Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 37

Mu Rika Mika Kanmu ga Jehobah

Mu Rika Mika Kanmu ga Jehobah

“Ashe, ba za mu fi yarda da horon Ubanmu . . . ba?”​—IBRAN. 12:9.

WAƘA TA 9 Jehobah Ne Sarkinmu!

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Me ya sa muke bukatar mu miƙa kanmu ga Jehobah?

MUNA bukatar mu miƙa kanmu ga Jehobah domin shi ne Mahaliccinmu. Saboda haka, yana da ikon gaya wa halittunsa abin da ya kamata su riƙa yi. (R. Yar. 4:11) Ban da haka, wani dalili da ya sa ya kamata mu riƙa yin biyayya ga Jehobah shi ne domin sarautarsa ce ta fi kyau. ’Yan Adam sun daɗe suna sarauta a kan ’yan’uwansu. Amma idan muka kwatanta su da Jehobah, za mu ga cewa Jehobah ya fi dukansu hikima da jinƙai kuma yana tausaya wa bayinsa.​—Fit. 34:6; Rom. 16:27; 1 Yoh. 4:8.

2. Waɗanne dalilai ne Ibraniyawa 12:​9-11 suka nuna da ya sa ya kamata mu riƙa miƙa kanmu ga Jehobah?

2 Jehobah yana so mu riƙa yi masa biyayya musamman don muna ƙaunar sa, kuma shi Ubanmu ne mai ƙauna, ba don kawai muna tsoron ɓata masa rai ba. A wasiƙar da Bulus ya rubuta ga Kiristoci Ibraniyawa, ya bayyana cewa “mu fi yarda da horon Ubanmu” domin yin haka zai sa mu amfana.​—Karanta Ibraniyawa 12:​9-11.

3. (a) Ta yaya za mu nuna cewa muna miƙa kanmu ga Jehobah? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

3 Muna miƙa kanmu ga Jehobah sa’ad da muka yi iya ƙoƙarinmu mu riƙa yi masa biyayya kuma muka guji dogara ga kanmu. (K. Mag. 3:5) Zai yi mana sauƙi mu riƙa miƙa kanmu ga Jehobah idan muka san halayensa masu kyau. Me ya sa? Domin waɗannan halaye ne suke motsa Jehobah ya yi dukan abubuwan da yake yi. (Zab. 145:9) Idan muka ci gaba da koya game da Jehobah, hakan zai sa mu riƙa ƙaunar sa. Kuma idan muna ƙaunar Jehobah, ba za mu bukaci a riƙa lissafa mana abubuwan da ya kamata mu yi da kuma waɗanda ba su dace mu yi ba. Za mu yi ƙoƙari mu kasance da ra’ayin Jehobah kuma mu guji yin abubuwan da ba su dace ba. (Zab. 97:10) Amma a wasu lokuta, yana iya yi mana wuya mu yi biyayya ga Jehobah. Me ya sa? Kuma wane darasi ne dattawa za su iya koya daga Nehemiya? Wane darasi ne magidanta za su iya koya daga Sarki Dauda? Kuma wane darasi ne iyaye mata za su iya koya daga Maryamu mahaifiyar Yesu? Za mu amsa tambayoyin nan a wannan talifin.

DALILIN DA YA SA MIƘA KAI GA JEHOBAH ZAI IYA YIN WUYA

4-5. Kamar yadda Romawa 7:​21-23 suka nuna, me ya sa zai iya yi mana wuya mu miƙa kanmu ga Jehobah?

4 Wani dalilin da ya sa zai iya yi mana wuya mu riƙa miƙa kanmu ga Jehobah shi ne don zunubi da kuma ajizanci da muka gāda. Saboda haka, a wasu lokuta ba ma son yin biyayya ga Allah. Sa’ad da Adamu da Hauwa’u suka yi rashin biyayya kuma suka ci ’ya’yan itacen, sun yanke wa kansu shawarar abin da ya dace da wanda bai dace ba. (Far. 3:22) A yau, yawancin mutane ba sa bin umurnin Allah, sun gwammace su riƙa yanke wa kansu shawarar abin da ya dace da kuma wanda bai dace ba.

