Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 36

Armageddon Albishiri Ne!

Armageddon Albishiri Ne!

Sun “tattara su . . . a wurin da ake ce da shi Armageddon.”​—R. YAR. 16:16.

WAƘA TA 150 Mu Bi Allah Don Mu Sami Ceto

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. (a) Me ya sa Armageddon albishiri ne? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a talifin nan?

WASU mutane sun yi imani cewa za a yi amfani da makaman nukiliya ko kuma bala’o’i wajen hallaka duniya. Amma ba abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki ke nan ba. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa nan ba da daɗewa ba, za a yi wani yaƙi da zai kawo sakamako mai kyau ga ʼyan Adam. (R. Yar. 1:3) Ana kiran wannan yaƙin Armageddon, kuma abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da yaƙin albishiri ne.

2 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah zai yi amfani da yaƙin Armageddon wajen ceton mutane a hanyoyin nan: Na ɗaya, zai cire mulkin ʼyan Adam. Na biyu, zai ceci mutane ta wajen cire mugaye, ya kuma taimaka wa adalai. Na uku, zai hana mutane hallaka wannan doron ƙasa. (R. Yar. 11:18) Don mu fahimci wannan batu sosai, bari mu tattauna waɗannan tambayoyi huɗu: Mene ne Armageddon? Waɗanne abubuwa ne za su faru kafin Armageddon? Me za mu yi don mu sami ceto? Ta yaya za mu kasance da aminci yanzu da ƙarshe ya kusa?

MENE NE ARMAGEDDON?

3. (a) Mene ne Armageddon yake nufi? (b) Kamar yadda Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 16:​14, 16 suka nuna, me ya sa muka ce Armageddon ba wuri na zahiri ba ne?

3 Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 16:​14, 16. Sau ɗaya ne kawai aka ambata “Armageddon” a cikin Littafi Mai Tsarki kuma kalma ce ta Ibrananci da ke nufin “Dutsen Megiddo.” (R. Yar. 16:16) Megiddo birni ne a Isra’ila a zamanin dā. (Yosh. 17:11) Amma Armageddon ba ya nufin wuri na zahiri a duniya. Yana nufin sa’ad da “dukan sarakunan duniya” suka haɗa kai don su yi gāba da Jehobah. (R. Yar. 16:14) Amma a wannan talifin, za mu kuma yi amfani da Armageddon sa’ad da muke magana game da yaƙin da za a yi bayan sarakunan duniya sun tattaru. Ta yaya muka san cewa Armageddon ba wuri na zahiri ba ne? Na farko, babu wani dutse mai suna Megiddo. Na biyu, birnin Megiddo ba zai iya ɗaukan “dukan sarakunan duniya” da rundunarsu da kuma makamansu ba. Na uku, za a soma yaƙin Armageddon sa’ad da sarakunan duniya suka kai wa bayin Allah da suke duniya hari. Za mu tattauna wannan batun a wannan talifin.

4. Me ya sa Jehobah ya kira yaƙin ƙarshe da zai yi Armageddon?

4 Me ya sa Jehobah ya kamanta yaƙin ƙarshe da zai yi da Megiddo? A zamanin dā, an yi yaƙe-yaƙe sosai a Megiddo da kuma Kwarin Jezreel da ke kusa da shi. A wasu lokuta, Jehobah ya taimaka wa mutanensa a wannan yaƙe-yaƙen. Alal misali, Allah ya taimaki Alƙali Barak ya ci nasara a kan shugaban sojojin Kan’aniyawa mai suna Sisera a “wajen rafin Megiddo.” Barak da annabiya Deborah sun gode wa Jehobah don yadda ya taimaka musu. Sun rera waƙa, suna cewa: “Daga sama, taurari sun yi yaƙi . . . da Sisera. Ambaliyar ruwan Kishon ta kwashe su.”​—Alƙa. 5:​19-21.

5. A wace hanya ce yaƙin Armageddon ya bambanta da yaƙe-yaƙen da Barak ya yi?

5 Barak da Deborah sun kammala waƙarsu da kalmomin nan: “Ya Yahweh! Kamar Sisera, bari dukan masu gābanka su halaka! Amma bari masu ƙaunar ka su haskaka kamar fitowar rana!” (Alƙa. 5:31) Hakazalika, a lokacin yaƙin Armageddon, Allah zai hallaka maƙiyansa kuma zai ceci mutanen da suke ƙaunar sa. Amma akwai wani bambanci mai muhimmanci tsakanin yaƙin Armageddon da yaƙe-yaƙen Barak. Wane bambanci ke nan? Bayin Allah ba za su saka hannu a yaƙin Armageddon ba. Ba za ma su riƙe makamai ba! Dogara ga Jehobah da mala’ikunsa da kuma “natsuwa” zai taimaka musu.​—Isha. 30:15; R. Yar. 19:​11-15.

