Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 27

Kada Ku Ɗauki Kanku da Girma Fiye da Kima

Kada Ku Ɗauki Kanku da Girma Fiye da Kima

“Ina yi wa kowane ɗayanku gargaɗi cewa kada kowa ya ɗauki kansa da girma fiye da yadda ya kamata ya yi. A maimakon haka kowa ya mai da hankali game da yadda yake ganin kansa.”​—ROM. 12:3.

WAƘA TA 130 Mu Riƙa Gafartawa

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Kamar yadda Filibiyawa 2:3 ta nuna, ta yaya sauƙin kai za ta kyautata dangantakarmu?

MUNA yin biyayya ga Jehobah a koyaushe domin ya san abin da ya fi dacewa da mu. (Afis. 4:​22-24) Idan muna da sauƙin kai, za mu riƙa son yin abin da zai faranta wa Jehobah rai, kuma za mu ga cewa sauran mutane sun fi mu muhimmanci. A sakamakon haka, za mu ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah da kuma ʼyan’uwanmu a ikilisiya.​—Karanta Filibiyawa 2:3.

2. Mene ne manzo Bulus ya ce ba laifi ba ne, kuma mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 Amma idan ba mu yi hankali ba, za mu yi koyi da halayen mutanen duniyar nan masu fahariya da sonkai. * Zai yiwu cewa wasu Kiristoci a zamanin dā sun yi koyi da halayen nan, shi ya sa Manzo Bulus ya rubuta wasiƙa ga Romawa. Ya ce: “Ina yi wa kowane ɗayanku gargaɗi cewa kada kowa ya ɗauki kansa da girma fiye da yadda ya kamata ya yi. A maimakon haka kowa ya mai da hankali game da yadda yake ganin kansa.” (Rom. 12:3) A ayar nan, Bulus ya faɗi cewa muna bukatar mu riƙa daraja kanmu. Amma idan muna da sauƙin kai, ba za mu yi hakan fiye da kima ba. A wannan talifin, za mu tattauna hanyoyi uku da za mu guji daraja kanmu fiye da kima. Hanyoyin nan su ne (1) a aurenmu, (2) ayyukan da muke yi a ikilisiya, da (3) yadda muke amfani da kafofin sada zumunta.

KA NUNA SAUƘIN KAI A AURENKA

3. Me zai iya jawo matsala a aure, kuma wane mataki ne wasu suke ɗaukawa idan hakan ya faru?

3 Jehobah yana so mata da miji su riƙa farin ciki. Amma da yake su ajizai ne, za su iya samun saɓani a wasu lokuta. Manzo Bulus ya rubuta cewa mutanen da suka yi aure za su fuskanci matsaloli a rayuwa. (1 Kor. 7:28) Wasu ma’aurata suna yawan gardama, kuma hakan yana iya sa su yi tunani cewa ba su dace da juna ba. Idan suna da ra’ayin mutanen duniya, za su yi tunani cewa kashe aurensu ne mafita. Za su mai da hankali ga kansu, kuma su yi tunani cewa kashe auren ne zai sa su farin ciki.

4. Mene ne ya kamata mu guji yi?

4 Wajibi ne mu guji yin tunani cewa ba za mu iya jin daɗin aurenmu ba. Mun san cewa zina ce kaɗai za ta iya sa ma’aurata kashe aurensu. (Mat. 5:32) Saboda haka, idan mun soma fuskantar matsaloli a aurenmu, kada mu yarda fahariya ta sa mu soma tunani cewa: ‘Matata ko maigidana ba ya kula da ni. Ba ya ƙauna ta yadda ya kamata. Wataƙila zan fi yin farin ciki idan na auri wani.’ Ku lura cewa mai yin irin tunanin nan ya fi mai da hankali ga kansa. Mutanen duniya za su shawarce ka cewa ka bi zuciyarka kuma ka yi abin da zai sa ka farin ciki, ko da za ka bukaci kashe aurenka. Amma Jehobah ya shawarce mu cewa ‘kada mu kula da kanmu kaɗai, amma mu kula da waɗansu kuma.’ (Filib. 2:4) Jehobah ba ya so ka kashe aurenka. (Mat. 19:6) Yana so ka faranta masa rai ba kanka ba.

