Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

Na Yi Abin da Ya Kamata In Yi

Na Yi Abin da Ya Kamata In Yi

ƊAN’UWA Donald Ridley lauya ne da ya yi fiye da shekaru 30 yana kāre Shaidun Jehobah a kotu. Ya taimaka wa likitoci su fahimci cewa majiyata suna da ’yanci ƙin karɓan ƙarin jini. Ya taimaka wa ƙungiyar Jehobah ta ci nasara a shari’o’i da yawa da aka yi a kotu a Amirka. Abokansa suna kiran shi Don, kuma shi mai ƙwazo ne da sauƙin kai kuma yana sadaukar da kai sosai.

A shekara ta 2019, an gano cewa Ɗan’uwa Don yana da wani ciwon ƙwaƙwalwa da bai da magani. Ciwon ya yi tsanani sosai, kuma Don ya rasu a ranar 16 ga Agusta, 2019. Ga labarinsa.

An haife ni a birni St. Paul a jihar Minnesota a Amirka, a shekara ta 1954. Muna bin addinin Katolika, kuma iyayena ba talakawa ba ne kuma ba masu arziki ba ne. Ni ne ɗa na biyu a cikin yara biyar da iyayena suka haifa. Na je makarantar Katolika kuma ni ne nake taimaka wa firist sa’ad da ake bukukuwa a coci. Duk da haka, ban san koyarwar Littafi Mai Tsarki sosai ba. Na yi imani cewa Allah ne ya halicci kome, amma ba na ganin cewa cocin Katolika zai taimaka mini in bauta wa Allah.

YADDA NA KOYI GASKIYA

Shaidun Jehobah sun ziyarci gidanmu a shekara ta farko da nake makarantar lauyoyi a William Mitchell College of Law. A lokacin ina wanki, kuma ma’auratan suka ce za su dawo. Sa’ad da suka dawo, na yi musu tambayoyi biyu cewa: “Me ya sa mutanen kirki ba sa yin arziki?” kuma “Mene ne mutum zai yi don ya riƙa farin ciki?” Sun ba ni littafin nan Gaskiya Mai-bishe Zuwa Rai Madawwami da kuma New World Translation of the Holy Scriptures. Na amince su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Hakan ya taimaka mini in koyi abubuwa masu kayatarwa. Sanin cewa Mulkin Allah ne gwamnatin da za ta mulki duniya ya burge ni sosai. A bayyane yake cewa mulkin ’yan Adam ba zai taimaka mana ba. Maimakon haka, ya jawo wahala da rashin adalci da kuma bala’i.

Na yi alkawarin bauta wa Jehobah a shekara ta 1982 kuma na yi baftisma a shekarar a taron yanki mai jigo “Kingdom Truth” wanda aka yi a wurin taron St. Paul Civic Center. Mun yi hayar wurin taron ne. Na sake komawa wurin da aka yi taron bayan mako ɗaya don in rubuta jarrabawar zama lauya. A farkon watan Oktoba, an sanar da ni cewa na ci jarrabawar, kuma hakan ya sa na zama lauya.

A wannan taron yankin “Kingdom Truth,” na haɗu da wani ɗan’uwa mai suna Mike Richardson da ke hidima a Bethel a Brooklyn. Ya gaya mini cewa an kafa sashen shari’a a hedkwatarmu. Hakan ya sa na tuna furucin Bahabashe da ke Ayyukan Manzanni 8:36 kuma na tambayi kaina, ‘Mene ne zai hana ni neman yin aiki a Sashen Shari’a?’ Sai na cika fom ɗin yin hidima a Bethel.

Iyayena ba su yi farin ciki cewa na zama Mashaidin Jehobah ba. Mahaifina ya tambaye ni ko yin hidima a Bethel a matsayin lauya zai taimaka mini. Na bayyana masa cewa aikin na son rai ne. Na gaya masa cewa za a riƙa ba ni guzurin dala 75 da ake ba waɗanda ke hidima a Bethel.

Domin na riga na soma aiki a wani kotu, ban sami damar zuwa Bethel nan da nan ba, amma na soma hidima a Bethel a Brooklyn, a shekara ta 1984. An tura ni yin hidima a Sashen Shari’a. Aikin da na yi a kotu ya taimaka mini in iya yin aiki a Sashen Shari’a a Bethel.

AN YI WA STANLEY THEATER KWASKWARIMA

Yadda filin wasan Stanley Theater yake sa’ad da aka saye shi

An sayi filin wasan Stanley Theater da ke birnin Jersey City a jihar New Jersey, a watan Nuwamba 1983. ’Yan’uwa sun nemi izini don su gyara wutan lantarki da kuma famfo da ke ginin. Sa’ad da suka haɗu da hukumomin, ’yan’uwan sun bayyana musu cewa suna so su riƙa yin amfani da ginin don yin taron yanki. Hakan ya jawo matsala, domin a dokar birnin, ya kamata wuraren ibada su kasance kusa da inda mutane ke zama. Amma Stanley Theater yana wurin da ake kasuwanci. Don haka, hukumomin sun ƙi ba da izinin. ’Yan’uwan sun ɗaukaka ƙara amma kotu ta ƙi ta saurare su.

