Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 39

Su Waye Ne Taro Mai Girma?

Su Waye Ne Taro Mai Girma?

“Na ga [taro mai girma] . . . wanda ya fi gaban ƙirge . . . suna tsaye a gaban kujerar mulkin da kuma a gaban Ɗan Ragon.”​—R. YAR. 7:9.

WAƘA TA 60 Domin Su Sami Ceto

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Wane irin yanayi ne manzo Yohanna yake ciki a ƙarshen shekara ta 95?

A WAJEN shekara ta 95 bayan haihuwar Yesu, manzo Yohanna ya sami kansa a wani mawuyacin yanayi. Manzon ya tsufa kuma an saka shi a kurkuku a tsibirin Batmos. Ban da haka, wataƙila shi kaɗai ne manzon da ke raye. (R. Yar. 1:9) Yohanna ya san cewa ’yan ridda suna koyar da ƙarairayi kuma suna raba kan Kiristoci. Kamar dai ba da daɗewa ba, Kiristoci na gaskiya za su ƙare.​—Yahu. 4; R. Yar. 2:​15, 20; 3:​1, 17.

Manzo Yohanna ya ga taro mai girma suna sanye da fararen riguna, kuma suna riƙe da rassan itacen dabino (Ka duba sakin layi na 2)

2. Kamar yadda Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:​9-14 suka nuna, wane wahayi ne Yohanna ya gani? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

2 Sa’ad da Yohanna yake fuskantar wannan mawuyacin yanayi, Allah ya sa ya ga wani wahayi mai ban mamaki. A wahayin, wani mala’ika ya gaya ma wasu mala’iku huɗu cewa kada su bari a soma ƙunci mai girma, har sai an kammala saka wa rukunin bayin Allah hatimi a goshinsu. (R. Yar. 7:​1-3) Waɗannan bayin Allah shafaffu 144,000 da za su yi mulki tare da Yesu a sama ne. (Luk. 12:32; R. Yar. 7:4) Bayan haka, ya sake ganin wani rukuni dabam. Ya ce: “Na duba sai na ga wani babban taro na tsarkaka da yawa wanda ya fi gaban ƙirge. Sun fito daga kowace al’umma, da zuriya, da ƙabila, da yare, suna tsaye a gaban kujerar mulkin da kuma a gaban Ɗan Ragon.” (Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:​9-14.) Hakika, Yohanna ya yi farin ciki sosai da ya san cewa mutane da yawa za su bauta wa Jehobah a nan gaba!

3. (a) Me ya sa wahayin Yohanna zai ƙarfafa mu? (b) Mene ne za mu koya a wannan talifin?

3 Babu shakka, wahayin nan ya ƙarfafa bangaskiyar Yohanna sosai. Amma zai fi ƙarfafa bangaskiyarmu da yake wahayin yana magana ne game da abubuwan da za su faru a zamaninmu! A yau, miliyoyi mutane sun soma bauta wa Jehobah kuma suna sa rai cewa za su tsira a lokacin ƙunci mai girma, kuma za su yi rayuwa har abada a duniya. A wannan talifin, za mu ga yadda Jehobah ya taimaka wa bayinsa fiye da shekara tamanin da suka shige su san ko su waye ne taro mai girma. Bayan haka, za mu tattauna abubuwa biyu game da wannan taro mai girma: (1) adadinsu, da kuma (2) inda suka fito. Abubuwan nan za su ƙarfafa bangaskiya waɗanda suke cikin wannan rukunin.

A WANE WURI NE TARO MAI GIRMA ZA SU KASANCE?

4. Wane gaskiyar Littafi Mai Tsarki ne mutanen da ba sa bauta wa Jehobah ba su fahimta ba, amma ta yaya Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka bambanta?

4 Mutanen da ba sa bauta wa Jehobah ba sa koyar da gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki cewa wata rana, adalai za su rayu har abada a duniya. (2 Kor. 4:​3, 4) A yau, yawancin addinai suna koyar da cewa adalai za su yi rayuwa a sama bayan sun mutu. Amma Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da suke wallafa Hasumiyar Tsaro daga 1879, sun bambanta domin ba su gaskata da hakan ba. Sun fahimci cewa Allah zai mayar da duniya ta zama aljanna kuma miliyoyin mutane masu biyayya za su yi rayuwa har abada a duniya ba a sama ba. Amma ya ɗau lokaci kafin su fahimci ko su waye ne waɗannan mutane masu biyayya.​—Mat. 6:10.

5. Mene ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka gaskata game da shafaffu 144,000?

5 Hakika, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun fahimci cewa za a kai wasu “daga duniya” zuwa sama don su yi mulki tare da Yesu. (R. Yar. 14:3) Wannan rukunin su ne Kiristoci 144,000 masu ƙwazo da suka yi alkawarin bauta wa Allah kuma suka bauta masa da aminci a duniya. Mene ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka gaskata game da taro mai girma?