5. Kamar yadda Afisawa 5:33 ta nuna, yaya ya kamata mata da miji su bi da juna?

5 Ya kamata mata da miji su riƙa ƙauna da kuma daraja juna. (Karanta Afisawa 5:33.) Littafi Mai Tsarki ya ce bayarwa ta fi karɓa albarka. (A. M. 20:35) Mene ne zai taimaka wa mata da miji su riƙa ƙauna da kuma daraja juna? Sauƙin kai ne. Mijin da ke da sauƙin kai zai fi mai da hankali ga bukatun matarsa ba na kansa ba. Abin da matarsa ma za ta yi ke nan.​—1 Kor. 10:24.

Ma’aurata masu tawali’u ba sa gasa da juna, amma suna taimaka wa juna (Ka duba sakin layi na 6)

6. Wane darasi ne ka koya daga labarin Steven da Stephanie?

6 Kasancewa da sauƙin kai ya taimaka wa Kiristoci ma’aurata da yawa su riƙa jin daɗin aurensu. Alal misali, wani magidanci mai suna Steven ya ce: “Idan kai da matarka kuna da haɗin kai, musamman sa’ad da matsaloli suka taso, za ku iya sasanta matsalolin. Maimakon yin tunani a kan ‘abin da ya fi dacewa da kai, za ka yi tunani a kan abin da ya fi dacewa da ku biyu.” Matar Steven mai suna Stephanie ma tana da irin wannan ra’ayin. Ta ce: “Babu wani da ke son zama da mutumin da ke son gardama. A duk lokacin da matsaloli suka taso, muna mai da hankali a kan abin da ya jawo su. Bayan haka sai mu yi addu’a, mu yi bincike, kuma mu tattauna batun. Muna sasanta matsalar, maimakon yin faɗa da juna.” Mata da miji za su fi farin ciki idan suka fi mai da hankali ga bukatun juna.

KU BAUTA WA JEHOBAH DA “TAWALI’U”

7. Wane hali ne ya kamata ɗan’uwa ya kasance da shi sa’ad da ya sami ƙarin ayyuka?

7 Yin hidima ga Jehobah gata ce babba. (Zab. 27:4; 84:10) Idan wani ɗan’uwa yana so ya yi ƙarin ayyuka a hidimar Jehobah, hakan abu ne mai kyau. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duk wanda yake marmarin zaman mai kula da jama’ar masu bi, aikin daraja yake marmarinsa ne.” (1 Tim. 3:1) Amma idan ya sami ƙarin ayyuka, bai kamata ya yi tunani game da kansa fiye da kima ba. (Luk. 17:​7-10) Ya kamata ya kasance da sauƙin kai a duk ayyukansa.​—2 Kor. 12:15.

8. Wane darasi ne muka koya daga misalan Diyotarifis da Uzziah da kuma Absalom?

8 Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da labaran mutanen da suka fi mai da hankali ga kansu. Diyotarifis bai da sauƙin kai, shi ya sa yake so “ya zama na farko fiye da kowa” a ikilisiya. (3 Yoh. 9) Fahariya ta sa Uzziah ya yi aikin da Jehobah bai ce ya yi ba. (2 Tar. 26:​16-21) Absalom ya so ya zama sarki. Saboda haka, ya yi kamar ya damu da Isra’ilawa sosai domin su goyi bayansa. (2 Sam. 15:​2-6) Kamar yadda misalan nan suka nuna, Jehobah ba ya son mutanen da ke ɗaukaka kansu. (K. Mag. 25:27) Masu fahariya da neman girma suna jawo wa kansu matsaloli sosai.​—K. Mag. 16:18.

9. Wane misali ne Yesu ya kafa mana?

9 Yesu ba ya kamar waɗannan mutanen domin “ko da yake ya kasance cikin surar Allah, bai yi tunanin zama daidai da Allah ba.” (Filib. 2:​6, New World Translation) Ko da yake Jehobah ne kaɗai ya fi Yesu iko, Yesu ba ya ɗaukan kansa da daraja fiye da kima. Ya gaya wa almajiransa cewa: “Wanda ya fi ƙanƙanta a cikinku duka, shi ne ya fi girma.” (Luk. 9:48) Muna jin daɗin yin hidima tare da majagaba da bayi masu hidima da dattawa da kuma masu kula da da’ira da suke nuna sauƙin kai kamar Yesu. Idan muna da sauƙin kai, za mu ƙaunaci mutane sosai kuma Yesu ya ce bayinsa za su riƙa ƙaunar juna.​—Yoh. 13:35.

