Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 38

Ka Yi Amfani da Zarafin da Kake da Shi Yanzu

Ka Yi Amfani da Zarafin da Kake da Shi Yanzu

“Ƙasar tana zaman lafiya. Babu yaƙoƙi a lokacin, gama Yahweh ya ba shi zaman salama.”​—2 TAR. 14:6.

WAƘA TA 60 Domin Su Sami Ceto

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. A wane lokaci ne yake iya yi mana wuya mu bauta wa Jehobah?

A WANE lokaci ne kake ganin zai fi wuya ka bauta wa Jehobah? Kana ganin a lokacin da kake da matsaloli ne ko kuma lokacin da ba ka da wata matsala? Yana da sauƙi mu dogara ga Jehobah sa’ad da muke fuskantar matsaloli. Amma mene ne muke yi sa’ad da ba mu da matsala? Shin muna mantawa cewa yana da muhimmanci mu bauta wa Jehobah? Jehobah ya yi wa Isra’ilawa gargaɗi cewa hakan yana iya faruwa.​—M. Sha. 6:​10-12.

Sarki Asa ya ɗauki mataki a kan bauta ta ƙarya (Ka duba sakin layi na 2) *

2. Wane misali ne Sarki Asa ya kafa?

2 Sarki Asa mutum ne da ya kafa misali mai kyau a yin dogara ga Jehobah sosai. Ya bauta wa Jehobah a mawuyanci lokaci da kuma a lokacin da akwai zaman lafiya. Tun Sarki Asa yana ƙarami, “ya miƙa zuciyarsa gaba ɗaya ga Yahweh.” (1 Sar. 15:14) Hanya ɗaya da Sarki Asa ya nuna cewa yana da aminci ga Jehobah ita ce ta wajen hana mutane bautar gumaka a Yahudiya. Littafi Mai Tsarki ya ce Sarki Asa “ya kawar da bagaden allolin kabilu da wuraren yin sujada da ba su dace ba. Ya rushe duwatsun sujada, ya kuma sassare gumakan Ashera.” (2 Tar. 14:​3, 5) Ƙari ga haka, ya cire kakarsa Ma’aka daga zama sarauniya. Me ya sa ya yi haka? Domin tana ƙarfafa mutane su bauta wa gunki.​—1 Sar. 15:​11-13.

3. Me za mu tattauna a wannan talifin?

3 Ba kawar da bautar ƙarya kaɗai Asa ya yi ba. Ya taimaka wa mutane a Yahudiya su soma bauta wa Jehobah. Jehobah ya albarkaci Asa da kuma Isra’ilawa kuma suka sami zaman lafiya a ƙasarsu. * Asa ya yi shekara goma yana sarauta kuma a lokacin “ƙasar tana zaman lafiya.” (2 Tar. 14:​1, 4, 6) A wannan talifin, za mu tattauna yadda Asa ya yi amfani da wannan lokacin zaman lafiya. Ƙari ga haka, za mu tattauna yadda za mu yi koyi da Kiristoci a ƙarni na farko waɗanda suka bi misalin Asa. A ƙarshe, za mu amsa wannan tambayar: Idan kana zama a ƙasar da kake da ’yancin bauta wa Jehobah, ta yaya za ka yi amfani da wannan zarafin da kyau?

YADDA ASA YA YI AMFANI DA LOKACIN ZAMA LAFIYA

4. Kamar yadda 2 Tarihi 14:​2, 6, 7 suka nuna, ta yaya Asa ya yi amfani da lokacin zaman lafiya?

4 Karanta 2 Tarihi 14:​2, 6, 7Asa ya gaya wa Isra’ilawa cewa Jehobah ne ya ba su “zaman” lafiya. Asa bai yi tunanin cewa wannan lokacin salama, lokaci ne na hutu ba. A maimakon haka, ya soma gina birane da katanga da hasumiyoyi da ƙofofi. Ya gaya wa mutanen Yahudiya cewa: “Wannan ƙasar tamu ce har yanzu.” Mene ne Asa yake nufi da wannan furucin? Yana nufin cewa mutanen za su sami ’yanci a ƙasarsu. Za su yi gini a ƙasar ba tare da wani ya taƙura musu ba. Ya ƙarfafa mutanen su yi amfani da wannan zarafin da kyau.

