Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 37

“Kada Ka Naɗa Hannuwanka”

“Kada Ka Naɗa Hannuwanka”

“Da safe ka shuka hatsinka, da yamma kada ka naɗa hannuwanka.”​—M. WA. 11:6.

WAƘA TA 68 Mu Taimaki Mutane Su Bauta wa Jehobah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Ta yaya Mai-Wa’azi 11:6 take magana game da yin wa’azi?

A WASU ƙasashe, mutane da yawa suna so a yi musu wa’azi. Suna ma ɗokin ganin wani ya zo ya yi musu wa’azi! A wasu ƙasashen kuma, mutane ba sa saurarawa. A ƙasarku fa? Mutane suna saurarawa kuwa? Ko da yaya yake, Jehobah yana so mu ci gaba da wa’azi har sai ya ce ya isa.

2 Jehobah ya ƙayyade lokacin da za a daina wa’azi, sa’an nan “ƙarshen” zai zo. (Mat. 24:​14, 36) Kafin wannan lokacin, ta yaya za mu bi umurnin nan “kada ka naɗa hannuwanka”? *​—Karanta Mai-Wa’azi 11:6.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 A talifin da ya gabata, an tattauna abubuwa huɗu da muke bukatar mu yi don mu ƙware a yin wa’azi. (Mat. 4:19) A wannan talifin, za mu tattauna hanyoyi uku da za mu ƙuduri niyyar ci gaba da yin wa’azi ko da wace matsala ce muke fuskanta. Za mu koya abin da ya sa yake da muhimmanci mu (1) guji barin wani abu ya raba hankalinmu, (2) zama masu haƙuri, da kuma (3) kasancewa da bangaskiya sosai.

KADA KA BAR WANI ABU YA RABA HANKALINKA

4. Me ya sa ya kamata mu mai da hankali ga aikin da Jehobah ya ce mu yi?

4 Yesu ya annabta abubuwan da za su nuna cewa muna kwanaki na ƙarshe. Kuma ya san cewa waɗannan abubuwa suna iya hana mabiyansa mai da hankali ga yin wa’azi. Yesu ya gaya wa almajiransa su “zauna da shiri.” (Mat. 24:42) A zamanin Nuhu, akwai abubuwa da yawa da suka hana mutane jin wa’azi. Irin waɗannan abubuwa suna iya raba hankalinmu a yau. (Mat. 24:​37-39; 2 Bit. 2:5) Shi ya sa ya kamata mu mai da hankali ga aikin da Jehobah ya ce mu yi.

5. Ta yaya littafin Ayyukan Manzanni 1:​6-8 ya kwatanta yawan yadda za a yi wa’azi?

5 A yau, muna bukatar mu mai da hankali ga yin wa’azi. Yesu ya ce mabiyansa za su ci gaba da yin wa’azi bayan ya mutu. Kuma za su yi hakan fiye da yadda ya yi. (Yoh. 14:12) Wasu cikin almajiran Yesu sun koma aikinsu na kamun kifi bayan ya rasu. Bayan an ta da Yesu daga mutuwa, ya yi wata mu’ujiza kuma ya taimaka ma wasu cikin almajiransa su kama kifaye da yawa. Ya yi amfani da wannan lokacin don ya nanata musu muhimmancin yin wa’azi da koyar da mutane. (Yoh. 21:​15-17) Kafin Yesu ya koma sama, ya gaya wa almajiransa cewa ba a Isra’ila kaɗai za su yi wannan wa’azin ba. (Karanta Ayyukan Manzanni 1:​6-8.) Bayan shekaru da yawa, Yesu ya nuna wa manzo Yohanna wahayin abin da zai faru a “ranar Ubangiji.” * Ɗaya cikin abubuwan da Yohanna ya gani shi ne wahayi mai ban mamaki da wani mala’ika yake shelar “madawwamin saƙo na labari mai daɗi” ga “kowace al’umma, da zuriya, da yare, da kabila.” (R. Yar. 1:10; 14:6) Hakan ya nuna cewa, Jehobah yana so mu yi wannan aikin a faɗin duniya har sai ya ce ya isa.