10. Me ya kamata ka yi idan kana ganin cewa dattawa ba su magance matsaloli yadda ya dace ba?

10 Me ya kamata ka yi idan ka lura cewa akwai wasu matsaloli a cikin ikilisiya, kuma kana ganin ba a magance su yadda ya kamata ba? Maimakon yin gunaguni, ka nuna cewa kai mai sauƙin kai ne ta wajen goyon bayan dattawa. (Ibran. 13:17) Abin da zai taimaka maka shi ne tambayoyin nan: ‘Shin matsalolin da na lura da su suna da tsanani sosai? Yanzu ne lokacin da ya fi dacewa a magance su? Hakkina ne in magance su? Idan na ɗauki mataki, hakan zai sa ʼyan’uwa su fi kasancewa da haɗin kai? Ina nema ne in ɗaukaka kaina?’

Ya kamata a san ʼyan’uwa masu ayyuka da yawa a ikilisiya a matsayin masu sauƙin kai, ba ƙwarewa kaɗai ba (Ka duba sakin layi na 11) *

11. Kamar yadda Afisawa 4:​2, 3 suka nuna, mene ne sakamakon kasancewa da sauƙin kai?

11 A wurin Jehobah, kasancewa da sauƙin kai da kuma haɗin kai ya fi iya aiki da kuma ƙwarewa. Saboda haka, ka yi iya ƙoƙarinka don ka zama mai sauƙin kai. Idan ka yi haka, za ka sa ʼyan’uwa a ikilisiya su kasance da haɗin kai. (Karanta Afisawa 4:​2, 3.) A waɗanne hanyoyi ne za ka iya nuna sauƙin kai? Ka kasance da ƙwazo a wa’azi. Ka nemi zarafin yin alheri ga mutane. Ka nuna wa kowa alheri, har ga mutanen da ba su da gata a cikin ikilisiya. (Mat. 6:​1-4; Luk. 14:​12-14) Yayin da ka ci gaba da nuna tawali’u, ʼyan’uwa a ikilisiya za su lura da hakan.

KA NUNA TAWALI’U SA’AD DA KAKE AMFANI DA KAFOFIN SADA ZUMUNTA

12. Shin Littafi Mai Tsarki ya haramta yin abokai ne? Ka bayyana.

12 Jehobah yana so mu ji daɗin yin cuɗanya da iyalanmu da kuma abokanmu. (Zab. 133:1) A lokacin da Yesu yake duniya, yana da abokan kirki. (Yoh. 15:15) Littafi Mai Tsarki ya faɗi amfanin samun abokan kirki. (K. Mag. 17:17; 18:24) Kuma ya gaya mana kada mu kaɗaita kanmu. (K. Mag. 18:1) Mutane da yawa suna ganin cewa kafofin sada zumunta hanya ce ta samun abokai da yawa, kuma zai hana mu kaɗaici. Amma muna bukatar mu yi hattara da yadda muke amfani da wannan dandalin.

13. Me ya sa wasu da suke amfani da kafofin yaɗa zumunta suke baƙin ciki da kaɗaici?

13 Binciken da aka yi ya nuna cewa mutanen da suke yawan ɓata lokaci suna kallon abubuwan da wasu suka saka a dandalin sada zumunta, suna fuskantar baƙin ciki da kaɗaici. Me ya sa? Domin mutane suna yawan saka hotunan abubuwa na musamman da suka faru a rayuwarsu da na abokansu da kuma wurare masu kyau da suka je. Mutumin da ke kallon waɗannan hotunan zai yi tunani cewa ba ya jin daɗin rayuwa. Wata ʼyar’uwa mai shekara 19 ta ce: “Na soma baƙin ciki sa’ad da na ga cewa mutane suna shaƙatawa a ƙarshen mako, ni kuma ina gida ba na kome.”

14. Ta yaya shawarar da ke 1 Bitrus 3:8 za ta iya taimaka mana game da yin amfani da dandalin sada zumunta?

14 Babu shakka, za a iya yin amfani da kafofin yaɗa zumunta a hanyoyi masu kyau. Alal misali, sadawa da abokai da iyalai. Amma ka lura cewa wasu abubuwa da mutane suke sakawa a kafofin sada zumunta don su ɗaukaka kansu ne. Kamar dai suna yin tallar kansu ne. Wasu suna ma yin ɗanyen magana ko baƙar magana game da hotunan da mutane suka saka. Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa Kiristoci su riƙa nuna ƙauna da sauƙin kai. Saboda haka, bai kamata su yi amfani da kafofin sada zumunta a wannan hanyar ba.​—Karanta 1 Bitrus 3:8.