5. Me ya sa Asa ya ƙarfafa sojojinsa?

5 Ƙari ga haka, Asa ya yi amfani da wannan zarafin don ya ƙarfafa sojojinsa. (2 Tar. 14:8) Hakan yana nufin cewa bai dogara ga Jehobah ba ne? A’a. A maimakon haka, Asa ya san cewa shi ne yake da hakkin shirya mutanen don matsalolin da za su iya fuskanta a nan gaba. Asa ya san cewa zaman lafiya a ƙasar ba za ta jure ba.

ABIN DA KIRISTOCI A ƘARNI NA FARKO SUKA YI

6. Ta yaya Kiristoci a ƙarni na farko suka yi amfani da lokacin zaman lafiya?

6 Ko da yake an tsananta wa Kiristoci a ƙarni na farko, akwai lokacin da suka yi zaman lafiya. Ta yaya manzannin suka yi amfani da wannan zarafin? Waɗannan mutane masu aminci sun yi wa’azi da ƙwazo sosai. Littafin Ayyukan Manzanni ya ce sun yi “rayuwa a cikin tsoron Ubangiji.” Sun ci gaba da yin wa’azi da ƙwazo kuma hakan ya sa sun “ƙaru sosai.” Babu shakka, Jehobah ya albarkaci wa’azinsu a wannan lokacin zaman lafiya.​—A. M. 9:​26-31.

7-8. Mene ne Bulus da sauran Kiristoci suka yi sa’ad da suka sami zarafi? Ka bayyana.

7 Kiristoci a ƙarni na farko sun yi amfani da dukan zarafin da suka samu don su yi wa’azi game da Mulkin Allah. Alal misali, sa’ad da Bulus ya ga cewa zai iya yi wa mutane da yawa wa’azi a Afisa, ya yi amfani da zarafin kuma ya taimaka wa mutane su bauta wa Allah.​—1 Kor. 16:​8, 9.

8 A shekara ta 49, Bulus da wasu Kiristoci sun sami zarafin yi wa mutane wa’azi sa’ad da aka sasanta batun kaciya. (A. M. 15:​23-29) Bayan an sanar da ikilisiyoyi game da shawarar da aka yanke, almajiran Yesu sun saka ƙwazo a “yin shelar kalmar Ubangiji.” (A. M. 15:​30-35) Wane sakamako aka samu? Littafi Mai Tsarki ya ce “jama’ar masu bi suka ƙara ƙarfi cikin bangaskiya, suna ƙara yawa kowace rana.”​—A. M. 16:​4, 5.

YIN AMFANI DA LOKACIN ZAMAN LAFIYA A YAU

9. Wane zarafi ne muke da shi a ƙasashe da yawa a yau, kuma wace tambaya ce muke bukatar mu yi wa kanmu?

9 A ƙasashe da yawa, muna da ’yancin yin wa’azi. Kana zama a irin wannan ƙasar ne? Idan haka ne, ka tambayi kanka, ‘Ta yaya nake yin amfani da wannan ’yancin?’ A wannan kwanaki na ƙarshe, bayin Jehobah suna saka ƙwazo a yin wa’azi da koyar da mutane a faɗin duniya. (Mar. 13:10) Da akwai abubuwa da yawa da za mu iya yi.

Mutane da yawa suna samun albarka sosai don suna wa’azi a wata ƙasa ko kuma a wani yare (Ka duba sakin layi na 10-12) *

10. Mene ne 2 Timoti 4:2 ta ƙarfafa mu mu yi?

10 Ta yaya za mu yi amfani da lokacin zaman lafiya? (Karanta 2 Timoti 4:2.) Kana iya bincika yanayinka don ka ga ko kai ko kuma wani a iyalinka yana iya ƙara ƙwazo a wa’azi. Yanzu ba lokacin neman abin duniya ba ne, domin ba za su amfane mu a lokacin ƙunci mai girma ba.​—K. Mag. 11:4; Mat. 6:​31-33; 1 Yoh. 2:​15-17.