5 Ba ma bin misalinsu domin mun san Jehobah kuma muna ƙaunar sa, amma a wasu lokuta yana iya yi mana wuya mu yi abubuwa yadda yake so. Manzo Bulus ma ya fuskanci wannan matsalar. (Karanta Romawa 7:​21-23.) Kamar Bulus, muna so mu riƙa faranta wa Jehobah rai. Don haka, muna bukatar mu riƙa yin ƙoƙari sosai don mu guji yin abubuwan da ba su dace ba.

6-7. Wane dalili ne kuma zai iya sa ya yi mana wuya mu miƙa kanmu ga Jehobah? Ka ba da misali.

6 Al’adunmu suna iya shafanmu sosai, kuma hakan yana iya sa ya yi mana wuya mu riƙa miƙa kanmu ga Jehobah. Mutane da yawa suna da ra’ayin da suka saɓa wa ƙa’idodin Jehobah. Don haka, muna bukatar mu yi ƙoƙari sosai don mu guji bin ra’ayinsu. Ka yi la’akari da misalin nan.

7 A wasu wurare, ana taƙura wa matasa su nemi aikin da zai sa su yi arziki. Wata ’yar’uwa mai suna Mary * ta fuskanci wannan matsalar. Kafin ta soma bauta wa Jehobah, ta yi karatu a shahararrun makarantu a ƙasarsu. Iyayen Mary sun tilasta mata ta nemi aikin da za a riƙa biyan ta albashi mai tsoka don mutane su riƙa daraja ta. Amma bayan ta koya game da Jehobah kuma ta soma ƙaunar sa, ta canja maƙasudanta. Hakan bai yi mata sauƙi ba. Ta ce: “A wasu lokuta, ina samun aikin da zai sa in sami kuɗi sosai, amma na san cewa yin aikin zai hana ni bauta wa Jehobah yadda nake yi a yanzu. Saboda yadda aka rene ni, yana yi mini wuya in ƙi yin aikin. Amma nakan roƙi Jehobah ya taimaka mini na guji yin aikin da zai hana ni yin iya ƙoƙarina a hidimarsa.”​—Mat. 6:24.

8. Mene ne za mu tattauna yanzu?

8 Za mu amfana sosai idan muka miƙa kanmu ga Jehobah. Amma idan dattawa da magidanta da kuma iyaye mata suka miƙa kai ga Allah, za su iya taimaka wa mutane. Bari mu tattauna wasu misalai a Littafi Mai Tsarki da za su koya mana yadda ya kamata mu bi da ikonmu a hanyar da zai faranta wa Jehobah rai.

DARASIN DA DATTAWA ZA SU IYA KOYA DAGA NEHEMIYA

Dattawa suna saka hannu a aikin da ake yi a Majami’ar Mulki, kamar yadda Nehemiya ya saka hannu sa’ad da ake gina ganuwar Urushalima (Ka duba sakin layi na 9-11) *

9. Waɗanne matsaloli ne Nehemiya ya fuskanta?

9 Jehobah ya ba dattawa aiki mai muhimmanci na kula da tumakinsa. (1 Bit. 5:2) Dattawa za su iya koyan darussa sosai idan suka yi nazarin yadda Nehemiya ya bi da mutanen Allah. A matsayin gwamna a Yahudiya, Nehemiya yana da iko sosai. (Neh. 1:11; 2:​7, 8; 5:14) Ka yi tunanin irin matsalolin da ya fuskata. Ya ga cewa mutanen sun ƙazamtar da haikali kuma ba sa tallafa wa Lawiyawa kamar yadda Allah ya umurce su a dokarsa. Ƙari ga haka, Yahudawan ba sa bin dokar Allah game da Assabaci kuma wasu cikinsu sun auro mata da ba Isra’ilawa ba. Nehemiya zai bukaci ya magance wannan matsalar.​—Neh. 13:​4-30.

