Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Rika Amincewa da Gyarar Jehobah

Ka Rika Amincewa da Gyarar Jehobah

“Ya Ubangiji, . . . kai kuwa kamar maginin tukwane. Kai ka halicce mu.”—ISHA. 64:8, Littafi Mai Tsarki.

WAƘOƘI: 89, 26

1. Me ya sa babu wani da ya iya ƙera abubuwa kamar Jehobah?

A WATAN Nuwamba a shekara ta 2010 a birnin Landan a ƙasar Ingila, an sayar da wani kaskon furanni da aka ƙera a Caina a ƙarni na 18 kusan dalla miliyan saba’in. Hakan ya nuna cewa maginin tukwane zai iya yin amfani da yumɓu don ya ƙera wani abu mai daraja kuma mai kyan gaske. Duk da haka, babu maginin ɗan Adam da ya iya ƙera abubuwa kamar Jehobah, don a kwana ta shida ta halitta, Allah “ya sifanta mutum daga turɓayar ƙasa” kuma ya zama kamiltacce wanda zai iya kasancewa da halayen Mahaliccinsa. (Far. 2:7) Ƙari ga haka, an kira wannan kamiltaccen mutum, wato Adamu, da aka halitta da turɓayar ƙasa ‘ɗan Allah.’—Luk. 3:38.

2, 3. Ta yaya za mu iya bin misalin Isra’ilawa da suka tuba?

2 Amma, sa’ad da Adamu ya yi wa Mahaliccinsa tawaye, ya rasa dangantakarsa da Allah. Duk da haka, tun daga lokacin Habila, ’yan Adam da dama sun goyi bayan sarautar Allah. (Ibran. 12:1) Ta wajen yin biyayya ga Mahaliccinsu, sun nuna cewa suna son ya zama Ubansu da mai mulmula su, ba Shaiɗan ba. (Yoh. 8:44) Amincinsu ya tuna mana abin da Ishaya ya ce game da Isra’ilawa da suka tuba: “Kai ne Ubanmu, ya Ubangiji. Mu kamar yumɓu ne, kai kuwa kamar maginin tukwane. Kai ka halicce mu.”—Isha. 64:8, LMT.

3 A yau, duk waɗanda suke bauta wa Jehobah cikin ruhu da gaskiya suna ƙoƙari su zama masu tawali’u da kuma masu biyayya. Sunan ganin gata ne su zama ’ya’ya a wurin Jehobah kuma suna ba da kai gare shi don ya mulmula su. Shin kana ɗaukan kanka a matsayin yumɓu a hannun Allah, kuma kana shirye ya mulmula ka kamar mai mulmula tukunya don ka zama mutum mai daraja a gabansa? Shin kana ɗaukan ’yan’uwanka kamar yumɓu da Allah yake mulmulawa? Don mu sami amsar waɗannan tambayoyin, za mu tattauna abubuwa uku da Jehobah yake yi don ya mulmula mu kamar maginin tukwane: Yadda yake zaɓan waɗanda yake mulmulawa da abin da ya sa yake mulmula su da kuma yadda yake yin hakan.

JEHOBAH YANA ZAƁAN WAƊANDA YAKE MULMULAWA

4. Yaya Jehobah yake zaɓan mutanen da yake so su bauta masa? Ka ba da misalai.

4 Jehobah ba ya mai da hankali ga siffar ’yan Adam sa’ad da yake lura da ayyukansu, amma yana duban zuciyarsu. (Karanta 1 Sama’ila 16:7b.) Allah ya nuna hakan a lokacin da ya kafa ikilisiyar Kirista. Ya ba mutane da yawa damar kusantar sa da kuma Ɗansa, duk da cewa ’yan Adam ba sa ɗaukan waɗannan mutanen da daraja. (Yoh. 6:44) Wani Bafarisi mai suna Saul yana cikinsu, shi “mai-saɓo ne dā, mai-tsanani, mai-ɓatanci.” (1 Tim. 1:13) Amma, Allah mai duban “zukata” bai ɗauki Saul a matsayin yumɓu marar amfani ba. (Mis. 17:3) Maimakon haka, Allah ya ga cewa za a iya mulmula shi ya zama kamar tukunya mai amfani wato, ‘santali zaɓaɓɓe’ don ya yi wa’azin bishara wa “al’ummai da sarakuna, da ’ya’yan Isra’ila.” (A. M. 9:15) Wasu da Allah yake ganin za su zama tukwane masu “daraja” sun ƙunshi mashaya a dā da masu lalata da kuma ɓarayi. (Rom. 9:21; 1 Kor. 6:9-11) Suna barin Jehobah ya mulmula su yayin da suke nazarin Littafi Mai Tsarki kuma suna ƙarfafa bangaskiyarsu a gare shi.