6. Ta yaya za mu mai da hankali ga yin wa’azi?

6 Za mu mai da hankali ga yin wa’azi idan muka yi tunani game da duk abubuwan da Jehobah yake yi don ya taimaka mana. Alal misali, Jehobah yana tanadar mana da abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarmu da shi. Hakan ya ƙunshi littattafai da aka buga da waɗanda ke na’ura da faifai da bidiyoyi da kuma shirye-shiryen JW. Ka yi tunanin wannan, a dandalinmu, an fassara abubuwa a harsuna fiye da 1,000! (Mat. 24:​45-47) A duniyar nan, mutane ba su da haɗin kai domin suna goyon bayan jam’iyyun siyasa dabam-dabam da addinai, kuma wasu mutane suna da arziki, wasu kuma talakawa ne. Amma bayin Jehobah fiye da miliyan takwas a duniya suna da haɗin kai. Alal misali, a ranar Jumma’a, 19 ga Afrilu 2019, Shaidun Jehobah a faɗin duniya sun saurari tattaunawar nassin yini a bidiyo. Da yamman nan, mutane 20,919,041 sun taru don su Tuna da Mutuwar Yesu. Ya kamata yin tunani a kan gatan da muke da shi na ganin waɗannan abubuwa masu ban al’ajabi, ya motsa mu mu daɗa ƙwazo a wa’azi.

Yesu bai bar kome ya raba hankalinsa a yin wa’azi ba (Ka duba sakin layi na 7)

7. Ta yaya yin koyi da Yesu zai taimaka mana mu ci gaba da yin wa’azi?

7 Wata hanya da za mu mai da hankali ga yin wa’azi ita ce ta yin koyi da Yesu. Bai bar wani abu ya raba hankalinsa ga yin wa’azi ba. (Yoh. 18:37) Bai faɗa cikin tarkon Shaiɗan sa’ad da ya ce zai ba shi “dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu.” Ban da haka, Yesu bai amince ba sa’ad da mutane suke so su naɗa shi sarki. (Mat. 4:​8, 9; Yoh. 6:15) Yesu bai bar mutane su rinjaye shi da abin duniya ba, kuma tsanantawa bai hana shi yin wa’azi ba. (Luk. 9:58; Yoh. 8:59) Sa’ad da ake jarraba mu, za mu mai da hankali ga yin wa’azi idan muka tuna shawarar manzo Bulus. Ya gaya wa Kiristoci su yi koyi da Yesu don ‘kada su gaji, ko kuwa su fid da zuciya’!​—Ibran. 12:3.

KA ZAMA MAI HAƘURI

8. Mene ne haƙuri, kuma me ya sa muke bukatar halin yanzu?

8 Masu haƙuri suna jimrewa har sai wani yanayi ya canja. Muna bukatar haƙuri idan muna jiran ƙarshen wani mugun yanayi ko kuma wani abu mai kyau ya faru. Annabi Habakkuk ya yi ɗokin ganin lokacin da mugunta zai ƙare a Yahuda. (Hab. 1:2) Almajiran Yesu sun yi zato cewa Mulkin “zai bayyana nan da nan” kuma ya cece su daga hannun Romawa. (Luk. 19:11) Muna ɗokin ranar da Mulkin Allah zai kawar da mugunta kuma ya kawo sabuwar duniya, inda masu adalci za su kasance. (2 Bit. 3:13) Duk da haka, muna bukatar mu jira lokacin da Jehobah zai yi hakan. Ga wasu hanyoyi da Jehobah yake koya mana mu zama masu haƙuri.

9. Waɗanne misalai ne suka nuna mana cewa Jehobah mai haƙuri ne?

9 Jehobah mai haƙuri ne sosai. Ya ba Nuhu isashen lokaci don ya gina jirgi kuma ya yi “wa’azin adalci.” (2 Bit. 2:5; 1 Bit. 3:20) Sa’ad da Jehobah ya ce zai halaka Saduma da Gwamarata, Ibrahim ya yi masa tambayoyi kuma Jehobah ya saurare shi. (Far. 18:​20-33) Jehobah ya daɗe yana haƙuri sosai da al’ummar Isra’ila masu taurin kai. (Neh. 9:​30, 31) A yau ma Jehobah yana ba ’yan Adam lokaci don su “tuba.” (2 Bit. 3:9; Yoh. 6:44; 1 Tim. 2:​3, 4) Yin koyi da Jehobah zai taimaka mana mu riƙa haƙuri yayin da muka ci gaba da yin wa’azi da koyarwa. Ban da haka, ya yi amfani da wani kwatanci da ke Kalmarsa don ya koya mana mu riƙa haƙuri.

Kamar manomi mai haƙuri, muna jiran samun sakamako mai kyau daga aikinmu (Ka duba sakin layi na 10-11)

10. Mene ne misalin manomi da ke Yaƙub 5:​7, 8, ya koya mana?

10 Karanta Yaƙub 5:​7, 8Yin noma yana koya mana yin haƙuri. Hakika, wasu shuke-shuke suna girma da sauri. Amma yawancinsu, musamman itatuwa suna ɗaukan shekaru sosai kafin su yi girma. Shuke-shuke a Isra’ila suna ɗaukan wata shida kafin su yi girma. Manomi yakan shuka iri bayan an yi ruwan sama na farko kuma ya yi girbi bayan damina. (Mar. 4:28) Zai dace mu yi koyi da yadda manomi yake haƙuri. Amma hakan ba shi da sauƙi.