10. Ta yaya Nehemiya ya magance matsalolin da ya fuskanta?

10 Nehemiya bai yi amfani da ikonsa don ya tilasta wa mutanen su bi ra’ayinsa ba. A maimakon haka, ya nemi taimakon Jehobah ta addu’a kuma ya koya wa mutanen dokokin Allah. (Neh. 1:​4-10; 13:​1-3) Ƙari ga haka, Nehemiya ya kasance da sauƙin kai kuma ya yi aiki tare da ’yan’uwansa wajen gina ganuwar Urushalima.​—Neh. 4:15.

11. Kamar yadda 1 Tasalonikawa 2:​7, 8 suka nuna, ta yaya dattawa za su bi da ’yan’uwa a ikilisiya?

11 Wataƙila dattawa ba za su fuskanci irin matsalolin da Nehemiya ya fuskanta ba, amma za su iya bin misalinsa a hanyoyi da yawa. Alal misali, suna yin aiki tuƙuru don su taimaka wa ’yan’uwansu. Kuma ba sa barin ikon da suke da shi ya sa su girman kai. A maimakon haka, suna kula da ’yan’uwa a cikin ikilisiya da ƙauna. (Karanta 1 Tasalonikawa 2:​7, 8.) Suna wa ’yan’uwansu magana da fara’a don suna da sauƙin kai kuma suna ƙaunar su. Wani dattijo mai suna Andrew da ya yi shekaru da yawa yana wannan hidimar, ya ce: “Na lura cewa idan dattijo yana da fara’a kuma yana nuna alheri, hakan yana ratsa zuciyar ’yan’uwa sosai. Kuma yana motsa su su riƙa bin umurnin dattawa.” Wani dattijo mai suna Tony da ya daɗe yana wannan hidima, ya ce: “Ina ƙoƙarin bin shawarar da ke Filibiyawa 2:3 kuma a kullum ina ƙoƙarin ɗaukan wasu da muhimmanci fiye da kaina. Hakan yana taimaka mini in guji tilasta wa ’yan’uwa su bi umurnina.”

12. Me ya sa ya kamata dattawa su kasance da sauƙin kai?

12 Dattawa suna bukatar su kasance da sauƙin kai kamar Jehobah. Duk da cewa Jehobah ne mafi iko, “yakan sunkuya daga can bisa” don ya taimaka wa “talakawa.” (Zab. 18:35; 113:​6, 7) Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah ya tsani masu girman kai.​—K. Mag. 16:5.

13. Me ya sa dattijo yake bukatar ya mai da hankali ga furucinsa?

13 Dattijo zai nuna cewa ya miƙa kai ga Jehobah ta wajen mai da hankali ga furucinsa da kuma ayyukansa. Idan bai yi hakan ba, yana iya faɗin abubuwan da ba su dace ba in wani bai girmama shi ba. (Yaƙ. 1:26; Gal. 5:​14, 15) Andrew wanda aka ambata ɗazu ya ce: “A wasu lokuta, ina ji kamar in yi baƙar magana ga ʼyan’uwan da ba su girmama ni a matsayin dattijo ba. Amma na yi tunanin sosai a kan misalan mutane masu aminci a zamanin dā, kuma hakan ya taimaka mini in koyi muhimmanci nuna sauƙin kai.” Dattawa suna nuna cewa sun miƙa kansu ga Jehobah sa’ad da suke yi wa ’yan’uwa maza da mata ko kuma sauran dattawa magana da fara’a.​—Kol. 4:6.

DARASIN DA MAGIDANTA ZA SU IYA KOYA DAGA DAUDA

14. Wane hakki ne Jehobah ya ba magidanta, kuma me yake bukata a gare su?

14 Jehobah ya ba magidanta hakkin yin ja-goranci a iyalinsu, kuma yana so magidanci ya horar da yaransa. (1 Kor. 11:3; Afis. 6:4) Amma hakan ba ya nufin cewa magidanta za su yi amfani da ikonsu yadda suka ga dama ba. Jehobah ne ya kafa iyali, don haka magidanta za su ba da lissafin yadda suka bi da iyalinsu. (Afis. 3:​14, 15) Magidanta suna nuna cewa sun miƙa kansu ga Jehobah ta wajen yin amfani da ikonsu a hanyar da za ta faranta wa Allah rai. Za su iya koyan darussa da yawa daga Sarki Dauda.

