Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 36

Kana a Shirye Ka Sa Mutane Su Soma Bauta wa Jehobah?

Kana a Shirye Ka Sa Mutane Su Soma Bauta wa Jehobah?

“Kada ka ji tsoro, daga yanzu mutane ne za ka dinga kamowa, ba kifi ba.”​—LUK. 5:10.

WAƘA TA 73 Ka Ba Mu Ƙarfin Zuciya

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Wace gayyata ce Yesu ya yi wa wasu masu kamun kifi, kuma mene ne suka yi?

BITRUS da Andarawus da Yaƙub da kuma Yohanna suna aikin kamun kifi. Babu shakka, sun yi mamaki sa’ad da Yesu ya ce musu: “Ku bi ni, zan mai da ku masu jawo mutane zuwa wurina.” Mene ne suka yi? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Nan da nan suka bar kayansu na kamun kifi suka bi shi.” (Mat. 4:​18-22) Wannan mataki da suka ɗauka zai canja rayuwarsu har abada. Maimakon su riƙa kamun kifi, za su riƙa jawo mutane ga Jehobah. (Luk. 5:10) A yau, Yesu yana gayyatar masu zuciyar kirki da suke son gaskiya su riƙa yin hakan. (Mat. 28:​19, 20) Ka amince da wannan gayyatar kuwa?

2. Me ya sa muke bukatar mu ɗauki shawarar zama mai shela da muhimmanci, kuma me zai taimaka mana mu ɗauki wannan matakin?

2 Wataƙila ka daɗe kana nazarin Littafi Mai Tsarki, ka yi canje-canje a rayuwarka kuma yanzu kana so ka yanke shawarar zama mai shela. Kada ka yi sanyin gwiwa idan kana jinkirin amincewa da gayyatar Yesu. Da yake kana jinkiri, hakan ya nuna cewa ka san muhimmancin wannan shawara. Littafi Mai Tsarki ya ce “nan da nan” Bitrus da abokansa suka bar kayansu na kamun kifi. Amma Bitrus da ɗan’uwansa ba su yanke wannan shawarar da garaje ba. Sun san Yesu fiye da watanni shida kafin lokacin, kuma sun amince cewa shi ne Almasihu. (Yoh. 1:​35-42) Hakazalika, wataƙila ka koya game da Jehobah da Yesu, kuma kana so ka ci gaba da kusantar su. Amma kada ka yanke wannan shawarar ba tare da yin tunani ba. Mene ne ya taimaka wa Bitrus da Andarawus da kuma sauran su yanke wannan shawarar?

3. Waɗanne halaye ne za su taimaka maka ka amince da gayyatar Yesu?

3 Almajiran Yesu na farko suna da ƙwazo da ilimi da ƙarfin zuciya da kuma kamun kai. Hakika waɗannan halayen sun taimaka musu su zama ƙwararrun masu wa’azi. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za ka iya kasancewa da waɗannan halaye don ka ƙware a yin wa’azi da koyar da mutane.

KA KASANCE DA ƘWAZON YIN WA’AZI

Bitrus da abokansa sun zama masu wa’azi. Har yanzu muna yin wannan aiki mai muhimmanci (Ka duba sakin layi na 4-5)

4. Mene ne ya sa Bitrus ya zama mai kamun kifi?

4 Bitrus bai yi aikin kamun kifi don kawai ya biya bukatun iyalinsa ba, amma don yana son aikin. (Yoh. 21:​3, 9-15) Ya kuma so yi wa mutane wa’azi. Jehobah ya taimaka masa ya ƙware a yin wannan aikin.​—A. M. 2:​14, 41.

5. Kamar yadda Luka 5:​8-11 suka nuna, me ya sa Bitrus ya ji tsoro, kuma mene ne zai taimaka mana mu daina jin hakan?

5 Muna wa’azi domin muna ƙaunar Jehobah, wannan shi ne dalili mafi muhimmanci na yin wannan aikin. Ƙaunarmu ga Jehobah za ta sa mu yi wa mutane wa’azi ko da muna ganin cewa ba mu cancanci yin hakan ba. Sa’ad da Yesu ya gayyaci Bitrus ya zama almajirinsa, ya gaya masa cewa: “Kada ka ji tsoro.” (Karanta Luka 5:​8-11.) Bitrus bai ji tsoron abin da zai faru idan ya zama mabiyin Yesu ba. A maimakon haka, ya yi mamaki sa’ad da Yesu ya yi mu’ujiza don ya taimaka musu su kama kifi da yawa, hakan sa ya ji cewa bai cancanci yin aiki tare da Yesu ba. Kamar Bitrus, kana iya ganin cewa ba ka cancanci zama almajirin Yesu ba, sa’ad da ka fahimci abin da yin hakan ya ƙunsa. Idan haka ne, ka daɗa ƙaunar Jehobah da Yesu da maƙwabcinka, yin hakan zai motsa ka ka amince da gayyatar Yesu na yin wa’azi.​—Mat. 22:​37, 39; Yoh. 14:15.

