Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

A wane lokaci ne Yesu ya zama Babban Firist, kuma a wane lokaci ne aka ƙaddamar da sabon alkawari?

A bayyane yake cewa Yesu ya zama Babban Firist a lokacin da ya yi baftisma a shekara ta 29. Mene ne ya tabbatar mana da hakan? A lokacin da Yesu ya yi baftisma, ya nuna cewa yana a shirye ya ba da ransa a kan bagade na alama da ke wakiltar “nufin” Allah. (Gal. 1:4; Ibran. 10:​5-10) Babu shakka, tun lokacin da aka kafa wannan bagaden, wato sa’ad da aka yi wa Yesu baftisma ne, haikali na alama da ke wakiltar shirye-shiryen da aka yi mana don mu bauta wa Jehobah ya soma aiki. Bagaden sashe ne mai muhimmanci a wannan haikalin.​—Mat. 3:​16, 17; Ibran. 5:​4-6.

Ana bukatar Babban Firist a wannan haikali na alama. Jehobah ya naɗa Yesu da “ruhu mai tsarki, da kuma iko” don ya zama Babban Firist. (A. M. 10:​37, 38; Mar. 1:​9-11) Amma ta yaya muka san cewa an naɗa Yesu a matsayin Babban Firist kafin ya mutu kuma aka ta da shi? Misalin Haruna da kuma Firistocin da suka biyo bayansa zai taimaka mana mu amsa tambayoyin nan.

A dokar da Allah ya ba Musa, ya umurce su cewa babban firist ne kaɗai yake da izinin shiga Wuri Mafi Tsarki. Akwai labule tsakanin Wuri Mafi Tsarki da Mai Tsarki. A ranar Kafara ne kaɗai Babban Firist yake shiga Wuri Mafi Tsarki. (Ibran. 9:​1-3, 6, 7) An naɗa Haruna da magādansa a matsayin babban firist kafin su wuce “ta labulen” mazaunin Jehobah. Hakazalika, an naɗa Yesu a matsayin Babban Firist na haikali na alama kafin ya mutu kuma bayan haka ya wuce “ta labulen nan, wato, jikinsa” zuwa sama. (Ibran. 10:20) Shi ya sa manzo Bulus ya ce Yesu zai zo “a matsayin Babban Firist” kuma zai shiga “cikin tenti mafi girma kuma mafi kyau, wadda ba mutum ne ya gina ba,” wato “sama.”​—Ibran. 9:​11, 24.

A wane lokaci ne aka ƙaddamar da sabon alkawari? Sa’ad da Yesu ya shiga sama kuma ya miƙa kamiltaccen ransa a madadinmu, ya ɗauki mataki na farko don ya ƙaddamar da sabon alkawari. Waɗanne abubuwa ne ya yi don hakan ya yiwu?

Na farko, Yesu ya bayyana a gaban Jehobah. Na biyu, Yesu ya miƙa kamiltaccen ransa a madadinmu. Kuma na uku, Jehobah ya amince da fansar Yesu. Sai bayan da Yesu ya yi abubuwan nan ne sabon alkawarin ya soma aiki.

Littafi Mai Tsarki bai faɗa mana ainihi lokacin da Jehobah ya amince da fansar Yesu ba. Saboda haka, ba za mu iya faɗin ainihin lokaci da aka ƙaddamar da sabon alkawarin kuma ya soma aiki ba. Amma mun san cewa Yesu ya je sama kwanaki goma kafin ranar Fentakos. (A. M. 1:3) A wannan gajeren lokaci ne Yesu ya miƙa kamiltaccen ransa ga Jehobah a madadinmu, kuma Jehobah ya amince da fansar. (Ibran. 9:12) Abin da ya faru a ranar Fentakos ya tabbatar da hakan sarai. (A. M. 2:​1-4, 32, 33) A lokacin, an riga an ƙaddamar da sabon alkawarin kuma ya soma aiki.

A taƙaice, an kafa da kuma ƙaddamar da sabon alkawarin bayan da Jehobah ya amince da fansar Yesu. A lokacin ne sabon alkawarin ya soma aiki kuma Yesu, Babban Firist, ya zama mai tsayawa tsakanin Allah da mutane.​—Ibran. 7:25; 8:​1-3, 6; 9:​13-15.