Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 30

Ka Ci Gaba da Bin Gaskiya

Ka Ci Gaba da Bin Gaskiya

“Ba abin da ya fi sa ni farin ciki fiye da in ji cewa ’ya’yana suna bin gaskiya.”​—3 YOH. 4.

WAƘA TA 54 ‘Wannan Ita Ce Hanyar Rai’

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Kamar yadda 3 Yohanna 3, 4 suka nuna, mene ne yake sa mu farin ciki?

BABU shakka, manzo Yohanna ya yi farin ciki sosai sa’ad da ya ji cewa mutanen da ya taimaka musu su koyi gaskiya sun ci gaba da bauta wa Jehobah. Kiristocin nan masu aminci da Yohanna ya ɗauka kamar ʼya’yansa sun fuskanci ƙalubale da yawa, kuma Yohanna ya ƙoƙarta sosai don ya ƙarfafa su. Hakazalika, muna matuƙar farin ciki sa’ad da yaranmu ko kuma mutanen da muka koya wa gaskiya suka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma suka ci gaba da bauta masa.​—Karanta 3 Yohanna 3, 4.

2. Me ya sa Yohanna ya rubuta wasiƙunsa?

2 Wataƙila Yohanna yana zama a Afisa ko kuma kusa da birnin a shekara ta 98. Mai yiwuwa, ya koma wurin ne sa’ad da aka sako shi daga kurkuku a tsibirin Batmusa. A lokacin ne ruhun Jehobah ya motsa shi ya rubuta wasiƙu uku. Ya rubuta wasiƙun ne don ya taimaka wa Kiristoci su riƙe amincinsu kuma su ci gaba da bin gaskiya.

3. Waɗanne tambayoyi ne za mu amsa a wannan talifin?

3 Yohanna ne ya fi tsawon rayuwa a cikin manzannin Yesu kuma ya damu sosai don yadda malaman ƙarya suke gurɓata ikilisiyoyi. * (1 Yoh. 2:​18, 19, 26) ʼYan ridda sun yi da’awar sanin Allah, amma ba sa bin dokokinsa. Bari mu tattauna shawarar da Yohanna ya bayar. A wannan talifin, za mu amsa tambayoyin nan uku: Mene ne bin gaskiya yake nufi? Waɗanne ƙalubale ne muke fuskanta? Kuma ta yaya za mu taimaka wa juna don mu riƙa bin gaskiya?

MENE NE BIN GASKIYA YAKE NUFI?

4. Kamar yadda 1 Yohanna 2:​3-6 da 2 Yohanna 4, 6 suka nuna, mene ne bin gaskiya yake nufi?

4 Idan muna so mu riƙa bin gaskiya, muna bukatar mu san gaskiyar da ke cikin Kalmar Allah. Ƙari ga haka, wajibi ne mu riƙa “biyayya da umarnin Allah.” (Karanta 1 Yohanna 2:​3-6; 2 Yohanna 4, 6.) Yesu ya koya mana misali mai kyau a bauta wa Jehobah. Saboda haka, hanya ɗaya da za mu yi biyayya ga Jehobah, ita ce ta wajen bin gurbin Yesu sawu-da-kafa.​—Yoh. 8:29; 1 Bit. 2:21.

5. Mene ne ya kamata mu tabbatar da shi?

5 Domin mu ci gaba da bin gaskiya, wajibi ne mu yarda cewa Jehobah Allah ne na gaskiya, kuma dukan abubuwan da ke cikin Kalmarsa gaskiya ne. Kuma wajibi ne mu yarda cewa Yesu ne Almasihun da Jehobah ya ce zai aiko. Mutane da yawa a yau suna shakka cewa an naɗa Yesu a matsayin Sarkin Mulkin Allah. Yohanna ya gargaɗe mu cewa akwai ‘mutane da yawa masu ruɗi,’ da za su iya yaudarar mutanen da ba su yarda sosai da gaskiya game da Jehobah da kuma Yesu ba. (2 Yoh. 7-11) Yohanna ya ce: “Wane ne wannan mai ƙarya? Ai, shi ne wanda yake mūsu cewa Yesu ne Almasihu.” (1 Yoh. 2:22) Hanya ɗaya tak da za mu kāre kanmu daga ruɗu ita ce ta wajen yin nazarin Kalmar Allah. Yin hakan ne kaɗai zai sa mu san Jehobah da kuma Yesu. (Yoh. 17:3) Kuma yin hakan ne zai sa mu tabbatar da cewa muna bin gaskiya.

WAƊANNE ƘALUBALE NE MUKE FUSKANTA?