6. Wane dalili ne kuma yake sa mu wa’azi?

6 Ka yi la’akari da wasu dalilai da suka sa muke wa’azi. Muna bin umurnin Yesu cewa: “Ku je . . . ku sa su zama almajiraina.” (Mat. 28:​19, 20) Ban da haka, muna wa’azi domin mutane “suna shan wahala kuma ba mai taimako” su. Don haka, suna bukatar su koyi gaskiya game da Mulkin Allah. (Mat. 9:36) Jehobah yana so dukan mutane su san gaskiya domin su sami ceto.​—1 Tim. 2:4.

7. Ta yaya Romawa 10:​13-15 suka nuna cewa yin wa’azi yana da muhimmanci?

7 Za mu so yin wa’azi idan muka yi tunanin yadda yin hakan zai ceci mutane. Mai kamun kifi yana sayar da kifin da ya kama ko kuma ya ci shi. Amma muna ‘kama’ mutane, wato sa su zama almajiran Yesu don su sami ceto.​—Karanta Romawa 10:​13-15; 1 Tim. 4:16.

KA KYAUTATA YADDA KAKE WA’AZI

8-9. Mene ne mai kamun kifi yake bukatar ya sani, kuma me ya sa?

8 A zamanin Yesu, Ba’isra’ile mai kamun kifi yana bukatar ya san irin kifin da yake so ya kama. (L. Fir. 11:​9-12) Ban da haka, yana bukatar ya san wurin da zai samu kifin. Kifaye suna yawan zama a ruwan da suke so kuma suke samun abinci. Lokacin da mai kamun kifin yake zuwa aiki ma yana da muhimmanci. Wani ɗan’uwan da ke wa’azi a tsibirin Fasifik ya fahimci cewa akwai lokaci mafi dacewa na zuwa kama kifi. Akwai wani Mashaidi da ya gayyace shi zuwa kama kifi, sai ya gaya wa Mashaidin cewa: “Mu haɗu da ƙarfe tara gobe da safe.” Sai Mashaidin ya ce: “Ba ka gane ba. Za mu je ne lokacin da kifaye suke fitowa, ba lokacin da muka sami zarafi ba.”

9 Hakazalika, masu wa’azi a ƙarni na farko suna zuwa wuraren da za su sami mutane da kuma a lokacin da za su same su. Alal misali, almajiran Yesu suna yin wa’azi a majami’u da gida-gida da kuma a kasuwa. (A. M. 5:42; 17:17; 18:4) Mu ma muna bukatar mu san lokacin da ake samun mutane a gida a yankinmu. Muna bukatar mu canja tsarin ayyukanmu domin mu sami mutane a lokaci da kuma wuraren da suke.​—1 Kor. 9:​19-23.

MASU KAMUN KIFI DA SUKA ƘWARE . . . 1. suna zuwa a lokaci da kuma wurin da za su sami kifi (Ka duba sakin layi na 8-9)

10. Waɗanne abubuwa ne ƙungiyar Jehobah ta ba mu don mu riƙa koyarwa da kyau?

10 Mai kamun kifi yana bukatar kayan aiki da suka dace kuma wajibi ne ya san yadda zai yi amfani da su. Mu ma muna bukatar kayan aikin da suka dace don yin wa’azi. Kuma muna bukatar mu san yadda za mu yi amfani da su. Yesu ya koya wa almajiransa yadda za su yi wa’azi. Ya gaya musu abin da bai kamata su ɗauka ba da inda za su yi wa’azi da kuma abin da za su faɗa. (Mat. 10:​5-7; Luk. 10:​1-11) A yau, ƙungiyar Jehobah ta yi mana tanadin abubuwan da za su taimaka mana mu yi koyarwa da kyau. * Kuma ana koya mana yadda za mu yi amfani da su. Wannan koyarwar tana taimaka mana mu kasance da ƙarfin zuciya kuma mu ƙware a yin wa’azi.​—2 Tim. 2:15.

