Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Tsofaffi Jehobah Yana Daraja Ku Don Amincinku

Tsofaffi Jehobah Yana Daraja Ku Don Amincinku

A FAƊIN duniya, dattawa suna jin daɗin hidimar da suke yi a ƙungiyar Jehobah, kuma hakan albarka ce sosai a gare mu! Amma ba a jima ba da aka yi wasu canje-canje da suka shafi tsofaffi. An gaya wa dattawa tsofaffi su miƙa aikinsu ga dattawa matasa. Ta yaya?

Sabon canjin shi ne cewa masu kula da da’ira da masu koyarwa a makarantun ƙungiyar Jehobah za su daina hidimarsu sa’ad da suka kai shekara 70. Ƙari ga haka, dattawan da suka kai shekara 80, kuma su masu tsara ayyukan Kwamitin Ofishinmu ne ko kuma masu tsara ayyukan rukunin dattawa za su ba matasa ayyukansu. Ta yaya waɗannan dattawa suke ji game da wannan canjin? Sun kasance da aminci ga Jehobah da kuma ƙungiyarsa!

Ɗan’uwa Ken wanda ya tsara ayyukan Kwamitin Ofishinmu da ke ƙasarsu kusan shekara 49, ya ce: “Na amince da wannan canjin da dukan zuciyata. A ranar da na ji game da wannan shirin, na yi addu’a ga Jehobah da safen cewa muna bukatar ɗan’uwa matashin da zai yi wannan hidimar.”’Yan’uwa tsofaffi da yawa masu aminci a faɗin duniya sun kasance da ra’ayin Ɗan’uwa Ken. Hakika, da farko sun yi baƙin ciki da yake suna son yi wa ’yan’uwansu hidima.

Ɗan’uwa Esperandio mai tsara ayyukan rukunin dattawa a ikilisiyarsu ya ce: “Na ɗan yi baƙin ciki, amma ina bukatar ƙarin lokaci don in kula da kaina da yake na soma rashin lafiya sosai.” Ɗan’uwa Esperandio ya ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci kuma yana da amfani sosai a ikilisiyarsu.

Masu kula da da’ira da daɗewa da suka soma yin wata hidima kuma fa? Ɗan’uwa Allan da ya yi hidimar mai kula mai ziyara shekara 38, ya ce, “Na yi baƙin ciki sa’ad da na ji game da wannan canjin.” Duk da haka, ya fahimci cewa yana da muhimmanci a koyar da matasa, kuma ya ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci.

Ɗan’uwa Russell wanda ya yi hidima na shekara 40 a matsayin mai kula mai ziyara kuma ya koyar a makarantun ƙungiyar Jehobah, ya ce da farko shi da matarsa sun yi baƙin ciki da aka canja hidimarsu. Ya ƙara cewa: “Muna farin ciki sosai a hidimarmu kuma muna ganin cewa muna da ƙarfin ci gaba da hidimar.” Ɗan’uwa Russell da matarsa suna amfani da abubuwan da suka koya don su taimaka wa ’yan’uwa a ikilisiyarsu, kuma masu shela da suke tare da su suna farin ciki sosai.

Ko da ba ka taɓa samun kanka cikin yanayin da aka ambata ɗazu ba, wani labarin da ke littafin 2 Sama’ila zai taimaka maka ka fahimci yanayin da ’yan’uwan suke ciki.

MUTUM MAI TAWALI’U DA YA SAN KASAWARSA

Ka tuna da abin da ya faru sa’ad da Absalom ɗan Sarki Dawuda ya yi tawaye. Dawuda ya gudu daga Urushalima zuwa Mahanayim a gabashin Kogin Urdun. Sa’ad da Dawuda da mutanensa suke wajen, sun bukaci abin biyan bukata. Ka tuna abin da ya faru?

Maza uku a yankin sun ba su gado da kayan abinci dabam-dabam da kuma kayan dahuwa da kwanuka da cokula. Barzillai yana cikin waɗannan mazan da suka taimaka wa Dawuda. (2 Sam. 17:​27-29) Sa’ad da aka yi nasara a kan Absalom, Barzillai ya raka Dawuda har zuwa Urdun sa’ad da yake so ya koma Urushalima. Dawuda ya roƙi Barzillai ya bi shi zuwa Urushalima. Ko da yake Barzillai “mai arziki ne sosai” Dawuda ya ce zai riƙa ciyar da shi. (2 Sam. 19:​31-33) Amma Dawuda yana so Barzillai ya kasance tare da shi kuma ya amfana daga shawarwarin da zai ba shi. Babu shakka, Barzillai zai sami gatar zama a fāda kuma ya riƙa aiki a wurin!

Barzillai mai tawali’u ne shi ya sa ya ce shi ɗan shekara 80 ne. Ya daɗa cewa: “Ina iya bambanta abin da yake mai daɗi da marar daɗi ne?” Mene ne yake nufi? Barzillai ya koyi abubuwa da yawa a rayuwarsa, kuma zai iya ba da shawara mai kyau, kamar yadda “tsofaffin maza” suka ba Sarki Rehobowam. (1 Sar. 12:​6, 7; Zab. 92:​12-14; K. Mag. 16:31) Saboda haka, sa’ad da Barzillai ya ce ba zai iya bambanta abin da yake mai daɗi da marar daɗi ba, yana nufin cewa ba zai iya yin abubuwa yadda yake yi a dā ba don ya tsufa. Ya ce ba ya iya jin ɗanɗanon abinci kuma ba ya ji sosai don ya tsufa. (M. Wa. 12:​4, 5) Shi ya sa Barzillai ya gaya wa Dawuda ya tafi da Kimham, wanda wataƙila ɗan Barzillai ne zuwa Urushalima.​—2 Sam. 19:​35-40.

