Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Tuna?

Ka Tuna?

Shin ka ji daɗin karanta talifofin Hasumiyar Tsaro na kwanan bayan nan kuwa? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:

Waɗanne abubuwa ne iyaye za su iya yi don su tarbiyyatar da yaransu su bauta wa Jehobah?

Wajibi ne iyaye su ƙaunaci yaransu kuma su nuna tawali’u ta wajen misalinsu. Ƙari ga haka, yana da muhimmanci iyaye su nuna basira kuma su yi ƙoƙari su fahimci yaransu.—w15 11/15, shafuffuka na 9-11.

Mene ne ya nuna cewa ba a kewaye birnin Yariko na dā na tsawon lokaci kafin a ci ta da yaƙi ba?

Idan sun kewaye birnin na tsawon lokaci, mazauna birnin za su cinye yawancin abincin da suke da shi. Ƙari ga haka, sa’ad da sojoji suka ci wani gari da yaƙi, sukan kwashe dukan abubuwan da suke so, har da abincin da ya rage a garin. Shi ya sa masu tonon ƙasa ba su sami raguwar abinci sosai ba a biranen Falasɗinu da aka ci da yaƙi ba. Tun da yake an sami hatsi mai yawa, hakan ya nuna cewa, kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ambata, sojojin Isra’ilawa sun kewaye birnin Yariko na ɗan lokaci ne kafin su halaka birnin.—w15 11/15, shafi na 13

Mene ne ya kamata mu yi la’akari da shi kafin mu yi magana?

Don mu yi furuci mai daɗin ji, muna bukata mu (1) san lokacin da ya kamata mu yi magana (M. Wa. 3:7), (2) abin da ya kamata mu faɗa (Mis. 12:18), da (3) yadda ya kamata mu yi magana (Mis. 25:15).—w15 12/15, shafuffuka na 19-22.

Yaya ya kamata mu bi da ’yan’uwa shafaffu?

Bai kamata Kiristoci su riƙa girmama shafaffu ainun ba. Wanda shi ainihi shafaffe ne ba zai so a riƙa girmama shi ba kuma ba zai so a riƙa gaya wa mutane game da matsayinsa da Allah ba. (Mat. 23:8-12)—w16.01, shafuffuka na 22-23.

Waɗanne ire-iren rashin gaskiya ne Kiristoci za su guje wa?

Kiristoci na gaskiya za su guji ƙarya da kuma tsegumi. Ba sa yin ƙarya da maƙirci don su ɓata sunan wasu, kuma ba sa yin zamba ko kuwa sata.—wp16.2, shafi na 10.

Mene ne za mu iya koya daga yadda Ibrahim ya zama abokin Allah?

Ibrahim ya koyi abubuwa game da Allah, wataƙila daga wurin Shem. Kuma Ibrahim ya ƙara koya game da Allah daga yadda Jehobah ya yi sha’ani da shi da iyalinsa. Mu ma muna iya yin hakan.—w16.02, shafuffuka na 4-5.

Shin Shaiɗan ya kai Yesu haikali na zahiri don ya jarabce shi ne?

Ba mu san ainihin yadda Shaiɗan ya yi hakan ba. Littafin Matta 4:5 da Luka 4:9 suna iya nufin cewa an kai Yesu haikali a cikin wahayi ko kuma ya tsaya a kan wurin da ya fi tsayi a haikalin.—w16.03, shafuffuka na 31-32.

A waɗanne hanyoyi ne wa’azin da muke yi yake kama da raɓa?

Raɓa tana sauka a hankali da wartsakarwa da kuma rayarwa. Raɓa albarka ce daga wurin Allah. (K. Sha. 33:13) Ƙoƙarin da mutanen Allah suke yi a wa’azin bishara yana kama da raɓa.—w16.04, shafi na 32.