Abubuwan da kake sakawa a kafofin sada zumunta suna nuna cewa kai mai tawali’u ne ko mai girman kai? (Ka duba sakin layi na 15)

15. Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu guji ɗaukaka kanmu?

15 Idan kana yin amfani da dandalin sada zumunta, ka yi wa kanka tambayoyin nan: ‘Shin hotuna da bidiyoyi da kuma furucin da na saka suna sa mutane su ji cewa ina fahariya ne? Hakan zai iya sa mutane kishi ne?’ Littafi Mai Tsarki ya ce: “Dukan abubuwan da suke a duniya, kamar neman biyan sha’awa ta jiki, da kwaɗayin ido, da kuma taƙama da abubuwan rayuwa. Waɗannan dai ba daga wurin Uba suka fito ba, amma daga duniya ne suka fito.” (1 Yoh. 2:16) Ga yadda aka fassara furucin nan “taƙama da abubuwan rayuwa” a wani juyin Littafi Mai Tsarki, “son nuna cewa kana da daraja sosai.” Bai kamata Kiristoci su riƙa taƙama da kansu ba. Suna bin shawarar nan da ke Littafi Mai Tsarki: “Kada mu zama masu girman kai ko masu tā da hankalin juna ko masu kishin juna.” (Gal. 5:26) Idan muna da sauƙin kai, ba za mu faɗa cikin wannan tarkon ba.

MU ‘MAI DA HANKALI A KAN YADDA MUKE GANIN KANMU’

16. Me ya sa za mu guji yin fahariya?

16 Muna bukatar mu zama masu sauƙin kai domin masu fahariya suna ‘ganin kansu’ yadda bai dace ba. (Rom. 12:3) Masu fahariya suna gasa da kuma ji da kansu. Tunaninsu da kuma ayyukansu na yawan ɓata wa mutane rai. Idan ba su canja ra’ayinsu ba, za su zama masu fahariya sosai kuma Shaiɗan zai gurɓata zukatansu da kuma tunaninsu. (2 Kor. 4:4; 11:3) Amma mai sauƙin kai yana ganin kansa yadda ya dace kuma ya san cewa wasu sun fi shi daraja. (Filib. 2:3) Ya san cewa “Allah yana gāba da masu girman kai, amma yana yi wa masu sauƙin kai alheri.” (1 Bit. 5:5) Irin mutanen nan ba sa so su ɓata dangantakarsu da Jehobah.

17. Me za mu yi don mu ci gaba da zama masu sauƙin kai?

17 Idan muna so mu ci gaba da zama masu sauƙin kai, wajibi ne mu bi shawarar nan da ta ce mu ‘kawar da halinmu na dā da ayyukansa,’ kuma mu “ɗauki sabon hali.” Yin hakan ba cin tuwo ba ne. Muna bukatar mu yi nazari game da ayyukan Yesu kuma mu yi koyi da shi. (Kol. 3:​9, 10; 1 Bit. 2:21) Idan mun yi hakan, za mu amfana sosai. Idan mun zama masu sauƙin kai, iyalinmu za su zauna lafiya, za mu sa ʼyan’uwa a ikilisiya su kasance da haɗin kai, kuma za mu yi amfani da kafofin yaɗa zumunta yadda ya dace. Ban da haka ma, Jehobah zai albarkace mu kuma za mu sami amincewarsa.

WAƘA TA 117 Mu Riƙa Yin Alheri Kamar Allah

^ sakin layi na 5 A yau, mutane masu fahariya da sonkai sun cika ko’ina. Ya kamata mu mai da hankali don kada mu koyi halayensu. A wannan talifin, za mu tattauna hanyoyi uku da ya kamata mu mai da hankali don kada mu ɗauki kanmu da girma fiye da kima.

^ sakin layi na 2 MA’ANAR WASU KALMOMI: Mutumin da ke da fahariya yana ganin ya fi sauran mutane daraja. Saboda haka, mutum mai fahariya yana sonkai. Amma mai sauƙin kai ba ya nuna sonkai. Idan kai mai tawali’u ne, ba za ka riƙa yin girman kai ba ko kuma ka yi tunanin cewa ka fi kowa daraja ba.

^ sakin layi na 56 BAYANI A KAN HOTUNA: Wani dattijo da ya iya yin jawabi sosai a taron yanki da kuma ja-goranci a aikin gini, yana ja-goranci a wa’azi kuma yana share Majami’ar Mulki.