Yadda magidanci Kirista yake addu’a zai iya nuna wa iyalinsa cewa yana da sauƙin kai (Ka duba sakin layi na 15-16) *

15. Me ya sa magidanta suke bukatar su bi misalin Sarki Dauda?

15 Jehobah ya ba Dauda hakkin yi wa iyalinsa da kuma al’ummar Isra’ila ja-goranci. A matsayin sarki, Dauda yana da iko sosai. A wasu lokuta, ya yi amfani da ikon a hanyar da ba ta dace ba. (2 Sam. 11:​14, 15) Amma ya nuna cewa ya miƙa kansa ga Jehobah ta wajen amincewa da horon da ya yi masa. Dauda ya gaya wa Jehobah dukan abin da ke zuciyarsa a addu’a, kuma ya ƙoƙarta don ya bi umurninsa. (Zab. 51:​1-4) Ƙari ga haka, ya nuna sauƙin kai kuma ya saurari shawarwari masu kyau da maza da mata suka ba shi. (1 Sam. 19:​11, 12; 25:​32, 33) Dauda ya koyi darussa daga kurakurensa kuma ya sa bauta wa Jehobah ya zama abu mafi muhimmanci a rayuwarsa.

16. Wane darasi ne magidanta za su iya koya daga Sarki Dauda?

16 Ka yi la’akari da wasu darussan da magidanta za su iya koya daga Sarki Dauda: Kada ku yi amfani da ikon da Jehobah ya ba ku a hanyar da ba ta dace ba. In kun yi kuskure, ku amince cewa kun yi hakan, kuma ku bi shawarar Littafi Mai Tsarki da aka ba ku. Idan kun yi hakan, iyalinku za ta girmama ku domin sauƙin kai da kuke nunawa. Sa’ad da kuke addu’a tare da iyalinku, ku gaya wa Jehobah dukan abin da ke zuciyarku. Yin hakan zai sa su san cewa kuna neman taimakon Jehobah da ja-gorancinsa. Kuma ku sa hidimarku ga Jehobah ta zama abu mafi muhimmanci. (M. Sha. 6:​6-9) Misalinku mai kyau ne kyauta mafi daraja da za ku iya ba iyalinku.

DARASIN DA IYAYE MATA ZA SU IYA KOYA DAGA MARYAMU

17. Wane aiki ne Jehobah ya ba iyaye mata?

17 Jehobah ya ba iyaye mata aiki mai muhimmanci a iyali da kuma iko a kan yaransu. (K. Mag. 6:20) Furucin iyaye mata da kuma ayyukansu na iya shafan yaransu muddar ransu. (K. Mag. 22:6) Ka yi la’akari da darussan da iyaye mata za su iya koya daga Maryamu mahaifiyar Yesu.

18-19. Mene ne iyaye mata za su iya koya daga misalin Maryamu?

18 Maryamu ta san Nassosi sosai. Ta daraja Jehobah kuma ta kasance da dangantaka mai kyau da shi. Ta miƙa kanta ga Jehobah duk da cewa yin hakan zai canja rayuwarta gabaki ɗaya.​—Luk. 1:​35-38, 46-55.

Ya kamata iyaye mata su ƙoƙarta sosai don su nuna wa iyalinsu cewa suna ƙaunar su, musamman a lokacin da suka gaji (Ka duba sakin layi na 19) *

19 Iyaye mata, za ku iya bin misalin Maryamu a hanyoyi da yawa. Ta yaya? Na farko, kuna bukatar ku ƙarfafa dangantakarku da Jehobah ta wajen yin nazarin Kalmarsa a kai a kai da kuma addu’a. Na biyu, ku kasance a shirye don yin canja-canje a rayuwarku don ku faranta wa Jehobah rai. Alal misali, wataƙila iyayenku suna saurin yin fushi kuma sukan yi muku magana a cikin ɓacin rai. Ko kuma kun girma da ra’ayi cewa hakan ne ya kamata a yi renon yara. Ko da yake kun koyi yadda Jehobah yake so ku riƙa bi da yaranku, a wasu lokuta yana iya yi muku wuya ku kwantar da hankalinku sa’ad da yaranku suka ɓata muku rai, musamman a lokacin da kuka gaji. (Afis. 4:31) Idan kuna jin hakan, kuna bukatar ku roƙi Jehobah ya taimaka muku. Wata mahaifiya mai suna Lydia ta ce: “A wasu lokuta, ina yin addu’a sosai don kada na yi wa yarona magana da fushi sa’ad da ya yi rashin biyayya. Na taɓa katse wa kaina magana sa’ad da nake so na yi wa yarona baƙar magana, sai na yi addu’a Jehobah ya taimaka mini. Yin addu’a yana taimaka mini in kame kaina.”​—Zab. 37:5.