MASU KAMUN KIFI DA SUKA ƘWARE . . . 2. an koya musu yin amfani da kayan aikin da ya dace (Ka duba sakin layi na 10)

KA KASANCE DA ƘARFIN ZUCIYA

11. Me ya sa masu wa’azi suke bukatar ƙarfin zuciya?

11 Masu sana’ar kamun kifi suna bukatar ƙarfin zuciya. A wasu lokuta, suna fuskantar wasu matsaloli da ba su yi zato ba a teku. Suna yawan aiki da daddare a teku kuma guguwa tana iya tasowa. Masu wa’azi ma suna bukatar ƙarfin zuciya. Sa’ad da muka zama Shaidun Jehobah, muna iya fuskantar tsanantawa daga danginmu, ba’a daga abokanmu kuma mutane suna iya ƙin saurarar wa’azinmu. Hakan ba abin mamaki ba ne. Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa mutanen da za su yi wa wa’azi za su tsananta musu.​—Mat. 10:16.

12. Kamar yadda Yoshuwa 1:​7-9 suka nuna, mene ne zai taimaka mana mu kasance da ƙarfin zuciya?

12 Ta yaya za mu kasance da ƙarfin zuciya? Na farko, kana bukatar ka kasance da tabbaci cewa har yanzu, Yesu yana ja-goranci daga sama. (Yoh. 16:33; R. Yar. 14:​14-16) Na biyu, ka kasance da bangaskiya cewa Jehobah zai cika alkawarinsa na kula da kai. (Mat. 6:​32-34) Idan ka ƙarfafa bangaskiyarka, hakan zai taimaka maka ka kasance da ƙarfin zuciya. Bitrus da abokansa sun nuna ƙarfin zuciya sosai sa’ad da suka bar sana’arsu kuma suka bi Yesu. Kana da bangaskiya sosai sa’ad da ka gaya wa abokanka da membobin iyalinka cewa ka soma yin nazari da Shaidun Jehobah kuma kana halartan taronsu! Babu shakka, ka yi canje-canje sosai a rayuwarka don ka riƙa bin ƙa’idodin Jehobah. Yin hakan ya bukaci bangaskiya da kuma ƙarfin zuciya sosai. Yayin da ka ci gaba da kasancewa da ƙarfin zuciya, ka tabbatar da cewa Jehobah ‘Allahnka na tare da kai duk inda za ka tafi.’​—Karanta Yoshuwa 1:​7-9.

MASU KAMUN KIFI DA SUKA ƘWARE . . . 3. suna aiki da ƙarfin zuciya a kowane yanayi (Ka duba sakin layi na 11-12)

13. Ta yaya yin bimbini da kuma addu’a za su taimaka maka ka yi ƙarfin zuciya?

13 Ta yaya za ka kasance da ƙarfin zuciya? Ka roƙi Jehobah ya ba ka ƙarfin zuciya. (A. M. 4:​29, 31) Jehobah zai amsa addu’arka kuma ba zai taɓa yasar da kai ba. Zai riƙa ƙarfafa ka a kowane lokaci. Ban da haka, kana iya yin bimbini a kan yadda Jehobah ya ceci mutanensa a dā. Ka yi tunanin yadda ya taimake ka sa’ad da kake fuskantar matsaloli da kuma yadda ya ƙarfafa ka ka yi canje-canje a rayuwarka. Babu shakka, Allahn da ya ja-goranci mutanensa a Jar Teku zai iya taimaka maka ka zama almajirin Yesu. (Fit. 14:13) Ka kasance da tabbaci kamar wani marubucin zabura da ya ce: “Yahweh yana tare da ni, ba zan ji tsoro ba, me mutum zai iya yi mini?”​—Zab. 118:6.

14. Mene ne ka koya daga labarin Masae da Tomoyo?

14 Wata hanya kuma da za mu kasance da ƙarfin zuciya ita ce ta wajen koyan yadda Jehobah ya taimaka wa mutanen da suke jin kunya su zama masu ƙarfin zuciya. Ka yi la’akari da labarin wata ’yar’uwa mai suna Masae. Tana jin kunya sosai kuma ta ɗauka cewa ba za ta iya yin wa’azi ba. Tana ganin cewa yi wa mutanen da ba ta sani ba wa’azi yana kamar hawan katanga mai tsayi sosai, kuma ta ɗauka cewa ba za ta iya yin hakan ba. Saboda haka, ta yi iya ƙoƙarinta don ta ƙara ƙaunar Jehobah da maƙwabtanta. Ta yi tunanin abin da ya sa muke bukatar yin wa’azi da gaggawa kuma ta roƙi Jehobah ya ba ta ƙarfin zuciyar yin wa’azi. Ta daina jin tsoro, kuma ta zama majagaba na kullum. Jehobah zai taimaka wa sabbi su kasance da “ƙarfin zuciya.” Ka yi la’akari da labarin wata ’yar’uwa mai suna Tomoyo. A lokacin da ta fara wa’azi, ta haɗu da wata mata a gida na farko da ta shiga kuma matar da yi mata ihu ta ce: “Ba na saurarar Shaidun Jehobah!” Kuma ta rufe ƙofarta. Tomoyo ba ta ji tsoro ba amma ta gaya wa wadda suke wa’azi tare cewa: “Kin ji abin da ta faɗa? Ban ce kome ba, amma ta gane cewa ni Mashaidiya ce. Ina farin ciki!” Yanzu, Tomoyo tana hidimar majagaba na kullum.