6. A dā, mene ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka gaskata game da taro mai girma?

6 A wahayin, Yohanna ya ga mutanen “suna tsaye a gaban kujerar mulkin da kuma a gaban Ɗan Ragon.” (R. Yar. 7:9) Wannan furucin ya sa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki su yi zato cewa taro mai girma ma za su yi rayuwa a sama. Idan shafaffu 144,000 da kuma taro mai girma za su yi rayuwa a sama, mene ne zai bambanta su? Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun ɗauka cewa taro mai girma ya ƙunshi Kiristocin da ba su yi wa Allah biyayya sosai ba sa’ad da suke duniya. Ko da yake sun bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, amma wasu cikinsu ba su fita daga addinan ƙarya ba. Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun yi zato cewa mutanen suna ƙaunar Allah, amma ƙaunarsu ba ta kai wadda za ta sa su yi mulki da Yesu ba. Domin ƙaunarsu ga Allah ba ta da ƙarfi sosai, za su sami damar kasancewa a gaban kujerar mulkin, amma ba za su zauna a kan kujerar ba.

7. Su waye ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka ce za su rayu a duniya a lokacin sarautar Yesu, kuma mene ne suka gaskata game da bayin Allah na zamanin dā da suka mutu?

7 To, su waye ne za su rayu a duniyar nan? A dā, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun yi imani cewa bayan mutane 144,000 da kuma taro mai girma sun koma sama, sauran miliyoyin mutane da suka rage za su sami zarafin yin rayuwa a ƙarƙashin mulkin Yesu. Ɗaliban Littafi Mai Tsarki ba su sa rai cewa waɗannan miliyoyin mutane za su bauta wa Jehobah kafin Yesu ya soma sarauta ba. Maimakon haka, sun yi zato cewa mutanen za su koya game da Jehobah a lokacin sarautar Yesu. Bayan haka, waɗanda suka yi biyayya ga Jehobah za su sami rai na har abada, amma waɗanda suka ƙi biyayya za su hallaka. Sun kuma yi tsammani cewa wasu da za su yi mulki a duniya a wannan lokacin za su koma sama bayan sarautar Yesu ta shekara dubu. Sun kuma ce waɗannan mutanen sun haɗa da bayin Allah da suka yi rayuwa kafin zamanin Yesu da za su tashi daga matattu.​—Zab. 45:16.

8. Rukuni nawa ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka yi zato cewa akwai?

8 Saboda haka, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun yi tsammani cewa akwai rukuni uku: (1) mutane 144,000 da za su yi sarauta da Yesu a sama. (2) taro mai girma na Kiristoci da ba su da aminci sosai, su ne za su kasance a gaban kujerar mulkin Yesu a sama; da kuma (3) miliyoyin mutane da za a koya musu hanyoyin Jehobah a nan duniya a lokacin sarautar Yesu na shekara dubu. * Amma a kwana a tashi, sai aka soma samun ƙarin haske a kan wannan batun.​—K. Mag. 4:18.

GASKIYA TA ƘARA HASKAKAWA

A taron da aka yi a 1935, mutane da yawa da suke sa ran yin rayuwa a duniya sun yi baftisma (Ka duba sakin layi na 9)

9. (a) A wace hanya ce taro mai girma suke tsaye “a gaban kujerar mulkin da kuma a gaban Ɗan Ragon”? (b) Me ya sa wannan ƙarin haske da aka samu game da annabcin ya fi dacewa?

9 A shekara ta 1935, Shaidun Jehobah sun fahimci ko su waye ne taro mai girma. Sun fahimci cewa taro mai girma ba za su bukaci su je sama kafin su tsaya “a gaban kujerar mulkin da kuma a gaban Ɗan Ragon” ba. Wannan furuci ba abin da zai faru a zahiri ba ne. Ko da yake taro mai girma za su yi rayuwa a duniya, za su tsaya “a gaban kujerar mulkin” ta wajen gaskata cewa Jehobah ne Maɗaukaki da kuma yin biyayya da shi. (Isha. 66:1) Sun tsaya a “gaban Ɗan Ragon” ta wajen yin imani ga hadayar Yesu Kristi. Hakazalika, a littafin Matiyu 25:​31, 32, an ce “za a tara duk mutanen duniya,” har da miyagu “a gaban” kujerar mulkin Yesu Kristi. Hakika, dukan mutanen nan ba sa sama, amma suna duniya. Wannan ƙarin haske ya fi dacewa. Ya bayyana dalilin da ya sa Littafi Mai Tsarki bai ce za a kai taro mai girma sama ba. Rukuni ɗaya ne kawai Allah ya yi musu alkawari cewa za su rayu har abada a sama. Rukunin nan shi ne mutane 144,000, da za su “yi mulki a kan duniya” tare da Yesu.​—R. Yar. 5:10.

