Wane ne Kake So Ya Amince da Kai?
“Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai ƙyale ayyukanku da kuka yi ba, da ƙaunar da kuka nuna masa.”—IBRAN. 6:10.
1. Mene ne muke so a yi mana, kuma mene ne hakan ya ƙunsa?
YAYA za ka ji idan mutumin da ka sani kuma kake daraja shi ya manta sunanka ko kuma bai gane ka ba? Irin wannan lamarin yana iya sa mutum sanyin gwiwa. Me ya sa? Dalilin shi ne dukanmu muna so mutanen da muka sani su san da mu. Amma ba sanin mu kawai muke so su yi ba. Muna so su san waɗanne irin mutane ne mu da kuma abubuwan da muka cim ma.—L. Ƙid 11:16; Ayu. 31:6.
2, 3. Me zai iya faruwa idan muna yawan son mutane su amince da mu? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)
2 Amma idan ba mu mai da hankali ba, burin son mutane su amince da mu yana iya wuce gona da iri saboda ajizancinmu. Wannan muguwar duniyar Shaiɗan tana iya sa mu soma sha’awar yin suna ko kuma a san da mu. Idan hakan ya faru, ba za mu riƙa ɗaukaka Jehobah Ubanmu da ke sama da kuma bauta masa yadda ya kamata ba.—R. Yar. 4:11.
3 A zamanin Yesu, ra’ayin wasu malaman addini game da samun amincewar mutane bai dace ba. Yesu ya yi wa Luk. 20:46, 47) Akasin haka, Yesu ya yaba ma wata gwauruwa domin ta ba da gudummawa da dukan kuɗin da take da shi. Kuma da alama cewa mutane ba su lura da hakan ba. (Luk. 21:1-4) Ra’ayin Yesu game da samun amincewa ya bambanta sosai da na wasu. Wannan talifin zai taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace game da samun amincewa, wato irin ra’ayin da Jehobah yake so mu kasance da shi.
mabiyansa gargaɗi cewa: “Ku yi hankali da malaman Koyarwar Musa, su masu son sa manyan riguna suna yawo, masu so a gaishe su a kasuwa, masu so a ba su wuraren zama masu daraja a majami’u, da wuraren zama masu kyau a wurin biki.” Ya ƙara da cewa: “Su za su sha hukunci mafi tsanani.” (AMINCEWA DA TA FI MUHIMMANCI
4. Wace irin amincewa ce ta fi muhimmanci, kuma me ya sa?
4 Wace irin amincewa ce ta fi muhimmanci? Shin kana ganin amincewar da makaranta ko sana’a ko kuma nishaɗin wannan duniyar ke kawowa ce ta fi muhimmanci? Bulus ya bayyana irin amincewar da ta fi muhimmanci sa’ad da ya ce: ‘Yanzu da kuka san Allah, ko mu dai a ce Allah ya san ku, ta yaya za ku sāke komawa a kan raunanan al’adu marasa biyan bukata, har kuna neman komawa ga bautarsu?’ (Gal. 4:9) Babu shakka, gata ce babba Allah Maɗaukakin Sarki ‘ya san mu!’ Jehobah ya san mu kuma yana ƙaunar mu. Ban da haka, yana so mu zama abokansa shi ya sa ya halicce mu.—M. Wa. 12:13, 14.
5. Me muke bukatar mu yi domin Jehobah ya san mu?
5 Musa ya sami albarka daga Jehobah. A lokacin da ya roƙi Jehobah ya koya masa hanyoyinsa, Jehobah ya ce masa: “Zan yi daidai yadda ka roƙa, gama ka sami farin jini a gare ni, na kuma san ka da suna.” (Fit. 33:12-17) Mu ma za mu sami albarka idan Jehobah ya san mu. Amma mene ne za mu yi domin Jehobah ya san mu? Muna bukatar mu ƙaunace shi kuma mu yi alkawarin bauta masa.—Karanta 1 Korintiyawa 8:3.
6, 7. Mene ne zai iya ɓata dangantakarmu da Jehobah?