KA RIƘA HORAR DA KANKA

15. Ta yaya masu kamun kifi da suka ƙware suke horar da kansu, kuma me ya sa hakan ke da muhimmanci ga Kiristoci?

15 Masu kamun kifi da suka ƙware suna horar da kansu don su cim ma ayyukansu. Alal misali, wajibi ne su riƙa tashi da sassafe kuma su ci gaba da yin aiki ko da ana iska ko ruwan sama sosai. Mu ma muna bukatar mu horar da kanmu idan muna so mu riƙa jimrewa kuma mu kammala aikinmu.​—Mat. 10:22.

16. Ta yaya za mu horar da kanmu?

16 Ba mu gāji wannan halin ba. A yawancin lokuta, muna son yin abubuwa masu sauƙi, amma muna bukatar kamun kai don mu iya horar da kanmu. Saboda haka, muna bukatar taimako don mu iya yin abubuwa masu wuya. Jehobah yana amfani da ruhu mai tsarki don ya taimaka mana.​—Gal. 5:​22, 23.

17. Kamar yadda 1 Korintiyawa 9:​25-27 suka nuna, mene ne Bulus ya ce ya yi don ya horar da kansa?

17 Manzo Bulus ya horar da kansa. Ya ce ya ‘horar’ da jikinsa sosai don ya yi abin da ya dace. (Karanta 1 Korintiyawa 9:​25-27.) Ya ƙarfafa mutane su horar da kansu kuma su yi kome “yadda ya kamata, a shirye kuma.” (1 Kor. 14:40) Muna bukatar mu yi aiki tuƙuru don mu bauta wa Jehobah, hakan ya haɗa da yin wa’azi a kai a kai da kuma koyar da mutane.​—A. M. 2:46.

KADA KA YI JINKIRI

18. Mene ne zai sa Jehobah ya ɗauke mu a matsayin mutanen da suka yi nasara?

18 Mai sana’ar kamun kifi yana ganin ya yi nasara idan ya kama kifaye da yawa. Akasin haka, ba yawan mutanen da muka taimaka wa su soma bauta wa Jehobah ne ke nuna cewa mun yi nasara ba. (Luk. 8:​11-15) Idan mun ci gaba yin wa’azi da kuma koyar da mutane, Jehobah zai ɗauke mu a matsayin mutanen da suka yi nasara. Me ya sa? Domin muna wa shi da Ɗansa biyayya.​—Mar. 13:10; A. M. 5:​28, 29.

19-20. Wane dalili na musamman ne muke da shi na yin wa’azi?

19 A wasu ƙasashe, an haramta kamun kifi a wasu watanni. A waɗannan ƙasashen, mai kamun kifi zai sa ƙwazo sosai musamman sa’ad da lokacin kamun kifi ya kusan shigewa. A matsayinmu na masu wa’azi, ya kamata mu yi wa’azi da gaggawa domin ƙarshen wannan zamanin ya yi kusa! Lokacin yin wannan aikin yana ƙurewa. Kada ka jira har sai kome ya yi sumul a rayuwarka kafin ka yi wannan aikin.​—M. Wa. 11:4.

20 A yanzu, ka ƙarfafa kanka, ka riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki, ka kasance da ƙarfin zuciya kuma ka horar da kanka. Ka yi wa’azi tare da masu shela fiye da miliyan takwas a faɗin duniya, kuma Jehobah zai albarkace ka. (Neh. 8:10) Ka ci gaba da yin wa’azi da ƙwazo har sai lokacin da Jehobah ya ce ya isa. A talifi na gaba, za mu tattauna hanyoyi uku da za su taimaka mana mu ci gaba da yin wa’azi game da Mulkin Allah.

WAƘA TA 66 Mu Riƙa Yaɗa Bishara

^ sakin layi na 5 Yesu ya gayyaci maza masu sauƙin kai da suke aiki tuƙuru don su zama almajiransa. A yau, Yesu yana gayyatar mutane da ke da irin waɗannan halayen su zama almajiransa kuma su riƙa wa’azi. A wannan talifin, za mu tattauna abin da ɗaliban da suke jinkirin amincewa da gayyatar Yesu suke bukatar su yi.

^ sakin layi na 10 Ka duba talifin nan “Ka Riƙa Koyar da Gaskiya” a Hasumiyar Tsaro ta Oktoba 2018, shafuffuka na 11-16.