Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 38

“Ku Zo Gare Ni, . . . Zan Ba Ku Hutawa”

“Ku Zo Gare Ni, . . . Zan Ba Ku Hutawa”

“Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji, kuma kuna fama da kaya masu nauyi a kanku, zan ba ku hutawa.”​—MAT. 11:28.

WAƘA TA 17 “Na Yarda”

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Wane alkawari ne Yesu ya yi, kamar yadda Matiyu 11:​28-30 suka nuna?

YESU ya yi wa masu sauraron sa alkawari mai ƙayatarwa. Ya ce musu: “Ku zo gare ni, . . . zan ba ku hutawa.” (Karanta Matiyu 11:​28-30.) Yesu zai cika wannan alkawarin da ya yi. Alal misali, ka yi tunani a kan abin da ya yi ma wata mata da ke fama da rashin lafiya mai tsanani.

2. Mene ne Yesu ya yi ma wata mata da ke rashin lafiya?

2 Matar tana bukatar taimako da gaggawa. Ta je wajen likitoci da yawa don su taimaka mata. Ta yi shekaru 12 tana shan wahala amma babu wanda zai iya taimaka mata. Ƙari ga haka, dokar da Allah ya ba Musa ta bayyana cewa matar ba ta da tsarki. (L. Fir. 15:25) Matar ta ji cewa Yesu yana warkar da marasa lafiya, sai ta neme shi. Sa’ad da ta gan shi, ta taɓa shafin rigarsa kuma nan da nan ta warke! Amma ba warkar da ita kaɗai Yesu ya yi ba. Ta ga cewa yana ƙaunar ta kuma yana daraja ta don yadda ya bi da ita. Alal misali, ya nuna hakan ta wajen yin amfani da kalmar nan “yata.” Hakika, matar ta sami ƙarfafa sosai!​—Luk. 8:​43-48.

3. Waɗanne tambayoyi ne za mu amsa?

3 Ka lura cewa matar ce ta je ta nemi Yesu. Ita ce ta saka ƙwazo. Haka ma a yau, muna bukatar mu saka ƙwazo don mu je wurin Yesu. A yau, Yesu ba zai yi amfani da mu’ujiza don warkar da marasa lafiya da suka je gare shi ba. Duk da haka, yana gayyatar su cewa: “Ku zo gare ni, . . . zan ba ku hutawa.” A wannan talifin, za mu tattauna tambayoyi biyar: Me muke bukata don mu bi furucin nan na Yesu, “ku zo gare ni”? Mene ne Yesu yake nufi sa’ad da ya ce: “Ku miƙa kanku ga umarnaina”? Wane darasi ne za mu iya koya daga Yesu? Me ya sa aikin da ya ba mu yake sa mu sami hutu a zuciyarmu? Kuma ta yaya za mu ci gaba da samun ƙarfafawa yayin da muke ɗauke da gungumen Yesu?

“KU ZO GARE NI’’

4-5. A waɗanne hanyoyi ne za mu amince da gayyatar Yesu cewa “ku zo gare ni”?

4 Hanya ɗaya da za mu iya amsa gayyatar Yesu ita ce ta wajen sanin furucinsa da kuma ayyukansa. (Luk. 1:​1-4) Babu mutumin da zai taya mu yin hakan. Hakkinmu ne mu yi nazari game da Yesu a Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, za mu amince da gayyatar Yesu cewa “ku zo gare ni” idan muka yanke shawarar yin baftisma kuma muka zama mabiyansa.