6 Ƙari ga haka, muna bukatar mu ci gaba da kasancewa abokan Jehobah. Kamar yadda Kiristoci a Galatiya suka yi, muna bukatar mu guji biɗan kayan “banza” na duniyar nan, har ma da son a san da mu. (Gal. 4:9) Waɗannan Kiristoci a ƙarni na farko sun san Allah kuma shi ma ya san su. Amma Bulus ya ce waɗannan ’yan’uwan sun ‘koma’ biɗan kayan banza na duniya. A taƙaice dai Bulus yana gaya musu ne cewa: “Me ya sa kuka koma biɗan kayan banza na duniyar nan?”
7 Zai yiwu mu ma mu faɗa cikin irin wannan yanayin a yau? Ƙwarai kuwa! A lokacin da muka soma bauta wa Jehobah, kamar Bulus, wataƙila mun bar abubuwan da a duniyar Shaiɗan suke da muhimmanci. (Karanta Filibiyawa 3:7, 8.) Wataƙila mun ƙi zuwa jami’a ko mun ƙi karɓan karin girma a wurin aikinmu ko kuma yin sana’ar da za ta sa mu yi arziki. Mai yiwuwa da mun yi arziki da kuma suna don muna da baiwar yin waƙa ko kuma wasannin. Amma mun ƙi yin dukan waɗannan abubuwan. (Ibran. 11:24-27) Ba zai dace yanzu mu soma yin da-na-sani ba! Yin hakan yana iya sa mu koma biɗan abubuwan da muka tabbatar wa kanmu suna cikin kayan “banza” na duniyar nan.
KA ƘUDURI NIYYAR SAMUN AMINCEWAR JEHOBAH
8. Mene ne zai taimaka mana mu ƙuduri niyyar biɗan amincewar Jehobah?
8 Ta yaya za mu ƙuduri niyyar samun amincewar Jehobah ba na duniya ba? Muna bukatar mu mai da hankali ga abubuwa biyu. Na farko, Jehobah yana amince da mutanen da suke bauta masa yadda yake so. (Karanta Ibraniyawa 6:10; 11:6) Jehobah yana ɗaukan dukan masu bauta masa da tamani. Don hakan, a gare shi rashin “adalci” ne ya manta da waɗanda suka bauta masa da aminci. Jehobah “ya san waɗanda suke nasa.” (2 Tim. 2:19) Ƙari ga haka, “yana lura da hanyar masu adalci” kuma ya san yadda zai cece su daga matsala.—Zab. 1:6; 2 Bit. 2:9.
9. Ku ba da misalin da ya nuna yadda Jehobah ya amince da mutanensa.
9 A wasu lokuta, Jehobah ya nuna ya amince da mutanensa a hanyoyi na musamman. (2 Tar. 20:20, 29) Alal misali, Jehobah ya ceci mutanensa daga Jar Teku a lokacin da Fir’auna da sojojinsa suka bi su. (Fit. 14:21-30; Zab. 106:9-11) Wannan abun ban mamaki ne sosai da har bayan shekaru 40 mutane a wannan ɓangaren duniya suna magana a kai. (Josh. 2:9-11) Babu shakka, yadda Jehobah ya ceci mutanensa kuma yake ƙaunar su yana ƙarfafa mu domin za mu fuskanci hari daga Gog na ƙasar Magog a nan gaba! (Ezek. 38:8-12) A wannan lokacin, za mu yi farin ciki sosai domin mun biɗi amincewar Jehobah ba na duniya ba.
10. Mene ne muke bukatar mu mai da wa hankali?
10 Wani abu kuma da muke bukatar mu mai da wa hankali shi ne cewa: Jehobah yana iya nuna ya amince da mu a hanyoyin da ba mu yi zato ba. Jehobah ba zai taɓa sāka wa mutanen da suke yin ayyuka masu kyau domin suna so wasu su amince da su ba. Me ya sa? Yesu ya bayyana cewa idan mutane sun yaba musu, sun sami iyakar ladarsu ke nan. (Karanta Matiyu 6:1-5.) Amma Yesu ya ce Ubansa yana ganin dukan abubuwa masu kyau da bayinsa suke yi a “ɓoye.” Yana lura da ayyuka masu kyau da mutane suke yi, kuma zai albarkace su. Amma a wasu lokuta, Jehobah yana yi mana albarka a wasu hanyoyin da ba mu yi zato ba. Bari mu ga wasu misalai.