11. Ta yaya haƙuri zai taimaka mana a hidimarmu?

11 ’Yan Adam suna so su sami amfanin aikinsu nan da nan. Amma idan muna so gonarmu ta ba da amfani, muna bukatar mu yi huɗa da dasa iri da noma da kuma ban-ruwa. Hakazalika, idan muna so mutane su bauta wa Jehobah, wajibi ne mu yi aiki sosai. Koya wa ɗalibi ya daina nuna wariya da ƙabilanci yana ɗaukan lokaci sosai. Yin haƙuri zai hana mu sanyin gwiwa sa’ad da muke fuskantar matsaloli. Ko da mutane sun saurare mu, muna bukatar mu zama masu haƙuri. Ba za mu iya tilasta wa ɗalibi ya kasance da bangaskiya ba. A wasu lokuta, har almajiran Yesu ba su fahimci ma’anar koyarwarsa ba. (Yoh. 14:9) Ya kamata mu riƙa tuna cewa mu ne ke yin shuki da ban-ruwa, amma Allah ne yake sa ya yi girma.​—1 Kor. 3:6.

12. Ta yaya za mu zama masu haƙuri sa’ad da muke wa danginmu wa’azi?

12 Kasancewa da haƙuri zai iya yi mana wuya sa’ad da muke yi wa danginmu da ba Shaidu ba wa’azi. Ƙa’idar da ke Mai-Wa’azi 3:​1, 7, za ta iya taimaka mana. Ayoyin sun ce: “Akwai lokacin yin shiru, da lokacin yin magana.” Halayenmu masu kyau suna iya sa danginmu su saurare mu, amma wajibi ne mu kasance a shirye mu riƙa gaya musu game da Jehobah. (1 Bit. 3:​1, 2) Ya kamata mu yi haƙuri da dukan mutane da muke wa wa’azi har da danginmu ma.

13-14. Waɗanne misalai ne za mu iya yin koyi da su?

13 Za mu iya koyan yin haƙuri daga misalan bayin Jehobah na dā masu aminci da kuma na yanzu. Habakkuk ya yi ɗokin lokacin da za a kawo ƙarshen mugunta amma ya yi haƙuri kuma ya ce: “Zan haura domin in duba, in tsaya a kan gini mai tsayi, in duba.” (Hab. 2:1) Manzo Bulus ya ce yana so ya “kammala” hidimarsa. Duk da haka ya ci gaba da “shaida labari mai daɗi.”​—A. M. 20:24.

14 Ka yi la’akari da labarin wasu ma’aurata da suka sauke karatu daga Makarantar Gilead kuma aka tura su wa’azi a ƙasar da babu Shaidu sosai. Yawancin mutane a ƙasar ba Kiristoci ba ne kuma da yawa a cikinsu ba sa so a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Amma yawancin abokan ajinsu a Gilead suna tura musu labarai game da ɗalibansu. Sun ci gaba da wa’azi duk da cewa yawanci a yankinsu ba sa saurarar su. Bayan sun yi shekaru takwas suna wa’azi a wannan yankin, sun yi farin cikin ganin ɗaya cikin ɗalibansu ta yi baftisma. Wace alaƙa ce ke tsakanin bayin Jehobah na dā da na yau? Waɗannan bayin Jehobah masu aminci ba su daina ƙwazo ba kuma ba su yi sanyin gwiwa ba. A sakamakon haka, Jehobah ya albarkace su sosai. Bari mu yi koyi da “waɗanda suka ba da gaskiya, suka yi haƙuri har suka karɓi abin da Allah ya yi alkawari zai ba su.”​—Ibran. 6:​10-12.

KA KASANCE DA BANGASKIYA SOSAI

15. A wace hanya ɗaya ce bangaskiya ke ƙarfafa mu mu yi wa’azi?

15 Mun gaskata da saƙon da muke wa’azin sa. Saboda haka, muna ɗokin gaya wa mutane da yawa saƙon. Mun gaskata da alkawuran da ke cikin Kalmar Allah. (Zab. 119:42; Isha. 40:8) Ban da haka, muna ganin cikar annabcin Littafi Mai Tsarki a zamaninmu. Mun ga yadda mutane suka kyautata rayuwarsu sa’ad da suka soma bin shawarar Littafi Mai Tsarki. Hakan ya taimaka mana mu gaskata cewa ya kamata kowa ya ji wa’azi game da Mulkin Allah.