5 Wata hanya kuma da za mu iya yin hakan, ita ce ta wajen zuwa wurin dattawa idan muna bukatar taimako. Yesu yana yin amfani da wannan “baiwa iri-iri” don ya kula da tumakinsa. (Afis. 4:​7, 8, 11; Yoh. 21:16; 1 Bit. 5:​1-3) Muna bukatar mu ɗauki mataki don neman taimakonsu. Ba zai dace mu yi zaton cewa dattawa za su san tunaninmu da kuma bukatunmu ba. Wani ɗan’uwa mai suna Julian ya ce: “Na daina hidima a Bethel domin ina rashin lafiya, kuma wani abokina ya ƙarfafa ni in gaya wa dattawa su ziyarce ni don su ƙarfafa ni. Da farko, na ɗauka ba na bukatar yin hakan. Amma daga baya, na nemi taimako kuma dattawa sun kawo mini ziyarar ƙarfafawa. Wannan ziyarar tana cikin kyauta mafi daraja da aka taɓa ba ni.” Dattawa masu aminci kamar waɗanda suka ziyarci Julian za su iya taimaka mana mu san ra’ayin Kristi kuma mu koyi nuna halayensa. (1 Kor. 2:16; 1 Bit. 2:21) Hakika, wannan kyauta ce mai daraja da za su iya ba mu.

“KU MIƘA KANKU GA UMARNAINA”

6. Mene ne Yesu yake nufi sa’ad da ya ce: “Ku miƙa kanku ga umarnaina”?

6 Sa’ad da Yesu ya ce: “Ku miƙa kanku ga umarnaina kamar yadda saniya takan miƙa wuyanta ga gungumen noma,” ƙila yana nufin cewa “mu amince da ja-gorancinsa.” Ko kuma yana nufin cewa “mu goyi bayansa don mu cim ma hidimar Jehobah.” Ko da me yake nufi, muna bukatar mu yi wa Ubangijinmu aiki.

7. Kamar yadda Matiyu 28:​18-20 suka nuna, wane aiki ne aka ba mu, kuma wane tabbaci ne muke bukatar mu kasance da shi?

7 Muna amincewa da gayyatar Yesu sa’ad da muka yi alkawarin bauta wa Allah kuma muka yi baftisma. Yesu yana gayyatar kowa ya zo gare shi, kuma zai marabce su. (Yoh. 6:​37, 38) Dukan mabiyan Kristi suna da gatan yin aikin da Jehobah ya ba Yesu. Muna bukatar mu kasance da tabbaci cewa Yesu zai taimaka mana mu yi wannan aikin.​—Karanta Matiyu 28:​18-20.

“KU KOYA DAGA WURINA”

Ka ƙarfafa mutane yadda Yesu ya yi (Ka duba sakin layi na 8-11) *

8-9. Me ya sa mutane masu sauƙin kai suke son kusantar Yesu, kuma waɗanne tambayoyi ne muke bukatar mu yi wa kanmu?

8 Mutane masu sauƙin kai suna son kusantar Yesu. (Mat. 19:​13, 14; Luk. 7:​37, 38) Me ya sa? Ka yi la’akari da bambancin da ke tsakanin Yesu da kuma Farisiyawa. Waɗannan malaman addinai ba su da ƙauna kuma suna da girman kai. (Mat. 12:​9-14) Yesu yana da ƙauna kuma yana da sauƙin kai. Farisiyawa suna so a riƙa daraja su. Yesu ya koya wa mabiyansa cewa bai kamata su zama masu girman kai ba. Ya ce su zama masu sauƙi kai kuma su riƙa yi wa mutane hidima. (Mat. 23:​2, 6-11) Farisiyawa suna tsorata mutane don su bi umurninsu. (Yoh. 9:​13, 22) Yesu ya ƙarfafa mutane ta yadda yake bi da su da kuma kalmominsa masu daɗi.

9 Ka koyi darussan nan daga Yesu kuwa? Ka tambayi kanka: ‘An san ni a matsayin mai sauƙin kai kuwa? Ina taimaka wa mutane yin ƙananan ayyuka kuwa? Ina yi wa mutane alheri kuwa?’