6. Mene ne Jehobah zai iya yin amfani da shi wajen hallaka maƙiyansa a Armageddon?

6 Ta yaya Jehobah zai ci nasara a kan maƙiyansa a Armageddon? Zai iya yin amfani da hanyoyi dabam-dabam. Alal misali, zai iya amfani da girgizar ƙasa ko duwatsun ƙanƙara ko kuma walƙiya. (Ayu. 38:​22, 23; Ezek. 38:​19-22) Zai iya sa maƙiyansa su yaƙi kansu. (2 Tar. 20:​17, 22, 23) Kuma zai iya yin amfani da mala’ikunsa wajen hallaka mugaye. (Isha. 37:36) Ko da wace hanya ce Jehobah ya yi amfani da ita, mun san cewa zai yi nasara. Zai hallaka dukan maƙiyansa kuma zai ceci dukan amintattu.​—K. Mag. 3:​25, 26.

WAƊANNE ABUBUWA NE ZA SU FARU KAFIN ARMAGEDDON?

7-8. (a) Kamar yadda 1 Tasalonikawa 5:​1-6 suka nuna, wane furuci ne za a yi? (b) Me ya sa wannan furucin zai ruɗar da mutane sosai?

7 Za a ce an sami “zaman lafiya da salama” kafin “Ranar” Jehobah. (Karanta 1 Tasalonikawa 5:​1-6.) Ranar Jehobah da aka ambata a 1 Tasalonikawa 5:​2, tana nufin ƙunci mai girma. (R. Yar. 7:14) Ta yaya za mu san lokacin da ƙuncin yake gab da farawa? Kalmar Allah ta ce za a yi wani furuci mai ban mamaki kuma zai nuna cewa an soma ƙunci mai girma.

8 Za su ce an sami “zaman lafiya da salama.” Me ya sa shugabannin duniya za su yi wannan furucin? Shin shugabannin addinai ma za su yi wannan furucin? Zai yiwu. Amma wannan furucin zai zama ɗaya cikin ƙarairayin aljannu. Furucin zai ruɗar da mutane sosai. Me ya sa? Domin zai sa su kwantar da hankulansu jim kaɗan kafin a soma ƙunci mafi girma. Amma farat ɗaya, “halaka za ta auko musu, kamar yadda zafin haifuwa yakan kama mace mai ciki.” Me zai faru da amintattun bayin Jehobah? Da yake ba su san daidai lokacin da za a soma ƙunci mai girma ba, za su iya yin mamaki, amma za su kasance a shirye.

9. A wace hanya ce Jehobah zai hallaka duniyar Shaiɗan?

9 Jehobah ba zai hallaka duniyar Shaiɗan gabaki ɗaya a lokaci guda ba yadda ya yi a zamanin Nuhu. A maimakon haka, zai fara hallaka sashe na farko, sannan ya hallaka sashe na biyu. Sashe na farko da zai hallaka shi ne Babila Babba, wato dukan addinan ƙarya. Sa’an nan zai yi amfani da yaƙin Armageddon wajen hallaka sauran sashe na duniyar Shaiɗan da ya rage, wato sashen siyasa da rundunar yaƙi da kuma kasuwanci. Yanzu, bari mu tattauna waɗannan sassa biyu.

10. Me ya sa Jehobah zai hallaka Babila Babba, kamar yadda Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 17:​1, 6 da 18:24 suka nuna?

10 “Za a hukunta wannan babbar karuwa.” (Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 17:​1, 6; 18:24.) Babila Babba ta ɓata sunan Allah sosai. Tana koyar da ƙarairayi game da Allah. Ita ƙaruwa ce domin tana cuɗanya da sarakunan duniya. Tana yin amfani da ikonta wajen cutar da mabiyanta. Bugu da ƙari, ta kashe mutane sosai, har da bayin Allah. (R. Yar. 19:2) A wace hanya ce Jehobah zai hallaka Babila Babba?