11. Mene ne wasu suka yi don su yi wa mutane da yawa wa’azi?

11 Masu shela da yawa sun koyi sabon yare don su yi wa mutane wa’azi da kuma koyar da su. Ƙungiyar Jehobah ta yi tanadin abubuwa da yawa a harsuna dabam-dabam don ta taimaka mana mu ƙara ƙwazo a wa’azi. Alal misali, a shekara ta 2010, muna da littattafai a harsuna wajen 500, amma a yau, adadin ya ƙaru zuwa fiye da harsuna 1,000!

12. Ta yaya mutane suke amfana idan suka ji wa’azi a yarensu? Ka ba da misali.

12 Yaya mutane suke ji sa’ad da aka yi musu wa’azi a yarensu? Ka yi la’akari da labarin wata ’yar’uwa da ta amfana daga taron yanki da aka yi a birnin Memphis da ke jihar Tennessee a Amirka. An yi taron da yaren Kinyarwanda wanda ake yi a ƙasar Ruwanda da Kwango Kinshasa da kuma Yuganda. Bayan taron, ’yar’uwar ta ce: “Wannan ne lokaci na farko da na fahimci taron yanki tun shekara 17 da na koma Amirka.” Hakika, wannan taro da aka yi da yaren ’yar’uwar ya ratsa zuciyarta. Za ka iya koyan wani yaren don ka taimaka a wani yankin da ake da bukata? Hakan zai dace musamman idan a yankinku akwai mutanen da suke yin wani yare. Yin hakan zai sa ka farin ciki.

13. Ta yaya ’yan’uwa a Rasha suka yi amfani da zarafin da suka samu?

13 Ba dukan ’yan’uwa ba ne suke da ’yancin yin wa’azi a sāke ba. A wasu ƙasashe, ’yan’uwa ba sa iya yin wa’azi domin gwamnati ta saka wa aikinmu taƙunƙumi. Alal misali, an yi shekaru ana tsananta wa ’yan’uwanmu a Rasha. Amma a watan Maris 1991, an ɗage taƙunƙumin. A lokacin, akwai Shaidu wajen 16,000 a ƙasar Rasha. Bayan shekara ashirin, adadin ya ƙaru zuwa fiye da 160,000! Hakika, ’yan’uwanmu sun yi amfani da ’yancin yin wa’azi da suka samu da kyau. Amma wannan ’yancin bai daɗe ba. Duk da cewa yanayinsu ya canja, sun ci gaba da bauta wa Jehobah da ƙwazo.

LOKACIN ZAMAN LAFIYA BA ZAI DAƊE BA

Sarki Asa ya yi addu’a ga Jehobah sosai, kuma Jehobah ya taimaka masa ya ci maƙiyansa a yaƙi (Ka duba sakin layi na 14-15)

14-15. Ta yaya Jehobah ya taimaka wa Asa?

14 Akwai lokacin da aka daina zaman lafiya a zamanin Asa. Sojoji fiye da miliyan ɗaya na Habasha sun kai musu hari. Kwamandan sojojin mai suna Zerah yana da tabbaci cewa shi da sojojinsa za su ci Yahudiya a yaƙi. Amma Sarki Asa ya dogara ga Jehobah ba ga adadin sojojinsa ba. Asa ya yi addu’a cewa: “Ka taimake mu, ya Yahweh Allahnmu, gama muna dogara a gare ka! Ya Yahweh, a cikin Sunanka muka zo domin mu fuskanci rundunar dubban sojojin nan.”​—2 Tar. 14:11.

15 Duk da cewa sojojin Habasha sun kusan ninka sojojin Asa, ya san cewa Jehobah yana da iko sosai kuma zai iya taimaka wa mutanensa. Jehobah ya taimaka wa mutanensa kuma suka ci sojojin Habasha a yaƙi.​—2 Tar. 14:​8-13.

16. Ta yaya muka san cewa lokacin zaman lafiya zai ƙare?

16 Ko da yake ba mu san abin da zai faru da mu a nan gaba ba, amma mun san cewa ’yancin da bayin Allah suke da shi na ɗan lokaci ne. Yesu ya annabta cewa a kwanaki na ƙarshe, “duniya duk za ta ƙi” mabiyansa. (Mat. 24:9) Ƙari ga haka, manzo Bulus ya ce “duk wanda yake so ya yi rayuwa irin hali na Allah a cikin Almasihu Yesu zai sha tsanani.” (2 Tim. 3:12) Shaiɗan yana “fushi” sosai kuma ba zai yiwu mu yi tunanin cewa fushinsa ba zai shafe mu ba.​—R. Yar. 12:12.

