TALIFIN NAZARI NA 29
Sa’ad da Ba Ni da Karfi Ne Nake da Karfi
“Na gamsu da rashin ƙarfina, da cin mutuncin da ake yi mini, da shan wahala, da tsanani, da masifu saboda Almasihu.”—2 KOR. 12:10.
WAƘA TA 38 Zai Ƙarfafa Ka
ABIN DA ZA A TATTAUNA *
1. Mene ne Bulus ya faɗa game da kansa?
MANZO BULUS ya bayyana sarai cewa akwai lokutan da ya yi sanyin gwiwa. Ya ce jikinsa “yana ta lalacewa,” yana famar yin abin da ya dace, kuma ba a kowane lokaci ba ne Jehobah yake amsa addu’o’insa yadda yake zato ba. (2 Kor. 4:16; 12:7-9; Rom. 7:21-23) Bulus ya kuma ce maƙiyansa suna ganin shi marar ƙarfi ne. * Amma bai ƙyale baƙaƙen maganganu da mutane suka yi game da shi ko kuma kasawarsa su sa shi sanyin gwiwa ba.—2 Kor. 10:10-12, 17, 18.
2. Kamar yadda 2 Korintiyawa 12:9, 10 suka nuna, wane darasi mai kyau ne Bulus ya koya?
2 Bulus ya koyi darasi mai kyau cewa za mu iya kasancewa da ƙarfi ko da muna sanyin gwiwa. (Karanta 2 Korintiyawa 12:9, 10.) Jehobah ya gaya wa Bulus cewa “alherina ya ishe ka,” wato Jehobah yana nufin cewa zai ba Bulus ƙarfin da yake bukata. Bari mu fara tattauna dalilin da ya sa bai kamata mu yi fushi ba idan maƙiyanmu suka zage mu.
KA “GAMSU DA . . . CIN MUTUNCI”
3. Me ya sa ya kamata mu gamsu da cin mutunci?
3 Babu wani a cikinmu da yake so a ci mutuncinsa. Amma, muna iya yin sanyin gwiwa idan maƙiyanmu suka ci mutuncinmu kuma muka yi fushi sosai don abin da suka faɗa. (K. Mag. 24:10) To, ta yaya za mu ɗauki zage-zage da maƙiyanmu suke mana? Kamar Bulus, zai dace mu “gamsu da . . . cin mutunci.” (2 Kor. 12:10) Me ya sa? Domin idan mutane suna tsananta mana kuma suna ci mana mutunci, hakan yana nuna cewa mu almajiran Yesu ne na gaske. (1 Bit. 4:14) Yesu ya ce za a tsananta wa mabiyansa. (Yoh. 15:18-20) Hakan ya faru a ƙarni na farko. A lokacin, waɗanda suke bin al’adun Girkawa suna ganin cewa Kiristoci jahilai ne marasa ƙarfi. Ƙari ga haka, Yahudawa suna ganin cewa Kiristoci ‘marasa ilimi ne, da talakawa’ kamar manzo Bitrus da Yohanna. (A. M. 4:13) Kiristoci ba sa saka hannu a siyasa kuma ba sa shiga aikin soja. Saboda haka, mutane da yawa suna ganin cewa su marasa ƙarfi ne kuma ba wanda zai taimaka musu.