10. Me ya sa taro mai girma za su bukaci su koya game da Jehobah kafin Yesu ya soma sarauta?

10 Tun shekara ta 1935, Shaidun Jehobah sun fahimci cewa taro mai girma da Yohanna ya gani a wahayinsa Kiristoci ne masu aminci da suke sa ran yin rayuwa har abada a duniya. Waɗannan Kiristocin za su bukaci su koya game da Jehobah kuma su riƙa bin dokokinsa kafin Yesu ya soma sarautarsa. Za su bukaci su nuna bangaskiya domin su “sami ƙarfin kuɓuce wa dukan waɗannan abubuwan da za su faru” kafin Yesu ya soma sarauta.​—Luk. 21:​34-36.

11. Me ya sa wasu cikin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka yi zato cewa wasu za su koma sama bayan sarautar Yesu ta shekara dubu?

11 A dā, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suna da ra’ayi cewa wasu mutane masu aminci a duniya za su koma sama bayan sarautar Yesu ta shekara dubu. An ambata hakan a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Fabrairu, 1913. Shin hakan daidai ne? A lokacin, wasu sun ce ba zai dace a ba amintattun bayin Allah a zamanin dā ladar yin rayuwa a duniya kaɗai ba, sai kuma a ba Kiristocin da ba su kai su aminci ba ladar yin rayuwa a sama. Sun kasance da wannan ra’ayin domin sun yi zato cewa: (1) taro mai girma za su yi rayuwa a sama, kuma (2) Kiristoci da ba su da aminci sosai za su kasance cikin taro mai girma.

12-13. Mene ne shafaffu da taro mai girma suka sani game da ladarsu?

12 Amma kamar yadda muka koya, tun shekara ta 1935, Shaidun Jehobah sun fahimci cewa mutane da za su tsira a lokacin Armageddon ne taro mai girma da Yohanna ya gani a wahayinsa. Za su “fito daga azabar nan mai zafi” a duniya, kuma za su “tā da babbar murya suna cewa: ‘Ceto ya fito daga wurin Allahnmu ne, wannan da yake a zaune a kujerar mulki da kuma daga wurin Ɗan Ragon!’” (R. Yar. 7:​10, 14) Bugu da ƙari, Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa mutane da aka tayar zuwa sama suna da “abu mafi kyau” fiye da na amintattun bayin Jehobah a zamanin dā. (Ibran. 11:40) Sai ʼyan’uwanmu suka soma gayyatar mutane su bauta wa Jehobah don su rayu har abada a duniya.

13 Taro mai girma suna farin ciki don ladar da suke ɗokin samu. Sun san cewa Jehobah ne zai zaɓi inda bayinsa za su yi masa hidima, wato a sama ko a duniya. Shafaffun Kiristoci da taro mai girma sun san cewa ladar da suke da shi kyauta ce kawai daga Jehobah don hadayar da Ɗansa ya yi a madadinmu, ba domin hakkinsu ba ne.​—Rom. 3:24.

TARON YANA DA GIRMA SOSAI

14. Bayan 1935, me ya sa mutane da yawa suka yi mamaki a kan yadda annabci game da taro mai girma zai cika?

14 Bayan Shaidun Jehobah sun sami ƙarin haske a shekara ta 1935, mutane da yawa sun yi mamaki a kan yadda mutanen da ke sa ran yin rayuwa a duniya za su iya yin yawa har su zama taro mai girma. Alal misali, Ɗan’uwa Ronald Parkin ɗan shekara 12 ne a lokacin da aka sami ƙarin haske a kan taro mai girma. Ya ce: “A lokacin, akwai masu shela kusan 56,000 a faɗin duniya kuma ƙila yawancinsu shafaffu ne. Saboda haka, adadin taro mai girma bai da yawa.”

15. Ta yaya adadin taro mai girma ya bunƙasa?

15 A shekaru da yawa da suka biyo baya, an tura masu wa’azi a ƙasashen waje zuwa ƙasashe da yawa kuma hakan ya bunƙasa adadin Shaidun Jehobah. Sai a shekara ta 1968, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka soma yin amfani da littafin nan Gaskiya Mai Bishe Zuwa Rai Madauwami. Yadda aka bayyana gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki a hanya mai sauƙi ya ratsa zukatan mutane sosai. An yi wa mutane fiye da dubu ɗari biyar baftisma a cikin shekara huɗu. A lokacin, Cocin Katolika ya soma rasa rinjayarsa a Amirka ta Tsakiya da kuma wasu ƙasashe, kuma an cire takunkumin da aka saka wa aikinmu a Gabashin Turai da wasu wurare a Afirka. A sakamakon haka, miliyoyin mutane suka yi baftisma. (Isha. 60:22) Ƙari ga haka, a kwana kwanan nan, ƙungiyar Jehobah ta tanadar da abubuwan da ke taimaka wa mutane su koyi gaskiya. Babu shakka, an sami ƙaruwa a adadin taro mai girma kuma yanzu adadinsu fiye da miliyan takwas ne.

