƙaunar Littafi Mai Tsarki da Jehobah ya ba mu?

14 Babu shakka, muna godiya da yadda Jehobah ya ba mu Kalmarsa, ko ba haka ba? Ba wai kawai ya ba ’yan Adam ba ne, amma ya yi alkawari cewa Kalmarsa za ta tabbata ko dawwama. (1 Bit. 1:​24, 25) Don haka, zai dace mu riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana, mu bi shawararta kuma mu taimaka ma wasu da shi. Idan muka yi hakan, muna nuna cewa muna ƙaunar Kalmar Allah da kuma daraja shi. Ban da hakan ma, abu mafi muhimmanci shi ne yin hakan zai nuna muna daraja Jehobah wanda ya wallafa ta.