4. Mene ne Kiristoci a dā suka yi sa’ad da aka yi baƙaƙen maganganu game da su?
4 Shin waɗannan Kiristoci sun bar baƙaƙen maganganu na maƙiyansu su sa su sanyin gwiwa? A’a. Alal misali, manzo Bitrus da Yohanna suna ganin gata ne a tsananta musu don bin Yesu da kuma koya wa mutane game da shi. (A. M. 4:18-21; 5:27-29, 40-42.) Bai kamata manzannin su ji kunya ba. Ko da yake mutane sun rena Kiristocin, amma alherin da suka yi ga mutane ya fi na maƙiyansu. Alal misali, littattafan Littafi Mai Tsarki da Kiristocin suka rubuta suna ci gaba da taimaka wa miliyoyin mutane har yau. Yesu yana sarauta yanzu a Mulkin da suka yi wa’azi game da shi, kuma nan ba da daɗewa ba, dukan ʼyan Adam za su amfana daga Mulkin. (Mat. 24:14) Sarakunan ƙasar Roma da suka tsananta wa Kiristoci sosai sun daina wanzuwa. Amma waɗannan manzannin Yesu masu aminci suna sarauta a sama yanzu. Babu shakka, abokan gabansu sun riga sun mutu, amma idan akwai wani cikinsu da aka tayar daga matattu, za su zama talakawan Mulkin da Kiristocin nan suka yi shelar sa.—R. Yar. 5:10.
5. Kamar yadda Yohanna 15:19 ta nuna, me ya sa ake rena Shaidun Jehobah?
5 A yau, wasu mutane sun rena mu kuma suna ganin cewa mu jahilai ne da kuma marasa ƙarfi. Me ya sa? Domin ba mu da irin halayen mutanen duniya. Mu masu sauƙin kai ne da kuma biyayya. Amma mutanen duniya suna son masu fahariya da kuma taurin kai. Ƙari ga haka, ba ma shiga siyasa ko kuma aikin soja. Mun yi dabam da mutanen duniya, shi ya sa suke rena mu.—Karanta Yohanna 15:19; Rom. 12:2.
6. Mene ne Jehobah yake amfani da bayinsa don ya cim ma?
6 Duk da cewa mutanen duniya sun rena mu, amma Jehobah yana amfani da mu don cim ma abubuwa da dama. Muna wa’azin da ba a taɓa yin irinsa ba. Mujallunmu ne aka fi fassarawa da kuma rarrabawa a duniya. Kuma muna amfani da Littafi Mai Tsarki wajen kyautata rayuwar miliyoyin mutane. Jehobah ne yake sa a cim ma abubuwan nan. Shi ne yake amfani da bayinsa waɗanda mutanen duniya suka rena don ya yi abubuwan nan masu ban mamaki. Jehobah zai iya yin amfani da kowannenmu kuwa? Idan haka ne, me muke bukatar mu yi don ya taimaka mana? Yanzu, bari mu tattauna darussa uku da za mu iya koya daga misalin manzo Bulus.
KADA KA DOGARA GA ƘARFINKA
7. Wane darasi ne muka koya daga misalin Bulus?
7 Ga darasi ɗaya da muka koya daga A. M. 5:34; 22:3) Kuma akwai lokacin da Yahudawa da yawa suke girmama Bulus sosai. Ya ce: “Kun kuma san yadda a addinin Yahudanci na fi yawancin Yahudawa waɗanda muka yi girma tare.” (Gal. 1:13, 14; A. M. 26:4) Amma Bulus bai dogara ga kansa ba.
misalin Bulus: Kada mu dogara ga ƙarfinmu ko iyawarmu a matsayinmu na bayin Jehobah. Manzo Bulus yana da abubuwan da za su iya sa shi girman kai da kuma dogara da kansa. Ya yi girma a Tarsus, babban birnin wani lardi a ƙasar Roma. Tarsus birni ne mai arziki da kuma sanannun makarantu. Bulus ya karantu sosai. Wani sanannen Bayahude mai suna Gamaliyel ne ya koyar da shi. (8. Kamar yadda Filibiyawa 3:8 ta nuna, ta yaya Bulus ya ɗauki abubuwan da ya yasar, kuma me ya sa ya ce “na gamsu da rashin ƙarfina”?