6. Wane ƙalubale ne Shaidu matasa suke fuskanta?

6 Ya kamata dukan Kiristoci su guje wa ra’ayoyin ʼyan Adam. (1 Yoh. 2:26) Kiristoci matasa ne ya kamata su fi mai da hankali. Wata ʼyar shekara 25 daga ƙasar Faransa mai suna Alexia, * ta ce: “A lokacin da nake makaranta, an koya mana ra’ayin bayyanau da dai sauransu, kuma hakan ya ruɗar da ni sosai. A wasu lokuta, ina son koyarwar. Amma na ga cewa ba zai dace in yarda da dukan abubuwan da ake koya mana, kuma in yi watsi da koyarwar Littafi Mai Tsarki ba.” Alexia ta yi nazarin littafin nan Life​—How Did It Get Here? By Evolution or by Creation? Bayan ʼyan makonni, sai ta daina shakka. Alexia ta ce: “Na tabbatar wa kaina cewa abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki gaskiya ne. Kuma na ga cewa bin shawarwarin da ke cikinsa zai sa ni farin ciki da kuma kwanciyar rai.”

7. Me ya kamata mu riƙa yi, kuma me ya sa?

7 Wajibi ne Kiristoci yara da manya su riƙa bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya. Yohanna ya ce ba zai yiwu mu riƙa bauta wa Jehobah, har ila mu riƙa yin munanan abubuwa ba. (1 Yoh. 1:6) Idan muna so mu riƙa faranta wa Jehobah rai a kowane lokaci, ya kamata mu san cewa Jehobah yana ganin dukan abubuwan da muke yi. Ko da mutane ba sa ganin abubuwan da muke yi, amma Jehobah yana gani.​—Ibran. 4:13.

8. Wane ra’ayi ne ya kamata mu guje wa?

8 Ya kamata mu guji kasancewa da ra’ayin mutanen duniya game da zunubi. Manzo Yohanna ya ce: “Idan mun ce ba mu da zunubi, ruɗin kanmu muke yi.” (1 Yoh. 1:8) A zamanin manzo Yohanna, ʼyan ridda sun yi da’awa cewa mutum zai iya ci gaba da bauta wa Allah yayin da yake zunubin ganganci. Mutane ma a yau suna da irin wannan ra’ayin. Mutane da yawa suna da’awa cewa sun yi imani da Allah, amma ba su yarda da abin da Jehobah ya faɗa game da zunubi ba. Alal misali, mutanen nan ba su yarda da abin da Jehobah ya ce game da jima’i ba. Sun ce suna da ’yancin bin ra’ayinsu a batutuwan da Jehobah ya ce zunubi ne.

Matasa, ku yi bincike don ku san dalilan da suka sa Jehobah ya yarda mu yi wasu abubuwa, kuma ya haramta wasu. Hakan zai taimaka muku ku kāre imaninku (Ka duba sakin layi na 9) *

9. Me ya sa ya dace matasa su bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki?

9 Zai iya yi wa Kiristoci matasa wuya su bi ra’ayin Jehobah game da jima’i sa’ad da abokan makarantarsu ko abokan aiki suke nema su rinjaye su. Abin da ya faru da Aleksandar ke nan. Ya ce: “Wasu ʼyan mata a makaranta suna neman su tilasta mini in kwana da su. Sun ce ni ɗan daudu ne tun da ba ni da budurwa.” Idan kana fuskantar irin wannan matsalar, ka tuna cewa bin imaninka zai sa ka mutunta kanka, ka sami ƙoshin lafiya kuma ka kyautata dangantakarka da Jehobah. Kuma a duk lokacin da ba ka faɗa cikin jarrabawa ba, zai yi maka sauƙi ka yi abin da ya dace. Ka tuna cewa Shaiɗan ne yake sa mutane su kasance da ra’ayi marar kyau game da jima’i. Saboda haka, idan ba ka bi ra’ayinsa ba, za ka “ci nasara a kan Mugun nan.”​—1 Yoh. 2:14.