A mako na farko da na yi a Bethel, ƙungiyarmu ta kai ƙara kotu cewa bai kamata a ƙi ba su izinin yin amfani da wurin taron ba. Domin na yi aikin shekara biyu a kotu a birnin St. Paul da ke Minnesota, na saba fuskantar irin wannan batun. Ɗaya daga cikin lauyoyinmu ya ce an sha yin amfani da wurin don kallon fina-finai da kuma kaɗe-kaɗe. To, me ya sa za a ce ba zai dace a yi ayyukan ibada a wurin ba? Kotu ta bincika batun kuma ta yanke hukunci cewa hukumomi a Jersey City ba su daraja ’yancin da mutane ke shi na bin addininsu ba. Kotu ta ba da umurni cewa hukumomi su ba da izinin yin amfani da wurin don yin ayyukan ibada. Hakan ya sa na ga cewa Jehobah ya albarkaci yadda ƙungiyarsa ke amfani da lauyoyi don kāre hakkinmu na yin wa’azi. Na yi farin ciki cewa na saka hannu a wannan batun.

’Yan’uwa sun soma aiki sosai don su yi wa wurin kwaskwarima. Bayan haka, an yi taron sauke karatu na aji na 79 na Makarantar Gilead a Majami’ar Babban Taro da ke Jersey City a ranar 8 ga Satumba, 1985, bayan shekara ɗaya da aka soma kwaskwarimar. Na yi farin ciki sosai don na taimaka wajen yi wa Jehobah wannan aikin. Aikin ya sa ni farin ciki sosai fiye da wanda na yi kafin in je Bethel. Ban san cewa Jehobah zai yi amfani da ni a wasu batutuwan shari’a ba.

KĀRE ’YANCIN ƘIN KARƁAN JINI

A shekara ta 1980 zuwa 1989, likitoci da asibitoci ba sa daraja ’yancin Shaidu na ƙin karɓan ƙarin jini. Mata masu juna biyu ne suka fi fuskantar ƙalubale domin alƙalai suna ganin cewa ba su da ’yancin ƙin karɓan ƙarin jini. Alƙalan sun ce idan mahaifiyar ba ta karɓi ƙarin jini ba, tana iya mutuwa kuma hakan yana nufin cewa yaron zai yi girma ba mahaifiya.

A ranar 29 ga Disamba, 1988, wata ’yar’uwa mai suna Denise Nicoleau ta yi fama da yoyon jini bayan ta haihu. Jininta ya ragu sosai, kuma likitan da ke kula da ita ya ce ta amince a ƙara mata jini. Amma ’yar’uwa Nicoleau ta ƙi amincewa. Washegari da safe, asibitin ta nemi izinin kotu don su ƙara wa ’yar’uwar jini ƙarfi-da-yaji. Ba tare da jin ra’ayin ’Yar’uwa Nicoleau ko mijinta ba, alƙalin ya ba da izini a ba ta ƙarin jini.

A ranar Jumma’a, 30 ga Disamba, ma’aikatan asibitin sun ba ’yar’uwar ƙarin jini duk da cewa mijin ’yar’uwar da kuma iyalinta sun ƙin amincewa da hakan. A ranar da yamma, ’yan sanda sun kama ’yan iyalin da yawa da kuma dattawa biyu domin sun yi yunƙurin hana ma’aikata a asibitin ba ’yar’uwar ƙarin jini. A ranar Asabar, 31 ga Disamba da safe, kafofin yaɗa labarai a jihar New York da kuma Long Island sun ba da labarin ’yan’uwan da aka kama.

Ni da Ɗan’uwa Philip Brumley sa’ad da ba mu tsufa ba

A ranar Litinin da safe, na tattauna da alƙalin babban kotu mai suna Milton Mollen. Na bayyana masa abin da ya faru cewa alƙalin da ya yanke hukuncin ya ba da izinin ba da ƙarin jini ba tare da ya saurari ra’ayin majiyyacin ba. Alƙali Mollen ya ce in zo ofishinsa da rana don mu tattauna dokokin da suka shafi batun. Ɗan’uwan da ke kula da Sashen Shari’a mai suna Philip Brumley ya bi ni don mu je ofishin Alƙali Mollen da yamma. Alƙalin ya gayyaci lauyan asibitin zuwa ofishinsa. Mun yi mūsu sosai. Har Ɗan’uwa Brumley ya yi ɗan rubuta ya miƙa mini cewa “in natsu.” Shawarar da ya ba ni ta dace sosai domin raina ya soma ɓacewa sa’ad da nake ƙoƙarin nuna wa lauyan cewa abin da suka yi bai dace ba.

