Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

A cikar annabcin nan a zamaninmu, mutumin da yake riƙe da ƙaho na ajiyar tawada yana wakiltar Yesu Kristi. Shi ne yake saka wa mutanen da za su tsira shaida

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Wane ne mai riƙe da ƙaho na ajiyar tawada da kuma mutane shida masu makami da aka ambata a wahayin Ezekiyel suke wakilta?

Suna wakiltar runduna na sama da suka halaka Urushalima kuma su ne za su halaka wannan muguwar duniyar Shaiɗan a lokacin yaƙin Armageddon. Me ya sa wannan ƙarin hasken ya dace?

Bayan Ezekiyel ya ga abubuwan ban ƙyama da mutanen Urushalima da suke bauta wa alloli ƙarya suke yi kafin a halaka birnin a shekara ta 607 kafin haihuwar Yesu, an nuna masa wahayin abubuwan da za su kai ga halakar birnin. Ya ga maza shida suna riƙe da makamai. Ƙari ga haka, ya ga wani mutum tare da su, ‘mai-yafe da lilin’ da kuma ‘ƙaho na ajiyar tawada.’ (Ezek. 8:6-12; 9:2, 3) An gaya wa wannan mutumin: “Je ka, ka ratsa ta tsakiyar birni, . . . ka sa shaida a goshin mutanen da ke ajiyar zuci, suna kuwa kuka saboda dukan ƙazanta da a ke yi a cikinta.” Bayan haka, an gaya wa mutanen da ke riƙe da makamai cewa su shiga cikin birnin kuma su kashe dukan waɗanda ba su da wannan shaidar a goshinsu. (Ezek. 9:4-7) Mene ne wannan wahayin ya koya mana, kuma wane ne wannan mutumin mai riƙe da ƙaho na ajiyar tawada?

An yi wannan annabci a shekara ta 612 kafin haihuwar Yesu. Wannan annabcin ya fara cika bayan shekara biyar sa’ad da Jehobah ya ƙyale sojojin Babila su halaka Urushalima. Ta hakan, Jehobah ya yi amfani da mutanen Babila don ya halaka Urushalima. (Irm. 25:9, 15-18) Amma ba kowa ba ne aka halaka a lokacin ba. Ba a halaka masu adalci tare da mugaye ba. Da yake Jehobah Allah mai ƙauna ne, ya yi tanadin hanyar da zai ceci Yahudawan da suka ƙi saka hannu a abubuwan ban ƙyama da ake yi a birnin.

A wahayin, Ezekiyel ba ya cikin waɗanda suka saka shaida a goshin mutane ko kuma halaka birnin. Maimakon haka, mala’iku ne suka ja-goranci wannan halakar. Saboda haka, wannan wahayin ya ba mu damar ganin abin da yake faruwa a sama. Jehobah ya umurci mala’ikunsa su shirya halakar birnin kuma su tabbata cewa ba a halaka masu adalci tare da mugaye ba. *

Wannan wahayin zai sake cika a zamaninmu. Amma a dā, mun bayyana cewa wannan mutumin da ke riƙe da ƙaho na ajiyar tawada yana wakilta shafaffu da suka rage a duniya. Ƙari ga haka, mun ce waɗanda suka saurare wa’azin bisharar da muke yi ne za su tsira. Amma shekarun nan, mun ga cewa ya dace a yi gyara a kan wannan bayanin. Bisa ga abin da ke cikin littafin Matta 25:31-33, Yesu ne yake yi wa mutane shari’a. Zai yi shari’arsa na ƙarshe a lokacin ƙunci mai girma, ta wajen ware tumaki daga awaki, wato ware waɗanda za su tsira daga waɗanda za a halaka.

Saboda da wannan ƙarin haske da aka yi a kan wannan wahayin, waɗanne darussa ne muka koya daga wahayin Ezekiyel? Muna da aƙalla guda biyar:

  1.  Kafin a halaka Urushalima, Ezekiyel da Irmiya sun gargaɗi mutane game da abin da zai faru da ƙasar kamar yadda Ishaya ya yi a dā. Hakazalika, a yau ma Jehobah yana amfani da wani ƙaramin rukunin shafaffu faɗakar da mutanensa da kuma wasu game da ƙunci mai girma. Ƙari ga haka, dukan mutanen Allah, wato iyalin gidan Kristi suna yin wannan faɗakarwa.—Mat. 24:45-47.

  2.  Ezekiyel ba ya cikin waɗanda suka saka wa mutanen da za su tsira shaida, haka ma yake da mutanen Allah a yau. Aikinsu kawai shi ne su yi wa mutane wa’azin bishara kuma su gargaɗe su game da abin da zai faru a nan gaba. Ana wannan wa’azin bisharar da taimakon mala’iku.—R. Yoh. 14:6.

  3.  A zamanin Ezekiyel, babu wanda aka yi masa shaida na zahiri a goshinsa. Haka ma yake a yau. Amma mene ne mutane suke bukata su yi don su sami alama don ceto? Suna bukata su saurari wa’azin bishara kuma su kasance da halaye irin na Kristi. Ƙari ga haka, suna bukata su keɓe kansu ga Jehobah kuma su goyi bayan ’yan’uwan Kristi. (Mat. 25:35-40) Waɗanda suke yin waɗannan abubuwan za su sami alama don ceto a lokacin ƙunci mai girma.

  4.  A cikar annabcin nan a zamaninmu, mutumin da yake riƙe da ƙaho na ajiyar tawada yana wakiltar Yesu Kristi. Shi ne yake saka wa mutanen da za su tsira shaida a goshinsu. Taro mai-girma za su sami shaidarsu sa’ad da aka yi musu shari’a a matsayin masu kama da tumaki a lokacin ƙunci mai girma. Hakan zai sa su sami damar yin rayuwa har abada a nan duniya.—Mat. 25:34, 46. *

  5.  A cikar annabcin nan a zamaninmu, maza shida da suke riƙe da makamai suna wakiltar Yesu tare da rundunan sama. Za su halaka al’ummai kuma su kawo ƙarshen mugunta nan ba da daɗewa ba.—Ezek. 9:2, 6, 7; R. Yoh. 19:11-21.

Fahimtar waɗannan darussa za su ƙarfafa mu mu kasance da gaba gaɗi cewa Jehobah ba zai halaka masu adalci tare da mugaye ba. (2 Bit. 2:9; 3:9) Ƙari ga haka, an nuna mana muhimmancin yin wa’azin bishara a zamaninmu. Mutane gabaki ɗaya suna bukata su ji wa’azin kafin ƙarshen ya zo!—Mat. 24:14.

^ sakin layi na 6 Waɗanda suka tsira kamar Baruch (sakataren Irmiya) da Ebed-melech Ba-kushi da kuma zuriyar Rekab ba su da shaida a goshinsu. (Irm. 35:1-19; 39:15-18; 45:1-5) An sa musu shaida na alama don ceto.

^ sakin layi na 12 Shafaffun da suka kasance da aminci ba sa bukata su sami wannan alama don ceto. A maimakon haka, za su sami hatimi na ƙarshe kafin su mutu ko kuma gab da farawar ƙunci mai girma.—R. Yoh. 7:1, 3.