8 Bulus ya yi farin cikin yin watsi da abubuwan nan da mutane suke ganin suna da muhimmanci. Ya ga cewa abubuwan nan da ya bari “abin banza” ne, wato suna kamar shara. (Karanta Filibiyawa 3:8.) Bulus ya sha wahala sosai don ya zama mabiyin Yesu. Mutanen ƙasarsu sun tsane shi. (A. M. 23:12-14) Shi ɗan ƙasar Roma ne, amma mutanen ƙasar sun yi masa dūka kuma suka saka shi a kurkuku. (A. M. 16:19-24, 37) Ƙari ga haka, Bulus ya san cewa shi ajizi ne kuma yin abin da ya dace bai da sauƙi. (Rom. 7:21-25) Ya ci gaba da bin Yesu duk da matsalolin da yake da shi. Ya ce: “Na gamsu da rashin ƙarfina.” Me ya sa? Domin a lokacin da yake sanyin gwiwa ne Allah ya taimaka masa.—2 Kor. 4:7; 12:10.
9. Yaya ya kamata mu ɗauki abubuwan da za su iya sa mu sanyin gwiwa?
9 Idan muna so Jehobah ya ƙarfafa mu, bai kamata mu yi tunani cewa iliminmu ko al’adarmu ko kuma wadatarmu zai sa Jehobah ya daraja mu ba. Babu shakka, kaɗan daga cikin bayin Jehobah ne ‘suke da hikima bisa ga ganin mutum, kaɗan kuma daga cikinmu ne suke riƙe da babban matsayi, kuma kaɗan ne suke ʼya’yan manya. Duk da haka, Jehobah ya ‘zaɓi abin da mutane suke gani kamar ya kāsa.’ 1 Kor. 1:26, 27) Saboda haka, kada ka yi tsammani cewa idan ba ka da abubuwan nan da aka ambata, ba za ka iya bauta wa Jehobah ba. Maimakon haka, ka kasance da ra’ayin da ya dace. Ta yaya za ka yi hakan? Ka tuna cewa idan ba ka da abubuwan da mutanen duniya suke darajawa, za ka sami damar ganin yadda Jehobah yake taimaka maka. Alal misali, idan kana tsoron mutanen da suke sa ka yi shakkar imaninka, ka roƙi Jehobah ya ba ka ƙarfin zuciya don ka kāre imaninka. (Afis. 6:19, 20) Idan kana fama da rashin lafiya mai tsanani, ka roƙi Jehobah ya ba ka ƙarfin yin iya ƙoƙarinka a hidimarsa. A duk lokacin da Jehobah ya taimaka maka, hakan zai ƙarfafa bangaskiyarka, kuma za ka ƙara ƙarfi.
(KA YI KOYI DA MUTANEN DĀ
10. Me ya sa ya kamata mu yi nazarin labaran bayin Jehobah na dā da aka ambata a Ibraniyawa 11:32-34?
10 Bulus ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki sosai. Ya koyi darussa da yawa daga labaran bayin Jehobah masu aminci da ya karanta labaransu. A lokacin da ya rubuta wasiƙa ga Kiristoci Ibraniyawa, ya ce su yi la’akari da misalan bayin Jehobah na zamanin dā masu aminci. (Karanta Ibraniyawa 11:32-34.) Ka yi la’akari da misalin ɗaya daga cikinsu, wato Sarki Dauda. Ya fuskanci tsanantawa daga maƙiyansa da kuma wasu abokansa. Yayin da muke tattauna misalin Dauda, za mu fahimci yadda misalinsa ya taimaka wa Bulus, da kuma yadda za mu yi koyi da Bulus.
11. Me ya sa Goliyat ya yi zato cewa Dauda marar ƙarfi ne? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)
11 Goliyat yana da ƙarfi sosai kuma yana ganin Dauda marar ƙarfi ne. A lokacin da Goliyat ya ga Dauda, “sai ya rena shi.” Goliyat ƙato ne, yana da makamai kuma shi jarumi ne. Dauda kuma ƙaramin yaro ne kuma bai iya yaƙi ba. Duk da haka, yana da ƙarfi sosai. Ya dogara ga Jehobah kuma Jehobah ya taimaka masa ya yi nasara a kan Goliyat.—1 Sam. 17:41-45, 50.