WATA BUDURWA MAI TAWALI’U TA SAMU AMINCEWAR JEHOBAH
11. Ta yaya Jehobah ya nuna cewa ya amince da Maryamu?
11 Jehobah ya zaɓi Maryamu, mace mai tawali’u don ta haifi Ɗansa Yesu. Maryamu tana zama a Nazarat wani ƙarami birni da ke da nisa daga Urushalima da kuma haikali. (Karanta Luka 1:26-33.) Me ya sa aka zaɓi Maryamu? Mala’ika Jibra’ilu ya gaya mata cewa ta “sami tagomashi wurin Allah.” Daga baya abin da Maryamu ta faɗa sa’ad da ta ziyarci Alisabatu ya nuna cewa tana da dangantaka mai kyau da Jehobah. (Luk. 1:46-55) Hakika, Jehobah ya lura da amincin Maryamu kuma ya yi mata albarka a hanyar da ba ta taɓa zato ba.
12, 13. Yaya Jehobah ya nuna ya amince da Yesu sa’ad da aka haife shi da kuma a lokacin da aka kai shi haikali bayan kwana 40 da haihuwa?
12 A lokacin da Maryamu ta haifi Yesu, Jehobah ya nuna cewa ya amince da shi a hanyar da ba a yi zato ba. Su waye ne Jehobah ya sanar wa haihuwar Yesu? Jehobah bai sanar da manyan hukumomi da kuma masu mulkin da Luk. 2:8-14) Bayan haka, waɗannan makiyaya suka je ganin yaron da aka haifa. (Luk. 2:15-17) Babu shakka, Yusufu da Maryamu sun yi mamaki cewa an amince da Yesu a wannan hanyar! Hakan ya nuna cewa yadda Jehobah yake yin abubuwa ya bambanta da yadda Shaiɗan yake yi. A lokacin da Shaiɗan ya tura masanan yanayin taurari su ziyarci Yesu da iyayensa, hankalin mutanen Urushalima gabaki ɗaya ya tashi don an haifi Yesu. (Mat. 2:3) A sakamakon haka, aka kashe yara da yawa.—Mat. 2:16.
ke Urushalima da kuma Bai’talami ba. A maimakon haka, ya tura mala’iku su sanar da makiyaya da ke kiwo a filayen Bai’talami. (13 A dokar da Jehobah ya ba Isra’ilawa, ya ce bayan kwana arba’in da haihuwar yaro, mahaifiyar tana bukatar ta kai shi haikalin Urushalima don ta miƙa hadaya ga Jehobah. Don haka, Maryamu da Yusufu, sun yi tafiyar wajen awa biyu daga Bai’talami zuwa haikalin da ke Urushalima. (Luk. 2:22-24) Sa’ad da Maryamu da Yusufu suke hanyar zuwa Urushalima, wataƙila Maryamu ta yi tunanin cewa idan suka kai Urushalima, firist ɗin zai yi wani abu na musamman don ya nuna abin da Yesu zai zama a nan gaba. An amince da Yesu, amma ba a hanyar da Maryamu ta zata ba. Jehobah ya yi amfani da wani mutum ‘mai adalci, mai bautar Allah’ mai suna Simeyon da kuma Hannatu wata gwauruwa mai shekara 84 da annabiya ce. Sun sanar cewa Yesu ne zai zama Almasihu ko kuma Kristi.—Luk. 2:25-38.
14. Ta yaya Jehobah ya albarkaci Maryamu?
14 Maryamu kuma fa? Shin Jehobah ya ci gaba da amincewa da ita don ta kula da Ɗansa da kuma renonsa? Ƙwarai kuwa. Allah ya sa an rubuta ayyukanta da kalaminta a cikin Littafi Mai Tsarki. Kamar dai Maryamu ba ta yi tafiye-tafiye da Yesu a lokacin hidimarsa na shekara uku da rabi a duniya ba. Wataƙila ta zauna a Nazarat tun da yake ita gwauruwa ce. Saboda haka, ba ta sami gatar da wasu suka samu ba. Amma tana wurin da aka kashe Yesu. (Yoh. 19:26) Daga baya, Maryamu ta kasance tare da almajiran Yesu a Urushalima sa’ad da suka sami ruhu mai tsarki a ranar Fentakos. (A. M. 1:13, 14) Da alama cewa an shafe ta tare da sauran almajiran, kuma hakan yana nufin cewa ta sami gatar kasancewa tare da Yesu a sama. Hakika, Jehobah ya albarkace ta don amincinta!