10. Yaya mutanen da suka yi aiki da Yesu suka ji?

10 Yesu ya sa abokan aikinsa su kasance da kwanciyar rai kuma ya ji daɗin koyar da su. (Luk. 10:​1, 19-21) Ya ƙarfafa mabiyansa cewa su riƙa yin tambayoyi, kuma yana son ya san ra’ayinsu. (Mat. 16:​13-16) Shuke-shuken da ake kula da su sosai suna yin kyau. Hakazalika, mabiyan Yesu sun yi nasara. Sun saurari abubuwan da Yesu ya koya musu kuma sun yi ayyuka masu kyau.

Ka zama mai fara’a

Ka zama mai ƙwazo

Ka zama mai aiki tuƙuru da sauƙin kai *

11. Waɗanne tambayoyi ne muke bukatar mu yi wa kanmu?

11 Shin kana da iko a kan wasu? Idan haka ne, ka tambayi kanka: ‘Ta yaya nake bi da mutane a wurin aiki ko kuma a gida? Ina so mutane su kasance da kwanciyar hankali? Ina ƙarfafa mutane su riƙa yin tambayoyi kuwa? Ina yin iya ƙoƙarina don in saurare su kuwa?’ Hakika, ba za mu so mu zama kamar Farisiyawa ba, waɗanda suke ƙin mutanen da ke yin tambayoyi kuma suke azabtar da mutanen da ke bayyana ra’ayin da ba ta jitu da nasu ba.​—Mar. 3:​1-6; Yoh. 9:​29-34.

“ZAN BA KU HUTAWA”

12-14. Me ya sa aikin da Yesu ya ba mu yake da ban-ƙarfafa?

12 Me ya sa za mu sami ƙarfafa sa’ad da muke yin aikin da Yesu ya ba mu? Akwai dalilai da yawa, amma ka yi la’akari da wasu daga cikinsu.

13 Muna da shugabanni nagari. Jehobah shugabanmu wanda ya fi kowa iko, yana nuna godiya sosai. Yana daraja aikin da muke yi masa. (Ibran. 6:10) Ƙari ga haka, yana ba mu ƙarfin da muke bukata don yin aikin. (2 Kor. 4:7; Gal. 6:5) Yesu Sarkinmu ya kafa mana misali mai kyau a yadda za mu riƙa bi da mutane. (Yoh. 13:15) Kuma dattawa da suke kula da mu suna ƙoƙarin bin misalin Yesu wanda shi ne “makiyayi mai girma.” (Ibran. 13:20; 1 Bit. 5:2) Suna yin iya ƙoƙarinsu don su nuna alheri, su riƙa ƙarfafa mu kuma su nuna ƙarfin zuciya sa’ad da suke koyar da mu da kuma kāre mu.

14 Muna da abokan kirki. Babu mutanen da ke da irin abokan kirki da muke da shi kuma suke yin irin aikin da muke yi. Ka yi tunani: Muna da gatan yin aiki tare da mutanen da suke da ɗabi’u masu kyau kuma ba sa tunani cewa sun fi wasu daraja. Ban da haka, suna da baiwa sosai amma ba sa nuna girman kai. A maimakon haka, suna ɗaukan mutane da daraja fiye da kansu. Suna ɗaukar mu a matsayin aminansu ba abokan aikinsu kaɗai ba. Suna ƙaunar mu sosai har za su iya ba da ransu a madadinmu!

15. Yaya ya kamata mu ji don aikin da muke yi?

15 Muna da aiki mafi kyau. Muna koyar da mutane gaskiya game da Jehobah kuma muna fallasa ƙarairayin Shaiɗan. (Yoh. 8:44) Shaiɗan yana amfani da ƙarairayi wajen wahalar da mutane. Alal misali, yana so mu gaskata cewa Jehobah ba zai gafarta zunubanmu ba kuma ba zai ƙaunace mu ba. Hakika, waɗannan ƙarairayi ne da ke sa mutane sanyin gwiwa! Idan muka amince da gayyatar Yesu, zai gafarta zunubanmu. Kuma babu shakka, Jehobah yana ƙaunar dukanmu sosai. (Rom. 8:​32, 38, 39) Muna farin ciki sosai sa’ad da muka taimaka wa mutane su dogara ga Jehobah kuma su gyara salon rayuwarsu!