YIN SHIRI DON NAN GABA

Canje-canjen da suka shafi shekaru da aka ambata ɗazu sun yi daidai da irin halin da Barzillai ya nuna. Hakika a zamaninmu, ba yanayin mutum ɗaya da iyawarsa kawai aka yi la’akari da shi ba yadda aka yi da Barzillai. Amma an yi la’akari da abin da zai fi taimaka wa dattawa a faɗin duniya.

Waɗannan ’yan’uwa tsofaffi masu tawali’u sun san cewa za a ƙarfafa ƙungiyar Jehobah idan aka ɗanka wa matasa aikin da tsofaffin suka daɗe suna yi. A yawancin lokaci, tsofaffi ne ke koyar da matasa, kamar yadda Barzillai ya koyar da ɗansa kuma manzo Bulus ya koyar da Timoti. (1 Kor. 4:17; Filib. 2:​20-22) Waɗannan matasa suna nuna cewa su maza ne masu “baiwa iri-iri” kuma suna ƙarfafa ’yan’uwa a ƙungiyar Jehobah.​—Afis. 4:​8-12; gwada Littafin Ƙidaya 11:​16, 17, 29.

ZARAFIN YIN HIDIMA DABAM-DABAM

’Yan’uwa maza da yawa da ke ƙungiyar Jehobah a faɗin duniya da suka ba matasa aikinsu sun yi amfani da wannan zarafin don su faɗaɗa hidimarsu ga Jehobah.

Wani ɗan’uwa mai suna Marco da ya yi hidimar mai kula mai ziyara shekara 19 ya ce: “Wannan zarafin ya ba ni damar taimaka wa mazaje da ba sa bauta wa Jehobah amma matansu suna ikilisiyarmu.”

Geraldo wanda ya yi hidimar mai kula mai ziyara shekara 28 ya ce: “Sabon maƙasudinmu ya ƙunshi taimaka wa waɗanda suka daina wa’azi da zuwa taro, da kuma yin nazari da mutane.” Ya ce yanzu shi da matarsa suna nazari da mutane 15 kuma waɗanda suka daina halartan taro suna yin hakan yanzu.

Allan da aka ambata ɗazu ya ce: “Yanzu muna da zarafin yin wa’azi sosai. Muna jin daɗin yin wa’azi ga jama’a da kuma a wurin da ake kasuwanci da kuma yi wa maƙwabtanmu wa’azi, kuma biyu cikinsu sun halarci taro a Majami’ar Mulki.”

Idan kai dattijo ne da ya manyanta kuma ka sami sabon aiki a ƙungiyar Jehobah, da akwai wata hanya ta musamman da za ka taimaka. Za ka tallafa wa ƙungiyar Jehobah ta wurin koya wa matasan da ke ikilisiya abubuwan da ka koya. Russell da aka ambata ɗazu ya ce, “Jehobah yana koyar da matasa masu baiwa sosai kuma yana amfani da su. Ƙungiyar Jehobah tana amfana sosai daga koyarwa da ziyarar ƙarfafa da waɗannan matasa suke yi a ikilisiya!”​—Ka duba akwatin nan “ Ku Taimaka wa Matasa Su Ƙware Sosai.”

JEHOBAH YANA FARIN CIKI DON AMINCINKU

Idan kun soma wata hidima kwanan nan, ku kasance da ra’ayin da ya dace. Kun riga ku taimaka wa mutane da yawa da hidimar ku, kuma za ku iya ci gaba da yin hakan. Ana ƙaunar ku kuma za a ci gaba da yin hakan.

Abin da ya fi muhimmanci shi ne kun faranta wa Jehobah rai sosai. Kuma ba zai “manta da aikinku da ƙauna wadda kuka nuna ga sunansa, yayin da kuka hidimta ma tsarkaka” ba. (Ibran. 6:​10, Littafi Mai Tsarki Cikin Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Wannan ayar ta tabbatar mana da cewa Jehobah zai ci gaba da ƙaunar ku. Kuna da daraja a gare shi sosai kuma ba zai manta da ayyukanku na dā da waɗanda kuka ci gaba da yi don ku faranta ransa ba!

Idan ba ka cikin waɗanda aka canja musu hidima kamar yadda aka ambata ɗazu fa? Har ila wannan batun ya shafe ka. Ta yaya?

Idan kana abokantaka da wani ɗan’uwa tsoho da ya soma wata hidima, za ka amfana sosai daga abubuwan da ya koya. Ka nemi shawararsa kuma ka riƙa lura da yadda yake yin amfani da abin da ya koya a hidimarsa.

Ɗan’uwa tsoho da ya soma wata hidima ko kuma ɗan’uwa ko ’yar’uwa da suke amfana daga ayyukansa kuma fa? Ya kamata su riƙa tuna cewa Jehobah yana daraja amincin waɗanda suka daɗe suna bauta masa da waɗanda suka ci gaba da yin hakan.