Daga hagu zuwa dama: Richard Moake da Gregory Olds da Paul Polidoro da Philip Brumley da ni da kuma Mario Moreno. Su lauyoyinmu ne sa’ad da ake shari’a a kotun ƙoli na Amirka tsakanin Watchtower da Village of Stratton. Ka duba mujallar Awake! na 8 ga Janairu, 2003

Bayan awa guda, alƙali Mollen ya gaya mana cewa shari’ar ce za a fara yi washegari. Sa’ad da muke barin ofishinsa, Alƙali Mollen ya gaya wa lauyan asibitin cewa yana da “aiki mai wuya gobe.” Hakan yana nufin cewa ba zai yi masa sauƙi ya nuna cewa asibitin yana da izinin ba ’yar’uwa Nicoleau ƙarin jini ƙarfi-da-yaji ba. Na ji kamar Jehobah yana tabbatar mini cewa za mu yi nasara a wannan shari’a. Abin ban mamaki ne ganin yadda Jehobah yake yin amfani da mu don cika nufinsa.

Mun yi aiki har dare don mu shirya abin da za mu faɗa a kotun washegari. Kotun yana kusa da Bethel da ke Brooklyn, don haka yawancin ’yan’uwan da ke aiki a Sashen Shari’a sun taka zuwa kotun. Bayan alƙalai huɗu sun saurari ƙarar, sun yanke hukunci cewa bai dace da aka ba ’yar’uwar ƙarin jini ba. Kotun ta yanke hukunci cewa ma’aikatan asibitin sun yi laifi, kuma sun taka hakkin ʼYar’uwa Nicoleau sa’ad da suka ba ta ƙarin jini ba tare da jin ra’ayinta ba.

Ba da daɗewa ba, babban kotun da ke jihar New York ta amince cewa ’Yar’uwa Nicoleau tana da ʼyancin yin jinya ba tare da ƙarin jini ba. Wannan shi ne batun ƙarin jini na farko cikin huɗu da kotu ta yi shari’a a kai kuma gata ce babba da na sami damar saka hannu a waɗannan batutuwan. (Ka duba akwatin nan “ Nasarorin da Aka Ci a Kotun Ƙoli.”) Ban da haka, ni da wasu lauyoyi a Bethel mukan yi shari’a da ta shafi batun riƙon yara da kashe aure da yin amfani da fili da kuma gine-gine.

AURENA DA KUMA IYALINA

Ni da matata Dawn

Matata Dawn bazawara ce mai yara uku sa’ad da muka haɗu. Tana aiki da kuma hidimar majagaba. Ta fuskanci matsaloli sosai a rayuwa, kuma yadda ta ƙuduri niyyar bauta wa Jehobah ne ya burge ni. A shekara ta 1992, mun halarci taron yanki mai jigo “Masu-Ɗauke da Haske” kuma a wurin ne na gaya mata mu soma fita zance. Bayan shekara ɗaya, sai muka yi aure. Samun mata da ke ƙaunar Jehobah kuma da ke da fara’a kyauta ce daga Allah. Na yi farin ciki a dukan shekarun da muka yi tare da matata.​—K. Mag. 31:12.

A lokacin da muka yi aure, shekarun yaran matata 11 da 13 da kuma 16 ne. Ina so in zama mahaifi nagari, saboda haka, na karanta kuma na bi dukan shawarwarin da ke littattafanmu na zama mahaifin kirki. Mun fuskanci ƙalubale, amma ina farin ciki cewa yaran sun ɗauke ni a matsayin abokin kirki da kuma uba mai ƙauna. Muna marabtar abokan yaranmu kuma muna jin daɗin yin cuɗanya da su.

A shekara ta 2013, ni da matata mun ƙaura zuwa jihar Wisconsin don mu kula da iyayen matata da suka tsufa. Na yi farin ciki cewa hakan bai hana ni yin hidima a wasu lokuta a Bethel ba. Ina hidima na ɗan lokaci a sashen shari’a.

CANJI FARAT ƊAYA

A watan Satumba 2018, na lura cewa ina yawan yin tari kafin in yi magana. Na je wurin likitan da ke yankinmu, amma bai gano abin da ke damuna ba. Daga baya, wani likita ya ce in je wurin likitan ƙwaƙwalwa. A watan Janairu 2019, likitan ya gano cewa ina da wata cutar ƙwaƙwalwa da ke naƙasar da gaɓoɓin jikina da ake kira Progressive Supranuclear Palsy (PSP).

Bayan kwana uku, sa’ad da nake wasa, sai na faɗi na karya hannun damana. Na daɗe ina yin wannan wasan kuma na ƙware sosai. Abin da ya faru ya sa na san cewa gaɓoɓin jikina sun soma sanyi. Yadda ciwon ya yi tsanani da sauri ya ba ni mamaki sosai, domin ya sa ba na iya yin magana da kyau da tafiya, kuma haɗiye abu yana min wuya.

Ina farin ciki sosai cewa na taimaka wa ƙungiyar Jehobah a matsayin lauya. Na yi farin ciki cewa na rubuta talifofin a jaridu da likitoci da lauyoyi da kuma alƙalai suka karanta. Ban da haka, na ba da jawabai a faɗin duniya don kāre ’yancin Shaidun Jehobah na yin jinya ba tare da ƙarin jini ba. Har ila ina da irin ra’ayin marubucin Luka 17:10 da ya ce: ‘Ni bawa ne marar cancanta. Na dai yi abin da ya kamata in yi ne kawai.’