KU CI GABA DA BIN UMURNIN YESU DON KU SAMI HUTAWA

16. Ta yaya kayan da Yesu ya ce mu ɗauka ta bambanta da wasu kayan da muke ɗaukawa?

16 Kayan da Yesu ya ce mu ɗauka ya bambanta da kayan da muke bukatar mu ɗauka. Alal misali, bayan an tashi a aiki, mutane da yawa suna gajiya kuma ba sa farin ciki. Akasin haka, bayan mun daɗe muna yi wa Jehobah da Yesu hidima, muna farin ciki sosai. Muna iya gajiya sosai daga aiki kuma mu tilasta wa kanmu don mu halarci taro a ranar. Amma a yawanci lokaci, mukan koma gida cike da ƙarfi. Haka ma yake sa’ad da muka saka ƙwazo don yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Idan muka yi hakan, za mu sami ƙarfin gwiwa sosai!

17. Me muke bukatar mu fahimta game da yanayinmu, kuma me muke bukatar mu mai da wa hankali?

17 Muna bukatar mu fahimci cewa kowannenmu yana da ƙarfi daidai gwargwado. Don haka, muna bukatar mu mai da hankali ga abubuwan da muke ƙoƙarin yi. Alal misali, muna iya ɓata lokacinmu wajen neman abin duniya. Ka yi la’akari da abin da Yesu ya gaya wa wani matashi mai arziki da ya tambaye shi cewa: “Me zan yi in sami rai na har abada?” Matashin yana bin dokar Allah kuma ƙila shi mutumin kirki ne domin littafin Markus ya ce Yesu ya ‘ƙaunace’ shi. Yesu ya gaya masa cewa: “Ka je ka sayar da duk abin da kake da shi.” Yesu ya ƙara cewa: “Sa’an nan ka zo ka bi ni.” Matashin yana so ya zama mabiyin Yesu, amma ya ƙi rabuwa da ‘arzikinsa.’ (Mar. 10:​17-22) A sakamakon haka, ya ƙi ɗaukan gungumen Yesu kuma ya ci gaba da neman “kuɗi.” (Mat. 6:24) Me za ka yi da a ce kai ne?

18. Me muke bukatar mu riƙa yi a wasu lokuta, kuma me ya sa?

18 Ya kamata mu riƙa yin la’akari da abubuwan da muka fi mai da wa hankali. Me ya sa? Yin hakan zai sa mu san ko muna yin amfani da ƙarfinmu a hanyar da ta dace. Ka yi la’akari da abin da wani matashi mai suna Mark ya fuskanta. Ya ce: “Na yi shekaru da yawa ina tunanin cewa na sauƙaƙa salon rayuwata. Ina yin hidimar majagaba, amma ina yawan yin tunanin kuɗi da kuma yadda zan ji daɗin rayuwa. Ban san dalilin da ya sa ban gamsu ba. Daga baya, na fahimci cewa na fi mai da hankali ga bukatuna kuma ina ba Jehobah raguwan lokacina da kuma ƙarfina.” Mark ya yi gyara ga salon rayuwarsa da kuma tunaninsa don ya sami lokacin yi wa Jehobah hidima sosai. Ya ƙara da cewa: “A wasu lokuta, ina damuwa, amma da taimakon Jehobah da kuma goyon bayan Yesu, na magance matsalolin da na fuskanta.”