20. Wace matsala ce wasu iyaye mata suke fuskanta, kuma ta yaya za su iya magance wannan matsalar?

20 Wata matsala kuma da wasu iyaye mata ke fuskanta ita ce ba sa iya nuna wa yaransu cewa suna ƙaunar su. (Tit. 2:​3, 4) Wasu an rene su ne a iyalin da iyaye ba sa ƙulla abokantaka da yaransu. Idan haka aka rene ku, kada ku yi irin kuskuren da iyayenku suka yi. Mahaifiyar da ta miƙa kanta ga Jehobah, tana bukatar ta koyi nuna wa yaranta cewa tana ƙaunar su. Yana iya yi mata wuya ta canja ra’ayinta da kuma ayyukanta. Amma tana iya yin waɗannan canja-canje kuma iyalinta za su amfana.

KU CI GABA DA MIƘA KAI GA JEHOBAH

21-22. Kamar yadda Ishaya 65:​13, 14 suka nuna, ta yaya za mu amfana idan muka miƙa kanmu ga Jehobah?

21 Sarki Dauda ya san muhimmancin miƙa kai ga Jehobah. Ya ce: “Ƙa’idodin Yahweh daidai suke, suna farantar da zuciya. Umarnan Yahweh masu sauƙin ganewa ne, sukan fahimtar da zuciya. Ta wurinsu bawanka yakan sami gargaɗi, ta wurin kiyaye su akwai lada mai yawa.” (Zab. 19:​8, 11) A yau, muna ganin bambanci da ke tsakanin waɗanda suke miƙa kansu ga Jehobah da kuma waɗanda suka ƙi yin hakan. Waɗanda suke miƙa kansu ga Jehobah suna “rera waƙa domin farin ciki a zuciyarsu.”​—Karanta Ishaya 65:​13, 14.

22 Idan dattawa da magidanta da kuma iyaye mata suka miƙa kansu ga Jehobah, za su amfana, iyalansu za su riƙa farin ciki, kuma ’yan’uwa a ikilisiya za su kasance da haɗin kai. Amma abu mafi muhimmanci shi ne, za su faranta wa Jehobah rai. (K. Mag. 27:11) Wannan shi ne abin da zai fi sa mu farin ciki!

WAƘA TA 123 Mu Riƙa Bin Ja-gorancin Jehobah

^ sakin layi na 5 A wannan talifin, za mu tattauna dalilin da ya sa muke bukatar mu riƙa miƙa kanmu ga Jehobah. Ban da haka, da yake dattawa da iyaye suna da iko, za mu tattauna darussan da za su iya koya daga Nehemiya da Sarki Dauda da kuma Maryamu mahaifiyar Yesu.

^ sakin layi na 7 An canja wasu sunaye a wannan talifin.

^ sakin layi na 61 BAYANI A KAN HOTO: Wani dattijo yana yin aiki tare da yaronsa don kula da Majami’ar Mulki, yadda Nehemiya ya taimaka sa’ad da ake gina ganuwar Urushalima.

^ sakin layi na 63 BAYANI A KAN HOTO: Wani magidanci yana yin addu’a tare da iyalinsa.

^ sakin layi na 65 BAYANI A KAN HOTO: Wani yaro ya ɗau sa’o’i yana wasa kuma bai yi aikin da aka ba shi ba. Mahaifiyarsa da ta dawo aiki a gajiye ta horar da shi ba tare da yin fushi da kuma baƙar magana ba.