11. Mene ne wannan “jar dabba” take wakilta, kuma ta yaya Jehobah zai yi amfani da ita wajen hallaka Babila Babba?

11 Jehobah zai yi amfani da “ƙahoni goma” na ‘jar dabbar,’ wajen hallaka “wannan karuwa.” Wannan dabbar tana wakiltar Majalisar Ɗinkin Duniya. Ƙahoni goma na wakiltar sarakunan da ke goyon bayan wannan ƙungiyar. Waɗannan sarakunan za su kai wa karuwar, wato Babila Babba hari. “Za su ƙwace kome da take da shi su kuma bar ta tsirara,” ta wajen ƙwace dukan wadatarta da kuma fallasa muguntarta. (R. Yar. 17:​3, 16) Wannan hallakar za ta faru farat ɗaya, wato kamar cikin kwana ɗaya kuma za ta rikitar da magoya bayanta. Me ya sa za su rikice? Domin ta yi fahariya cewa: “Ni sarauniya ce a kujerar mulkina! Ni ba matar mutum da mijinta ya mutu ba ce, kuma ba zan taɓa yin baƙin ciki ba!”​—R. Yar. 18:​7, 8.

12. Mene ne Jehobah ba zai yarda al’ummai su yi ba, kuma me ya sa?

12 Jehobah ba zai yarda al’ummai su hallaka bayinsa ba. Ana kiransu da sunan Allah kuma sun yi biyayya ga umurninsa cewa su fita daga Babila Babba. (A. M. 15:​16, 17; R. Yar. 18:4) Sun kuma taimaka wa mutane da yawa su fita daga cikinta. Saboda haka, bayin Jehobah ba za su “shiga cikin zunubanta” ba. Duk da haka, za a jarraba bangaskiyarsu.

Ko da a ina bayin Allah suke a duniya, za su dogara ga Jehobah sa’ad da aka kawo musu hari (Ka duba sakin layi na 13) *

13. (a) Waye ne Gog? (b) Kamar yadda Ezekiyel 38:​2, 8, 9 suka nuna, mene ne zai sa Gog ya kawo hari a kan bayin Allah?

13 Harin da Gog zai kawo. (Karanta Ezekiyel 38:​2, 8, 9.) Bayan an hallaka dukan addinan ƙarya, mutanen Allah ne kaɗai za su rage kamar bishiyar da ta tsira sa’ad da aka yi mahaukaciyar guguwa. Amma hakan zai sa Shaiɗan fushi sosai. A sakamako, zai yi amfani da aljanu wajen yaɗa jita-jita domin al’ummai su kawo wa bayin Allah hari. (R. Yar. 16:​13, 14) Waɗannan al’ummai da suka haɗa kai ne ake kira ‘Gog na yankin Magog.’ A lokacin da al’ummai suka kawo wannan hari, to sun riga sun zo wurin da ake kira Armageddon a alamance.​—R. Yar. 16:16.

14. Mene ne Gog zai sani daga baya?

14 Gog zai dogara ga “iko na jiki,” wato makamansa. (2 Tar. 32:8) Amma mu za mu dogara ga Jehobah, kuma mutane za su ɗauka cewa hakan wawanci ne. Ballantana ma, allolin Babila Babba mai iko sosai a dā ba su cece ta daga hannun “dabbar” da ‘ƙahoninta goma’ ba. (R. Yar. 17:16) Saboda haka, Gog zai soma murna cewa karensa ya kama zaki. Zai ɗauka cewa hallaka bayin Allah zai yi sauƙi sosai. Zai “fāɗa wa jama’ar [Jehobah] . . . kamar yadda girgije yake duhunta fuskar ƙasa.” (Ezek. 38:16) Amma jikinsa zai gaya masa. Irin abin da ya faru da Fir’auna zai faru da Gog domin zai san cewa yana yaƙi ne da Jehobah.​—Fit. 14:​1-4; Ezek. 38:​3, 4, 18, 21-23.

15. Mene ne Yesu da rundunarsa za su yi a yaƙin Armageddon?

15 Yesu da rundunarsa za su kāre bayin Allah kuma za su hallaka Gog da magoya bayansa. (R. Yar. 19:​11, 14, 15) Amma me zai faru da Shaiɗan da ya zuga al’ummai su kai wa bayin Allah hari? Yesu zai jefa shi da aljanunsa cikin rami marar matuƙa, kuma za su kasance a ciki har shekara dubu.​—R. Yar. 20:​1-3.

ME ZA KA YI DON KA SAMI CETO?

16. (a) Ta yaya za mu nuna cewa mun “san Allah”? (b) A lokacin Armageddon, me zai faru da mutane da suka san Allah?