5, 6. Ta yaya yadda muke dogara ga Jehobah a matsayinsa na mai mulmula mu kamar maginin tukwane zai shafi yadda muke bi da (a) mutane a yankinmu? (b) ’yan’uwanmu?

5 Ta yaya waɗannan misalan za su taimaka mana? Da yake Jehobah ya san abin da ke cikin zuciyar mutum kuma yana ba waɗanda ya zaɓa damar bauta masa, ba zai dace mu riƙa kūshe mutane a yankinmu da kuma ikilisiyarmu ba. Ka yi la’akari da misalin wani mai suna Michael. Ya ce: “Sa’ad da Shaidun Jehobah suka zo gidanmu, nakan rufe ƙofa kuma na yi banza da su. Ina yi musu rashin mutunci! Akwai lokacin da na haɗu da wani iyalin da nake son halinsu sosai. Amma wata rana na yi mamakin sanin cewa su Shaidun Jehobah ne! Halinsu ya sa na sake yin tunani game da yadda nake bi da Shaidun Jehobah. Ba da daɗewa ba na fahimci cewa ina yin waɗannan abubuwa don rashin sani da kuma abubuwan da mutane suke faɗa game da su.” Don Michael ya ƙara sanin Shaidun Jehobah, sai ya yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Daga baya, ya soma bauta wa Jehobah kuma ya soma hidima ta cikakken lokaci.

6 Amincewa da Jehobah a matsayin mai mulmula mu kamar maginin tukwane zai shafi yadda muke bi da ’yan’uwanmu. Shin kana ɗaukan ’yan’uwanka yadda Allah yake ɗaukansu, wato kamar waɗanda yake mulmulawa har ila? Jehobah yana iya ganin zuciyar mutum da kuma abin da zai zama idan ya gama mulmula shi. Shi ya sa Jehobah yake da ra’ayi mai kyau game da mutane kuma ba ya mai da hankali ga ajizancinsu. (Zab. 130:3) Za mu iya yin koyi da shi ta wajen yin tunani mai kyau game da bayinsa. Hakika, za mu iya yin aiki tare da Jehobah ta wajen taimaka wa ’yan’uwanmu yayin da suke ƙoƙari su sami ci gaba a bautarsu ga Jehobah. (1 Tas. 5:14, 15) Tun da yake Allah ya tanadar da dattawa a matsayin “kyautai ga mutane,” ya kamata su kafa misali mai kyau a wannan batun.—Afis. 4:8, 11-13.

ME YA SA JEHOBAH YAKE MULMULA MU?

7. Me ya sa kake amincewa da horon da Jehobah yake maka?

7 Wataƙila ka taɓa jin wani ya ce: ‘Lokacin da na haifi yara ne na san cewa tarbiyyar da iyayena suka yi mini tana da amfani sosai.’ Sa’ad da muka manyanta, muna iya ganin cewa Jehobah yana yi mana horo don yana ƙaunarmu. (Karanta Ibraniyawa 12:5, 6, 11.) Hakika, don Jehobah yana ƙaunar mu, yana mulmula mu cikin haƙuri. Yana son mu zama masu hikima, mu riƙa farin ciki kuma mu ƙaunace shi. (Mis. 23:15) Ƙari ga haka, ba ya son mu riƙa shan wahala kuma mu mutu duk da cewa mun gāji zunubi da mutuwa daga Adamu.—Afis. 2:2, 3.

8, 9. Ta yaya Jehobah yake koyar da mu a yau, kuma ta yaya zai ci gaba da yin haka a nan gaba?

8 A dā mu “’ya’yan kangara,” ne kuma muna da munanan halaye da ke ɓata wa Allah rai. Amma, mun canja waɗannan halayen domin Jehobah ya mulmula mu, kuma mun kasance da tawali’u kamar ’ya’yan rago. (Isha. 11:6-8; Kol. 3:9, 10) Saboda haka, za a iya kwatanta wannan yanayin da Jehobah yake mulmula mu da salama da muke mora a ƙungiyar Jehobah. Muna da kwanciyar hankali duk da cewa muna cikin wannan muguwar duniya. Ban da haka, a irin wannan yanayi ne za a iya nuna ƙauna ta gaskiya ga waɗanda suka tashi a iyalan da babu zaman lafiya. (Yoh. 13:35) Ƙari ga haka, mun koyi cewa mu riƙa ƙaunar mutane, domin mun san Jehobah kuma yanzu muna shaida ƙaunarsa a gare mu.—Yaƙ. 4:8.