16. Ta yaya Zabura 46:​1-3 suka nuna cewa yin imani da Jehobah da Yesu zai sa mu daɗa ƙwazo a wa’azi?

16 Mun kuma yi imani da Allahn da ke da saƙon da muke wa’azi a kai da kuma Ɗansa, Yesu da ya naɗa a matsayin Sarkin Mulkinsa. (Yoh. 14:1) Jehobah zai ci gaba da zama mafakarmu ko da wane yanayi ne muke ciki. (Karanta Zabura 46:​1-3.) Ƙari ga haka, muna da tabbaci cewa Yesu yana mana ja-goranci a wa’azin da muke yi kuma yana amfani da ikon da Jehobah ya ba shi.​—Mat. 28:​18-20.

17. Ka ba da misalin da ya nuna dalilin da ya kamata mu ci gaba da wa’azi.

17 Kasancewa da bangaskiya zai sa mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai albarkace mu a hanyoyi da ba mu yi zato ba. (M. Wa. 11:6) Alal misali a kowace rana, dubban mutane suna ganin tebura ko amalanke da muke ajiye littattafanmu a kai. Ana samun sakamako mai kyau ta wannan hanyar kuwa? Ƙwarai kuwa! Hidimarmu ta Mulki ta Nuwamba 2014 ta ba da labarin wata matashiya da ke makarantar jami’a kuma tana so ta rubuta rahoto game da Shaidun Jehobah. Ba ta iya zuwa Majami’ar Mulki ba, amma ta ga amalanke da ke ɗauke da littattafanmu a makarantarsu. Hakan ya taimaka mata ta samu littafin da za ta yi amfani da shi don rubuta rahotonta. Daga baya ta zama Mashaidiya kuma yanzu tana hidimar majagaba na kullum. Irin labaran nan suna ƙarfafa mu mu ci gaba da wa’azi domin sun nuna cewa da akwai mutane da suke bukatar su ji wa’azi.

KADA KA YI SANYIN GWIWA

18. Me ya sa muke da tabbaci cewa za a gama wa’azi game da Mulkin Allah a lokacin da ya dace?

18 Muna da tabbaci cewa za a gama wa’azi game da Mulkin Allah a lokacin da ya dace. Ka yi la’akari da abin da ya faru a zamanin Nuhu. Jehobah ya nuna cewa yana yin abubuwa a lokacin da ya fi dacewa. Tun shekaru 120 kafin Ambaliyar, Jehobah ya ƙayyade lokacin da hakan zai faru. Shekaru da yawa kafin wannan ambaliyar, Jehobah ya gaya wa Nuhu ya gina jirgin ruwa. Nuhu ya yi wannan aikin wataƙila na tsawon shekara 40 ko 50 kafin a soma Ambaliyar. Duk da cewa mutane sun ƙi saurarar Nuhu, ya ci gaba da idar da saƙon da Jehobah ya ba shi har sai lokacin da ya shigar da dabbobi cikin jirgin ruwan da ya gina. A lokacin da ya dace, “Yahweh ya rufe ƙofar.”​—Far. 6:3; 7:​1, 2, 16.

19. Wace albarka ce za mu samu idan ba mu yi sanyin gwiwa ba?

19 Nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai ce mu daina yin wa’azi. Zai kawar da wannan zamanin kuma ya kawo sabuwar duniya. Kafin wannan lokacin, muna iya yin koyi da Nuhu da Habakkuk da kuma wasu da ba su yi sanyin gwiwa ba. Bari mu ci gaba da mai da hankali ga yin wa’azi, mu zama masu haƙuri kuma mu kasance da bangaskiya sosai cewa Jehobah zai cika alkawuransa.

WAƘA TA 75 ‘Ga Ni! Ka Aike Ni’

^ sakin layi na 5 A talifin da ya gabata an ƙarfafa masu nazarin Littafi Mai Tsarki da suke samun ci gaba su amince da gayyatar Yesu kuma su zama masu yin wa’azi. A wannan talifin, za mu tattauna hanyoyi uku da dukan masu shela za su ƙarfafa ƙudurinsu na ci gaba da yin wa’azi har sai Jehobah ya ce ya isa.

^ sakin layi na 2 MA’ANAR WASU KALMOMI: A wannan talifin, furucin nan “kada ka naɗa hannuwanka” yana nufin cewa ya kamata mu ƙuduri niyya ci gaba da yin wa’azi har sai Jehobah ya ce ya isa.

^ sakin layi na 5 “Ranar Ubangiji” ta soma a lokacin da Yesu ya zama Sarki a shekara ta 1914, kuma za ta ci gaba har ƙarshen Sarautarsa ta Shekara Dubu.