16 Ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah ko a’a, wajibi ne mu nuna cewa mun ‘san Allah’ kuma muna “biyayya da labari mai daɗi na Ubangijinmu Yesu.” (2 Tas. 1:​7-9) Za mu nuna cewa mun ‘san Allah’ sa’ad a muka san abubuwan da yake so da waɗanda ba ya so da kuma ƙa’idodinsa. Za mu kuma nuna cewa mun san shi sa’ad da muka ƙaunace shi, muka yi masa biyayya kuma muka bauta masa da zuciya ɗaya. (1 Yoh. 2:​3-5; 5:3) Idan mun nuna cewa mun san Allah, ‘Allah zai san da mu,’ kuma hakan zai sa mu sami ceto a Armageddon! (1 Kor. 8:3) Idan ‘Allah ya san da mu,’ to ya amince da mu ke nan.

17. Mene ne yake nufi a yi “biyayya da labari mai daɗi na Ubangijinmu Yesu”?

17 “Labari mai daɗi na Ubangijinmu Yesu” ya haɗa da dukan gaskiyar da ke cikin Kalmar Allah da Yesu ya koyar. Muna yin biyayya ga wannan labari mai daɗi sa’ad da muka yi amfani da koyarwar Yesu a rayuwarmu. Yin hakan ya haɗa da saka al’amura na Mulkin Allah farko da bin ƙa’idodin Jehobah da kuma yin wa’azi game da Mulkinsa. (Mat. 6:33; 24:14) Ƙari ga haka, za mu goyi bayan ʼyan’uwan Yesu yayin da suke kula da ayyukansu masu muhimmanci.​—Mat. 25:​31-40.

18. A wace hanya ce shafaffu za su albarkaci taro mai girma?

18 Nan ba da daɗewa ba, shafaffu za su albarkaci “waɗansu tumaki” don alherin da suka yi musu. (Yoh. 10:16) Ta yaya za su yi hakan? Kafin a soma yaƙin Armageddon, dukan shafaffu 144,000 za su sami ladarsu a sama kuma za su sami rai marar mutuwa. Bayan haka, za su kasance cikin rundunar da za su hallaka Gog kuma su kāre “taro” mai girma, wato amintattun bayin Allah. (R. Yar. 2:​26, 27; 7:​9, 10) Babu shakka, taro mai girma za su yi farin ciki cewa sun goyi bayan shafaffu a lokacin da suke duniya!

TA YAYA ZA MU KASANCE DA AMINCI YANZU DA ƘARSHE YA KUSA?

19-20. Mene ne zai taimaka mana mu jimre yanzu da Armageddon ya kusa sosai?

19 Bayin Jehobah da yawa suna cikin mawuyacin yanayi a waɗannan kwanaki na ƙarshe. Duk da haka, za mu iya yin farin ciki yayin da muke jimrewa. (Yaƙ. 1:​2-4) Abu na musamman da zai taimaka mana shi ne nacewa a yin addu’a. (Luk. 21:36) Dole ne kuma mu riƙa nazarta Kalmar Allah kowace rana da yin tunani a kan abin da muka karanta, har da annabcin da aka yi game da zamaninmu. (Zab. 77:12) Yin abubuwan nan da kuma yin wa’azi da ƙwazo za su ƙarfafa bangaskiyarmu.

20 Ka yi tunanin irin farin cikin da za ka yi sa’ad da aka hallaka Babila Babba kuma aka kammala yaƙin Armageddon! Mafi muhimmanci ma, ka yi tunanin yadda za ka yi murna a lokacin da aka tsarkake sunan Allah kuma aka ɗaukaka ikonsa! (Ezek. 38:23) Babu shakka, Armageddon albishiri ne ga mutanen da suka san Allah, suke biyayya ga Ɗansa kuma suka jimre har ƙarshe.​—Mat. 24:13.

WAƘA TA 143 Mu Ci Gaba da Ƙwazo da Tsaro da Jira

^ sakin layi na 5 Bayin Jehobah sun daɗe suna jiran Armageddon. A wannan talifin, za mu tattauna ma’anar Armageddon, abubuwan da za su faru kafin ya zo da kuma yadda za mu kasance da aminci yanzu da ƙarshe ya yi kusa sosai.

^ sakin layi na 71 BAYANI A KAN HOTO: Abubuwa na musamman za su faru. (1) Za mu ci gaba da yin wa’azi idan ya yiwu; (2) za mu ci gaba da yin nazarin Kalmar Allah, kuma (3) za mu ci ga da dogara ga Allah.

^ sakin layi na 85 BAYANI A KAN HOTO: Wasu ʼyan sanda suna so su shiga gidan wasu bayin Jehobah da suka dogara cewa Yesu da mala’ikunsa sun san abin da ke faruwa.