9 A sabuwar duniya za mu mori yanayin salama fiye da yadda muke mora a yanzu. A sabuwar aljanna za mu ji daɗin rayuwa a ƙarƙashin Mulkin Allah. A wannan lokacin ne za a canja yanayin duniya gabaki ɗaya kuma Jehobah zai ci gaba da mulmula mutane, zai koyar da su sosai fiye da yadda muke tsammani. (Isha. 11:9) Ƙari ga haka, Allah zai sa hankalinmu da jikinmu su zama kamiltattu, domin mu bi ƙa’idodinsa kuma mu yi nufinsa ba tare da yin kuskure ba. Saboda haka, bari mu yi ƙudiri cewa za mu yi biyayya ga Jehobah. Ta hakan, za mu nuna masa cewa mun san yana mulmula mu ne don yana ƙaunar mu.—Mis. 3:11, 12.

YADDA JEHOBAH YAKE MULMULA MU

10. Ta yaya Yesu ya bi misalin Jehobah a nuna haƙuri da kuma ƙwarewa?

10 Kamar maginin tukwane da ya ƙware sosai, Jehobah ya san irin “yumɓu” da yake amfani da shi, kuma yana mulmula shi yadda ya dace. (Karanta Zabura 103:10-14.) Hakika, yana yin la’akari da kasawarmu da kuma iyakar manyantar mu yayin da yake bi da kowanenmu. Ɗansa Yesu Kristi ya yi koyi da shi a yadda ya bi da bayin Allah ajizai. Ka yi la’akari da yadda Yesu ya bi da kasawar manzanninsa, musamman ma yadda suka yi gardama game da wanda ya fi girma a tsakaninsu. Idan ka ga yadda manzannin suke gardama, shin za ka yi tunani cewa ba za a iya mulmula su su zama masu tawali’u ba? Duk da haka, Yesu ya kasance da ra’ayin da ya dace game da manzanninsa. Ya san cewa zai iya mulmula manzanninsa masu aminci idan ya bi da su a hankali, ya ba su shawara kuma ya nuna tawali’u, ta hakan ya kafa musu misali mai kyau. (Mar. 9:33-37; 10:37, 41-45; Luk. 22:24-27) Bayan an ta da Yesu daga mutuwa kuma aka sauko wa manzannin ruhu mai tsarki, sun mai da hankali ga aikin da aka ba su, ba neman matsayi ba.—A. M. 5:42.

11. A wace hanya ce Dauda ya nuna cewa yana kama da yumɓu, kuma ta yaya za mu yi koyi da shi?

11 A yau, Jehobah yana amfani da Kalmarsa da ruhu mai tsarki da kuma ikilisiyar Kirista don ya mulmula mu. Kalmar Allah tana iya mulmula mu sa’ad da muka karanta ta, muka yi bimbini a kai kuma muka roƙi Jehobah ya taimaka mana don mu bi shawarwarin da ke cikinta. Dauda ya ce: “Sa’anda ina tuna da kai a kan shimfiɗata, Ina tunaninka cikin tsaro na dare.” (Zab. 63:6) Ya kuma ƙara cewa: “Zan albarkaci Ubangiji, wanda ya yi mani shawara: I, da dare zuciyata tana gargaɗar da ni.” (Zab. 16:7) Hakika, Dauda ya ƙyale shawarar da ke Kalmar Allah ta mulmula shi kuma hakan ya shafi tunaninsa da ra’ayinsa, ko da bin shawarar bai kasance masa da sauƙi ba. (2 Sam. 12:1-13) Dauda ya kasance da tawali’u kuma ya yi biyayya, ta hakan ya kafa mana misali mai kyau! Shin kai ma kana yin bimbinin Kalmar Allah kuwa? Kana barin Kalmar Allah ta mulmula yadda kake tunani? Shin kana bukatar ka daɗa yin ƙoƙari a wannan fannin ne?—Zab. 1:2, 3.

12, 13. Ta yaya Jehobah yake amfani da ruhu mai tsarki da kuma ikilisiyar Kirista don ya mulmula mu?

12 Ruhu mai tsarki yana iya mulmula mu a hanyoyi dabam-dabam. Alal misali, yana iya taimaka mana mu kasance da halaye irin na Kristi kuma hakan ya ƙunshi ’ya’yan ruhu. (Gal. 5:22, 23) Wani fanni na ’ya’yan ruhu shi ne ƙauna. Muna ƙaunar Allah kuma muna so mu yi masa biyayya shi ya sa muke so ya mulmula mu don mun san cewa dokokinsa ba su da wuyan bi. Ƙari ga haka, ruhu mai tsarki yana ba mu ƙarfin guje wa mugun tasirin wannan duniya. (Afis. 2:2) Sa’ad da manzo Bulus yake matashi, ya nuna girman kai kamar malaman Yahudawa. Amma ya bar ruhu mai tsarki ya mulmula shi. Saboda haka, ya ce: “Zan iya yin abu duka ta wurin Kristi da yake ƙarfafani.” (Filib. 4:13) Bari mu bi misali Bulus ta wajen roƙon Allah ya ba mu ruhu mai tsarki. Jehobah zai ji addu’ar da muka yi da zuciya ɗaya.—Zab. 10:17.