SUN FITO DAGA WURARE DABAM-DABAM

16. Daga ina ne taro mai girma suka fito?

16 A wahayin da Yohanna ya rubuta, ya ce taro mai girma za su fito daga “kowace al’umma, da zuriya, da ƙabila, da yare.” Annabi Zakariya ma ya yi annabci makamancin wannan. Ya ce: “A waɗannan kwanaki mutum goma za su kama hannun rigar mutumin Yahuda. Mutanen nan za su zo daga kowane yare na kowace al’umma suna cewa, ‘Ka bar mu mu bi ka gama mun ji cewa Allah yana tare da ku.’ ”​—Zak. 8:23.

17. Me ake yi yanzu don a taimaka wa mutane daga ƙabilu da harsuna dabam-dabam?

17 Shaidun Jehobah sun san cewa dole ne a yi wa’azi a harsuna da yawa don annabcin ya cika. Mun kwashi sama da shekara 130 muna fassara littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki. A yanzu haka, muna fassara littattafanmu a harsuna fiye da 900 kuma babu wani da ya taɓa yin fassara a harsuna da yawa kamar haka. Babu shakka, Jehobah yana yin mu’ujiza a zamaninmu, wato yana tattara taro mai girma daga dukan ƙabilu. Da yake akwai littattafai a harsuna da yawa, Shaidun Jehobah suna bauta wa Jehobah cikin haɗin kai ko da yake sun fito ne daga ƙasashe dabam-dabam. Bugu da ƙari, an san Shaidun Jehobah da yin wa’azi da ƙwazo da kuma nuna ƙauna ga ʼyan’uwansu. Wannan abu ne mai ban ƙarfafa sosai!​—Mat. 24:14; Yoh. 13:35.

TA YAYA WAHAYIN YA SHAFE MU?

18. (a) Kamar yadda Ishaya 46:​10, 11 suka nuna, me ya sa ba ma mamaki cewa Jehobah ya cika annabci game da taro mai girma? (b) Me ya sa mutanen da ke begen yin rayuwa a duniya ba sa fushi cewa su ba shafaffu ba ne?

18 Hakika, muna da dalilan so mu san ma’anar annabci game da taro mai girma! Ba mu yi mamaki cewa Jehobah ya cika annabcin a hanya mai ban mamaki ba. (Karanta Ishaya 46:​10, 11.) Taro mai girma suna farin ciki don begen da Jehobah ya ba su. Ba sa fushi cewa Allah bai naɗa su da ruhunsa don su yi sarauta da Yesu a sama ba. Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da labaran maza da mata da ruhun Allah ya taimaka musu su cim ma abubuwa da yawa, amma duk da haka, ba sa cikin mutanen nan 144,000. Ɗaya cikinsu Yohanna Mai Baftisma ne. (Mat. 11:11) Wani kuma shi ne Dauda. (A. M. 2:34) Waɗannan mutanen da kuma sauran adalai masu ɗimbin yawa za su tashi daga matattu don su yi rayuwa cikin aljanna a duniyar nan. Dukansu tare da taro mai girma za su sami zarafin nuna amincinsu ga Jehobah kuma su goyi bayan sarautarsa.

19. Wane mataki ne za mu ɗauka idan muka fahimci annabci game da taro mai girma?

19 Yanzu ne lokaci na farko da Allah ya tattara miliyoyin mutane daga dukan ƙasashe don su bauta masa tare. Ko da muna sa ran yin rayuwa a sama ko a duniya, muna bukatar mu taimaka wa mutane da yawa su kasance cikin taro mai girma na “waɗansu tumaki.” (Yoh. 10:16) Nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai kawo ƙunci mai girma don a hallaka dukan gwamnatoci da addinan da ke jawo wa mutane wahala. Babu shakka, dukan taro mai girma suna da gatan bauta wa Jehobah a duniya har abada!​—R. Yar. 7:14.

WAƘA TA 139 Rayuwa a Cikin Aljanna

^ sakin layi na 5 A wannan talifin, za mu tattauna wahayin da manzo Yohanna ya gani game da “taro mai girma.” Babu shakka, wannan talifin zai ƙarfafa bangaskiyar dukan waɗanda suke ɗokin yin rayuwa a duniya.

^ sakin layi na 8 Ka duba littafin nan Jehovah’s Witnesses​—Proclaimers of God’s Kingdom, shafuffuka na 159-163.

^ sakin layi na 67 Lambar nan 1 zuwa 8 tana nufin miliyan 1 zuwa miliyan 8.