12. Wane ƙalubale ne kuma Dauda ya fuskanta?
12 Akwai wani ƙalubale kuma da zai iya sa Dauda sanyin gwiwa. Dauda ya yi wa Saul, sarkin da Jehobah ya naɗa a Isra’ila hidima. Da farko, sarki Saul yana daraja Dauda. Amma daga baya, fahariya ta sa Saul ya soma ƙishin Dauda. Saul ya wulaƙanta Dauda, har ma ya so ya kashe shi.—1 Sam. 18:6-9, 29; 19:9-11.
13. Mene ne Dauda ya yi sa’ad da Sarki Saul ya wulaƙanta shi?
13 Sarki Saul ya wulaƙanta Dauda, amma duk da haka, Dauda ya ci gaba da daraja shi a matsayin sarkin da Jehobah ya naɗa. (1 Sam. 24:6) Dauda bai ɗaura wa Jehobah laifi ba don munanan abubuwa da Saul ya yi ba. Maimakon haka, Dauda ya dogara ga Jehobah don ya ba shi ƙarfin jimre jarrabawar.—Zab. 18:1, rubutun da ke sama.
14. Wane yanayi ne manzo Bulus ya fuskanta da ya yi kama da na Dauda?
14 Manzo Bulus ma ya fuskanci irin yanayin Dauda. Maƙiyan Bulus sun fi shi ƙarfi sosai. Manyan mutane da yawa a zamaninsa sun tsane shi. Sau da yawa, sun sa a yi masa dūkan tsiya kuma aka jefa shi cikin kurkuku. Kamar Dauda, mutanen da ya kamata su zama abokan Bulus ne suka wulaƙanta shi. Wasu a cikin ikilisiya ma sun yi adawa da shi. (2 Kor. 12:11; Filib. 3:18) Amma Bulus ya yi nasara a kan dukan mutanen da suka yi adawa da shi. Ta yaya? Ya ci gaba da yin wa’azi duk da tsanantawar da ya fuskanta. Ya kasance da aminci ga ʼyan’uwansa, har a lokacin da suka ɓata masa rai. Kuma mafi muhimmanci, ya ci gaba da bauta wa Jehobah har mutuwa. (2 Tim. 4:8) Ba da ƙarfinsa ya cim ma abubuwan nan ba, amma domin ya dogara ga Jehobah.
15. Mene ne maƙasudinmu, kuma ta yaya za mu cim ma su?
15 Abokan makarantarku ko abokan aikinku ko kuma danginku da ba Shaidu ba suna zaginka ko kuma tsananta maka? Shin wani a cikin ikilisiya ya taɓa ɓata maka rai ne? Idan haka ne, ka yi koyi da Dauda da Bulus. Za ka iya ci gaba da yin “nasara a kan mugunta ta wurin aikata abin da yake mai kyau.” (Rom. 12:21) Sa’ad da mutane suka yi adawa da mu, bai kamata mu yi faɗa da su yadda Dauda ya yi da Goliyat ba. Maimakon haka, mu taimaka musu ta wajen koya musu game da Jehobah da kuma Littafi Mai Tsarki. Za mu iya yin hakan ta wajen yin amfani da Littafi Mai Tsarki sa’ad da muke amsa tambayoyin mutane da kuma mutunta mutanen da suka wulaƙanta mu. Ƙari ga haka, mu yi alheri ga kowa, har da maƙiyanmu.—Mat. 5:44; 1 Bit. 3:15-17.
KA YARDA MUTANE SU TAIMAKA MAKA
16-17. Mene ne Bulus bai taɓa mantawa ba?