Jehobah yana amfani da dattawa don ya mulmula mu, kuma wajibi ne mu saurari shawarar su (Ka duba sakin layi na 12, 13)

13 Jehobah yana amfani da ikilisiyar Kirista da kuma dattawa don ya mulmula mu. Alal misali, idan dattawa suka gano cewa muna da wata matsala da za ta shafi dangantakarmu da Allah, suna iya ƙoƙarinsu don su taimaka mana. Amma ba sa ba mu shawara bisa ga ra’ayinsu. (Gal. 6:1) Maimakon haka, suna roƙon Allah ya ba su basira da kuma hikima. Sai su yi la’akari da yanayinmu yayin da suke bincika Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu. Hakan yana sa su ba mu shawara ko taimakon da ya dace da yanayinmu. Alal misali, idan suka ba ka shawara game da irin tufafin da kake sakawa, shin za ka ɗauki shawararsu a matsayin ƙaunar Allah a gare ka? Ta yin hakan, ka nuna cewa kana kamar yumɓu ne a hannun Jehobah kuma kana so ya mulmula ka don ka amfana.

14. Ko da yake Jehobah yana da ikon ya mulmula mu, mene ne ba ya tilasta mana mu yi?

14 Idan muka fahimci yadda Jehobah yake mulmula mu, hakan zai taimaka mana mu kasance da dangantaka mai kyau da ’yan’uwa a ikilisiya da kuma mutanen da suke yankinmu har da ɗalibanmu na Littafi Mai Tsarki. A lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, maginin tukwane ba ya ɗiban yumɓu haka kawai kuma ya soma mulmula shi nan da nan. Amma yana somawa ne ta wajen cire duwatsun da suke ciki da kuma wasu abubuwan da ba a bukata a ciki. Hakazalika, Allah yana shirya zuciyar mutane don ya mulmula su. Ba ya tilasta wa mutane su yi canji a rayuwarsu amma yana bayyana musu ƙa’idodinsa don su yi canjin da yardan rai.

15, 16. Ta yaya ɗaliban Littafi Mai Tsarki suke nuna cewa suna son Jehobah ya mulmula su? Ka ba da misali.

15 Ka yi la’akari da misalin wata ’yar’uwa da ke zama a ƙasar Ostareliya mai suna Tessie. ’Yar’uwan da ta yi nazari da ita, ta ce: “Tessie tana saurin fahimtar koyarwa Littafi Mai Tsarki, amma ba ta samun ci gaba kuma ba ta halartan taron ikilisiya. Bayan na yi addu’a sosai a kan batun, sai na tsai da shawara cewa zan daina nazari da ita. Sai wani abin mamaki ya faru. Ranar da na yi shawara cewa zan daina yin nazari da ita, sai Tessie ta gaya mini dalilin da ya sa ba ta samun ci gaba. Ta ce tana ji kamar ita munafuka ce domin tana yin caca. Amma yanzu ta tsai da shawara za ta daina yin caca.”

16 Ba da daɗewa ba, Tessie ta soma halartan taro kuma ta soma nuna halaye masu kyau duk da cewa abokanta suna yi mata ba’a. ’Yar’uwar ta ce: “Da shigewar lokaci, Tessie ta yi baftisma kuma daga baya ta yi hidimar majagaba na kullum, ko da yake tana da ƙananan yara.” Hakika, sa’ad da ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka soma canja halayensu don su faranta wa Allah rai, zai kusace su kuma ya mulmula su don su zama kamar tukwane masu daraja.

17. (a) Me ya sa kake son Jehobah ya mulmula ka? (b) Waɗanne abubuwa ne za a tattauna a talifi na gaba?

17 Har wa yau akwai wasu tukwane da ake mulmulawa da hannu kuma suna da kyan gaske. Hakan nan ma, Jehobah yana haƙuri da mu don ya mulmula mu ta wajen ba mu shawara kuma yana lura ko za mu bi ta. (Karanta Zabura 32:8.) Shin kana ganin cewa Jehobah ya damu da kai? Shin kana ganin cewa yana mulmula ka? Idan haka ne, waɗanne halaye ne za su taimaka maka ka zama kamar yumɓu mai laushi da Jehobah zai iya mulmulawa? Waɗanne halaye ya kamata ka guji don kada ka zama kamar yumɓu mai ƙarfi da ba za a iya mulmulawa ba? Kuma ta yaya iyaye za su haɗa hannu da Jehobah don su mulmula yaransu? Za a tattauna waɗannan abubuwa a talifi na gaba.