Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yesu Ya Mutu Domin Ni Kuwa?

Yesu Ya Mutu Domin Ni Kuwa?

LITTAFI MAI TSARKI yana ɗauke da furuci dabam-dabam daga mutane “kamar mu.” (Yaƙ. 5:17) Alal misali, mun fahimci abin da manzo Bulus ya faɗa a littafin Romawa 7:​21-24 sosai. Ya ce: “Idan ina so in yi nagarta, sai in ga mugunta tare da ni. . . . Kaitona! Abin tausayi ne ni!” Wannan furucin da ya yi yana sosa zuciyarmu a duk lokacin da muke fama da ajizancinmu.

Akwai wasu abubuwa kuma da Bulus ya faɗa. A Galatiyawa 2:​20, Bulus ya furta da tabbaci cewa Yesu “ya ƙaunace [shi] har ya ba da ransa domin[sa].” Kai ma kana da irin wannan ra’ayin kuwa? Wataƙila ba a kowane lokaci ba.

Idan muna fama da baƙin ciki saboda wani zunubin da muka yi a dā, yana iya yi mana wuya a wasu lokuta mu yarda cewa Jehobah yana ƙaunar mu kuma ya gafarta mana. Bugu da ƙari, zai yi mana wuya mu yarda cewa Yesu ya mutu dominmu. Amma Yesu yana so mu kasance da tabbaci cewa ya mutu dominmu kuwa? Idan haka ne, me zai taimaka mana mu amince da hakan? Bari mu tattauna waɗannan tambayoyi biyu.

YADDA YESU YA ƊAUKI SADAUKARWAR DA YA YI

Hakika, Yesu Kristi ya mutu dominmu. Yana so mu kasance da wannan tabbacin. Ka yi la’akari da abin da ke littafin Luka 23:​39-43. Littafin ya ambata yadda aka rataye wani mutum a gungume kusa da Yesu. Mutumin ya yarda cewa ya yi zunubai. Babu shakka, zunubai masu tsanani ne sosai mutumin ya yi domin an yanke masa hukuncin kisa. Cike da baƙin ciki, mutumin ya roƙi Yesu cewa: “Ka tuna da ni sa’ad da ka shiga mulkinka!”

Mene ne Yesu ya ce? Ka yi tunanin yadda Yesu ya juya fuska da kyar don ya kalli mutumin. Duk da cewa yana cikin ƙunci, ya ɗan yi murmushi kuma ya tabbatar masa da cewa: ‘Hakika ina gaya maka yau ɗin nan, za ka zauna tare da ni a Firdausi [aljanna].’ Yesu zai iya gaya masa cewa Ai Ɗan mutum ya zo don ya “ba da ransa domin ceton mutane da yawa.” (Mat. 20:28) Amma ka lura da abin da Yesu ya yi? Ya gaya masa yadda hadayarsa ta shafi mutumin. Kalmomin nan “ka” da “ni” da ya yi amfani da su sun kwantar wa mutumin da rai. Kuma ya gaya wa mutumin cewa zai kasance a cikin aljanna a duniya.

Babu shakka, Yesu yana so mutumin ya san cewa zai amfana daga fansar da Yesu zai yi. Idan Yesu yana da irin wannan ra’ayi game da mutumin da bai tuba samun zarafin bauta wa Allah ba, babu shakka, zai fi mutunta wa Kirista da ya yi baftisma kuma yake bauta wa Allah. Mene ne zai taimaka mana mu tabbatar wa kanmu cewa fansar Yesu za ta amfane mu duk da zunubanmu?

ABIN DA YA TAIMAKI BULUS

Hidimar Bulus ta shafi yadda yake ɗaukar fansar Yesu. Ta yaya? Ya bayyana cewa: “Ina gode wa Almasihu Yesu Ubangijinmu, wanda ya ba ni ƙarfi domin aikin nan. Ya amince da ni har ya kira ni zuwa ga hidimarsa, ko da yake a dā ni mai saɓon Allah ne, mai tsananta masa, kuma mai wulaƙanta shi.” (1 Tim. 1:​12-14) Hidimar da aka ba Bulus ya sa ya san cewa Yesu ya nuna masa jinƙai da ƙauna kuma ya amince da shi. Yesu ya ba kowannenmu a yau hidima. (Mat. 28:​19, 20) Shin hidimarmu ta yin wa’azi za ta iya taimaka mana mu san cewa Yesu ya mutu dominmu?

Wani mai suna Albert da bai daɗe da dawowa ƙungiyar Jehobah ba bayan an yi masa yankan zumunci kusan shekara 34, ya ce: “Zunubaina suna a gabana kullum. Amma sa’ad da nake wa’azi, ina ji cewa Yesu ya ba ni hidima yadda ya yi da manzo Bulus. Hakan yana sa ni farin ciki, da daraja kaina da kuma kasancewa da bege.”​—Zab. 51:3.

Yayin da muke nazari da mutane dabam-dabam, mu tabbatar musu da cewa Yesu yana ƙaunar su kuma yana nuna musu jinƙai

Wani mai suna Allan wanda a dā ya yi laifuffuka dabam-dabam kuma yana so yin faɗa sosai, ya ce: “Har yau, ina tunawa da laifuffukan da na yi wa mutane. A wasu lokuta, hakan yana sa ni baƙin ciki sosai. Amma ina godiya ga Jehobah cewa ya ƙyale mai zunubi kamar ni ya riƙa yin shela ga mutane. Idan na ga yadda mutane suke amfana daga wa’azi, ina tunawa cewa Jehobah Allah ne mai ƙauna da kuma alheri sosai. Ina ji cewa yana yin amfani da ni wajen taimaka wa mutanen da suke fama da irin kasawata.”

Idan muna wa’azi, muna yin abu mai kyau kuma muna tunani mai kyau. Hakan yana tabbatar mana da cewa Yesu yana ƙaunar mu, yana nuna mana jinƙai kuma ya amince da mu.

JEHOBAH YA FI ZUCIYARMU

A wannan muguwar duniya da muke ciki, zuciyarmu za ta ci gaba da damun mu don wani zunubin da muka taɓa yi. Amma, mene ne zai taimaka mana mu magance hakan?

Wata mai suna Jean da take yawan fama da baƙin ciki don zunuban da ta yi sa’ad da take matashiya ta ce: “Ina farin ciki domin ‘Allah ya fi zuciyarmu.’ ” (1 Yoh. 3:​19, 20) Mu ma za mu iya samun ƙarfafa don sanin cewa Jehobah da kuma Yesu sun san cewa mu ajizai ne. Ku tuna cewa sun yi tanadin fansa, ba don kamiltattun mutane ba, amma don ʼyan Adam ajizai da suka tuba.​—1 Tim. 1:15.

Muna tabbatar wa kanmu cewa Yesu ya mutu domin kowannenmu sa’ad da muka yi bimbini sosai a kan yadda Yesu ya bi da ʼyan Adam ajizai kuma muka yi iya ƙoƙarinmu a hidimar da aka danƙa mana. Idan muka yi haka, za mu iya furtawa da tabbaci kamar manzo Bulus cewa: Yesu ‘ya ƙaunace ni har ya ba da ransa domina.’