Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Shin littafin Mai-Wa’azi 5:8 yana magana ne game da shugabanni ’yan Adam ko kuma Jehobah?
Wannan aya mai ƙayatarwa ta ce: “Idan ka ga ana yi wa talakawa danniya, da yadda ake saɓa adalci da gaskiya, kada ka yi mamaki game da abin da yake faruwa. Gama kowane shugaba yana da shugaban da yake a bisansa, haka ma akwai manyan shugabannin da suke a bisansu duka.”—M. Wa. 5:8.
Idan ba mu yi tunani a kan ra’ayin Jehobah game da wannan ayar ba, muna iya cewa tana magana ne game da hukumomi. Amma idan muka yi tunani sosai, za mu ga cewa ayar tana faɗin wata gaskiya game da Jehobah kuma sanin hakan zai ƙarfafa mu.
Littafin Mai-Wa’azi 5:8 ya yi magana game da wani shugaba da ke yi wa talakawa rashin adalci. Amma shugaban yana bukatar ya tuna cewa akwai wanda ya fi shi iko ko mukami, kuma yana ganin abubuwan da yake yi. Ban da haka ma, akwai waɗanda suka fi shi matsayi. Amma abin taƙaici, gwamnatocin ’yan Adam ba sa yin adalci, kuma hakan yana sa mutane shan wahala.
Amma ko da ana yi mana rashin adalci sosai, sanin cewa Jehobah yana lura da abubuwan da shugabanni suke yi zai ƙarfafa mu. Muna iya roƙan Allah ya taimaka mana. (Zab. 55:22; Filib. 4:6, 7) Mun san cewa “idanun Yahweh suna kai da kawowa ko’ina a duniya domin ya ƙarfafa waɗanda suka dogara gare shi da zuciya ɗaya.”—2 Tar. 16:9.
Don haka, littafin Mai-Wa’azi 5:8 ya tuna mana abubuwan da ke faruwa a duniya, kuma ya tuna mana cewa akwai shugaba mafi iko. Amma mafi muhimmanci, ayar ta taimaka mana mu ga cewa Jehobah ne ya fi iko domin shi ne Maɗaukaki. Yanzu yana yin amfani da Ɗansa, Yesu Kristi don ya yi mulki. Jehobah Maɗaukaki, mai adalci ne, yana ganin dukan abubuwan da ke faruwa, kuma Ɗansa ma yana da irin halayensa.