JEHOBAH YA NUNA CEWA YA AMINCE DA ƊANSA
15. Ta yaya Jehobah ya nuna ya amince da Ɗansa, Yesu Kristi sa’ad da yake duniya?
15 Yesu bai so limamai ko shugabanni na zamaninsa su girmama shi ba. Amma ya sami ƙarfafa sa’ad da Jehobah ya yi magana daga sama sau uku a lokaci dabam-dabam don ya nuna yana ƙaunar sa. Jim kaɗan bayan Yesu ya yi baftisma a Kogin Urdun, Jehobah ya ce: “Wannan shi ne Ɗana da nake ƙauna, wanda nake jin daɗinsa ƙwarai.” (Mat. 3:17) Babu shakka, Yesu da Yohanna Mai Baftisma ne kaɗai suka ji abin da Jehobah ya faɗa. Bayan hakan, kusan shekara ɗaya kafin Yesu ya mutu, manzanninsa guda uku sun ji sa’ad da Jehobah ya ce game da Yesu: “Wannan shi ne Ɗana, wanda nake ƙauna, ina jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!” (Mat. 17:5) Ƙari ga haka, ’yan kwanaki kafin Yesu ya mutu, Jehobah ya sake yi wa Ɗansa magana daga sama.—Yoh. 12:28.
16, 17. Ta yaya Jehobah ya nuna cewa ya amince da Yesu a hanyar da ba a zata ba?
Mat. 26:39, 42) Domin yana son amincewar Jehobah ba na duniya ba, ya jimre wa gungumen azaba, “ya mai da abin kunya ba kome ba.” (Ibran. 12:2) Ta yaya Jehobah ya nuna ya amince da Yesu?
16 Yesu ya san cewa mutane za su kira shi mai saɓo kuma zai yi mutuwar wulaƙanci. Duk da haka, ya yi addu’a a yi abin da Jehobah yake so ba abin da yake so ba. (17 Sa’ad da Yesu yake duniya ya yi addu’a ya sami matsayi da yake da shi a dā. (Yoh. 17:5) Littafi Mai Tsarki bai faɗa cewa Yesu yana neman ƙarin gata a sama ba. Ko kuma ya sami gata na musamman don ya yi nufin Jehobah a duniya ba. Amma, mene ne Jehobah ya yi? Ya nuna ya amince da Yesu a hanyar da ba a yi zato ba ta wajen “ɗaukaka shi fiye da kome.” Jehobah ya kuma ba Yesu rai marar mutuwa, wannan abu ne da babu wanda ya taɓa samu a lokacin! * (Filib. 2:9; 1 Tim. 6:16) Wannan hanya ce ta musamman na yi wa Yesu albarka don amincinsa!
18. Mene ne zai taimaka mana mu guji neman amincewa daga wannan duniyar?
18 Mene ne zai taimaka mana mu guji neman amincewa daga wannan duniyar? Ya kamata mu riƙa tuna cewa a koyaushe, Jehobah yana amincewa da bayinsa masu aminci kuma yana musu albarka. Ƙari ga haka, sau da yawa yana ba su lada a hanyoyin da ba su yi zato ba. Ba mu san yadda Jehobah zai albarkace mu a nan gaba ba. Amma, yanzu muna jimrewa da wahala da matsaloli a wannan muguwar duniya. Bari mu riƙa tuna cewa wannan muguwar duniyar za ta wuce. Kuma dukan amincewar da take yi wa mutane za ta wuce. (1 Yoh. 2:17) Jehobah, Uba mai ƙauna ‘ba marar adalci ba ne. Ba zai ƙyale ayyukanmu da muka yi ba, da ƙaunar da muka nuna masa.’ (Ibran. 6:10) Hakika, zai yi mana albarka, wataƙila a hanyoyin da ba za mu taɓa zato ba a yanzu!
^ sakin layi na 17 Wannan albarka ce da ba a yi zato ba don ba a ambata rai marar mutuwa a cikin Nassosin Ibrananci ba.