19. Me ya sa kasancewa da ra’ayin da ya dace yake da muhimmanci?

19 Za mu ci gaba da samun ƙarfafawa idan muka yi abubuwa guda uku nan. Na farko, mu kasance da ra’ayin da ya dace. Muna yin aikin Allah, saboda haka, muna bukatar mu yi aikin a hanyar da yake so. Mu ma’aikata ne, Jehobah shi ne Shugabanmu. (Luk. 17:10) Idan muna yin aikin Allah a hanyar da muke so, za mu jawo wa kanmu matsaloli. Hakika, shanu mai ƙarfi da ke yin huɗa a gona, yana iya jin rauni idan yana ƙoƙarin bin nasa tafarkin maimakon ja-gorancin makiyayinsa. Idan muka yi aikin Jehobah a hanyar da yake so, za mu iya cim ma ayyukan da muke tunanin cewa ba za mu iya yi ba. Ƙari ga haka, za mu iya magance dukan matsalolin da muke fuskanta. Mu tuna cewa babu wanda zai iya hana Jehobah cika nufinsa!​—Rom. 8:31; 1 Yoh. 4:4.

20. Wane ra’ayi ne muke bukatar mu kasance da shi yayin da muke bin umurnan Yesu?

20 Na biyu, muna bukatar mu yi aikin Allah da ra’ayin da ya dace. Burinmu shi ne mu sa mutane su ɗaukaka Jehobah, Ubanmu mai ƙauna. Mutane masu sonkai da haɗama a zamanin Yesu sun daina farin ciki da kuma bin umurnan Yesu. (Yoh. 6:​25-27, 51, 60, 66; Filib. 3:​18, 19) Amma waɗanda suke ƙaunar Allah da kuma maƙwabtansu sun yi farin ciki yayin da suka ci gaba da bin umurnan Yesu muddar ransu. Ƙari ga haka, sun sa rai cewa za su kasance da Yesu a sama. Kamar mutanen nan, za mu ci gaba da yin farin ciki idan muna bin umurnan Yesu da zuciya ɗaya.

21. Kamar yadda Matiyu 6:​31-33 suka nuna, me muke sa rai cewa Jehobah zai yi mana?

21 Na uku, mu tabbata cewa Jehobah zai taimaka mana. Mun zaɓi mu yi rayuwar sadaukar da kai da kuma yin aiki tuƙuru. Yesu ya gargaɗe mu cewa za a tsananta mana. Amma mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai ba mu ƙarfin gwiwa don mu jimre matsaloli. Idan muka ci gaba da jimrewa, za mu yi ƙarfi sosai. (Yaƙ. 1:​2-4) Ƙari ga haka, muna bukatar mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai yi mana tanadi, Yesu zai yi mana ja-goranci, kuma ’yan’uwanmu za su ƙarfafa mu. (Karanta Matiyu 6:​31-33; Yoh. 10:14; 1 Tas. 5:11) Saboda haka, muna da dukan abin da muke bukata don mu riƙa jimrewa!

22. Wane abu ne yake sa mu farin ciki?

22 Matar da Yesu ya warkar ta yi farin ciki sosai a ranar da ta sami lafiya. Za mu ci gaba da yin farin ciki idan muka zama mabiyan Kristi. Me kake ganin cewa matar ta yi? Idan ta amince ta zama mabiyar Yesu, za ta sami ladar kasancewa da shi a sama! Kuma wannan ladar ta fi dukan abubuwan da wataƙila ta sadaukar don ta zama mabiyar Yesu. Ko da muna sa ran yin rayuwa a duniya ko a sama, muna murna domin mun amince da gayyatar da Yesu ya yi mana cewa: “Ku zo gare ni”!

WAƘA TA 13 Mu Riƙa Bin Misali Yesu

^ sakin layi na 5 Yesu ya gayyace mu mu zo gare shi. Mene ne muke bukatar mu yi don mu nuna cewa mun aminci da wannan gayyatar? Za mu tattauna tambayar nan a wannan talifin, kuma za mu ga yadda za mu sami hutu yayin da muke aiki tare da Yesu.

^ sakin layi na 60 BAYANI A KAN HOTO: Yesu ya ƙarfafa mutane a hanyoyi da yawa

^ sakin layi na 66 BAYANI A KAN HOTO: Hakazalika, wani ɗan’uwa ma yana ƙarfafa mutane a hanyoyi da yawa.