10. Ta yaya Yohanna 1:9 ta taimaka mana mu bauta wa Jehobah da zuciya mai tsabta?

10 Mun yarda cewa Jehobah yana da ikon gaya mana abin da ya dace da wanda bai dace ba. Kuma muna ƙoƙartawa don kada mu yi zunubi. Amma idan mun yi zunubi, ya kamata mu yi ikirarin laifinmu ga Jehobah a addu’a. (Karanta 1 Yohanna 1:9.) Idan mun yi zunubi mai tsanani, ya kamata mu nemi taimako wajen dattawan da Jehobah ya naɗa su kula da mu. (Yaƙ. 5:​14-16) Amma bai kamata mu ci gaba da damun kanmu a kan zunuban da muka yi a dā ba. Me ya sa? Domin Ubanmu mai ƙauna ya riga ya aiko da Ɗansa ya gafarta zunubanmu. Jehobah ya ce zai gafarta zunubanmu idan mun yi tuban gaske. Kuma babu shakka, zai yi hakan. Saboda haka, kada mu yarda wani abu ya hana mu bauta wa Jehobah da zuciya mai tsabta.​—1 Yoh. 2:​1, 2, 12; 3:​19, 20.

11. Ta yaya za mu iya kāre kanmu daga koyarwar da za su iya raunana bangaskiyarmu?

11 Wajibi ne mu guji koyarwar ʼyan ridda. Tun lokacin da aka kafa ikilisiyar Kirista, Shaiɗan ya ci gaba da ƙoƙartawa don ya raunana bangaskiyar bayin Jehobah. Saboda haka, ya kamata mu san bambanci tsakanin gaskiya da ƙarya. * Maƙiya suna iya yaɗa ƙarairayi ta Intane ko kafofin sada zumunta don su raunana ƙaunarmu ga Jehobah da kuma ʼyan’uwanmu. Kada ku yarda da ƙarairayin nan domin Shaiɗan ne yake yaɗa su!​—1 Yoh. 4:​1, 6; R. Yar. 12:9.

12. Me ya sa ya kamata mu ƙarfafa bangaskiyarmu?

12 Don mu guji faɗawa cikin tarkon Shaiɗan, muna bukatar mu yi imani ga Yesu sosai da kuma yadda Jehobah yake amfani da shi don ya cika nufinsa. Muna kuma bukatar mu goyi bayan waɗanda Jehobah yake amfani da su don yin ja-goranci a ƙungiyarsa a yau. (Mat. 24:​45-47) Yin nazarin Kalmar Allah zai sa mu ƙarfafa bangaskiyarmu. Idan mun yi haka, bangaskiyarmu za ta zama kamar bishiyar da jijiyoyinta sun shiga ƙasa sosai. Sa’ad da Bulus ya rubuta wasiƙa ga ikilisiyar Kolosi, ya yi amfani da irin wannan kwatanci. Ya ce: “Tun da kun yarda cewa Yesu Almasihu shi ne Ubangijinku, sai ku ci gaba da yin tafiyarku a cikinsa. Kuna iya yin haka idan kun kafu sosai a cikinsa, kuna kuma gina kanku a tushen nan, kuma kuna tsayawa a kan bangaskiyarku.” (Kol. 2:​6, 7) Idan mun ƙarfafa bangaskiyarmu, Shaiɗan da magoya bayansa ba za su iya hana mu bin gaskiya ba.​—2 Yoh. 8, 9.

13. Me ya kamata mu sa rai cewa zai faru, kuma me ya sa?

13 Babu shakka, mutanen duniya za su tsane mu. (1 Yoh. 3:13) Yohanna ya tunasar mana cewa “duniya duka tana a hannun mugun nan.” (1 Yoh. 5:19) Yayin da ƙarshen zamanin nan yake kusatowa, Shaiɗan yana ƙara yin fushi. (R. Yar. 12:12) Ba lalata da ƙarairayin ʼyan ridda kaɗai Shaiɗan yake amfani da su don ya rinjaye mu ba. Yana yin amfani da tsanantawa ma. Shaiɗan ya san cewa lokacinsa ya ƙure, shi ya sa yake ƙoƙartawa don ya hana mu yin wa’azi kuma ya raunana bangaskiyarmu. Shi ya sa ba ma yin mamaki cewa an saka wa aikinmu takunkumi a ƙasashe da yawa. Duk da haka, ʼyan’uwa da ke ƙasashen suna jimrewa. Sun nuna cewa kome muguntar Shaiɗan, za mu ci gaba da jimrewa!

MU TAIMAKI JUNA DON MU RIƘA BIN GASKIYA

14. Me za mu yi don mu taimaka wa ʼyan’uwanmu su riƙa bin gaskiya?

14 Idan muna so mu taimaka wa ʼyan’uwanmu su riƙa bin gaskiya, dole ne mu zama masu juyayi. (1 Yoh. 3:​10, 11, 16-18) Muna bukatar mu ƙaunaci ʼyan’uwanmu har a lokacin da akwai matsaloli. Alal misali, ka san wani da aka yi masa rasuwa kuma yana bukatar taimako ko kuma ƙarfafawa? Ko kuma ka ji labarin wasu ʼyan’uwa da bala’i ya afko musu kuma suna bukatar taimako don su gina Majami’un Mulkinsu ko kuma gidajensu? Hanya ta musamman da za mu nuna cewa muna ƙaunar ʼyan’uwanmu kuma muna tausaya musu ita ce ta ayyukanmu ba ta furucinmu kaɗai ba.