16 Kafin manzo Bulus ya zama mabiyin Kristi, shi marar kunya ne da ke tsananta wa mabiyan Yesu. (A. M. 7:58; 1 Tim. 1:13) Yesu da kansa ne ya sa Bulus ya daina tsananta wa Kiristoci. Yesu ya yi wa Bulus magana daga sama kuma ya makantar da shi. Don Bulus ya soma gani, yana bukatar ya nemi taimako daga mutanen da yake tsananta wa. Ya amince da taimakon wani almajirin Yesu mai suna Hananiya, kuma ya warkar da Bulus.—A. M. 9:3-9, 17, 18.
17 Daga baya, Bulus ya zama sananne a ikilisiyar Kirista, amma bai taɓa manta da darasin da Yesu ya koya masa a hanyar Kol. 4:10, 11.
Dimashƙu ba. Bulus ya kasance da sauƙin kai kuma ya amince ʼyan’uwa su taimaka masa. Ya ce su “abin ta’aziyya” ne a gare shi.—18. Me zai iya sa mu jinkirin amincewa da taimako daga ʼyan’uwanmu?
18 Wane darasi ne za mu iya koya daga Bulus? A lokacin da muka soma tarayya da mutanen Jehobah, mun amince ʼyan’uwa su taimaka mana domin mun san cewa sun fi mu sanin Littafi Mai Tsarki. (1 Kor. 3:1, 2) Amma muna yin hakan har yanzu? Idan mun daɗe muna bauta wa Jehobah kuma mun manyanta sosai, amincewa da taimako zai iya yi mana wuya, musamman idan wani da muka riga yin baftisma ne yake so ya taimaka mana. Amma mu tuna cewa Jehobah yana yin amfani da ʼyan’uwanmu don ya ƙarfafa mu. (Rom. 1:11, 12) Saboda haka, idan muna so Jehobah ya ƙarfafa mu, muna bukatar mu amince da taimakon ʼyan’uwanmu.
19. Me ya sa Bulus ya yi nasara?
19 Manzo Bulus ya cim ma wasu abubuwa masu ban mamaki, bayan da ya zama Kirista. Me ya sa? Domin ya koyi cewa ba ƙarfin mutum ko iliminsa ko wadatarsa ko kuma al’adarsa ba ne yake sa ya yi nasara a rayuwa ba. Amma idan mutum yana da sauƙin kai kuma ya dogara ga Jehobah, zai iya cim ma abubuwa masu kyau da yawa. Bari dukanmu mu yi koyi da Bulus ta wajen (1) dogara ga Jehobah, da (2) koyan darussa daga mutanen da aka ambata a Littafi Mai Tsarki (3) da kuma amincewa da taimako daga ʼyan’uwanmu. Idan mun yi hakan, Jehobah zai ƙarfafa mu ko da mun yi sanyin gwiwa!
WAƘA TA 71 Mu Rundunar Jehobah Ne!
^ sakin layi na 5 A wannan talifin, za mu tattauna misalin manzo Bulus. Za mu ga cewa idan muna da sauƙin kai, Jehobah zai ba mu ƙarfin jimre ba’a kuma za mu magance kasawarmu.
^ sakin layi na 1 MA’ANAR WASU KALMOMI: Za mu iya yin sanyin gwiwa don ajizancinmu ko talauci ko rashin lafiya ko kuma don ba mu je makaranta sosai ba. Ƙari ga haka, maƙiyanmu suna neman su sa mu sanyin gwiwa ta wajen zaginmu ko kuma kawo mana hari.
^ sakin layi na 57 BAYANI A KAN HOTUNA: Sa’ad da Bulus ya zama Kirista, ya yi watsi da abubuwan da yake yi a dā a matsayinsa na Bafarisi. Wataƙila abubuwan nan sun haɗa da wasu littattafai da kuma ƙunshin ayoyi da ake ɗaurawa a goshi.
^ sakin layi na 61 BAYANI A KAN HOTUNA: Abokan aikin wani ɗan’uwa suna neman su matsa masa ya saka hannu a bikin ranar haihuwar wani abokin aikinsu.