17. A waɗanne hanyoyi ne za a iya jarraba bangaskiyarmu?

17 Nan ba da daɗewa ba, za a jarraba bangaskiya dukanmu. Za a yi ƙunci mai girma, wato “wata azaba mai zafi irin wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har zuwa yanzu.” (Mat. 24:21) A wannan lokacin, danginmu suna iya tsananta mana kuma gwamnati tana iya saka wa aikinmu taƙunƙumi. (Mat. 10:​35, 36) Za ka dogara ga Jehobah don ya kāre ka yadda Asa ya yi kuwa?

18. Kamar yadda Ibraniyawa 10:​38, 39 suka nuna, me zai taimaka mana mu yi shiri don abubuwan da za su faru a nan gaba?

18 Jehobah yana shirya mu don abubuwan da za su faru a nan gaba. Yana yi wa “bawan nan mai aminci, mai hikima” ja-goranci don ya tanadar da abinci “a kan lokaci.” (Mat. 24:45) Amma muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ƙarfafa bangaskiyarmu ga Jehobah.​—Karanta Ibraniyawa 10:​38, 39.

19-20. Bayan mun karanta 1 Tarihi 28:​9, me ya kamata mu tambayi kanmu, kuma me ya sa?

19 Muna bukatar mu “nemi” Jehobah kamar yadda Asa ya yi. (2 Tar. 14:4; 15:​1, 2) Za mu yi hakan ta wajen koya game da shi da kuma yin baftisma. Muna yin amfani da dukan zarafin da muke da shi don mu daɗa ƙaunar Jehobah. Don mu san ko muna yin hakan, muna iya tambayar kanmu, ‘Ina halartan taron ikilisiya a kai a kai kuwa?’ Idan mun halarci taron ikilisiya, muna samun ƙarfafawa daga ’yan’uwanmu don mu ci gaba da bauta wa Jehobah. (Mat. 11:28) Muna kuma iya wa kanmu tambayoyin nan, ‘Shin ina nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai kuwa?’ Idan kana tare da iyalinka, shin kana keɓe lokaci a kowane mako don yin ibada ta iyali? Ko kuma idan ba ka da aure, kana keɓe lokacin yin nazari? Kuma kana yin wa’azi da ƙwazo sosai kuwa?

20 Me ya sa muke bukatar mu yi waɗannan tambayoyin? Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah yana bincika zuciyarmu kuma ya kamata mu ma mu riƙa yin hakan. (Karanta 1 Tarihi 28:9.) Idan mun lura cewa muna bukatar mu yi wasu canje-canje a salon rayuwarmu ko maƙasudanmu ko kuma tunaninmu, zai dace mu roƙi Jehobah ya taimaka mana. Yanzu ne ya kamata mu shirya kanmu don abubuwan da za mu fuskanta a nan gaba. Kada ka bar wani abu ya hana ka yin amfani da zarafin da kake da shi yanzu da kyau!

WAƘA TA 62 Sabuwar Waƙa

^ sakin layi na 5 Shin kana zama a ƙasar da kake da ’yancin bauta wa Jehobah? Idan haka ne, kana amfani da wannan zarafin kuwa? Wannan talifin zai taimaka maka ka yi koyi da Sarki Asa na Yahudiya da kuma Kiristoci a ƙarni na farko. Sun yi amfani da lokacin da suke da ’yancin bauta wa Jehobah da kyau.

^ sakin layi na 3 MA’ANAR WASU KALMOMI: Kalmar nan “zaman lafiya” tana nufin zama cikin lumana ba tare da yaƙi ba. A Ibraniyanci, kalmar tana kuma nufin ƙoshin lafiya da rigakafi da kuma kwanciyar rai.

^ sakin layi na 57 BAYANI A KAN HOTUNA: Sarki Asa ya tsige kakarsa daga matsayinta domin tana ƙarfafa mutane su bauta wa allolin ƙarya. Masu goyon bayan Asa sun bi misalinsa kuma sun halaka gumaka.

^ sakin layi na 59 BAYANI A KAN HOTUNA: Wasu ma’aurata masu ƙwazo sun sauƙaƙa rayuwarsu don su yi hidima a inda ake da bukata sosai.