15. Kamar yadda 1 Yohanna 4:​7, 8 suka nuna, me muke bukata mu yi?

15 Idan muna ƙaunar juna, muna yin koyi da Jehobah. (Karanta 1 Yohanna 4:​7, 8.) Hanya ta musamman da za mu nuna ƙauna ita ce ta gafarta wa juna. Alal misali, wani zai iya ɓata mana rai. Idan mun gafarta masa kuma muka mance da batun, za mu nuna cewa muna ƙaunar sa. (Kol. 3:13) Wani ɗan’uwa mai suna Aldo ya fuskanci wannan jarrabawar sa’ad da wani ɗan’uwa da ya daraja ya yi baƙar magana game da ƙabilarsa. Aldo ya ce, “Na yi addu’a ga Jehobah sau da sau don kada in tsani ɗan’uwan nan.” Amma Aldo ya yi wani abu kuma. Ya gaya wa ɗan’uwan su fita wa’azi tare. Sa’ad da suke wa’azi, sai Aldo ya gaya wa ɗan’uwan yadda furucinsa ya shafe shi. Aldo ya ce: “Sa’ad da na gaya wa ɗan’uwan yadda furucinsa ya shafe ni, sai ya ba ni haƙuri. Yadda ya yi magana ya nuna mini cewa ya yi da-na-sani sosai. Bayan haka, mun mance da batun kuma mun zama abokai na ƙwarai.”

16-17. Me ya kamata mu ƙuduri niyyar yi?

16 Manzo Yohanna yana ƙaunar ʼyan’uwansa sosai kuma yana so bangaskiyarsu ta yi ƙarfi, shi ya sa ya rubuta musu waɗannan wasiƙu uku. Abin ban-ƙarfafa ne sanin cewa maza da mata da za su yi sarauta da Yesu a sama suna da ƙauna kamar Yohanna!​—1 Yoh. 2:27.

17 Bari mu ci gaba da tunawa da batutuwan da muka tattauna. Bari mu ƙuduri niyyar bin gaskiya, wato yin biyayya ga Jehobah a dukan fannonin rayuwarmu. Mu riƙa yin nazarin Kalmar Allah kuma mu dogara gare shi. Mu yi imani sosai ga Yesu. Mu nisanta kanmu daga ra’ayin mutane da koyarwar ʼyan ridda. Kada mu riƙa bauta wa Jehobah, sa’an nan mu riƙa yin munanan abubuwa a ɓoye. Kuma kada mu saurari mutanen da suke so su rinjaye mu mu bi ra’ayinsu. Mu riƙa bin ƙa’idodin Jehobah. Kuma mu taimaka wa ʼyan’uwanmu su riƙa bin gaskiya ta wajen gafarta laifofinsu da kuma taimaka wa mabukata. Idan mun yi haka, dukanmu za mu ci gaba da bin gaskiya duk da famar da muke yi.

WAƘA TA 49 Mu Riƙa Faranta Ran Jehobah

^ sakin layi na 5 Shaiɗan uban ƙarya ne yake mulkin wannan duniyar. Saboda haka, muna fama kullum don mu riƙa bin gaskiya. Kiristoci a ƙarni na farko ma sun fuskanci wannan ƙalubalen. Jehobah ya hure manzo Yohanna ya rubuta wasiƙu uku domin ya taimaka musu da kuma mu a yau. Wasiƙun za su nuna mana abubuwan da za su iya hana mu bin gaskiya, da kuma matakan da za mu iya ɗaukawa.

^ sakin layi na 6 An canja wasu sunayen.

^ sakin layi na 11 Ka duba talifin nazarin nan “Ka San Gaskiyar Lamarin Kuwa?” a Hasumiyar Tsaro ta Agusta 2018.

^ sakin layi na 59 BAYANI A KAN HOTUNA: A makaranta, wata ʼyar’uwa matashiya tana yawan jin batutuwa game da luwaɗi. (A wasu al’adu, kalar bakar gizo tana wakiltar luwaɗi.) Daga baya, sai ta yi bincike don ta ƙarfafa bangaskiyarta. Hakan ya taimaka mata ta yanke shawara mai kyau.